← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 79

Sashe 59

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tabbs kuwa, kuma Prince É—in ma na cikin Jaharku, wato É—an gidan Sarki Abdallah ne, Sarkin Wasai."
Zeee ta faÉ—a tana mai cigaba da kallon Billy.
Yayin da ita kuma ta buÉ—e baki fuskar ta É—auke da murmushi, tana mai faÉ—in.
"Kice abun zai zamto mai sauƙi ma a gare ni.
To duk ba wannan ba ma, koma waye ne shi É—in, to yana gab da zama nawa, domin kuwa kallo É—aya nai masa ya tafi da komai nawa, kuma ayanzu haka ina jin zan iyayin komai akan sa."

Wani irin kallon rainin hankali Zee tabi Billy da shi baki asake, tukun daga bisani ta saki wani shegen murmushi, irin wanda ma'anar sa take nufin da wanda aka yiwa shi É—in bai san kansa ba, wato shi da mahaukaci duk É—aya suke.
Kana daga bisani ta tsaya da murmushin da take tana mai buÉ—e baki, idanuwan ta a cikin na billy tace.
"Shin kin san abun da kike faÉ—e kuwa Billy?
Ko da yake bazan ga laifin ki ba dan kinyi irin wannan furucin akan Asad, sabo da ke É—in sabuwa ce baki san komai daga cikin halayyar saba, amma shawarar da zan iya baki a yanzu ita ce, ki gaggauta kawar da wannan abun daga cikin zuciyar ki tun kafin yayi zurfi, domin kuwa dubun ki sunyi irin haka, koma nace fiye da haka, kuma har yanzu suna kanyi amma har yau babu nasara akan Prince."
Zee ta faÉ—a babu alamun wasa a cikin magan-ganun nata idanuwan ta a cikin na Billy.
Yayin da Billy kuma ta rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi tun lokacin da Zee tace akwai dubbanta, kana yanzu ta buɗe su har sun ɗan sauya launi daga fari zuwa ɗan ja, sannan ta buɗe baki cikin muryar gaskiya da gaskiya, tana mai faɗin.
"Please Zee daga yau karki ƙara danganta sa da wasu matan muddin ina tsaye a wuri, domin kuwa ni ɗin nan da kika gani ina da zazzafan kishi akan abun da nake so, kana kuma dan su sun buga sun kasa ba shi ke nufin nima zan kasa ba, domin kuwa sunbi nasu salon ne, haka nima zanbi nawa salon wanda kuma ba lallaine ya zamto ɗaya da wanda suka bi ba.
Abu É—aya kawai da zan sake mai maita miki shine, na gansa ina son sa, kuma wallai tallahi sai na bar tarihi tunda har ance wasu sun kasa."
Billy ta faÉ—i haka da tsantsar gaskiyar ta tana mai kallon Zee.
Yayin da ita kuma Zee ta fara girgiza kai tana mai jifan Billy da kallon tabbas bakya cikin hayyacin ki, domin kuwa babu wata hallayar Asad wadda bata san labarin ta ba, kana tasan Ƴammata da dama waƴan da sukafi Billy komai da komai da suke hauka akan sa, amma ko kallo basu ishe sa ba, hakan yasa ta buɗe baki tana mai faɗin.
"Shin kin san inkiyar sa ma kuwa?"
Ta faɗa tana mai ƙara sakin murmushin rainin wayo, tukun ta ɗora da cewar.
"Baka so sai dai asoka! Haukata Ƴammata su yini su kwana suna dambe! Sanya ƙawa da ƙawa gaba!
Wannan shine iƙirarin da abokanan sa hausawa suke masa a cikin school ɗin nan."

