← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 79

Sashe 27

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Gaban wani tafkeken dutse Bir ya watsar da iccinan, yana mai komawa jikin sa daga gefe ya durƙushe aƙasa tare da rumtse idanuwan sa da tsantsar ƙarfi.

"Shin ka shirya faɗamun amsar tambaya ta ayau, ko kuwa har yanzu taurin kan naka bai ƙare ba ƙasƙantaccen Bawa mara galihu!"
Sautin muryar ta ya daki dodon kunnen sa ba tare da yay zaton jin saba.
Take awurin kuwa yaji wata irin jarumta ta zomasa agaba É—aya ilahirin jikin sa.

Ahankali ya fara ɗago ƙwayar idanuwan sa yana mai sauke su akan fuskar ta, tukun daga bisani ya mayar dasu zuwa kan ɗan ƙaramin bakin ta da take futar da munanan kalamai akan sa daga cikin sa.
Wani irin abu yaji yana fuzgar sa zuwa gare ta wanda bai taɓa jin makamancin sa ba, hakan ne yasa ya sake kafe ɗan ƙaramin bakin ta da idanuwan sa yana mai cigaba da kallon yarce take motsa su, tare da yarce jajayen laɓɓan dake akan su suke futar da ƙyallin man leɓen da aka shafa musu alokacin da ake mata kwalliya.

Ko kaɗan bai san lokacin da ya fara yunƙurin miƙewa ba, sai dai kawai jin sa da yayi tsaye akan ƙafafuwan sa, sabo da yarce yake jin wani irin abu na fuzgar sa zuwa gare ta, ta sanadin jajayen laɓɓan ta da yake kallo.

Ahankali ya fara ɗaga ƙafafuwan sa da suke tsartuwa jini yana mai dosar inda take.
Yayin da ita kuma ta kafe sa da idanuwa tana mai yin shiru dan taga abun da zai aikata da ya miƙe yayo kanta
Ganin da tayi yana gab da haÉ—e jikin ta da nashi ne ya sanya ta fara ja da baya da baya ba tare da tasan lokacin da ta fara yin hakan ba tana mai kallon cikin idanuwan sa.
Yayin da shima ya cigaba da biyo ta har lokacin idanuwan sa ƙur akan laɓɓan ta, ahaka har ta ƙarasa jikin bango.
Cigaba da matsawa yayi gare ta gadan -gadan.
Dasauri ta kalle sa tun daga saman sa har zuwa ƙasa, tukun ta sake sauke idanuwan ta akan faffaɗan ƙirjin sa da yake cike da yalwatacce gashi akan sa, gashi dama babu riga ajikin sa.
Wata irin faɗuwar gaba taji ta ziyarce ta wacce bata taɓa jin makamanciyar taba dan suna tare da shi, hakan yasa ta buɗe baki cikin tsawa tana mai faɗin. "Dakata! Dakata nace maka ƙasƙantacce!!!"

Wani irin kyau ya ƙara ganin laɓɓan ta sun masa acikin idanuwan sa, sabo da yarce ta ɗaga su, hakan ne yasa sa cigaba da nufar ta har ya zamto yazo gab da ita, tayarce har ƙirjin sa da nata suka fara tokarar juna.

Dasauri tayi gefe tana mai shirin hucewa tanan, amma sai Bir yayi sauri ya sanya hannun sa dake futar da jini akan bangon yana mai tokare hanyar da shi, ya zamto bata da hanyar wucewa ko kaɗan, tukun ya sake sanya ƙirjin sa yana mai danne nata da shi, sannan ya fara matsar da fuskar sa ahankali zuwa ga tata idanuwan sa ƙur akan laɓɓan ta.

Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta adai dai lokacin da taji saukar tausasan laɓɓan sa akan nata, tukun ta dunƙule tafin hannun ta tana mai yin w.................✍

*KAR MUTUM YA SHIGO MUN GROUOP MUDDIN YASAN BAI IYA COMMNET BA, IDAN KUMA KA SHIGO TO FA TABBAS ZAKAJI KA A WAJE.*

*MUYI HUTUN K'ARSHEN MAKO LAFIYA, SAI KUMA RANAR MONDAY.*

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 11*

Wasu irin surutai acikin zuciyar ta jikin ta na tsan-tsar karkarwa, domin kuwa ko kaÉ—an bai bata damar da zata iya yin wani furuci ba, sabo da yarce ya fara shirin tura harshen sa zuwa cikin bakin ta.
Cigaba da surutan da take yi azuciyar ta tayi ranta na sake matuƙar dugunzuma, tukun daga bisani ta wara idanuwan ta akan fuskar sa tana mai buɗe tafin hannun ta ta watsa masa wasu abubuwa da suka bayyana acikin sa.

Wata irin gigitattar ƙara Bir ya saki tayarce har sai da duka wurin ya amsa, yana mai sakin bakin ta ya zube aƙasa wanwar.

Yayin da ita kuma taja baya da sauri tana mai sakin wani irin huci yarce kasan zakanya, ga idanuwan ta da sukayi wani irin jajahur yarce kasan gauta!
Cigaba da kallon sa tayi yana birgima cikin yashin dake wurin cikin zafin rai, tana mai jin wani irin bamin ciki da takaici na sake tokare ƙawon zuciyar ta, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta da suke futar da sautin saraƙuna tana mai yin wurin da yake.
Tana ƙarasawa kusa da shi ta ɗaga ƙafar ta ɗaya tana mai harbin cikin sa da ita da matuƙar ƙarfi, tare da sakin huci.

