Sashe 16
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama ta sake gyarawa tana mai ƙara fuskantar sa, tukun ta ƙara gyara zaman hijab ɗin dake sanye ajikin ta, sannan ta ɗora da cewa. "Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wassallam yana cewa. Babu wani zunubi daya fi sanya azaba da wuri fiye da zalunci da yanke zumunci. Azzalumi ana bugeshi aduniya koda kuwa an masa gafara da rahama alahira, sabo da adalci tsarine acikin komai da komai, idan aka tsayar da al'amarin duniya akan adalci sai komai ya tsaya, koda kuwa ma'abocin duniyar nan bashi da rabo alahira, idan kuwa ba atsayar da al'amuran duniya akan adalci ba, to lamarin bazai tsaya ba, koda kuwa ma'abocin sa yana da imani da zai ishesa alahira. (Duba maj'mu'ul fatawa 28/146).
Hakanan shugaba ya zama ƙarfi wajen zartar da abun da yake gaskiya ne acikin talakawan sa, ya nisanci zalunci, da ƙarya, da cin amana, da ha'inci da sauran munanan halaye. Wannan sune kaɗan daga cikin haƙƙoƙin talakawa akan shuwagabannin su, dan haka wajibi ne akan shuwagabanni su kiyaye waƴan nan haƙƙoƙin, sabo da al'amuran talakawan su amana ce awuyan su, kuma Allah zai tambaye su abun da ya basu kiwo daga bayin sa."
Ta ƙarashe maganar tana mai sa hannu ta zame hijab ɗin dake sanye ajikin ta, tukun ta miƙe daga kan prayer mat ɗin da take kai tana mai komawa bakin gado ta zauna.
"Nagode sosai Mamy na, Allah ya saka da alkhairi, rabbi yayi mana jagora cikin duka harkokin mu albarkacin fiyayyen halitta."
Babban yaya ya faɗa yana mai miƙewa ya koma kan wata mayyar royal chair da take kafe daga jikin bango.
"Amin ya rabbi." Mahaifiyar tasa ta faɗa tana kallon sa, tukun daga biani ta ɗora da faɗin. "Ina ƙanin naka yake ne, rabon da muhaɗu tun safe yau, ɗazu kuma Baby take cemun yace mata ta kirani tazo bata saman ba?"
"Uhm! Mamy ai Asad ɗin naki ne sai dai addu'a kawai, amma yaron nan kullum girma yake ƙarawa amaimakon yayi hankali sai dai wani sabon salon shirmen da yake ƙara futowa da shi, dama yanzu haka ma akan batun sa nazo wurin ki." Babban Yaya ya faɗa yana mai kallon mahaifiyar tasa.
Yayin da ita kuma ta girgiza kai tana mai lumshe idanuwan ta ba tare da tace komai ba, sai dai kuma kallo ɗaya kawai zaka mata kasan akwai damuwa aƙasan ranta, sabo da yarce yanayin fuskar ta ya nuna, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata akan fuskar Ciroma tana mai faɗin. "To yanzu kai me kazo da shi akan batun kenan?"
Wai Mamy ace Asad ko bakin fada bai jeba balle harya hau doki ayi hawa da shi, kai ataƙaice ma duka baya cikin gidan nan ya fuce ya tafi yawon sa. "Cewar Babban Yaya" ransa duk ba daɗi.
Murmushi mahaifiyar tasu ta saki, wanda kana ganin sa basai anfaɗa maka ba zaka san na yaƙe ne, tukun daga bisani ta buɗe baki idanuwan ta akan Ciroma tana mai faɗin.
"Kaima fa abun da ka riga kasani ne, babu tayarce za'ayi ZAKI yaje fada, tunda yasan irin mutanen da zai tarar aciki da kuma kalar shigar da kowa keyi wacce shi yake ganin ƙauyanci ce agaresa idan yayi ta, sannan kuma shi kansa wurin hawan kasan ba zaije saba duk yarce yake da maitar doki, ko da ko bai bar cikin gidan nan ba, tunda yasan ana kaɗa-kaɗe da bushe-bushen da bai son jin kalar su." Ta faɗa tana mai cigaba da sakin murmushin yaƙe, tukun daga bisani ta tsayar da murmushin da take yin tana mai ɗorawa da faɗin. "Akullm akuma kowane daren duniya sai na kai goshina ƙasa ina roƙon Allah ya canza masa dabi'un sa, ya dawo mutumin ƙwairai kamar kowa, amma shiru kake ji har yanzu." Ta ƙarasa maganar jikin ta na yin sanyi.
