← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 79

Sashe 74

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita kuwa Billy sai da tagama sanya kayan tas tayi har rolling d'in mayafin abayar, sannan ta juyo b'arin da yake tana mai zama akan kujerar tare da watsa idanuwan ta a kansa.
Amma amai-makon ta gansa a yanayin da tayi tinanin zata gansa, sai kawai taga ko kad'an hankalin sa baya kanta ma.

Sosai kuwa ta k'ara jinjina k'arfin girman kan Yarima Asad a cikin ranta.
Yayin da shi kuma ya d'ago kansa alokacin yana mai watsa lumsassun idanuwansa da suka d'an canza launi akan fuskar ta.
Kana daga bisani ya bud'e baki cikin wata irin murya wacce tafi kama data gargad'i, yana mai fad'in.

"Muddin mutum yana so yay mu'amala dani, to dole ne ya k'auracewa duk wani banza da yake tare da shi, kana ya kiyayi yimun shish-shigi acikin harkoki na, sannan kuma ya zamto ma'abocin tsafta da k'amshi.
To muddin mutum yayi haka zamu shirya da shi, idan kuma aka kauce to fa zamu raba hanya ne, ko d'an gidan uban waye kuwa shi d'in."
Ya k'arasa maganar yana mai sanya hannu a cikin aljihun sa ya zaro wrapper dolers, tukun ya hullawa Billy su akan jikin ta daga wurin da yake zaune, yana mai fad'in.
"Gasu nan wa'yannan naki ne, zakuma ki iya tafiya yanzu."
Ya k'arasa maganar yana mai shirin mik'ewa tsaye.
Yayin da ita kuma Billy taji wani irin rashin dad'in yadda yayi mata maganganun, da kuma kud'in daya watso mata a jikinta.

_"Ko dan gidan uban waye."_

Ta fad'a acikin ranta tana mai jinjina kanta.
Kana daga bisani tasa hannu ta d'auki kud'in tana mai jujjuya su, tukun daga bisani kuma ta d'aga ido tana mai kallon sa adai-dai lokacin daya juya yana tafiya, kana ta bud'e baki tana mai cewa.

"Me zanyi da kud'in kuma, a a ka barshi kawai na gode."

Ta k'arasa maganar cikin sanyi idanuwanta akan bayan sa.

Bai tsaya daga tafiyar da yake ba kamar yadda bai amsa mata ba, har sai da yaje bakin k'ofar bedroom d'in sa, tukun yaja ya tsaya ba tare kuma da ya juyo gare ta ba ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Hak'k'in ki ne ai su d'in, wato ladan aikin ki kenan."

Ya k'arasa maganar yana mai murd'a handle d'in k'ofar, tukun ya tura kansa ciki tare da rufo ta.

Ita kuwa Billy rumste idanuwanta tayi da k'arfi, tana mai jin saukar kalamin sa da matuk'ar zafi acikin kunnuwan ta.
Kana daga bisani ta bud'e su tana mai fad'in.

"Wato karuwa ma ya mayar dani kenan, shiyasa dan mun d'anyi d'an wannan abun kawai zaice zai biyani."
Ta k'arasa maganar tana mai mik'ewa tsaye cikin fushi, tare da dire kud'in akan center table d'in da yake a cikin falon, tukun ta juya tana mai kama hanyar da zata sadata da waje.

Cak ta tsaya adai-dai bakin k'ofar futa daga cikin d'akin tana mai rumste idanuwan ta, sabo da tinawa da tayi muddin Yarima Asad yazo ya samu kud'in nan anan wurin tsaf zai iya rabuwa da ita daga yau, wanda ita kuma baza ta tab'a son haka ta faru ba, asalima idan hakan ta kasance tana ji ajikin ta tabbas zata iya macewa, sabo da ba k'aramun son sa ta kamu da shi ba.
Hakan ne yasa tayi saurin juyawa da sauri tana mai komawa ta suri kud'in nan, sannan ta bud'e zip d'in jakar ta tana mai watsa su ciki.
Kana ta juya tana mai fucewa daga cikin d'akin.

Tun daga wannan ranar Yarima Asad da Billy sukayi matauk'ar k'ullewa, ta yadda har ya zamto an fara sanin su tare a cikin school d'in ta su.
Yayin da har lokacin kuma Yarima Asad bai yadda ya kusanci Billy ba, sai dai kawai romance da sukeyi.

Ita kuwa babu kalar dabarar da batayi ba domin ta samu ya zarce duka amma abanza.

Sosai take tsananin buk'atar sa, amma take daurewa tana kame kanta, sabo da tino abun da yayiwa baturiyar nan da take yi akan idanuwan ta.
Hakan yasa wani lokacin idan ta bar wurin sa dole take sawa ta kira wani saurayin ta da ya kasance shima d'an k'asar hausa, d'an wani shahararren attajiri ya biya mata buk'atar ta, sai dai kuma sosai take yin kaffa-kaffa gudun kar Asad ya gano ta ya rabu da ita, domin kuwa a kullum idan zasu kasance tare da shi sai ya nuna mata shi d'in fa mai kishi ne.