"Ina mai tabbatar maka da ka tarowa kanka bala'in da yafu ƙarfin ka, ka tarowa kanka masifar data ƙarfin duka ahalin ka, domin ko nayi rantsuwa da abun Bauta Gargabilu sai na illata rayuwar ka, tunda har kayi gigin kusantar jiki na." Ta faɗa cikin zafin rai tana mai sake ɗaga ƙafa ta harbi cikin sa da ita.

Wata irin ƙara ya saki ƙasa-ƙasa yana mai sanya hannu ya dafe cikin nasa da shi, tukun daga bisani ya fara ɗago kansa ahankali-ahankali harya sauke idanuwan sa akan fuskar ta, da gaba ɗaya ta canza yarce kasan ba ita bace wacce take murmushi ɗazu.
Sanya idanuwan sa yayi acikin nata, tukun ya sanya haƙwaran sa yana mai taune leɓen sa na ƙasa da su ahankali, kana daga bisani ya sake su yana mai sakar mata wani shegen murmushi, idanuwan sa akanta.

Rumtse idanuwa Gimbiya Tasmir ta sakeyi da ƙarfi tana mai girgiza kanta, tukun daga bisani ta juya tana mai miƙar wata hanya ta tafi ba tare da ta sake kallon sa ba.
Yayin da shi kuma ya cigaba da birgima acikin yashin da yake, har lokacin kuma jikin sa bai bar futar da jini ba.

Ko minti biyar batayi da tafiya ba sai gatanan ta dawo tare da wasu danƙara-danƙaran baƙaƙen maza da suke sanye da baƙin gajeran wando kawai ajikin su, ga wasu irin murɗaɗɗun bulalai da suke riƙe a hannuwan su suna biye da ita abaya.
Kallo ɗaya mutum zaiwa ƙartan nan ya yayi matuƙar firgita muddin ba saba ganin su yayi ba.

"Daƙiƙa ukku kawai na baku, ku tabbatar kun ɗauke shi daga wurin nan kun kai shi gidan azaba na gefen taku, sannan ku gana masa azaba irin azabar da baku taɓa yiwa wani mahaluki itaba agidan duniya, ku tsoma kansa acikin ruwa, ku kuma haɗa kansa gware da duwar-watsu, sannan kuma kutabbatar kun baɗe duk jikin sa da gishiri bayan kun gama dukan sa, domin ko ina son koda ya iya tashi ya zamto ya na kasa!" Ta fara bawa mutanen da suke biye abayan ta umarni tun kafin ta ƙaraso inda Bir yake kwance, idanuwan ta ƙur akansa.

Dasauri sukayi kansa suna masu funciko sa daga kwancen da yake ya miƙe tsaye, tukun ɗaya daga cikin su ya fara shirin saɓa sa akafaɗar sa.

"Kul! Kar ka kuskura ka fara ɗaukar sa, domin kuwa ba daɗi nace kajiyar da shi ba, dan haka maza ka dire sa aƙasa, sannan kafara jansa daga nan har zuwa can, kuma bance akaucewa dutse ko bishiya ba, kamar yacce bance abisa ahankali ba!" Gimbiya Tasmir ta faɗa da matuƙar ƙarfi, tana mai ɗaga ƙafarta ɗaya ta dire ta aƙasa, sabo da yarce taga daya daga cikin mutanen nata na shirin ɗaukar sa.
Sakin sa yayi aƙasa daga tsayen da yake, tukun ya durƙusa yana mai cafko ƙafar sa da matuƙar ƙarfi, sannan ya fara jansa acikin wurin mai duwatsu suna masu yin gaba.

"Ina bazai yuwu ba! Ba zai yuwu ba wallahi! Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai dafe goshin ta da hannu, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Shin akan me zaka hanani hukun tasa Baba? Wane irin daliline da har zai sa bazai kasu ba? Shin meya sa, meya sa, meya sa nace?
Me yasa zan barsa ne haka kawai, bayan akkulum rainin sa ƙara hauhawa yake fiye dana baya? Me yasa zaka hanani hukunta sa Baba, gashi nan kajamun, kajamun raini mafi muni daga cikin rainika Baba!" Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kaiwa iska naushi, tukun daga bisani ta durƙushe aƙasa kan guiwoyin ta tana mai fashewa da wani irin kukan baƙin ciki.
Ita kanta bazata iya tina tsawon shekrun data É—auka rabon ta da zubda hawaye ba ko kaÉ—an, kai zama ta iya cewa rabon ta da zubda hawaye tun kafin ayaye ta, amma sai gashi yau itace har da kuka, kukan ma ba irin kuka na hankali ba, kuka irin na tashin hankali.
Wani irin suya da raɗaɗi take jin zuciyar ta na mata, idan har ta tuna da yarce wancan ƙasƙantacce Bawan ya haɗa jikin sa da nata, ita da ko fuskar ta ba'a iya kallo, ita da ko sautin takun ta ba'a son sauraro, ita da ake tseren gudu aduk lokacin da aka hangota daga nesa, amma sai gashi ayau an samu wani ya tsaya agabanta harma ya taɓa jikin ta, ya kuma lashi laɓɓan ta, wani, wanin ma kuma Bawa, Bawan kuma ƙasƙantacce mafi muni daga cikin Bayi, Bawa wanda shi kansa bai san asalin saba shi ya karya alkadarin ta, shi ya take kwarjinin ta, sannan kuma yayi fatali da izzar ta, hakan yasa take jin inama ace ubangiji Gargabilu ya karɓi ranta tuntuni kafin zuwan wannan Baƙar ranar gare ta!
Chapter 27 · 0% Book details