Sashe 41
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta gama shafe sa da mai tas, sannan ta ɗauki hoda ta shafa masa akan fuskar sa, tukun ta miƙa sa zuwa hannun wani mutumi da yake zaune a gefen ta shima da irin shigar su ta Bayi.
Karɓar yaron yayi a hannun sa, sannan ya juya ɓarin sa na dama yana mai janyo wata ƴar ƙaramar roba a kusa da shi, tukun ya buɗe murfin robar.
Wani baƙin abu ne mai kama da baƙin fenti a cikin ta, sai kuma tambarin Baƙar Masarauta ɗan ƙarami na soso, da yake a cikin baƙin fentin.
Hannun sa na hagu yasan ya a cikin robar yana mai zaro soson, sannan ya futo da shi waje yana mai manna sa akan farar fatar jinjirin.
Take kuwa tambarin masarautar tasu ya futo ɗas a jikin sa baƙiƙƙirin da shi, haka mutumin yay ta manna masa tambarin a fatar sa har kan fuskar sa, sai da ya tabbatar da ko ina tambarin ya futo, tukun ya janyo wani ɗan mitsitsin baƙin wando na yadi irin na jarirai, yana mai ɗago jinjirin, sannan ya sanya masa shi a jikin sa, kana ya buɗe baki yana mai faɗin. "Daga yau za'ana kiran sa da suna BIR, domin kuwa shine sunan da aka raɗa masa." Ya ƙarasa maganar yana mai miƙawa Iyar Bayi shi.
Miƙo hannun ta tayi ta karɓe sa fuskar ta ɗauke da tsantsar far'a, tukun ta janyo wani sabon farin yadi tana mai sanya sa a ciki, ba tare da tasa masa ko riga ba, kamar yadda sauran bayi mazan wurin suke duka, babu mai riga a jikin sa.
Kallon yaron tayi tana mai sakin murmushi, yayin da shi kuma yake ta faman yin wutsi-wutsil da ƙafafuwan sa, yana mai kallon wurare daban-daban, alamun yana cikin ƙoshin lafiya kenan.
Sosai yaron ya ƙara girma da wayo a sati ɗayan da yayi kawai a duniya, ko kaɗan basa da damuwar komai, domin kuwa da zarar yayi kuka Iyar Bayi take ɗaukar madara ta basa, sannan kuma tasa zani ta goye sa a bayan ta idan ya gama sha.
Fari ne kar yadda kasan a taɓa sa jini ya ɓullo, kyakkyawa ne sosai, domin kuwa ko kaɗan basa da makusa ta ko ina jinjirin, hakan yasa su kansu sauran Bayin suke matuƙar sonsa, sannan kuma kowa yake mararin ɗaukar sa.
Miƙewa Iyar Bayi tayi tsaye da ɗan a hannun ta, tana mai faɗin. "Suna yayi daɗi, dan haka bara muje ashelan tawa jama'a, a kuma shiga tsakiyar fili ai rawar suna da jinjiri." Ta ƙarasa maganar tana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Kai tsaye ta doshi wurin da sautin kiÉ—a ke tashi, kasancewar anan ne ta hango dan-dazon jama'a maza da mata suna rawa.
Itama rawar ta farayi tun daga wurin da take tana tafiya, a haka har ta ƙarasa cikin filin hannun ta riƙe da Ɗan.
"Kai ku gafara nan gamu nan mun iso, suna ya raÉ—u yaro zama *BIR*." Ta faÉ—a tana mai kutsawa cikin filin rawar.
Take kuwa a wurin kiÉ—a da rawar da ake suka sauya salo, yayin da jama'ar wurin kuma keta sakin tafi da rawa suna zagaye Iyar Bayi da jinjirin a tsakiyar su, bakunan su na furta.
"Barka da zuwan BIR! Marhabun da zuwan BIR."
Haka suke ta faɗe suna zagaye Iyar Bayi da jinjirin da matuƙar ƙarfi, sunayi suna sakin tafi.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Yau take ranar suna a cikin Wasarutar Wasai, hakan yasan ya ko ina ka kalla a cikin Masarautar kake ganin jama'a tun daga kan hadimai, kuyangu suna ta giftawa ta ko ina.