"Tabbas kuwa lokacin ɓacewar sunayen ne yazo, domin kuwa tabbaci nake baki akan sai ya koma na Billy bada kan ka asar..."
"Hhhhhhhhhhhhhh!" Zee ta kwashe da wata mahaukaciyar dariya wacce ta sanya Billy dakatawa da maganar da take kanyi dan dole tana kallon ta, ba tare da ta kai ƙarshe ba.
Tukun daga bisani kuma ta gimtse dariyar ta lokaci guda, kana ta ɗaga kafaɗun ta sama tana mai taɓe baki tace.
"Any way naji yanzu kuma zanjira lokaci, dan haka please let us go ko mayi abun da ya kawo mu."
Zee ta faÉ—a tana mai yin gaba.
Girgiza kai Billy tayi tana mai bin bayan Zee da kallo, domin kuwa ba ƙaramun shaƙa tayi ba da dariyar da tai mata, tukun daga bisani itama ta ɗaga ƙafafuwan ta tana mai rufa mata baya.

Tun daga wannan ranar ta fara bin diddigin Yarima Asad, ya zamto duk wuraren da yake zuwa itama tana nan, haka zataci uban ado da ƙana-nan kaya tazo wurin daniyyar ta tun kare sa da batun abun da ke cikin ranta, amma sai dai kuma har kawo yau da aka ɗauki tsawon wata ɗaya da haɗuwar su ta farko bata iya zuwa ta tsaya ko agaban sa ba, ballan tana ta kaiga faɗar abun da take son faɗen, sabo da wani irin kwarjini da take ganin yana mata akullum idan ta ƙudir ta zuwa gare san.

Cigaba da tsayuwa tayi a wurin da take tana mai kallon sa, wata zuciyar nace mata taje kawai koma mai zai faru ya faru, yayin da wata zuciyar kuma take tunasar da ita kalaman Zee akan hallayar Asad da kullum take faÉ—a mata.

Sanye take da black jeans tare da wata ƴar red top ajikin ta, sai wani mahaukacin red hill shoe mai matuƙar tsini da yake sanye aƙafar ta, yayin da gashin atach ɗin da yake tufke akan ta kuma ya kasance zube agadon bayan ta.
Yafe take da wani ɗan mitsi-tsin mayafi da ya tsaya iya kar kan ƙirjin ta akan ta, sai ƴar ƙaramar jakarta wacce ta kasance ta mahaɗin takalmin ƙafar ta da take riƙe a hannun ta.

Acan kuwa ɓangaren Asad hankali kwance yake sipping ɗin copy ɗin sa, yana yi yana latsa wayar sa, sosai yake matuƙar jin daɗin wurin, sabo da yadda ya kasance tsit babu hayaniya, domin kuwa nan ɗin shine ya kasance vip na cikin wurin, ga kuma yadda wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi take dukan jikin sa, ta yadda har kwantaciyyar baƙar sumar da tayiwa hannuwan sa da ƙauri-kan sa ƙawanya take kaɗawa.

Billy na tsaye awurin nan taga giftawar wata baturiya da taci uban ado ta gaban ta, hakan ne yasa ta bita da kallo domin taga wurin da zatayi, ai'kuwa direct taga ta doshi wurin da Prince Asad yake cikin yauƙi.
Take kuwa a wurin Billy taji gaban ta yayi wata irin mahaukaciyar faɗuwa, kana taji wani irin abu ya caki zuciyar ta, bata gama jin wannan baƙin cikin ba idanuwan ta suka hango mata wannan baturiyar a gaban Yarima Asad.

Take kuwa jikin ta ya fara wata irin karkarwa, idanuwan ta na canza launi.

Yayin da ita kuma wannan baturiyar da ta ƙarasa gaban Yarima Asad, ta miƙa hannun ta ahankali zuwa kan mug ɗin da yake riƙe a hannun sa, tukun ta amshe sa tana mai ajiye sa akan plate ɗin da yake akan table ɗin dake a gaban sa.

