Sashe 38
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aɓangaren Hadima Larai kuwa cigaba da tafiya tayi tana mai sakin kalamai iri-iri, hannun ta ɗauke da jinjirin da yake ta aikin tsala kuka ko wanka ba ayi masa ba, tana mai nufar hanyar da zata sadata da wurin buga Tambarin murna, kasancewar haka al'adar gidan sarautar nasu take, muddin wata daga cikin matan gidan suka haihu, to da zarar an yanke wa abun da aka haifa cibi za'a ɗauke sa a tafi da shi wurin buga Tambari, shi kuma wannan Tambarin shine ke sanar da duk jama'ar dake cikin masarautar haihuwar, sabo da tsananin ƙarar sa, sannan kuma bawai kai tsaye ake bugasa ba da zarar an kai jinjiri, a'a sai sun fara dubawa sun ga namiji ne ko mace, tukun a ɗauki makaɗi a fara bugasa, kasancewar kowane jinsi yana da kalar bugun da ake masa, tayarce da zarar an buga sa mutanen dake cikin gidan suke fahimtar jinsin dlƊan da aka samu, mace ko namji ta hanyar kiɗan.
"Ayiri-yiri-yiririiiiiiiiiiiiiii."
Hadama Larai ta sake rangaÉ—a buÉ—a a dai-dai lokacin da ta shiga wurin, tana mai girgiza jinjirin da yake ta ai'kin tsanyara kuka shima.
Kafun kace tak, tuni mutnen da suke zaune cikin wurin sun futo da tsantsar gudu.
Tun kafin su ƙaraso wurin da take ta yaye showel ɗin dake ƙudun-dune a jikin jinjirin, tana mai ɗaga jaririn sama tayi musu nuni da shi.
Take kuwa wani dattijon tsohon mutum da yake sanye da babbar riga a jikin sa ya juya yana mai dosar wurin da wasu manyan ƙarafuna suke a kafe jikin bango, wato Tambarin murna.
Durƙusawa yayi ƙasa yana mai sa hannu ya ɗauki wani ƙarfe mai kama da taɓaryar ƙarfe, amma sai da shi wannan dogo ne sosai, tukun ya ɗago yana mai ɗaga sa ya fara dukan Tambarin farko da yake a ɓangaren wurin da yake a tsaye, wato na namiji kenan.
Take kuwa wani irin sauti mai daɗi ya fara tashi da matuƙar ƙarfi, tayarce har sai da ya karaɗe ko ina na cikin masarautar, yayin da su kuma mutanen dake cikin wannan hurin suka toshe kunnuwan su suna rawa tare da kaɗa manyan rigunan su, sabo da yadda sautin yake ratsa har cikin kwanyar su.
Ita kuwa Hadima Larai cigaba da É—aga Jinjirin nan sama tayi tana mai rawa a tsakiyar filin hurin, yayin da shi kuma jaririn keta aikin tsanyara kukan sa.
A ɓangaren Gimbiya Huwaila kuwa tashin ta kenan daga kan gado taji sautin bugun tambarin samuwar yaro namiji na dukan kunen ta.
Wata irin zabura tayi tana mai miƙewa zaune daga kwancen da take akan gado, tukun daga bisani ta fara girgiza kanta tana mai faɗin.
"Inaaa bazai yuwu ba Wallahi Tallahi, shin me bugun tambarin ÆŠa namijin da kunnuwa ne suke jiyo mun yake nufi kenan?"
Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai miƙewa tsaye, tukun ta duro daga kan gadon da take yarce kasan wata zararriya.
"ÆŠa namiji acikin gidan nan kuma? Shin dama akwai wata mai cikin ce bayan Fulani agidan nan ne da har kunnuwa ne suke jiyo mun sautin bugun tambarin ÆŠa namiji?"
Ta sake faÉ—a tana mai juyi acikin É—akin nata cikin tsantsar tashin hankali.
"A'a, babu wata bayan ita dake da ciki a cikin gidan nan, kenan hakan na nufin itace ta haifo Yaro namiji kuma yazo da ransa?
Inaaaa!!!! Hakan bazai yuwa ba, Wallahi Tallahi ƙarya ne..."
Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kama hanyar waje!
Æangaren Gimbiya Suwaiba matar mai martaba ta biyu kuwa, futowar ta kenan daga cikin bathroom bugun tambari samuwar yaro namiji acikin masarautar tasu ya daki dodon kunnen ta.
Da matuƙar sauri ta dafe bangon ɗakin ta, sabo da yarce taji ƙafafuwan ta sun zame tana shirin kifawa ƙasa, tukun daga bisani ta koma tana mai zama yaraf a ƙasa, wato zaman daɓaro, tare da ɗora hannuwa biyu aka.
A ɓangaren Jakadiya kuwa tamkar a mafarki taji bugun tambarin samuwar Ɗa namiji na dukan kunnuwan ta, kasancewar ita bata kaiga tashi ba a lokacin.
Ahankali ta fara buɗa idanuwan ta tana mai yamutsa fuska, kafin daga bisani kuma tayi wata irin miƙewa tsaye daga kwancen da take zumbur tana mai zaro idanuwa waje, tare da dafe ƙirjin ta da hannu, sabo da yadda ta jiyo sautin na dukan kunnen ta da matuƙar ƙarfi, alamun ba mafarki take ba a zahiri abun ke faruwa kenan.
"ÆŠa namiji?...Gimbiya...Fulani?..ta sake haihuwar sa yanzu ma?"
Ta faɗi magan-ganun a rarrabe, sannan kuma ta sigar tambaya, tana mai zaro idanuwanta waje, tukun daga bisani ta juya tana mai miƙa hannun ta ta janyo mayafin ta da tsantsar sauri, sannan ta durƙusa ƙasa tana mai ɗibar takalman ta a hannu ba tare data tsaya sanya su ba, ta doshi hanyar waje tamkar ta kifa a ƙasa sabo da saurin da takeyi.
A ɓangaren mai martaba kuwa futowar sa kenan daga bathroom ya ɗauro alwala, sautin bugun tambarin samuwar Ɗa namiji ya daki dodon kunnwan sa.
Cak ya tsaya a inda yake yana mai sakin baki da kunnuwa, kai harma da hanci, sabo da yarce yaji abun tamkar al'mara a kunnuwansa, yayin da shi kuma sautin nan ke cigaba da tashi da matuƙar ƙarfi ko kaɗan ba'a da niyyar denawa.
Sai da ya É—auki kimanin mintina tsawo biyar yana tsaye a wuri É—aya, tukun daga bisani yayi firgigit ya dawo hayyacin sa yana mai furta kalmar.
"Al'hamdulillah! Alhamdulillahi!! Alhamdulillah!!!"
Kafin daga bisani kuma ya durƙusa ƙasa yana mai kai goshin sa ƙasa yayi sujudu shukur ga rabbil izzati, sannan bayan ya gama ya ɗago idanuwan sa na zubar da ƙwallar murna, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Masha Allah, ashe nima ina da rabo sake haihuwar ÆŠa namiji a duniya, ashe wannan dalilin ne ya hana Fulani zuwa wurina jiya bayan nasa jakadiya ta kira ta, kai Alhmadulillahi rabbil alamin."
Ya faɗa cikin tsantsar murna yana mai miƙewa tsaye ya doshi hanyar waje, daga shi sai jallabiya ajikin sa ko al'kyabba bai yafaba kamar yacce ya saba ako da yashe, sabo da tsantsar farin cikin da ya tsinci kansa aciki wanda ya mantar da shi wata alkyabba ma.
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Da matuƙar sauri Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Ta haihu, dan haka kuyi maza maza ku shiga ciki ku anso mun shi tun kafin ta fara sabo da shi, domin kuwa wannan Yaron badan ita Ubangiji Gargabilu yayo saba, yayo sane domin mu."
Atare mutanen cikin jirgin suka fashe da kuka hatta da mazan dake ciki, sabo da jin furucin Sarki Barbaru da sukayi yana yi akan ÆŠan da ya diro duniya yanzu -yanzu.
Yayin da shi kuma jaririn ke aikin tsanyara kuka da matuƙar ƙarfi yana mai ciccila ƙafafuwan sa sama.
