Sashe 7
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cire takalman ta tayi tana mai hawa kan shimfiÉ—ar nan ta kishingiÉ—a akan tum-tum.
Dasauri tsun-tsaye nan suka mar-matso saitin shimfiɗar suna masu maƙal ƙalewa ajikin itatuwan bishiyun da suka yiwa ruwan da shimfidar rumfa gaba ɗayan su, sai ɗawisu kuma guda ɗaya babbar cikin su da ita kuma ta haye kan tum-tum ɗaya wanda yake kusa da wanda Gimbiya Haddiyal ta kishingiɗa tana mai ƙure ta da idanun ta.
Yayin da su kuma agwagi nan suka jajjeru acikin ruwan daga bakin sa, suma cikin su akwai wata fara da tafi duk sauran kyau da take agaban su, sai kuma sauran duka suka hau layi abayan ta.
Sai daga gefen shimfiɗun kuma kaji ne jera reras mazan su da matan su duk sun duddurƙusa suna kallon ta, suma acikin su akwai wacce take agaba fara, sai sauran abayan ta ajere.
Wato dai waÆ´an nan na gaban sune shuwagabbanin da Gimbiya Hadiyyal ta naÉ—a acikin iyalan nata, kuma ako da yaushe hakan suke idan har zasu gana da ita.
Lumshe idanuwan ta tayi bayan ta ɗaga kai sama tana mai sakin murmushi, yayin da su kuma tsuntsayen nan duka sukayi shiru tsit suna kallon ta, tukun daga bisani ta sauke kan nata ƙasa tana mai wara idanuwan ta akan tsun-tsaye nan, kana ta buɗe baki cikin zazzaƙar muryar ta, har kuma lokacin tana sakin murmushi tana mai faɗin. _"Babban wuri ne mai tsananin girma da kyawu, zagaye yake da korayen furanni masu matuƙar ƙamshi da ƙyalli, yayin da jinsin kyawawan tsun-tsaye suka kasan ce kewaye da wurin mazan su da matan su ko wanne yana harkokin sa, sai sassanyan ruwa fari kar dashi yana kwaranya acikin rami. Zaune yake acikin ruwan yana ta faman ɗaga sa sama da hannun sa, sannan sai ya watsa sa ajikin sa, yayin da ni kuma na kasan ce zaune agefen ruwan ina shan madara idanuwa na akan sa, ban an'kara ba banyi tsammani ba sai jinai an watso mun ruwa akan fuska, ina ɗago kai dan naga ko waye sai nayi ido huɗu da shi agabana yana sakar mun murmushin sa mai tsananin kyau, murmushin nima nayi masa ina mai ɗaukar yatsa ta na dunguri dogon hancin sa da shi, kana daga baya na buɗe baki ina mai cewa. Ina sanka Giɗaɗo na._
_Murmushi shima yayi mun, tukun ya sake komawa cikin ruwan yana mai yin nitso ya cigaba da wankan sa ba tare da ya bani amsa ba, daga nan kuma sai na tashi daga bacci na."_
Ta ƙarashe maganar idanuwan ta akan tsun-tsaye, kaji da agwagin nan, yayin da su kuma gaba ɗayan su suka fara sakin kuka suna masu jujjuya jiki alamun suna taya uwar ɗakin nasu farin ciki kenan.
"Tom kunji inda labari na na yau ya tsaya, sai kuma gobe idan na dawo zan baku sabon da zanyi yau, dan haka kowa yana iya komawa wurin sa masoya na." Ta faɗa tana mai miƙewa tsaye daga kan shimfiɗar.
Sosai tsun-tsaye suka rikice da ihu suna ta faman shawagi akan ta, wasu har suna dan gwalar ta da jelar su, tukun sai suyi gaba, suma kaji juyawa sukai agurguje suna masu komawa wurin da suke, yayin da agwagi ma suka sake yin nutso cikin ruwa suna cigaba da harkokin su.
Zura ƙafafuwan ta tayi cikin tattausan takalmin fatar ta, tukun ta juya tana mai sake ɗaukar wata hanyar duk acikin wurin.
