Sashe 6
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye tayi agaban sa tana mai kallon kanta acikin madubin.
Sanye take da kayan fulani irin na sarauta, riga da zani ne farare masu ɗauke da adon ja da koren zare ajikin su, sai ƙafar ta kuma da take sanye da plat farin half cover shoe na fata mai ɗauke da adon gashi ajikin sa mai tsananin kyau, yayin da kanta kuma ya kasan ce abuɗe ba ɗankwali akai, sai uban gashin da aka gama gyarawa da aka rabasa gida biyu, aka kikkitse jelolin suka zubo har kan cikin ta baƙiƙƙirin dasu gwanin ban sha'awa.
Farace tas kamar ataɓa ta jini ya ɓullo, tana da tsayi tare da ƴar ƙiba dai dai misali, irin waƴan da ake so mace ta kasan ce dasu, tana da dara daran idanuwa masu ɗauke da blue black ɗin ƙwaya acikin su, sai siririn hancin ta da yake zaune daram akan fuskar ta wanda baza'a kira sa da dogo can ba kuma baza ace nasa ɗan guntu ba, yayin da bakin ta kuma ya kasan ce ɗan tsukut dashi ɗauke da pink lips akan sa suna ta faman ƙyalli.
Ba wata kwalliya ce ɗauke afuskar ta ba sai kawai zallar powder data shafa, daga nan kuma bata ƙara komai akai ba sai suturar dake sanye ajikin ta da sukayi matuƙar zama das da su. GIMABIYYA HADDIYAL kenan. Ƴa mace ta farko ga Lamiɗon masarautar fulɗe, gimbiya ƴar gata wacce ake tsananin ji da ita, gimbiyar da take da matuƙar izza da kwarjini irin na ƴaƴan sarauta.
Gimbiyar da ta maida tsun-tsaye da shanaye abokan rayuwar ta fiye da komai acikin masarautar tasu, hakan ya sanya har mahaifin ta LamiÉ—o ya bata sarautar tsun-tsaye ta duka masarautar.
Lumshe idanuwan ta tayi agaban madubin fuskar ta É—auke da sassanyan murmushi, babu abun da take hange acikin idanuwan ta sai kyakkyawar fuskar sa yana aiko mata da sassanyan murmushin sa kamar yacce take ganin sa aduk lokacin da taso ganin sa muddin ta kulle idanuwa ko kuma ta kwanta bacci.
Ta ɗauki tsayin mintina biyar rufe da idanuwan tana sakin murmushi, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sake duban kanta ajikin madubin, kana ta juya tana mai dosar ƙofar da zata sadata da waje cikin takun ta wanda yake nuni da ita ɗin wata ce basai anfaɗa ba.
Wani danƙareren fallow ne mai tsananin kyau, wanda aka ƙawa tasa da kujerun ƙarafa masu ruwan zuma ta ɓulla cikin sa.
Gaba ɗaya bangon fallow'n zagaye yake da adon ja da bluen stara masu tsananin kyau, yayin da daga saman starorin kuma aka kafe wasu haɗaɗɗun ƙwarare da luwade harma da faifayen kaba kala kala akan su. Kallo ɗaya mutum zaiwa wurin ko da bai san saba yasan tabbas ya shigo cikin babbar masarautar fulani waƴan da suke ji da Al'adun su, sabo da yarce aka ƙawata ko ina da kayan ado irin na fulani.
Kai tsaye ta tunkari inda wata farar dattijuwar mace mai kimanin shekaru hamsin da ƴan kai take, kishingiɗe take akan tabarmar kaba wacce saman ta take ɗauke da lallausar sarrafaffar fata akai, sai wasu tum-tum da suke ajiye agefe da gefen shimfiɗar, yayin da ita kuma matar take kishingiɗe akan tum-tum ɗin ta miƙe ƙafafuwan ta duka akan kafet ɗin. sanye take da kayan fulani farare kar da su, sai al'kyabba wacce itama take ta mahaɗin kayan fara mai adon baƙi sanye ajikin ta.
Kallo ɗaya zaka yiwa matar ka gane itace ta haifi Gimbiya Haddiyal, sabo da tsananin kamar da suke yi, riƙe take da wani haɗaɗɗen kofin silba ahannun ta, wanda cikin sa ya kasan ce cike danƙam da madarar shanu mai matuƙar dumi tana sha. Sai daga can wuraren ƙafafuwan ta kuma wata dattijiwar mata ce mai kimanin shekaru kusan hamsin da biyar aduniya take riƙe da ƙafafuwan ta tana ta aikin mammatsa su.
Tunda ta hango tawowar ƴarta ta take ta faman sakin murmushi tana kallon fuskar ta har ta ƙaraso wurin da suke.
Cire takalman dake sanye aƙafafuwan ta tayi, tukun ta hau kan kafet ɗin tana mai zama ta tanƙwashe ƙafafuwan ta akai.
Dasauri wannan dattijuwar matar dake aikin lallatsa ƙafafuwa ta buɗe baki har tana ɗan ranƙwafa jiki wurin faɗin. "Barka da futowa ranki ya daɗe."
"Yawwa barkan ki dai Iya." Gimbiya Haddiyal ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi, tukun ta juya ɓarin da mahaifiyar tata take tana mai buɗe baki cikin sanyi, bayan ta durƙusar da kanta ƙasa tace. "Barka da hutawa dadde na."
Janye kofin madarar da takai baki tayi bayan ta ɗan kurɓe ta, tukun ta miƙawa dattijuwar matar nan da take zaune tana matsa mata ƙafafuwa shi.
Dasauri matar ta karɓa tana mai ajiye kofin agefe bayan ta rufe sa da murfin sa.
