← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 79

Sashe 28

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu tasa tana mai funcikar gashin kanta ta wargaza sa tas daga curen da yake, tana mai cigaba da sakin kuka!
Tukun daga bisani kuma ta miƙe tsaye tana mai juyawa ta kai idanuwan ta zuwa hanyar da sukabi da kallo, kana ta ɗaga laɓɓan ta cikin wata irin murya mai amo tana mai faɗin. "Haƙiƙa zan tabbatar maka dani ɗin ba sa'arka bace, tunda har kayi kuskuren shiga gona ta matsiyacin Bawa!" Ta ƙarasa maganar tana mai janye idanuwan ta daga kan hanyar, kana daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta da take jin sun mata wani irin nauyi, ta doshi hanyar da zata sadata da asalin cikin gidan su ba filin Biki ba, domin kuwa tasan muddin ta koma filin biki ahaka dole ne afahimci halin da take ciki, wanda ita kuma bazata so asan hakan ba, sabo da karma Baban nata ya sake sanya mata idanuwa, har ya gano abun da take shirin yiwa wancan ƙasƙantaccen Bawan ya hana ta.

*WAI WAYE ADON TAFIYA INJI MU HAUSAWA, DAN HAKA MU KOMA BAYA DOMIN MUJI TUSHEN LABARIN*

ƘASAR MALIN, BAƘAR MASARAUTA.

Kamar yacce mukaji tun farko, Baƙar masarauta dai ta kasance masarauta ce wacce basu san musulunci ba ko kaɗan, gaba ɗaya mutanen cikin ta basu san Allah ba, asalima suna bauta ne ga wani gunki wanda aka sassaƙe sa tun azamanin iyaye da kakannin su da yake ajiye, yayin da suke amfani da faɗar Vokan su wanda suka ɗauke sa amatsayin waliyin abun bautar su Gargabilu, domin kuwa shine ke sanar da su duk wani abu da zai faru agaba, da kuma wanda zai faru yanzu ta hanyar duban sa da yake, wanda aduk lokacin da yake aikin duban nasa suke faɗin yana saduwa ne da abun bautar su, amatsayin sa na waliyin sa.
Shi kuwa wannan bokan ba kowa bane face BOKA MAI HUTAR KASKO!

Tsoho ne tukuf mai kimanin shekaru tamanin da tara aduniya, shima kuma ya gaji bokancin ne awurin mahaifin sa, wanda ya mutu yana da shekaru ɗari da ashirin da biyu aduniya shi, sabo da shi kansa bokancin gado ne a Baƙar Masarauta, domin kuwa acewar su jinin waliyin abun Bauta ne kawai ke iya sake zama waliyin sa, kamar yacce ɗan Sarki ne kawai ke sake zamtowa sarki, kuma gaba ɗayan su suna amfani ne da Huta tare da Ƙasa wurin duban nasu, hakan yasa ake kiran duk wanda yake kan karagar ta bokancin da suna BOKA MAI HUTAR KASKO, sabo da ita wannan hutar dake ci acikin kasko itace mai haska masa gaban sa, kuma itace take fara isar masa da duk wani saƙon Gargabilu ga jama'a, hakan yasa ba'a taɓa barin ta ta mutu, ko da yaushe ake cikin ƙara izata a kowane lokaci.

Sarki Barbaru shine sarki na talatin alokacin, yayin da Boka mai hutar Kasko kuma ya zamto Boka na goma shabiyar awannnan lokacin.
Ko kaɗan ba aɗauki rai abakin komai ba acikin Baƙar Masauta, dan ko ataƙaice ma babu satin dake zuwa ya huce ba tare da an kashe rai sama da ukku ba acikin masarautar, kuma idan an tashi kisan anayin sane acikin bainar jama'a, gaban kowa da kowa, dan kuwa sai anyi sanarwa ma tukun ake ai'watarwa, kuma mafi akasarin kisan da akeyi bawai anayin sa bane kan an ai'kata wani Babban laifi ne ba, asalima ko Sarki ne yazo giftawa ko kuma ɗan sarki muddin bawa ya kuskura ya biyo hanyar, to hukuncin kisa ne akansa, hakan shine dalilin da ya sanya Bayi ke mugun tsoron Ƴaƴan Sarkin tare da shi kansa Sarkin, ga kuma tsafi da suke da shi na masifa, wanda ake basu shi tun aranar da suka zo duniya.

