Sashe 75
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai Yarima Asad yayi k'aurin suna acikin garin wasai fiye da duk sauran yaran cikin gidan sarautar, haka kuma kowa yasan halin sa, sabo da yadda ko titi idan ya futo baya sassautawa mota, kamar yadda bai yadda wani ya tuk'asa ba muddin ba tafiyar nesa zaiyi ba.
Yayin da motocin sa kuma suka kasance har guda goma shabiyu, gaba d'ayan su masu azabar kyau da tsada na zamani.
Ko wacce tana d'auke da number ta mai suna Prince Asad ajikin ta, tun daga kan number 1 har zuwa 12 ta k'arshe.
Sosai yake matuk'ar birge Matasa, sannan kuma suke mutuwar son sa da san salon sa, barin ma idan ya futo akan doki, kasancewar har yau yana hawa doki, kana kuma yana da su kusan har guda shida, gaba d'ayan su lafiyayyu k'osassu.
Yayin da manyan mutanen da suke a kusa da gidan sarki kuma suke alawadai da hallayar sa, wasu kuma suke masa fatan shiriya, sabo da kowa yasan yadda yake gudun al'adun hausawa yanzu, su kuwa manyan babu abun da suka tsana face irin shigar da yake yi, da kuma yadda suke jin labarin sa a gari na cewar yana da huraren shak'atawa da yake had'a 'yammata da samari kala-kala suna iskancin su.
Wannan dalilin ya sanya baya birge su kwata-kwata.
Mutuwar Ciroman gida wanda ya kasance k'ani ga mai martaba da yayi bayan wasu 'yan watanni ne ya sanya ake ta shirin nad'a Babban yaya a cikin satin nan, domin ma har an tsaida ranar da za'ayi nad'in, sabo da dubawar da akayi a kaga shine kawai ya cancanta da kujerar, dama kuma ita sarautar ciroma sarauta ce wacce ake bawa 'ya'yan sarki ita.
Wannan dalilin ya sanya aka futar da shi a matsayin wanda za'a d'ora akan karagar ta ciroman gida, wanda za'ayi bikin nad'in nan da sati d'aya mai zuwa.
*BABBAN ZAURE LOCUS*
Tsaye suke a cikin compound d'in gidan nasu, Sheikh Ahmad na furfuto da kayan da suke acikin boot d'in motar tasa irin su fulo, capet, buta, tare da kulolin abinci, wanda hakan ke nuni da cewar sun dawo daga asibiti ne, kuma da alamun sun d'an kwana biyu ne acan d'in da.
Yayin da matar sa kuma take rik'e da Aishatu, da yanzu ta koma hajiya Aishatu da sukaje saudiyya sukayi aikin hajji da ita da Ishak', harma da tsohuwa kaka a shekarar da ta huce, wanda Sheikh Ahmad ne ya biya musu gaba d'ayan su kuma, domin kuwa a yanzu sai dai suce Alhmadulillah, sabo iyakar rufin asiri na duniya Allah yayi musu shi, sai dai kawai suyi fatan da cewa da na lahira.
Da alamun dai itace mara lafiya da aka dawo da ita daga asibitin, duba da yadda tayi matauk'ar kwantsamewa, sai kuma Alhaji Ishak' mahaifin Sheikh Ahmad da shima ya futo daga gidan gaba.
'Dibar kayan sukayi suna masu shigewa da su cikin gidan gaba d'ayan su.
A d'an madai-daicin falon nasu da ya gaji da had'uwa da kayan ado, suka zube akan tausasan kujerun da suke a cikin sa wa'yan da suka kasance na k'asar turkey.
"Barka! Barka!! Barkan ku da isowa."
Muryar kaka ta ratsa dodon kunnuwan su a lokacin da take futowa daga cikin d'akin ta.
"Yawwa Kaka barkan ki da gida."
Sheikh Ahmad da matar sa suka fad'a suna masu kallon ta.