"Ki kwantar da hankalin ki Mamy na, akwai mafuta da nazo mana da ita, wacce sheikh Ahmad ya samar mun da ita, sannan kuma ina tinanin insha Allah idan har nayi aiki da ita komai zai zo ƙarshe bi'izinillah." Babban Yaya ya faɗa yana mai gyara zaman sa akan kujerar da yake kai.
Cikin sauri mahaifiyar tasa ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in. "Shin wata kalar mafuta ce kenan?"
"Ashekaranjiya da muka zauna karatu da sheikh Ahmad, bayan mun gama sai nake kora masa bayanai akan hallayar yaron nan, to shine ya cemun tunda har ni kaɗai ne wanda yake ganin girma na, sannan kuma duk abun da nace yayi yake yi baya iya ƙetarewa, kana kuma akwai tsantsar shaƙuwa da ƙaunar juna tsakanin mu, to kamata yay ya zamto koda yaushe yana gefe na, ma'ana dai in janyo sa ajiki na ya zamto duk inda zani in dinga jansa yana rakani, haka kuma aduk lokacin da na kasance ina cikin gida to in zamto ina kusa da shi koda kuwa awurin cin abinci ne, hakan shine zai sa ya rage yin wasu abubuwan da yake yi, sannan kuma zan samu damar ɗora sa akan hanyar da nake son yabi cikin sauƙi.
To bayan na dawo gida da na zauna na sake nazari akan magan-ganun sa, sai naga tabbas hakan itace mafita, dan haka shiyasa tun jiya na yanke hukuncin cewar zan fara aikina na farko amatsayina na Ciroman gida tare da shi, wato jibi zan jasa mutafi JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULƊE domin siyo shanun da za'ayi layya dasu acikin gida, kasancewar an aika musu da saƙon zuwan mu tun awancan satin daya huce." Babban yaya ya faɗa yana kallon mahaifiyar tasa.
"Masha Allah, tabbas hakan yayi sosai, sai dai kawai muyi fatan Allah ya shige mana gaba, dan nima na goyi bayan hakan É—ari bisa É—ari." Ta fada tana mai jin daÉ—i aranta, sai kace wacce take da tabbacin idan sukayi hakan zasuyi nasara.
*WASHE GARI.*
*JAHAR KAGUL MASARAUTAR FULÆŠE.*
Yau tun safe aketa shirya -shiryan tarbar Yariman Masarautar Yamma acikin masarautar fulÉ—e.
Yayin da ita uwar gayya wacce za'ayi zuwan domin ta ta kwana cikin tsantsar ƙunci da damuwa.
Zaune take agefen gado sanye da wasu haÉ—aÉ—É—un kayan fulani koraye irin na sarakai ajikin ta.
Yayin da gefe da gefen ta kuma wasu Ƴammatan bayi suka kasance zaune awurin suna masu aikin gyara mata mayawaicin baƙin gashin dake ɗauke akan ta.
Kallo ɗaya zaka mata kasan ko kaɗan bata farin ciki, sabo da yarce fuskar ta take amatuƙar ɗaure, babu alamun annuri tattare da ita, sai dai kuma duk da ɗaure fuskar da tai hakan bai hana tsantsar kyawun da Allah yayi ta da shi ba bayanna.
Sanye ƙafafuwan ta suke cikin wani plat shoe mai tsanin taushi da kyawu, yayin da hannuwan ta kuma suke sanye da wasu azababbun jajayen awar-waraye na fulani amma sarakai, sai wuyan ta da yake damɓare da wata haɗaɗɗiyar sarƙar duwatsu ja zaune akan sa.
