← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 79

Sashe 51

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da wani ɓata lokaci ba Sheikh Yaƙub ya fara haɗa magun-gunan sa, tukun ya matso gaban gadon da Asad yake hannun sa riƙe da wata ƴar kwalba, wacce take ɗauke da wani kalar mai a cikin ta.
Dangwalar man ya dinga yi yana mai shafa sa asaman goshin Asad da kuma kan ƴan tsunsa na ƙafa, tukun daga bisani ya juya bayan ya gama shafa masa, yana mai ɗauko wani turare ya zubasa a cikin electric burner ta turaren wuta, bayan ya maƙala ta a jikin socket.
Take kuwa ɗakin ya turnuƙe da wani irin hayaƙi mara daɗi ko kaɗan.
Ajiye sa yayi agefe yana mai juyawa ya tsiyoyo wani ruwa da yake a cikin jarka a cup, kana ya dawo gaban Asad yana mai zuba ruwan atafin hannun sa, tukun ya yarfa masa shi akan fuskar sa, sannan aƙarshe ya koma ya juye masa ruwan duka a fuska, ɗan sauran da yayi ragowa a cikin kofin kuma ya sanya mai martaba ya ɗago masa da kan sa tare da buɗa masa bakin sa, tukun ya tsiyaya masa shi a ciki yana mai hucewa cikin-cikin Yaron.
Yayin da hayaƙin nan kuma ke cigaba da tashi har lokacin yana bugun fuskar Asad.
Ruwan na gama shiga cikin-cikin sa ya fara É—an jujjuya kai idanuwan sa na motsawa, amma bawai sun buÉ—u bane ba.
Ganin hakan da mai martaba yayi ne yasan ya sa zaro idanuwa da sauri, sannan kuma cikin tsantsar farin ciki, tukun daga bisani ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in.
"Malam kagani fa yana motsi da kai yanzu, kuma ma naga kamar idanuwan nasa yake shirin buÉ—ewa.
Baba na! Baba na!! Baba na!!! BuÉ—e idanuwan ka kaganni kaji."
Mai Martaba ya faÉ—a cikin sauri yana mai cigaba da murza tafin hannun Asad.

"Hakan shike nuna tabbacin sihiri ne akai masa, kuma Insha Allah ba zaiyi wahalar samun sauƙi ba, amma sai dai kuma wannan motsin da yake bashi ke nufin zai buɗe idanuwan nasa yanzu ba, dan haka ina son ka kwantar da hankalin ka, insha Allah zai warke a nan kusa."
Cewar Sheik Yaƙub yana mai dafa kan Mai Martaba da shima duk ya zurma sosai, sabo da tashin hankali da fargabar kar ya rasa ɗan nasa.

Jinjina kai Mai Martaba yayi yana mai faÉ—in.
"Allah ya basa lafiya to."
"Amin! Amin!!" Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai komawa ya cigaba da haɗa magun-gunan sa.

Har suka ɗauki tsawo sati ɗaya da zuwa dai-dai Asad bai buɗe idanuwan sa ba, sai dai kuma akullum motsin sa na ƙara ƙaruwa fiye dana da daga kwancen da yake, domin kuwa yanzu har hannun sa yana ɗagawa ya ɗorsa akan ƙirjin sa, hakan yasa Mai Martaba yake ƙara kwantar da hankakin sa, sabo da cigaban da yake gani shida kansa a kullum.
Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya duƙufa wurin nemawa yaron magani da gasken-gaske.

Acan Ƙasar Hausa kuwa, a Jahar Wasai cikin Masarautar Wasai.

Sosai Gimbiya Fulani tayi wata irin kwantsamewa, ta jeme ta rame ta kuma yi duhu, sabo da tsan-tsar fargabar da take ciki, ga abinci da bata iya ci, sannan kuma ga rashin samun ishash-shen bacci, domin kuwa kwanan tsaye take tana kaiwa Allah kukan ta.