Tayi tafiya mai nisa, kana ta isa bakin wani farin ruwa da yake wucewa ƙal-ƙal da shi, yayin da gefe da gefen ruwan kuma wasu irin korayen ciyayi suka masa ƙawanya yayi gwanin ban sha'awa.
Zama tayi agefen ruwan kan ciyayin tana mai cire takalman dake sanye aƙafar ta, tukun ta zura ƙafafuwan nata cikin ruwan tana mai kar-kaɗa su tare da lumshe idanuwa, kana ta ɗaga laɓɓan cikin sanyi tana mai faɗin. "Shin sai yaushe ne zaka bayyana gare ni, sai yaushe ne zan ganka azahiri kaima ka ganni, nayi iyakar yina akan ka amma na kasa, sai dai ina so kasani muddin rai da numfashi suna tattare agangar jikin Gimbiya Haddiya, to soyayyar kama tana nan daram, haka kuma muddin zuciya na cigaba da bugu aƙirjin Haddiyal, to kasani koda yaushe ƙaunar ka na sake sambun ta ne.
Kamatso gare ni ya kai masoyi na, ka tawo gare ni yakai abun ƙauna ta, shin sai yaushe ne zan ganka ka ganni Giɗaɗo na? Ban sanka ba, ban taɓa ganin ka azahiri ba, amma na kamu da ƙaunar ka azuciya ta. Shin kai ɗin ma kasan da zama na ko ko ni kaɗai ce nake hauka akan ka? To kasani koda baka san dani ba babu wata mace da ta isa ta kasance agefen ka bayan ni! Har yau ba ahallici wacce zata soka ba bayan ni! Mutane na cewa kai ɗin ba mutum bane, amma ni na daɗe da sanin kai ɗin mutum ne kuma na daban acikin mutanen ma, ina son kaso ni kamar yacce na soka Giɗaɗo na, jiki na na bani zan ganka na kusa na sadu da kai nan kusa ba da daɗe wa ba."
Ta ƙarashe maganar ƙwalla na tsiyayowa ta gefen idanuwan ta, tukun daga bisani ta wara idanuwan ta tana mai sakin murmushi, kana ta zare ƙafafuwan ta acikin ruwan tana mai miƙewa tsaye.
Takalmanta ta sanya aƙafa, sannan ta sake yin wurin wasu korayen ganye har lokacin fuskar ta ɗauke da murmushi.
Tsaye tai agaban su tana mai sanya hannu ta fara bubbuga ganyayyakin.
Take kuwa Malam buɗa mana littafi (buterfly) suka mimmiƙe daga kan ganyayyakin masu tsananin kyau kala kala suna hawa kan jikin ta.
Dariya ta kwashe da ita tayarce har sai da sautin ta ya É—an futo, tukun ta buÉ—e tafin hannuwan ta duka biyun, yayin da su kuma birbillo nan (malam buda mana littafi) suka hau kan tafin hannuwan nata suna ta jujjuyawa.
Zagaye ta farayi awurin tana hajijiya tare da sakin dariya mai sauti, tukun daga bisani ta tsaida dariyar tana mai faɗin. "Kuyi haƙuri masoya na, ban so nayi muku kishiya ba, sai dai kuma nima ban san lokacin da soyayyar sa ta hudan zuciya ba, abu ɗaya kawai dana sani shine amafarki nasan sa, kuma amafarki nake gannin sa, amma sai da ina mugun kaunar sa, dan haka kuma ina san kuso sa masoya na, na muku al'ƙawarin kune na biyu acikin zuciyar Gimbiya Haddiyal daga ku babu ƙari."
Ta faÉ—a tana mai cigaba da shawagi da dariya ahaka har ta koma bakin ruwan nan data taso.
*ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ, CIKIN BAƘAR MASARAUTA*
Cikin tsantsar fushi da tafasar rai ta ƙarasa bakin ƙofar dake sada mutum da cikin gidan nasu.
Tsaye tayi ƙam abakin wurin, yayin da su kuma waƴan nan ƴammatan bayin da dakarun sukayi saurin zube guiwoyin su aƙasa.