Yayin da Ishak' da Aishatu kuma suka had'a baki wurin gaishe ta cikin tsantsar ladabi da biyayya.
Amsa musu kaka tayi tana mai zama akan kujerar da take facing d'in wacce Aishatu take zaune akai.
Kana ta bud'e baki idanuwan ta akan Aishatu tana mai fad'in.
"To ya kuma k'arfin jikin naki yanzu 'yannan?"
"Alhamdulillah."
Aishatu ta fad'a tana mai kallon ta itama.
Yayin da ita kuma Kaka ta k'ara gyara zaman ta, tukun ta d'ora da fad'in.
"Har yau na rasa gane wace irin macece ke Aishatu, tun kina bani tausayi ina zubar miki da hawaye ada har gashi yanzu kin fara bani haushi.
Haba, ace mutum kwata-kwata ya kasa yadda da k'addarar da Allah ya d'oro masa.
Yau kimanin kusan shekara talatin da faruwar wannan abun, tun kina da yarinta a jikin ki gashi nan har girma ya fara zuwar miki, amma kullum kina mayar da abu tamkar yanzu yake faruwa, bayan kuma kin san hakan babbar illace gare ki, domin kuwa gashi nan yanzu har likita yace kina gab da kamuwa da ciwon zuciya, bayan kuma tsinannen hawan jinin nan mara imani da yayi miki mugun kamu.
To ina ranar damuwar da kike sawa aranki?"
Kaka ta fad'a cikin fad'a fad'a tana mai hararar Aishatu.
Ita kuwa Aishatu lumshe idanuwan ta tayi tana mai jin furucin kaka na dukan zuciyar ta.
Ji take inama ace zata iyayin yadda suke so tayi, tabbas da babu abun da zai hana ta yin hakan, domin kuwa tafi kowa cutuwa da kalar halin da take ciki na yanzu.
Amma sai dai kuma ita kanta ta sani babu wanda zai tab'a fahimtar ta, sabo da shekara talatin ba kwana talatin bace ba.
Sai dai kuma ita a yanzu ma gaba d'aya ta fara futar da ran sake yin wani murmushi agidan duniya.
Sabo da mafarkin matashin kyakkyawan yaron da take yi a yanzu cikin mugun yanayin da yafi na baya sosai sosai, wanda hakan kuma shine musababbin tashin ciwon nata har ya kaita da kwanciya a asibiti na tsawon sati biyu yau kenan.
Sai dai kuma tasan babu mai fahimtar halin da take ciki kota fad'a yanzu, sabo da koda ita d'in ce ma ba lallai ta fahimta ba.
Sai dai kuma ta riga tabarwa Allah komai nata yanzu, babu abun da take aikin yi face addu'ar Allah yaye mata wannan damuwar, ya sanya mata dangana ko domin farin cikin ahalin ta.
Shi kuwa Sheikh Ahmad gyara zaman sa yayi akan kujerar da yake zaune akai yana mai karkata kansa, kana ya watasa dara-daran fararen idanuwan sa akan fuskar Kaka.
Sannan ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Kuji tsohuwar nan dan Allah, to yanzun da kika sata a gaba kina ta masifa dame kike so taji kenan, bayan kuma duk kema kina d'aya daga cikin zamtowa silar abun da ya faru."
Ya k'arasa maganar k'asa-k'asa yana mai d'an watsa mata hararar wasa.
"Yau na shiga ukku na lalace, yanzu Ahmadu ni kake zagi a haka akan idanuwa na sabo da nayiwa Uwarka fad'a.
To Ishak'u kana jifa fitsararren d'anka yana zagi na, amma kayi shiru kana kallon sa.
Innalillahi ke duniya ina zaki damu, yau naga abun da yafi k'arfin gani na, sannan naji kalamin da suke shirin toshe mun kunnuwa na."
Kaka ta fad'a da k'arfi tana mai fara k'wak'ulo- k'walla a cikin idanuwan ta tana goge ta a hab'ar zanin ta da ta kwanto sa, sabo da Ishak' yayiwa Sheikh Ahmad fad'a.