A ɓangaren Babban Yaya da sauran ƙannen sa suma sosai suka rame suka kwantsa me, barin ma Babban Yaya da shima bai fiye yin wadataccen bacci ba, sabo da yadda yake raba dare yana yiwa ƙanin nasa addu'oi cikin sallolin da yake yi.
Fannin Al'amin shima kullum rana sai yayi kukan rashin abokin sa, domin kuwa gaba É—aya ma baro part É—in su yayi ya dawo wurin Gimbiya Fulani, acewar sa da zarar su Asad sun dawo shi zai fara ganin sa.
Hakan da Gimbiya Fulani ta gani ne yasa tasanya akayi musu visa ta zuwa London su ukku, wato ita, sai Babban Yaya, sai kuma shi Al'amin É—in, yayin da jirgin nasu zai tashi a sati mai zuwa, wato rana ita yau.

Har yau cikin duka kishiyoyin nata biyu babu É—aya data zo mata jaje, hakan ne yasa gaba É—aya ta É—iga alamar tambaya akan su, wato take zargin sune suke da sa hannu akan ciwon É—an nata, sai dai kuma babu wanda ta faÉ—awa hakan, kana kuma koshi mai martaba tace bazata faÉ—a masa basu zo É—in ba.

_BAYAN SATI ÆŠAYA_

Yau ta kama sati biyu da fara yiwa Asad magani kenan, amma sai dai kuma har yau bai buɗe idanuwan sa ba, sai dai kuma a kullum jikin nasa na ƙara yin kyau daga kwancen da yake, sannan kuma zuwa yanzu gaba ɗaya zafin da jikin sa keyi ya ɓace tas, wato tempreture sa ta dawo dai-dai tamkar ta kowa.

Misalin ƙarfe ukku na rana an agogon nan london, su Gimbiya Fulani suka ƙaraso cikin gidan Sheikh Yaƙub, ta sanadin driver'n sa da yaje ya ɗauko su a airport.

Sosai dattijuwar matar Sheik Yaƙub ta musu tarbar mutunci cikin sakin fuska.

Basu iya cin wani abun kirki ba daga cikin lodin abubuwan da aka ajiye musu a gaban su, suka miƙe tsaye suna masu faɗin wazai kai su wurin su Asad ɗin, kasancewar suna can cikin ɗakin maganin har shi Sheik Yaƙub.

Ita da kanta ta sanya hijab É—in ta tana mai shiga gaba tace su biyo ta.

Shigar su cikin ɗakin tayi dai-dai da lokacin da Asad ya fara wani irin girgiza kai da matuƙar ƙarfi, yana mai ƙiƙƙifta idanuwan sa, sabo da wani tirare da Sheikh Yaƙub ya shaƙa masa a cikin hancin sa.
Da sauri dukan su suka ƙarasa zuwa gaban gadon suna masu tsayawa cirko-cirko, yayin da wasu irin hawaye masu mugun gudu suka ɓalle daga cikin idanuwan Gimbiya Fulani suna tsiyaya akan kuncin ta, sabo da yadda taga gaba ɗaya ɗan nata ya rame yayi baƙ,i yarce kasan ba kakkyawan Asad ɗin ta ta ɗan gayu ba.

Ahankali ya fara buÉ—e idanuwan sa har ya buÉ—e su duka akan fuskar jama'ar dake wurin, tukun daga bisani yayi saurin mayar dasu ya rumtse yana mai kai tafin hannun sa ya shafe su, sabo da wani irin haske da ya dalle masa idanuwan alokacin da ya buÉ—e sun.
Yayin da su kuma duka jama'ar a suke wurin suka buÉ—e baki cikin tsanrsar farin ciki, suna masu faÉ—in.
"Alhamdulillah."
Kana Gimbiya Fulani ta ɗaga ƙafafuwan ta cikin sauri tana mai zuwa ta zauna abakin gadon, tukun ta kamo tafin hannun Asad ta riƙe sa a cikin nata tana murzawa, bakin ta na furta kalmar.
"Zaki! Zaki!! Zaki!!! BuÉ—e idanuwan ka ka ganni kaji."

A hankali ya fara buÉ—e idanuwan nasa har ya sake buÉ—e su tas akan fuskar Mamy'n tasa.