Gida ukku suka kasa gashin kan nata, tukun ko wacce ta kama kaso É—aya na gefe da gefe suna masu kitse sa sukayi duk baya da su, sannan suka sake raba na tsakiyar gida biyu shima, kana ko wacce ta sake kama kaso É—aya suna masu kitse sa shi kuma yayi duk gaba, tayarce jelolin suka biyo takan goshin ta, tukun suka sauka akan kafaÉ—un ta suna masu hucewa har kan cikin ta.
Ɗauke duk abubuwan da sukayi amfani dasu wurin yin kitson sukayi, tukun suka koma gefe guda suna masu tsayawa cirko -cirko tare da durƙusar da kawunan su ƙasa.
Sai da sukayi tsayuwar kimanin mintina goma ba tare da ta ɗaga kai takalli ɗaya daga cikin su ba, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓa tana mai faɗin. "Kuna iya zuwa ku shirya kafin su ƙaraso." Acan cikin.
Amma da yake hankulan su da nutsuwar su duka suna gare ta shiyasa tana faɗin haka suka ɗan durƙusa atare suna masu faɗin. "Mun barki lafiya Gimbiya." Sannan suka juya suna masu fucewa daga cikin ɗakin nata.
Acan ɓangaren Lamiɗo mahaifin Gimbiya Haddiyal kuwa, shi da kansa ya sanya aka gyara wurin da ɗiyar tasa tare da sirikin sa zasu zauna idan ya iso, sannan yasa aka kai shimfiɗa ta al'farma da suke da ita acikin masarautar aka shimfiɗa, kana ya cewa Mahafiyar Gimbiya Haddiyal ta tura ƴan matan da zasu je su shirya ta aje afara shirya ta, ba dan komai ba kuma yake haka sai dan kasancewar su Aminai da shi da Lamidon Yamma.
Misalin ƙarfe shaɗaya na safe dai dai wata baiwa dake sanye da kayan fulani ta shigo ɗakin Gimbiya Haddiyal bakin ta ɗauke da sallama.
Amsa mata sallamar tayi daga kan gadon da take zaune ba tare da ta É—ago ta kalle ta ba.
"Allah ya taimakeki yake Gimbiyar Masarautar Fulɗe, Ance in sanar dake Jauro'n Yamma ya ƙaraso."
Baiwar ta faɗa kanta duƙe aƙasa.
Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal taji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce ta, tukun daga bisani ta lumshe dara-daran idanuwan ta ba tare da tace komai ba, kana ta buɗe su akan baiwar nan dake tsaye agaban ta tana mai kallon fuskar ta, kafin daga bisani kuma ta miƙe tsaye tana mai tsayawa akan ƙafafuwan ta.
Sosai tayi bala'in kyau cikin shigar dake sanye jikin ta.
Dasauri ƴammatan bayin da suke tsai-tsaiye agefen ta suka matso kusa da ita suna masu sa hannu suka ɗauki wata haɗaɗɗiyar jar alkyabba irin ta fulani mai adon duwatsu ajikin ta suna masu ɗora mata ita akan jikin ta, tukun suka koma daga bayan ta suna masu tsayawa, gaba ɗayan su suma sanye suke da kayan fulani na mata babu ko takalmi aƙafafuwan su. Yayin da ita kuma wannan ɗayar data kawo rahoto tai saurin juyawa tana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Cikin takun ta na isa da izza ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar bakin ƙofar ta, tukun su kuma ƴammatan bayin nan suka rufa mata baya suna masu ɗora ƙafafuwan su aduk inda ta cire nata, ahaka har suka ƙarasa tanƙashe-shen falon nan.
Kishingiɗe ta hangi mahaifiyar ta aƙasa kan tum-tum ana ta aikin mammatsa mata ƙafafuwa.
Direct ta doshi inda take fuskar nan tata babu alamun annuri bare far'ah.
"Barka da wutawa Dadde am."
Ta faɗa tana mai durƙusawa aƙasa bayan sun gama gaisawa da matar dake yiwa mahaifiyar tata tausa kanta duƙe aƙasa.