← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 79

Sashe 69

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan da Billy ta gani ne ya sanya ta miƙewa tsaye da sauri itama, kana ta ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryar ta tana mai cewa.
"Please can i get your phone number?"
Ta ƙarasa maganar a hankali, tana mai fatan Allah yasa kar yace a'a azuciyar ta.
Yayinda shi kuma ya cigaba da tafiyar sa yana mai yin tamkar baiji abun da ta faÉ—a ba.
Wani irin sanyi Billy taji jikin ta yayi.
Gaba É—aya murnar da take ta fara komawa ciki, sabo da ganin da tayi ya mata banza tamkar bai san da ita ba yana shirin shigewar sa cikin É—aki.

A fannin sa kuma yaji ta sarai amma yay tamkar baijitan ba, sai da har yaje bakin ƙofar da zata sadasa da cikin bedroom ɗin sa, tukun ya tsaya a wurin yana mai zira hannun sa cikin aljihun sa.
Kana ya zaro katin sa wanda yake É—auke da sunan sa da kuma number sa a cikin aljihun sa, yana mai cilla mata shi daga nan wurin da yake ba tare da ya juyo ba, sannan ya buÉ—e baki cikin maganar sa da sautin ta bai fiye futa ba, yana mai faÉ—in.
"Zaki iya tafiyar ki yanzu ok."
Ya ƙarasa maganar yana mai murɗa handle ɗin ƙofar tare da danna kansa ciki.

Yayin da Billy kuma ta buÉ—e baki cikin tsantsar farin ciki tana mai faÉ—in.
"Thank you Prince." Da ɗan ƙarfi yadda zai jiyo, tukun ta matsa wurin da katin sa yake tana mai durƙusawa ƙasa ta ɗauke sa.

PRINCE ASAD

Shine sunan da yake rubuce ɓaro-ɓaro da manyan baƙi ajikin katin nasa, yayin da special numbers ɗin wayar sa kuma da suka kasance har guda biyu suka biyu a ƙasan sunan.
Cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa Billy ta É—auki katin, kana ta suri jakarta tana mai juyawa ta kama hanyar waje fuskarta É—auke da tsantsar annuri.
Yayin da take jin zuciyar ta kuma tai haske fari ƙal, kana kuma ta ƙagu ta isa wurin Zee, domin ta ƙara tabbatar mata da cewar ita ɗin daban take da sauran fa, tamkar yadda ta faɗa mata bata yadda ba.

Rufe masa ƙofar sa tayi bayan ta fuce daga cikin falon, kana tayi gaba abunta tana mai tafiya wurin da lipter take domin ta sauke ta ƙasa, sannan ta huce mazaunin su.

*ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFU CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Sosai jikin Bir yayi matuƙar yin tsami sabo da dukan da yaci.
Sai dai kuma ko kaɗan hakan bai sa yaji cewar zai iya haƙura da ganin Gimbiya Tasmir ya gudu idan sun haɗu ba, domin kuwa tun abun ya faru a jiya har kawo yau hoton kyakkyawar fuskar ta bai-bar cikin idanuwan sa ba.
Asalima da zarar ya buɗe idanuwan ita yake gani durƙushe a gaban sa tana aiko masa da kallon ta, yayin da ko a cikin baccin sa na daren jiya shima ya kasance ɗauke da mafarkin ta gaba ɗayan sa.
A takaice dai lokacin É—aya yaji ta shiga ransa, sannan kuma zai iyayin komai domin ya samu ko kallon tane yayi.

Yana jin wasu irin abubuwa dan gane da Gimbiyar irin waƴan da bai taɓa jin makamantan su ba akan wata tun da yazo duniya.

Yanzu haka zaune yake a jikin bishiya, hannun sa riƙe da kwari da gwafar sa yayi shiru shi kaɗai.
Lokaci bayan lokaci yake É—an lumshe kyawawan idanuwansa yana mai sakin murmushi.
Wani irin shauƙi yake ji tattare da shi, irin wanda bazai misaltu ba.