Yana jin duk abun da take yi kuma ya gane ta, amma yaƙi daga kai ya kalle ta.
Yayin da ita kuma ta sake matsawa gare sa, tana mai ɗaukar hannun ta-ta ɗora su akan kafaɗun sa, tukun ta farayin ƙasa da kanta a hankali, tana mai kai fuskarta kan tasa.
"Hlo Baby!"
Ta faɗa ƙasa-ƙasa tana mai busa masa iskar bakin ta akan fuskar sa, tukun ta cigaba da matsar da fuskar ta zuwa ga tasa tana mai haɗe tsinin hancin ta da nasa, kana ahankali ta juya mazaunan ta tana mai zama akan cinyar sa, tukun ta haɗe lips ɗin ta da nasa wuri ɗaya.

Da matuƙar ƙarfi Billy ta rumtse idanuwan ta sabo da abun da ta gani, jikin ta na wata irin karkarwa..!

*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Abubuwa da yawa sun faru a cikin shekarun da suka gifta, na daÉ—i dana kishiyar sa a cikin masarautar.

A yanzu haka Bir yana da shekaru Ashirin da takwas zuwa da tara ne a duniya.
Sosai yake da tsananin kyau mai matuƙar ɗaukar hankalin duk wanda ya gansa, duk da kasancewar sa Bawa.
Fari ne kar tamkar a taɓa sa jini ya ɓullo, yana da manya-manyan fararen idanuwa masu ɗauke da baƙar ƙwaya wulik acikin su, yayin da karan hancin sa kuma ya kasance dogo, da yayi matuƙar ƙara ƙawata fuskar tasa, sai kuma ɗan ƙaramin bakin sa da yake ɗauke da jajayen laɓɓa akan sa, yayin da fuskar tasa kuma duka ta kasance zageye da wani irin baƙin saje mai tsananin laushi, da yayi masifar yi masa kyau.
Kana yana da wata iriyar suma mai matuƙar yawa da laushi, ga kuma baƙi, duk da dai bata kasance tana samun wani gyara ba, amma a hakan ba ƙaramun kyau take masa ba, domin kuwa tsabar yawan ta har kan kafaɗun sa sai da ta sakko.

Har kawo yau yana nan da maitar kwari da gwafar sa, kana kuma afannin taurin kansa ma babu abun da ya sauya.

Tun a wancan lokacin na shearun baya da Gimbiya Tasmir ta fara tasawa yake son su haÉ—u gaba da gaba ita, amma har kawo yau da ita kanta take da kusan shekaru Ashirin a duniya Allah bai haÉ—a su ba, gashi kuma a yanzu yana jin labarin abubuwan da takeyi da suka ninka na da, hakan ya sanya a kullum yake burin haÉ—uwar sa da ita gaba da gaba, domin yaga abun da zatayi akan sa.
Wannan dalilin ne ma yasan ya-ya samu abokan sa da suke tare ya tambaye su wuraren da take zuwa acikin masarautar, ba dan komai ba kuwa sai domin yaje ya tsaya akan hanyar da take wucewar, kasancewar kusan kullum a daji yake yini wurin harbe-harben sa, shi yasa bai taɓa cin karo da ita ba, sai dai idan ana wani biki acikin masarautar ya ganta, hakan yasa gaba ɗaya ya dena futa daji a ƴan kwanakin -nan, yake zaman sa a wurin su Mauzum, kullum yana hanyar da take bin domin su haɗu, sai dai kuma har kawo yau ita kuma bata biyo hanyar ba, da alamun dai ta kwana biyu bata futo shan'iska ba kamar yadda ta saba.

Zaune yake a gaban Iyar Bayi cikin ɗakin ta na iccina ya tanƙwashe ƙafafuwan sa yana kallon ta.
Yayin da ita É—in ma take zaune a gaban sa tana kallon sa, gaba É—ayan ta duk a wani rikice, da alamun dai babu natsuwa tattare da ita a yanzun ko kaÉ—an.
Chapter 59 · 0% Book details