Ai kuwa ta samu yadda take so.
Domin kuwa cikin tsantsar zafi Ishak' ya juyo b'arin da Sheikh Ahmad yake yana mai cewa.
"Kai dan Ubanka meye hakan kakeyi, bana son shirmen banza da wofi fa, ko kuwa ita d'in tsarar kace da zaka tsaya kana fad'a mata magan-ganu, to kasani har dai zaka iya yi mata rashin kunya nima tsaf zaka yi mun, domin kuwa itace komai nawa a duniyar nan."
Ishak ya fad'a cikin zafi yana mai kallon fuskar Sheikh Ahmad.
Shi kuwa Sheikh Ahmad kansa ya durk'usar k'asa yana mai d'an murza yatsun hannuwan sa.
Yayin da yake jin duk zuciyar sa babu dad'i, sbo da ran mahaifin nasa da yaga ya b'aci.
Hakan ne yasa cikin sanyi, kana cikin yin k'asa da murya ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Kayi hak'uri Abba ka gafarce ni, insha Allah irin haka bazata sake faruwa ba."
"Hhhhhhhhhh!
Kaji d'an kan Uba ko, ai wallahi ni d'in dai-dai nake da duk wani d'an banza a gidan nan."
Kaka ta kwashe da dariya tana mai kallon Sheikh Ahmad, yayin da take jin zuciyar tayi haske k'al.
Kana daga bisani kuma ta mayar da idanuwan ta kan matar Sheikh Ahmad da take zaune mai tana fad'in.
"Ke kuma lafiya kika zubo mun wa'yan nan mayun idanuwan naki, ke wai a dole mai miji kinji haushi an masa fad'a ko, to ai sai ki matso ki dake ni shine zan san ranki ya b'aci mara kunya matar fitsararre kawai.
Malaman k'arya malaman bogi."
Durk'usar da kai tayi tana mai d'an sakin murmushin yak'e, kana ta bud'e baki tana mai fad'in.
"Allah ya baki hak'uri kakus, ni ba haka nake nufi ba."
"Dallacan ni rufemun baki gafara kawai.
Kai Allah Sarki Huzaifah na, Allah ya nuna mun taka matar, kai daga gani nasan kyakkyawa 'yar gayu zaka zab'o mana ba irin su d'an ware ba, domin kuwa dama kowa yana d'auko kalar sane."
Ta k'arasa maganar tana mai sahafa kan Auta tare da hararar Sheikh Ahmad daga wurin da take zaune.
Shi kuwa Sheik Ahmad inda take bai d'ago ya kalla ba, saboda lura da yayi da neman rigima kawai take yi yau d'in, gashi kuma yaji Abban nasa ya biye mata, hakan ne yasa sa kama bakin sa yayi gum da shi ba tare da ya furta komai ba.
*JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*
Babu daren duniyar da zaizo ya tafi ba tare da Gimbiya Haddiyal tayi mafarkin Gid'ad'on ta ba har yau.
Yayin da soyayyar sa kuma ta k'ara mamaye gaba d'aya zuciya da ruhin ta, ta yadda har take jin komai zai iya faruwa da ita idan ta rasa sa.
A kullum bata da wani labari face nasa, babu abun da tafi son gani face kyakkyawar fuakar sa, hakan yasa ko da yaushe take cikin lumshe idanuwan ta dare da rana, domin kuwa da zarar ta lumshe sun take ganin sa tsaye a gaban ta yana mata murmushin sa.
Bata da abokan hira wa'yan da suka huce tsuntsayen ta, domin kuwa sune kad'ai take zama ta bawa labarin Gid'ad'on ta kuma su saurare ta har su taya ta farin ciki.
Yayin da sauran mutane kuma suke mata kallon wacce ta fara zaucewa, ta yadda har ake ta aikin samar mata da maganunuwa amma a banza.