Sashe 18
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Caraf taji Yarima ya cafki yatsun hannuwan ta adai dai lokacin da ta ɗaga ƙafa danniyar yin gaba.
Cak ta tsaya ai'nda take ba tare data juyo ba ranta na tsantsar ƙuna, yayin da shi kuma ya saki yatsun hannun nata yana mai sake komawa daga gaban ta.
Ɗauke kai tayi daga kansa tana mai kallon gefe tare da sakin huci, domin kuwa aduk lokacin da zata kalli fuskar sa ji take tamkar ta shaƙesa ya mutu dan baƙin ciki.
"Ya da jin haushi haka kuma Gimbiya ta, ko kuwa har kin sare ne tun yanzu sabo da kin san nine dana sara?" Ya faɗa yana mai jifan ta da murmushi, tukun ya sake ranƙwafawa dai dai saitin fuskar ta yana mai yin ƙasa-ƙasa da murya tare da faɗin. "Ki sani ina sonki, kuma akan sonki babu abun da bazan iya ai'katawa ba dan ganin na mallakeki, dan haka ina mai sake sanar miki da ki shaidawa shi wancan ɗin ya fara shiryawa, domin ko haɗuwa ta da tasa bazata taɓa yin kyau ba, nima kuma da zarar na koma gida zan sanarwa da Lamiɗon mu cewa na samu abokin karawa."
Ya ƙarasa maganar yana mai matsawa gefe ya bata hanya.
Sai lokacin ta ɗago kai tana mai jifan sa da wani irin matsiyacin kallo. Wata irin tsanar sa take ji aranta irin wacce bata taɓa yiwa wani mahaluki ita ba aduniya, sabo da ganin sa da take amatsayin barazana gare ta akan soyayyar ra da Giɗaɗon ta, tukun daga bisani ta janye idanuwan ta tana mai ɗaga ƙafafuwan ta tayi gaba ba tare da ta sake tanka masa ba.
Amai-makon tayi hanyar da zata sadata da gida sai kawai ta doshi hanyar wurin da tsuntsayen ta suke ranta atsantsar ɓace.
Yayin da shi kuma Yariman Yamma ya juya yana mai komawa kan shimfiÉ—ar nan ya zauna zuciyar sa na tsantsar tururi, sabo da ganin irin tarbar da tayi masa amatsayin sa na wanda zai zamto miji gare ta.
Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi da ƙarfi yana mai girgiza kansa tare da rumtse idanuwan sa, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai buɗe baki yace. "Tabbas ko kai wane ne sai na sanya ka kayi nadamar soyayyar da ka fara da wacce nake muradin aure, sai nasa kayi dana sanin-sanin ta amatsayin ƴa mace balle har kasota, domin ko wallahi wallahi Haddiyal tawace ni kaɗai!"
Ya faɗa cikin kaushi yana mai sake rumtse idanuwan sa, zuciyar sa na tsantsar tururi da ƙuna.
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ, CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Sosai shirye shiryen bikin godiya ga abun bauta Gargabilu da za'ayi ajibi ya kan-kama da gasken gaske acikin baƙar masarauta.
Gaba É—aya an sake sabon fenti akowane wuri tare da sabon tambari acikin masarautar, yayin da ko wane bawa da baiwa suka kasance suna ta shiri kuma har yau suna kan shirywa.
Acan filin biki ma bayi ne suke ta aikin share share da jera kujeru acikin sa.
Yayin da wasu kuma suke ta faman wucewa da wasu mahaukatan iccina É—auke akafaÉ—un su suna masu kai su wani fili su aje.
Acan wurin su Bir kuwa zaune yake agaban Iyar Bayi ya tanƙwashe ƙafafuwan sa suna tattaunawa.
Sake matsawa kusa da Bir Iyar Bayi tayi tana mai miƙa yatsun hannun ta ta riƙo nasa da su.