Yayin da sautin bushe bushen sarewa, algaitu, kakaki, kiɗan ƙwarya, harma da tambura keta tashi a cikin wurare daban daban na masarautar.
Ga kuma yadda bayi keta wucewa da niƙi-niƙin abinci kala-kala afarantai ta ko ina, sannan ga mutane da suke ta hucewa akan dawakuna sunci uban kwaliyya a jikin su, kamar yacce suka tsan-tsarawa dokunan nasu kwalliya.
Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, tun daga harabar part ɗin nata zakaci karo da maroƙa suna ta faman sakin kiɗa tare da kirare-kirare da matuƙar ƙarfi.
Faɗi suke. "Allah ya raya mana Ahmad ɗan gidan Abdallah jikan Ahmadu, ɗan gidan sa'a haihuwar sa'a jikan sa'a, fari farar aniya, jinin sarauta kafu ƙarfin raini, Ɗa ga gimbiyar mata, shugabar kyawawa kuma uwar Sarkin gobe, Ahmadu jinin alkhairi haihuwar nasara, ƙani ga Sarkin mu na gobe Usmanu Babban Yaya.
Allah ya raya mana Ahmadu Asadullahi Zakin Allah, mai Kakkani da yawa, mai Iyaye lodi-lodi, mai Yayye bila adadin. Kakan ka Ɗan Sarki Ubanka Ɗan Sarki, Mamar ka Ƴar Sarki kaima kuma Ɗan Sarki."
Haka suke ta sakin kirari da bushe-bushe da matuƙar ƙarfi, kasancewar an riga da an raɗa suna tun asubahi, yaro yaci suna Ahmad, wato sunan Mahaifin mai martaba, hakan yasa tun a wurin mai martaba ya ƙara masa da wani sunan akai wanda za'ana faɗa masa, wato ASAD, ma'an ZAKI kenan.
Hakan kuwa ba ƙaramun tafasa zuciyar magautan su ya sakeyi ba, barin ma yadda suka ga mai martaba na wani irin farin ciki da samuwar yaron, yadda kasan akan sa aka farayi masa haihuwa, ga kuma labarin da suka ji yana yawo, na cewar mai martaba da kansa yace yau akwai hawa irin hawan da ba'a taɓa yin sa ba a suna, za'ayi kilisa kalar kilisar da ba'a saba yin ta ba yau da yamma.
Hakan kuwa ba ƙaramu sake lona musu rai yayi ba, sannan kuma suka ɗauki alwashin ganin bayan jinjirin nan kota halin ƙaƙa ne.
Acan cikin É—akin Gimbiya Fulani kuwa zaune take a gefen gadon ta taci uban Ado mai tsananin kyau da É—aukar hankali da abubuwan kuÉ—i.
Sanye take da wani ɗan ubansu farin less, mai ratsin adon baƙi a jikin sa da yayi matuƙar amsar jikin ta, dinƙin riga da zani da ɗan kwali, sai wasu irin saraƙunan gwal da suke manne a jikin kunnuwan ta da wuyan ta, suna ta faman ɗaukar ido, ga wani irin azababben ƙamshin turarruka masu matuƙar daɗi da suke futa daga cikin jikin ta.
Yayin fa shi kuma Ɗan jarari Asad yake riƙe a hannun Hadima Larai, da itama taci uban Ado tana mai sake canza masa wasu kayan, sabo da futar da za'a sake yi da shi, harma da Gimbiya Fulani, sabo da yanzu aka aiko cewar mai Martaba yace su shirya su futo harabar gida za'ayi musu hotuna a tare.
Hakan yasa ake canza masa wasu sababbun kayan, duk da dai waÆ´an can na jikin nasa da aka cire masa suma basu fi minti goma ba duka da sanya masa su É—in.
Sosai yaron ya ƙara girma da kyawu asati ɗayan da yayi a duniya.
Kamar shi É—aya sak da mahaifiyar sa, basu da bam-banci ko kaÉ—an.
Cikin ƴan sakanni ta gama sanya masa kayan tas har takalmi, tukun ta ƙara fashe sa da wani haɗaɗɗen turare mai tsananin ƙamshi na jarirai.