Lumshe idanuwan ta tayi, kana ta buɗe su akan fuskar ƴar tata, tukun daga bisani ta buɗe baki fuskar ta ɗauke da murmushi tana mai faɗin. "Yawwa Bello (kyakkyawa) ta." Tukun daga bisani ta ɗora da cewar. "Me ɗazu Innahuro ta tamiki da kika mata rashin mutunci, tazo tashe mun bazata ƙara kula ki ba ta dena baki labari daga yau babu ruwan ta dake." Mahaifiyar tata ta faɗa har lokacin tana kallon fuskar ta.
Zaro idanuwa Gimbiya Haddiyal tayi tana sakin murmushi, tukun daga bisani tace. "Wai haka tashe miki kenan, barni da ita Dadde na ita da kanta zata zo har inda nake da anjima." Ta faɗa tana mai miƙewa tsaye.
"To yanzu kuma sai ina?" Mahaifiyar tata ta faÉ—a tana kallon ta.
Zan zaga bayan nan ne."Cewar Gimbiya Haddiyal" tana mai sanya takalman ta aƙafa.
"To adawo lafiya." Mahaifiyar tata da dattijuwar matar nan suka haÉ—a baki wurin faÉ—in haka.
Juyawa Gimbiya Haddiyal tayi tana mai kama hanyar waje.
Tsaye tai daga bakin ƙofa bayan ta futa tana mai kallon ɗirka ɗirkan shanun da ake shigewa dasu ta gaban ta.
Gaba ɗaya ginunuwa ne irin na fulani masarautar gare ta, ko ina ka kalla share yake ƙal babu alamun datti ko kaɗan.
Sai da har tagama kallon shigewar shanayen nan tukun ta sauka daga kan daɓen part ɗin nasu tana mai kama wata hanya ta miƙe ta samɓel tana tafiya.
Tafe take tana lumshe idanuwan ta tare da sakin murmushi akai akai, sabo da yarce take ganin fuskar sa aduk lokacin data lumshe idon, ga kuma yarce take jin daÉ—in yana yin garin nayau da ya kasan ce babu rana ko kaÉ—an, sai wata irin sassanyar iska dake kaÉ—awa tana dukan jikin ta, tayar ce har jelar gashin dake kitse kwance akan cikin ta suke juyawa.
Sai da tayi tafiya mai nisa daga cikin gidan sarautar tasu, tukun ta ɓulla cikin wani tafke-ken wuri wanda yake ɗauke da bishiyu kala-kala acikin sa, sosai wurin yake da tsananin kyau, sabo da yarce aka ƙawata sa da itatuwa iri daban daban akuma jere atsare, ga wata irin sassanyar iska da take kaɗawa mai matuƙar ƙamshin ganyaye tana dukan fuskar ta.
Wuri ne mai matuƙar girma, domin kuwa aƙalla idan akace mutun ya zagaye sa ataiƙace zaiyi tafiyar kusan awa biyar aƙafa kafun yaje ko ina na ciki.
Banda sautin kukan tsuntsaye iri iri babu abun da akeji yana tashi awurin.
Kai tsaye ta doshi wani wuri da yake daga can gaba wanda aka zagaye sa da iccina, mai É—auke da haÉ—aÉ—É—un bishiyu acikin sa.
Lumshe idanuwan ta tayi abakin wurin tana mai sakin murmushi, badan komai ba sai dan kawai sautin kukan abubuwan data fiso da taji yana dukan kunnuwan ta.
Ahankali ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana dosar cikin wurin bayan ta buɗe idanuwan ta, har kuma lokacin bata fasa sakin murmushi ba.
"Shale am!" (tsun-tsaye na). Ta faɗa cikin zazzaƙar muryar ta da matuƙar ƙarfi.
Aiko ko minti ɗaya batayi ba da rufe baki sai ga dan-dazon tsun-tsaye nan da matuƙar gudu sunyo wurin da take ko wanne na kalar kukan sa.
Tsaye sukai asaitin ta wasu daga bayan ta wasu kusa da fuskar ta, yayin da wasu kuma suke daga saman kanta kowanne da kalar kukan da yake, suna yi suna kar-kaÉ—a jela da fuka fukai, alamun suna farin ciki da zuwan nata kenan.
Lumshe idanuwan ta tayi cikin tsantsar shauƙin da take ji, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sakin murmushi, kana ta ɗaga laɓɓan ta cikin yin ƙasa -ƙasa da murya tana mai faɗin. "Kun san me, yau akwai babban labari da zan baku, labari ne mai daɗi wanda yafi duk na baya daɗi akan Giɗaɗo am."
Ta ƙarashe maganar cikin murmushi tana mai girgizawa tsun-tsayen nan kai, take awurin ko suma suka ƙara sautin kukan su suna masu cigaba da karkaɗa jelina da sauri da sauri alamun farin ciki kenan.
Tukun ta juya tayi gaba suma duka suka biyo ta abaya da matuƙar yawan su, sannan kuma kaloli daban- daban.
Bata tsaya ba har sai da taje wani haɗaɗɗen wuri wanda yake ɗauke da ruwa mai matuƙar girma acikin sa, tukun taja ta tsaya agaban wata shimfiɗar fata mai ɗauke da tum-tum da take agaban ruwan, yayin da cikin ruwan kuma ya kasan ce ɗauke da agwagi kala kala suna ta faman iyo aciki.
Suna ganin zuwan ta suma gaba ɗayan su sukayo bakin ruwan da gudu suna ta faman yin kuka tare da luma kawunan su acikin ruwa, wanda hakan ke nuni dasu ɗin ma farin ciki suke kenan. Tukun daga ƙarshe kuma sai ga dan-dazon kaji masu tsantsar kyau gaba ɗayan su jikin lukui-lukui dasu sunyo inda take suma suna nasu kukan.