Ɗago idanuwan sa yayi ya kalleta kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Al'farma nake roƙo awurin ka Jarumi na, ina son gobe ka zamto yaro nitsats-tse kamar yacce sauran yara suke, kayi abun da yake agaban ka karka kuskura ka kalli ko inda Gimbiya take balle har kaje wurin ta kajawa kanka bala'i kaji."
Uhm! "Iya ta kenan, to ni dama ai bawai ina zuwa wurin ta bane, itace dai take biyowa hanyar data kasance hanyar mu, ni kuma abu ɗaya dana sani shine banga abun da yake tattare da itaba wanda har zai firgita dan tazo wuri in gudu in ɓuya, wannan dalilin ne yasan ya aduk lokacin da tazo giftawa nake ƙara matsawa inda take domin naga ƙarshen ikon ta." Bir ya faɗa yana mai sakin murmushi idanuwan sa akan fuskar Iyar Bayi, yayin da ƙwaƙwalwar sa kuma ke hasko masa kyawun fuskar Gimbiya Tasmir tare da kyawun surar jikin ta.
"To wa gari ya waya kuma, wane yake wahala bayan kai Jarumi?" Iyar Bayi ta faɗa tana mai cigaba da kallon sa, tukun ta daga bisani ta ɗora da faɗin. "Tun kafuwar tarihin BAƘAR MASARAUTA ba ataɓa yin zamanin da ɗan sarki ko sarki yake zuwa giftawa ta wuri ba, asamu wata hallita da ke kasancewa awurin ba tare da sun gudu ba bayan ƴan rakiyar su kawai sai akan ka Jarumi, shin kai ɗin me zai hana kazamto kamar sauran ƴan uwanka bayi ko domin lafiyar ka Jarumi, domin ko kasan akan wannan abun da kake ai'katawa tsaf har ranka kana iya rasawa acikin BAƘAR MASARAUTA."
"Iya ta kenan, bazaki fahimci yarce nake ji bane kwata-kwata, sai dai kuma abun da zan faɗa miki shine, wallahi bazan iya nisantar ta ba, bazan iya jurewa jin sautin taba ba tare da na ɗaga ido na kalle ta ba." Bir ya faɗa yana mai kallon Iya, yayin da ita kuma Iya ta saki baki cikin firgici tana mai zaro idanuwa waje, tukun daga bisani ta fara ɗaga laɓɓa bakin ta na tsantsar rawa tana mai faɗin. "Shin kasan abun da kake faɗe kuwa Jarumi? Shin wai anya ma kana cikin hankalin kane Jarumi, to wai ma mekake nufi da bazaka iya jure jin sautin taba ba tare da ka ɗaga ido ka kalle ta ba?" Iyar bayi ta watso masa tambaya amatuƙar ruɗe tana mai futo da idanuwa waje.
"Shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba Iya, amma ba komai kawai ki kwantar da hankalin ki akwai lokacin da bake kaɗai ba hatta da sauran mutanen dake cikin masarautar nan zaku fahimta." Ya faɗa yana mai lumshe idanuwan sa, tukun daga bisani ya wara su yana mai zame ƴan yatsun hannuwan sa daga cikin na Iyar Bayi da ta saki baki take aikin kallon sa, kana ya miƙe tsaye yana mai juyawa zai tafi.
"Jarumi!" Iyar Bayi ta faɗa tana mai miƙewa tsaye itama.
Cak Bir ya tsaya a'inda yake ba tare da ya juyo ba, yayin da ita kuma Iya ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar inda yake.
Gaban sa ta ƙarasa ta tsaya tana mai kallon fuskar sa.
Lumshe idanuwan sa yayi agaban Iya ba tare da yace komai ba, domin ko yasan duk abun da zata faÉ—a masa ayanzu bama fahimta zai ba.
"Na roƙe ka Jarumi badan ni ba, na roƙe da abun bauta Gargabilu ka futa daga harkar Gimbiya Tasmir, domin ko tsaf ana iya fille kanka muddin irin wannan furucin da kayi ayanzu zai cigaba da futa daga cikin bakin ka acikin BAƘAR MASARAUTA."