"Haƙiƙa yanzu na fara shiga harkar ki Gimbiyar mu, koma nace yanzu zan fara shiga, saboda ada ban taɓa sanin haka kike da baiwar kyawu ba sai ajiya.
Tabbas jiya kin zamto rana mai daraja a gareni, rana irin wadda ta shiga cikin kundin tarihina ta zauna, ranar da aka dakeni acikin BAƘAR MASARAUTA dukan yayi matuƙar sanyaya mun zuciya.
Ranar da na fara ganin kyakkyawar fuska irin wacce ban taɓa yin tozali da makamanciyarta ba.
Tabbas zan jure duk wata kalar huya da zaki bani, muddin idanuwa na zasu dinga arba da kyakkyawar fuskar ki, domin kuwa jikina na bani cewar ke É—in zaki zamto hasken zuciya gare ni a wataran Gimbiyar mu."

Ya ƙarasa maganar ƙasa-ƙasa fiye da yadda ya fara ta, yana mai sake lumshe dara-daran idanuwan sa.
Yayinda yake jin tsigar jikin sa na wani irin mimmiƙewa, wani kalar yanayi na lulluɓe sa, sabo da hango ta da yayi acikin idanuwan nasa.
Kafin daga bisani kuma ya wara su a hankali yana mai mikewa tsaye.
Da ɗan ƙarfi ya taune leɓen sa na ƙasa, sabo da yadda yaji gaba ɗaya jikin sa a wani irin kakkame, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa cikin cizon leɓe, yana mai nufar hanyar da yake fatan ta sake sadasa da hasken zuciyar tasa.

A ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ba ita tabar cikin lambun nan ba jiya har sai da gari ya fara dubu.
Shima kuma bawai dan taji zuciyar ta tayi sanyi da abun da ƙasƙantaccen bawan can yayi mata ne ba, sai dan kawai sanin da tayi na yanzu za'a fara neman ta muddin aka duba akaga bata nan.
Wata irin tafar-fasa take jin zuciyar ta nayi mata aduk lokacin data tuno yadda bugun zuciyar ta ya sauya a gaban sa, ga kuma gizon da yake ta yi mata acikin idanuwan ta aduk lokacin data lumshe su, a lokacin da yake sakar mata kyakkayawan murmushin sa.
Wanda hakan kuma shi yake matuƙar ƙara tinzira ta.

Cikin tsantsar baƙin ciki ta doshi ɓangaren nasu, tana mai jin zuciyar ta na cigaba da ƙuna.
"Haƙiƙa kana gab da shaƙar numfashin ka na ƙarshe acikin duniyar BAƘAR MASARAUTA, muddin har zaka ƙara kuskuren shiga gona ta, domin kuwa ina mai rantsuwa da ubangiji Gargabilu sai na lalata maka wannan koɗaɗɗen jikin naka.
Sai na kassara rayuwar ka, ta yadda ko gobe ance ka sake tsayawa akan hanya ta ba zaka yi ba, wannan alƙawari ne na ɗaukarwa kaina akan ka ƙasƙantacce."
Ta ƙarasa maganar da ɗan sauti, tana mai danna kanta zuwa cikin tanƙashshen falon su na alfarma.

Tayi sa'a kuwa babu kowa acikin falon tamkar yadda tayi fata, hakan ne yasa ta kama hanyar da zata sadata da corridor É—in da zai kaita É—akin ta cikin sauri, gudun kar wani ma ya ganta a cikin yanayin da take yanzu.