Tukun ta miƙowa Gimbiya Fulani shi, da itama ta miƙe tsaye tana mai yafa wani haɗaɗɗen mayafi a jikin ta.
Karɓar sa tayi a cikin lafiyayen showel ɗin sa, tukun ta fara takawa tana mai dosar hanyar waje.
Tana futa tabi wata ƙofa dake a cikin ɗakin nata, wacce zata sadata da part ɗin mai Martaba kai tsaye, domin kuwa da aka tashi tsara ginin gidan, sai da yasa akayi masa hanyoyin da zasu kaisa duka ɓangaren matan nasa ukku daga cikin part ɗin sa, ba tare da ya futa ta babbar ƙofa ba.
Baifi minti goma tayi ba da shigar ta, sai ga sunan sun futo a jere ita da mai Martaba, ga kuma Babban yaya da yake daga bayan su da irin shigar mai martaba sak a jikin sa.
Sanye suke da farar shadda mai tsananin kyawu da tsada, banda ƙyalli da ɗaukar ido babu abun da take yi, yayin da kawunan su kuma suke ɗauke da baƙaƙen tare da farin rawani, kamar yacce takalman ƙafafuwan su suka kasance baƙaƙe suma, sai kuma wata haɗaɗɗiyar baƙar al'kyabba mai adon fari da take sanye a jikin su, su duka biyun.
Haka suka cigaba da takowa mai Martaba rungume da Asad a hannun sa.
Suna shigowa Babban falo gaba ɗaya matan dake zaune a cikin sa suka rangaɗa wata mahaukaciyar buɗa mai tsananin ƙara, suna masu miƙewa tsaye.
Yayin da masu hotuna kuma suka fara ɗaukar su tun daga nan tare da video, a haka har suka ƙarasa harabar gidan.
Suna futowa maroƙa da fadawa sukayo kan su gaba ɗaya, ko wanne da kalar kirarin da yake yi gare su.
"Barka da futowa Asadullahi, barka da isowa Zakin Allah, barka da isowa Yariman Wasai!
Yarima Damisan Yan Sarki, Yarima ÆŠan masu gari, ÆŠan bakin ruwa da ciyawa, ÆŠan uban gabasawa."
Gaba ɗaya maroƙan dake wurin suka faɗa a tare, suna masu sakin kiɗa duk alokaci ɗaya, yayin da su kuma Fadawan Sarki da suke tsaye a harabar wurin suka matso gare su da sauri, suna masu zagaye su, bakunan su na futar kalmomin. "Barka da futowa Sarkin Sarakai, barka da futiwa toron giwa! Sakaka Baban baƙo! Uban gabasawa!
Taka lafiya barden mahadi!
A Lafiya bahau da wani ba saukan wani!
Lafiya hana kangara!
Lafiya bango madafar Bayi!
Lafiya hadarin ƙasa maganin mai kabiɗo!
Lafiya dubu jiran mutum É—aya!
Lafiya gagara gasa!
Uban Yarima Usmanu, Uba ga Asadullahi sabon yaro, miji ga kyakkyawar Gimbiya mahaifiyar Sarkin mu na gobe.
Taka a lafiya jinjirin wata shakallo."
Fadawan keta faɗe suna masu binsu a baya, a haka har suka ƙarasa wurin da za ayi musu hotunan, tukun suka kauce suka bada wuri aka dinga musu hotuna kala-kala, sannan kuma da mutane daban -daban, domin kuwa harda su Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina sai da akayi musu hoton tare, duk da dai ko kaɗan bawai dan ransu yana soba suka tsaya akai hoton, sunyi ne kawai gudun kar suƙi zuwa mai Martaba ya zargi wani abun, kasancewar shi da kansa ya aika a kira su suzo ayi hoton.
Haka dai aka yini shan-shagalin suna a cikin gidan har zuwa yamma.
Tukun aka sake sabon shiri, sabon wanka, sannan kuma a kayi sabuwar futowa ana tafiya filin Hawa, kasancewar dama da yamna aka tsara za'ayi Hawan sunan.