Sarki Barbaru yana da mata biyu ne tare da Ƴaƴa biyu maza awancan lokacin.
Gimbya Haiwa itace matar sa ta farko, kuma uwar Ƴaƴan sa maza biyu.
Yarima Sauman shine ɗan sa na farko, kamar su ɗaya da uban sa sak, basu da bam-banci ko kaɗan, domin kuwa har halayyar sa ma irin ta ubansa ce tun yana ƙarami.
Sai kuma Yarima Sairan wanda ya kasance na biyu kuma ƙaramin su, kasancewar ita amaryar Sarki Barbaru mai suna Gimbiya Salwa bata haihu ba, ita kuma Gimbiya Haiwa Ƴaƴa biyu kawai ta haifa duk maza.
Gaba É—aya matan nasa biyu suma Æ´aÆ´an sarakai ne na wasu masarautun, waÆ´an da al'adun su suka kasance kusan duk iri É—aya ne.
Sosai Gimbiya Salwa take da sauƙin kai fiye da Gimbiya Haiwa, domin kuwa ita Gimbiya Salwa har ta hanyar Bayi tana iyabi idan ta futo zagaya gida, kuma koda ta haɗu da Bawa ko Baiwa akan hanya bata sanyawa akashe su, sai dai kawai tayi gaba abun ta, saɓanin Gimbiya Haiwa da ko hanyar su bata iya bi, ballan tana har ta iyayi musu gafara idan sun haɗu.
Wannan kenan.

ƘASAR HAUSA, MASARAUTAR WASAI.

Sarki Abdallah shine ya zamto sarki na Ashirin acikin sarakan da suka mulki Jahar Wasai.

Kamar yadda aka sani mafi akasarin gidajen Sarauta ana samun rikici, hassada, baƙin ciki, tare da munafurci acikin sa, to hakan ma ya kasance acikin Masarautar Wasai, domin kuwa Sarki Abdallah ya taso ne tare da Ƴan uba, wato yayye da ƙanne waƴan da suke uba ɗaya, amma uwa kowa da tasa, kasancewar Margayi Sarki Ahmadu ya auri mata har kimanin huɗu ne.
To hakan yasa koda aka fara shirye shiryen naɗa Sarki Abdallah kan karagar mulki abayan mutuwar Sarki Ahmdu aka sha rikici, tare da ƙulalla-ƙullata ta kowace hanya wurin ganin bai hau kan karagar mulki ba, duk da kasancewar sa babban Ɗa namiji kuwa acikin Ƴaƴan Sarki Ahmadu, amma da yake shi ɗin Allah yace zaiyi, haka sukayi duk mugun abun da zasuyi suka gama, kuma yazo ya hau kan karagar mulki.
Yayin da awancan lokacin Galadima da Waziri kuma suka kasance ƙannen baban sa duka biyun, sai bayan sun rasu kuma abayan mutuwar sarki Ahmadu, sannan aka naɗa mutum biyu daga cikin ƙannen Sarki Abdallah, waƴan da suka haɗa uba ɗaya akan muƙaman, wato Alhaji Kabir Galadima, sai kuma Alhaji Nuhu aka basa Waziri, yayin da sauran ƴan uwan nasu suma duka suka zamto suna da tasu sarautar.