Gaba É—ayan su murmushi suka saki suna masu matsowa gaban gadon cikin tsantsar farin ciki.
Da sauri Mai Martaba ya matsa kusa da shi yana mai miƙa hannun sa ya riƙo ɗayan tafin hannun Asad da shi, tukun ya buɗe baki cikin farin ciki shima yana mai faɗin.
"Baba na! Baba na!! Barkan ka da tashi kaji."
A hankali Asad ya sake juyawa yana mai kai idanuwan sa kan fuskar Mai Martaba.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya sakar masa murmushi yana mai faÉ—in.
"Sannu kaji Baba na."
Amma sai dai kuma gaba É—aya Asad É—in baice komai ba tun da ya buÉ—e idanuwan, sai kallon kawai da yake binsu da shi gaba É—ayan su.
Yayin da su kuma suke ta sake matsawa gare sa duka har Al'amin, kowa na yi masa magana.

Sai da suka ɗauki tsayin mintina goma suna abu ɗaya amma Asad bai tankawa kowa ba, ganin hakan da Sheikh Yaƙub yayi ne ya sanya sa cewa su ɗan matsa daga bakin gadon su basa wuri.
Take kuwa duk suka jajja baya, sai Mai Martaba ne kawai bai kauce ba.

"Ina yini malam."
Gimbiya Fulani da su Babban Yaya suka faÉ—a, kasancewar basu samu damar gaishe saba la okacin da suka shigo, sabo da murnar ganin Asad da sukayi ya buÉ—e musu ido data É—auke musu hankali.

"Lafiya ƙalau, fatan kuma kun iso lafiya."
Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai zama abakin gadon.
Da lafiya ƙalau suma suka amsa masa, yayin da shi kuma ya miƙa hannun sa ya mai riƙo tafin hannun Asad ɗaya da yake ta kallon sa da shi.
Tukun ya buÉ—e baki cikin sanyi yana mai faÉ—in.
"Asad! Asad!"
Ƙala Yarima Asad bai ce masa ba, sai idanuwa kawai da yake binsa da su.

"Asad kayi magana mana, ya jikin naka ne?"
Sheikh Yaƙub ya sake faɗe yana mai ɗan girgiza sa, amma still dai shiru sai kallon kawai, hakan da ya gani ne yasa ya ɗago sa daga kwancen da yake, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin.
Sauko ƙasa to kaji."

Take kuwa Asad ya fara zuro ƙafafuwan sa ƙasa, amma baice komai ba, ganin hakan da yayi ne yasa yace masa koma kazauna to basai ka sakko ɗin ba kaji."

Komawar yayi ya zauna kuwa, yana mai jin gina da bango ya cigaba da binsu da idanuwa.
Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya juyo gare su, gaba ɗayan su da duk sunyi shiru, yana mai kallon su murya asanyaye yace.
"To duk da haka dai Al'hamdullilah zamuce, domin kuwa munga sauƙi sosai fiye da baya, tun da gashi nan yanzu yana ganin kowa kuma yana jin muryar kowa, sannan kuma yana iya motsawa har tafiya ma zaiyi, sai dai kuma inda matsalar take a yanzu itace rashin magana, wato dai a gaskiya baya magana, kuma ba zai iya magana ba a yanzu, sai dai ko a nan gaba."
Sheikh Yaƙub ya ƙarasa mganar cikin sanyi.
Yayin da su kuma dukan su sukayi shiru, sai hawaye da suka ɓalle daga cikin idanuwan Gimbiya Fulani.

"To Alhmdulillah, hakan ma ai yafu da sosai, kuma maganar ma insha Allah muna saran zaiyi ta a nan kusa."
Mai Martaba ya FaÉ—a cikin sanyi yana mai murza hannun Asad É—in.
Yayin da shi kuma Shekh Yaƙub ya miƙe tsage yana mai juyawa ya fuce daga cikin ɗakin da shi da matar sa, sabo da su basu damar tattaunawa.
Chapter 51 · 0% Book details