Hmmmm! "Ki kwantar da hankalin ki Iya ta, ni da kaina na faÉ—a miki babu damuwa, sannan kuma babu abun da zai faru."
"To idan har hakane da gaske ina son yanzu kamun al'ƙwarin babu abun da zai haɗaka da Gimbiya Tasmir gobe." Iya ta faɗa tana kallon sa.
"To ai dama Iya ba daga ni bane matsalar, tambaya ce kawai take mun akan rayuwar ta ni kuma nake yarce naso da ita ta hakan, wannan fa shine kawai abun da ke faruwa."
"To amma mai zai hana ka bata amsar tambayar da taimakan idan ka sani ko domin hutun ka?"
"Iya kenan, shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba, amma ba komai yanzu dai na miki al'ƙwarin bazan ko kalli inda take ba gobe balle har wani abu ya shiga tsakanin mu Iya ta." Ya faɗa yana mai juayawa ya cigaba da tafiyar sa hankali kwance, yayin da ita kuma Iya ta juya tana mai komawa ta zauna tare da buga uban tagumi da hannu bibbiyu.
Acan ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa sosai ake shirya ta tun yau, wani irin gyara ake yiwa gashin kanta, yayin da ƙafafuwam ta da hannuwan ta kuma aka ƙunshe su da ƙunshi irin na jan lalle da yay tsananin yi mata kyau.
Zaune take akan wata kujerar ƙarfe mai azabar kyau ana mata gyaran gashi.
Sosai ta ƙagara ranar gobe tazo, domin kuwa gobe ne take ganin ranar da zata wuce duk baƙin cikin da wancan ƙas-ƙantaccen bawan ya ƙunsa mata cikin sauƙi!
*ƘASAR HAUSA JAHAR WASAI, CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Misalin ƙarfe goma na safe dai dai Babban yaya ya tura kansa cikin ɗakin Asad bakin sa ɗauke da sallama.
Kwance ya hange sa akan gado gaba ɗaya ya ƙudun dune jikin sa da eskimo, sai fuskar sa kawai da ya bari awaje yana shara-rar bacci.
Kallon haÉ—aÉ—É—en agogon bangon da yake manne ajikin bangon É—akin Babban yaya yayi, sabo da ganin da yay har yanzu Asad bai tashi ba.
Girgiza kai yayi bayan ya janye idanuwan sa daga kan agogon, tukun ya cigaba da takawa yana mai dosar bakin bed É—in.
Wuri ya samu daga gefen gadon ya zauna, tukun yakai tafin hannun sa zuwa jikin Yarima Asad yana mai ɗan bubbugasa, bakin sa na furta kalmar. "Kai Asad! Asad!! Asa..." "Wai kai dallacan me yasa mugun jarababben mutum ne kai!" Yarima Asad ya faɗa aharzuƙe yana mai buɗe idanuwan sa tare da miƙewa zaune.
Ƙam ya tsaya ayarce yake yana mai zaro idanuwa tare da buɗe baki, sabo da fuskar da yay araba da ita wacce ko kaɗan bai kawo cewar itan zai gani ba, kafin daga bisani kuma ya fara ɗan sosa ƙeya yana mai sakin yaƙe tare da faɗin. "Ashe Babban yaya nane ban sani ba."
Uhm! Babban yaya ya sauke É—an gajeren numfashi yana mai kafesa da idanuwa.
Sake sosa ƙeya yayi, sabo da yarce yaga yaƙi ya ɗauke ido daga kan sa, tukun daga bisani yace. "Kayi haƙuri Yaya na wallah na zata wancan masifaffen al'amin ɗin ne yazo, shiyasa kaji na faɗi haka."
Taɓe baki babbayn yaya yayi ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ina fatan dai kayi sallah, ba wai sai yanzu ka tashi ba ko?"