Sarki Abdallah ya kasance yana da mata Ukku ne cif.
Gimbiya Huwaila itace matar sa ta farko, Æ´ar sarki itama awata masarautar, sai kuma Gimbiya Amina matar sa ta biyu, itama É—in É—iyar Sarkin wata masarautar ne, sai amaryar sa kuma Gimbiya Khadija wacce akewa lakabi da Fulani, kasancewar ta bafullatana wacce kallo É—aya mutum zai mata ya fahimci hakan, sabo da tsantsar kyanta tare da hasken fatar ta, duk da dai shima Sarki Abdallah'n Fulani ne na sali suma.

Tun kafin ya hau kan karagar mulki suke tare da Gimbiya Huwaila tsawon shekaru goma shabiyar, Æ´ayan su huÉ—u suka haifa, sai dai kuma cikin su duka huÉ—un mata ne babu namiji ko É—aya.
Yarsu ta farko itace Gimbiya Rahama, sai ta biyu kuma mai suna Hafsat, sai kuma Fatima, daga ita kuma sai ƙaramar su mai suna Suwaiba.
Sosai jama'ar gidan suka sanyawa Sarki Abdallah ido tare da yin farinci, sabo da ganin da sukai bai taɓa haihuwar Ɗa namiji ba, wanda hakan yasa kowanne suke ta mafarkin wataran Sarautar tana iya juyewa ta koma ɗakin su.
Watan Sarki Abdallah ukku da hawa mulki ya sake yo sabon aure, inda ya auro Gimbiya Amina. Sosai hankalin Gimbiya Huwaila yayi matuƙar tashi alokacin da akai auren, domin kuwa tsoron ta ɗaya, shine kar Gimbiya Amina tazo ta haifi magajin Sarki Abdallah ba tare da ita ta ta haifo ba, amatsayin ta na matar farko, yayin da suma duka dangi suka zuba idanuwa suna jiran sukaga da abun da zata fara ita.
Sai dai kuma har tayi haihuwa biyu itama Allah bai bata É—a namiji ba, duka biyun suka zamto mata, Wato Gimbiya Sumayya da Kuma Gimbiya Hafsat.
Sosai hankalin jama'ar gidan nasu masu jiran mulki ya sake kwanciya, sabo da ganin haka da sukayi, yayin da masu yin asiri akan hakan suke ganin aikin su naci sosai.
Itama Gimbiya Huwaila sosai taji daÉ—i, sannan kuma hankalin ta ya kwanta, sabo da ganin yarce Gimbiya Amina ta jero mata duka kamar ita, hakan yasa ta cigaba da fatan ta zamto uwar magajin masarauta.
Afannin Sarki Abdallah shima sosai abun ya dame sa, ba kuma wai dan baya son su Æ´aÆ´an nasa mata da ake haifar masa ba, sai dai kuma ko banza shima yan son ace É—an sane zai É—ora daga inda ya tsaya, kamar yacce ya zamto shima ya É—ora daga wurin da mahaifin sa ya tsaya, sannan kuma ko badan mulki bama, yana son ace ya haÉ—a ko wanne jinsi daga mazan har matan cikin Æ´aÆ´an sa, domin kuwa ko wanne daga cikin su yana da daÉ—i tare da amfanin sa.
Hakan yasa ko shekara biyar ba'a rufa da auren su da Gimbiya Amina ba ya sake yo wani auren. Wato Gimbiya Khadija wacce ake kira da Fulani.
Sosai hankalin jama'ar gidan dana kishiyoyin ta ya sake tashi a lokacin da aka kawo ta gidan, ba dan komai ba kuwa sai dan kar suje ita ta haifo ɗa namiji, hakan yasa kusan duk suka duƙufa wurin ganin ba asamu ɗa nimiji ba, itama ta haifo mace kamar yacce sauran sukai, sai dai kuma suna nasu Allah na tashi, haka kuma muddin Allah yace ga yarce yake to babu wanda ya isa ya canza sa, domin kuwa watan Gimbiya Fulani goma shaɗaya dai dai acikin Masarautar Wasai, ta haifo ɗan ta namiji ƙatoto da shi, sannan kuma kyakkyawa mai tsananin kama da ita.
Chapter 28 · 0% Book details