Babban abun da yafi bata haushi da Asad shine, rashin sanin darajar ta da baiyi ba ko kad'an, gashi kuma a kullum idan zasu d'anyi wani abun da shi sai ya zaro kud'i ya bata, duk da yadda ta nuna nasa bata son hakan kuwa.
Domin kuwa acewar sa ai hak'k'in ta ne, dan haka ya zama dole ya bata, sai dai idan ko ya batan ta zubar da su daga baya.
Ga kuma yadda bata isa ta nuna kishi akan sa ba dan ta gansa da wata, yanzu sai yace mata ai ba dole ya mata ba ta kulasa, kai ak'arshe ma shine yake yin fushi, ta tadda har sai taci wuya tukun take samu ta shawo kansa.

Har kawo yau bai tab'a yadda ta kwana a wurin sa ba, duk da yadda take mutuwar son yin hakan kuwa, domin kuwa acewar sa bai ga uban da zata zauna tayi masa ba tun da ba wani babban abu yake da ita ba, asalima kuma shi ba d'an iska bane ba, sabo da tun da yake a rayuwar sa har yau baisan wani abu sex ba.

B'angaren su Al'amin kuwa sosai suma suka cin karen su ba babbaka, domin kuwa su mai gaba d'aya ma suke yi babu ruwan su da tinanin lahira, a haka har Allah yasa suka kamalla karatun su na master's gaba d'aya, a lokacin kuma itama Billy saura shekara d'aya ta gama degree d'in ta.

Haka su Yarima Asad suka tattaro komai nasu suka dawo Ka'sar Hausa, Jahar Wasai Cikin Masarautar su.
Inda sukazo suka tarar da ko wanne an sake tsara masa mazaunin sa acikin part d'in mahaifiyar sa, wanda hakan kuma ya zamto duk aikin mai martaba ne, domin kuwa ba k'aramun farin ciki yayi ba da kammala karatun d'an nasa mafi soyuwa a ransa ba, sabo da sanin da yayi na yanzu shikenan ya dawo gaban sa, babu kuma zancen sake yin nisa da shi anan kusa, dan kuwa yace koda zai barsa yayi Phd to sai bayan ya tabbatar da ya nutsu ya dawo tamkar yadda Babban Yaya yake, tukun zai barsa ya k'ara yin nesa da shi, domin kuwa sun d'aura d'amarar ganin sun dawo da shi kan hanya daga shi har Fulani, kai harma da Babban yaya.

Watan su biyu da dawowa dai-dai mai martaba da waziri harma da galadima suka same su da zancen aure.
Take a wurin Al'amin ya gabatar musu da budurwar sa wadda suka had'u da ita acan school d'in, amma ita yanzu take kanyin degree d'in ta, wato dai mate d'in Billy ce, duka-duka ba zasu k'ara ko shekara d'aya a school d'in ba suma zasu kammala.
Yayin da shi kuma Asad ya nuna musu cewar bai san wannan batun ba kwata-kwata, kai atak'aice ma a k'arshe haka yace shi har yau baiga wacce tayi masa ba.
Hakan ne yasa waziri ya yanke masa lokaci zuwa nan da shekara d'aya a wadace kenan, sannan yace masa muddin lokacin kuma ya cika bai futar da matar aure ba to ya sani su da kansu zasu zab'a masa cikin 'yammatan su na nan gida da sukaji labarin suna haukar son sa, kana a ka'rshe suka sallame su gaba d'ayan su, bayan sun yanke hukuncin zuwa su nemar wa Al'amin auren yarinyar da yace yana so.

Ko kad'an Yarima Asad bai d'auki maganarsu da muhimmanci ba, sai ma ya watsar da ita a wurin da suka gama yinta, tukun ya taso ya baro wurin.

_BAYAN SHU'DEWAE WASU WATANNI._

Sosai Yarima Asad yake buga tsiyar sa yanda ransa yake so.
Yayin da Babban Yaya, Gimbiya Fulani da Mai Martaba suke k'ok'arin ganin ya dawo kan hanya a kullum amma a banza.

Tini Billy sunyi graduation harma ta dawo gida, ta yadda har suka d'ora da mu'amalar su daga wurin da suka tsaya ita da Prince d'in ta.
Yayin da sunan Yarima Asad kuma ya karad'e kunnen ko wane mutum da yake da kusanci da Billy, ciki kuwa har da mahaifin ta mai girma gwamna, sai dai kuma har kawo yau bai tab'a zuwa gidan su ba, sai dai ita tazo ta same sa a cikin Asadullah Palace.
Yayin da Al'amin kuma akayi maganar auren sa harma da sa rana, inda za'a had'a bikin nasa dana 'yammata da yawa da suke a cikin Masarautar Wasai, cikin su kuwa har da masu hauka akan Yarima Asad da suka gaji suka hak'ura, sabo da ganin da sukayi baya ta su ko kad'an.
Yayin da ita kuwa Fa'iza k'awar Baby da suka kammala degree d'in su yanzu take tsantsar haukar sonsa, amma sai dai kuma ko darajar kallo bata samu daga gare sa.
Chapter 74 · 0% Book details