Ko da dare yayi haka tai ta juyi akan tamfatsen-tsen bed ɗin ta bacci yaƙi ya dauke ta, sabo da baƙin cikin abun da yayi mata da yake cigaba da sukar zuciyar ta.
Tun da take arayuwar ta bata san wata aba mai suna damuwa ba sai yau, bata sai meye tinanin ba sai yau, haka bata san ɓacin rai ba sai yau data haɗu da wancan ƙasƙantaccen fitsararren bawan mara kunya, hakan yasa take jin ƙarin tsanar sa na ƙara turnuƙe zuciya da ruhin ta aduk bayan wanzuwar wata daƙiƙar.
Ba ita ta samu bacci ya ɗauke taba sai misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, bayan ita ada ƙarfe takwas da ƴan mintuna ma tayi bacci.
Haka kuma ko da ta tashi a yau da tinanin abun da yay mata a zuciyar ta tashin.
Hakan ne yasa gaba ɗaya yau ɗin taji bata sha'awar futa ko daga cikin ɗakin ta ko kaɗan, balle har ta sake arba da wata fuskar ta ƙarasa tarwatsa mata zuciya da baƙin ciki.

Wannan dalilin ne yasa koda Bir yaje kan hanyar ya zauna har ya shafe sama da awa biyar ba tazo ba.
Hakan ne yasa ya miƙe cikin sanyi riƙe da kwari da gwafar sa a hannun sa zuciya duk ba dadi, yana mai komawa ɓangaren su.

*ENGLAND*
Cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa Billy ta tura kanta zuwa cikin É—akin su.

Hango Zee da tayi zaune akan kujera ne ya sanya ta sakin ihu da matuƙar ƙarfi, tana mai yin kanta a guje tare da faɗawa jikin ta tamkar zata karya ta.

Da matuƙar sauri Zee ta ɗago gare ta tana mai faɗin.
"A Beb meye haka? Lafiyarki É—aya kuwa da kike shirin karyawa Dady da Momy Autar su?"

"Ke Beb i got him! I got Prince Asad!
Finally he is my own know!"............... ✍

_CIKIN ABU UKKU TABBAS DAYA ZAI FARU, WATO DAI KO KU GYARA KU DINGA COMMENTS DA SHARHI, KO KUMA BAKAR MASARAUTA BOOK 2 YA ZAMTO NA KUDI, KO NA DENASA GABA DAYA, SABODA HAR YANZU LABARIN BAI DAU ZAFI BAMA, DAN HAKA ZABI YA RAGE GAREKU. KO A ADENA GABA DAYA, KO KUMA YA SAKE KOMAWA NA KUDI, KO KU FARA COMMENTS DA SHARHI_

*GA MASU BUKATAR SHIGA CIKIN GROUP DIN DA AKE POSTING, COMMENT DA SHARHI SAI KU TUNTUBENI TA WHATSAPP NMBER TA KAMAR HAKA. 08038135929*

*BY*
UMAR FARUQ*D

*BAK'AR MASARAUTA*

*NA*

UMAR FARUQ*D*

*PAGE 28*

"Kamar ya kin same sa? Waye kike nufin ya zama naki?
Please kiyi mun bayani yadda zan gane, saboda kwata-kwata ban fahimci abun da kalamanki suke nufi ba."
Zee ta fad'a cikin wani irin yanayi mai nuni da zallar mamaki da aljabin da suka rufe ta, tana mai sa hannu ta d'ago Billy daga jikin ta, tare da kafe ta da idanuwa.

Hakan da Billy taji ne ya sanya ta bud'e zip d'in jakar ta cikin sauri, tana mai zaro d'an katin da Yarima Asad ya hullo mata.
Kana ta mik'awa Zee shi ba tare da ta furta komai ba, sai zallar farin cikin da yake kance akan fuskar ta ta yadda har ya gaza b'oyuwa a fili.

Cikin sakin baki Zee ta mik'a hannu jiki a matuk'ar sanyaye, tana mai amsar katin ta rik'e sa acikin tafin hannun ta, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance k'ur akan katin, kafin daga bisani kuma ta d'ago tafin hannun ta tana mai kai sa kan idanuwan ta ta murza su sosai, a cewar ta ko idanuwan nata basu gane mata rubutun da tayi arba da shi ba akan katin dai-dai, domin kuwa ko a mafarki bata tab'a tinanin Billy zata samu karb'uwa a wurin Yarima Asad ba, duba da irin yawan 'yammatan da suke hauka akan sa, amma ko kallo basu ishe sa ba.
Chapter 69 · 0% Book details