Miƙar da hannun ta tayi gefe ba tare da tace komai ba, yayin da idanuwan ta kuma da ɓacin rai ya mayar dasu ja suka kasan ce kafe akan ƙofar dake kallon su.
Dasauri wannan badakaran ya tawo da baya da baya har ya ƙaraso inda take, tukun ya zube gwuiwoyin sa aƙasa yana mai durƙusar da kai ƙasa, kana ya sanya hannu ya zaro takobin nan tata yana mai ɗora mata ita akan tafin hannu.
Damƙeta tayi da ƙarfi fiye da irin riƙon da take mata abaya, yayin da shi kuma wannan badakaran yayi saurin miƙewa yana mai juya baya ya koma inda yake ya tsaya.
Cikin tsantsar izza ta fara ɗaga ƙafafuwan ta da suke futar da sautin gwalagwalai tana mai dosar ƙofar dake kallon ta.
Cak ta tsaya adai dai lokacin data ɓulla cikin tafkeken falon da yake zagaye da kayan alatu tare da Tambarin masarautar tasu tako ina acikin sa, sabo da abun da idanuwan ta suka gane mata daga shigar tata.
Sosai kanta ya kulle, mamaki da tinanin abun da ya kawo sa cikin falon su awannan lokacin yayi matuƙar ɗaure mata kai, tayarce har ta kasa buɗar baki tayi magana kamar yacce ta kasa ɗaga ƙafa tai gaba.
Cikin tsantsar fushin da bata taɓa ganin sa acikin sa ba tun lokacin da tazo duniya tagan sa adai dai lokacin da ya juyo ɓarin da take yana mai watsa jajayen idanuwan sa cikin nata!
Wata irin faɗuwar gaba ta samu kanta aciki, sabo da tunda take bata taɓa ganin idanuwan sa sun sauya haka ba, yayin da shi kuma ya fara tinkaro inda take cikin takun sa wanda yake nuni dashi ɗin ko waye fuskar sa amatuƙar ɗaure.
Rawa jikin ta ya kamayi sabo da yarce taga ya nufo ta gadan gadan, abun da tunda take bata taɓa tsintsar kanta aciki ba, wato tsoron da ya ziyarci zuciyar ta yanzu!
Cak ya tsaya agaban ta yana mai É—an ranÆ™wafowa ya rage tsayin sa fuskar sa ta kasan ce dai dai tata fuskar, tukun ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in. "Sh.............âœ
🎠*BAƘAR MASARAUTA* ðŸŽ
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
ðŸðŸŽ ðŸ„ðŸ¹
_*NA*_
UMAR FARUQ*D*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*PAGE 03*
"Shin ashe dama har akwai lokacin da zaizo wanda ƴa zata yaƙi ubanta! Wato ke yanzu har kinyi girman da zaki iya ja dani, sannan ki rushe mun ginin da na ɗauki tsawon shekara da shekaru ina yin sa! Shin kin san kalar hanyar dana bi kuwa kafun na samu wannan mafutar da ke kike shirin wargazata yanzu?"
Ya faɗa cikin ƙaraji jajajyen idanuwan sa duk sunyo waje yana mai kafe ta da su.
Yayin da ita kuma jikin ta ya É—auki wata irin kakkarwa, hankalin ta idan yay dubu sai da duka ya tashi, domin ko ko kaÉ—an bata fahimci inda maganar mahaifin nata ta dosa ba balle har ta gano kalar laifin data aikata masa.
Sake gyara tsayuwa yayi agaban ta yana mai sake fuskantar ta fuskar nan tasa babu alamun rahama tattare da ta, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Labarin dogo ne, tarihin murɗaɗɗe ne, al'amarin kuma mai girma ne, sannan kuma rikitacce ne wanda yafi ƙarfin iko na!
Tsahon shekara talatin kenan da Ubangiji mai girma Gargabilu ya samar mun da mafuta, amma sai gashi rana tsaka Æ´ata ta ciki na tana shirin rushe duk mafutar da aka samar tun kafun wanzuwar cikin ta agidan duniya!"
Ya faÉ—a yana mai sake watsa idanuwan sa cikin nata.