Cikin sauri matan nan suka fara ƙoƙarin gyarawa Aishatu jikinta, sabo da jin furucin Sarki Barbaru da sukayi, domin kuwa sun san da zarar mutanen sun iso zasu kwaye zannuwan da sukai mata sutura da su.
Yayin da ita kuma Aishatu ta miƙa hannu da sauri tana mai shirin ɗaukar ƙatoton farin jaririnta mai tsananin kyau a ƙasa, wanda ada duk suke tinanin cikin sa bai huce wata takwas ba, sai kuma gashi a yanzu take ganin girman Ɗan yafi ƙarfin a kira sa da Ɗan wata twakas.
Hannuwan ta suna tsantsar rawa, kamar yadda jikin ta ke rawa ta miƙa su tana shirin ɗaukar jaririn dake cigaba da tsanyara kuka tare da cilla ƴan ƙafafuwa sama, amma sai dai kuma hannun nata yana daf da kaiwa jikin Ɗan taji ansa ƙafa an make sa da matuƙar ƙarfi, tayarce har sai da ta tuntsira baya tana mai faɗawa jikin Ishaƙ da yayi saurin tarota, kasancewar babu ƙwari jikin nata ko kaɗan.
Wani danƙareren baƙin badakare ne da yake riƙe da zureriyar takobi a hannunsa, yasa ƙatuwar ƙafar sa ya bige hannun nata da ita, tukun ya durƙusa ƙasa yana mai sa hannu ɗaya ya tallabo jinjirin da yake ɓace da jini zuwa jikin sa.
Wata irin gigitattar ƙara Aishatu ta saki tana mai miƙewa tsaye tayi kan mutumin nan, tare da buga tsalle ta shaƙi wuyan sa yadda kasan ba itace ta haihu yanzu ba, domin kuwa lokaci ɗaya gaba ɗaya taji ciwon da takeji a jikin ta ya ɓace ɓat, sai ma wani irin ƙarfi da taji yazo mata, tayarce har take jin zata iya yaƙar uban kowa akan jinjiri nata.
Guiwar hannun sa badakaran nan yasa yana mai dukan cikin ta da ita.
Take kuwa ta saki wuyan sa tana mai yin baya luuu ta kifa akan jikin IshaÆ™ da yayi saurin matsawa wurin da take, a lokacin da take shirin faÉ—uwa.
Banda aikin kuka tamkar ransa zai futa babu abun da yake iyawa, yayin da ita kuma Aishatu ta faɗa jikin sa tana mai wani irin zare idanuwa, tare da taunar leɓen ta da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani ta saki leɓen nata tana mai buɗe baki tana wuri-wuri da idanuwa, gaba ɗayan ta ta fuce daga hayyacinta, sabo da yadda cikin ta yayi wata irin ƙullewa ta sanadin dukan da mutumin nan ya mata.
Banda koke-koke babu abun da ke tashi a cikin jirgin, domin kuwa zuwa yanzu babu wani mahaluƙi dake cikin jirgin da ya iya cigaba da riƙe kukan sa.
Wata irin ƙara Aishatu ta ƙara saki tana mai sake miƙewa zumbur, a lokacin da idanuwan ta suka hango mata badakaran nan yana tafiya ɗauke da jinjirin ta a hannu da yake ta tsala kuka.
Da sauri Ishaƙ ya miƙe tsaye shima yana mai shirin riƙota, amma tuni ta funcike hannun ta tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta a guje ta nufi hurin da ta hangi mutumin nan.
Da sauri wani badakare ya tare ta ta hanyar tsayawa a gaban ta, tare da babbake wurin da yayi.
Yayin da shi kuma wannan badakaran da yake riƙe da jaririn ya fuce daga cikin jirgin duka yana mai dosar shimfiɗar da Boka mai wutar kasko tare da Sarki Barbaru suke, hakan da Aishatu ta gani ne yasan ta ya ta sake sakin wata irin ƙara mai matuƙar ƙaraji tana mai girgiza kanta, tukun daga bisani ta ɗaga ƙafar ta ɗaya daniyyar ta sake zurawa a guje, amma sai gaba ɗaya ta koma tayi baya luuu, tana mai zubewa a ƙasa sumamma!