← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 79

Sashe 3

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa tayi cikin tsantsar ɓacin rai tana mai dosar hanyar waje, banda sautin sarƙoƙin gwal ɗin dake sanye aƙafafuwan ta babu abun da akeji yana tashi awaurin.

Tana fucewa waje gaba ɗaya dakarun nan dasu da ƴammatan bayin suka zube wanwar aƙasa suna masu yin ribda ciki.

Ba tare da ta ɗaga kai ta kalli ko mutum ɗaya daga cikin su ba ta cigaba da tafiya har ta ƙarasa wurin da ta tsaya kafun ta shiga ɗakin nan.

Sai da ta ɗauki tsayin minti biyar da tsayuwa, tukun dukan su suka mimmiƙe suna masu durƙusar da kansu ƙasa.

Hannun daman ta ta miƙar gefe ba tare da tace tak ba.
Kamar yacce ya faru ɗazu haka yanzu ma wannan badakaran ya tawo da baya baya har ya ƙarso inda take.
Tukun ya zube guiwoyin sa aƙasa, sannan ya zaro takobin nan daga cikin jikin sa yana mai ɗora mata ita akan tafin hannun ta.
Dunƙule ta tayi gam acikin hannun, tukun ta miƙar da ita tana mai nuna ɗakin da huƙar, kana daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Gargabiluuu."

Ahankali ƙofar ta fara rufewa har ta rufe gaba ɗayan ta, sannan ta ƙara miƙar da hannun ta gefe shi kuma wannan badakaran ya miƙa hannu ya ɗauki takobin.

Tashi yayi ya koma inda yake da baya da baya kamar yacce yazo.

Juyi tayi cikin zafin nama ba tare da ta kalli kowa acikin su ba, har lokacin bata bar sakin huci ba tana mai kallon hanyar da suka biyo sukazo wurin.
Dasauri waƴan nan ƴammatan bayin suka mimmiƙe daga durƙushen da suke suna masu kama wasu sashika daga jikin rigar dake sanye ajikin ta, sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da suka biyo sukazo cikin sauri.
Gaba É—aya suma dakarun nata rufa mata baya sukai cikin sauri suna binta.

*ƘASAR HAUSA CIKIN MASARAUTAR WASAI*

Tun daga bakin masarautar mutum zai fahimci yau ɗin ana wani gagarumin bikin ne aciki basai an faɗa masa ba. Sabo da yarce sautin kaɗe-kaɗe da bushe-bushen algaitu, sarewa, kakaki, tambura, kalangu, harma da kiɗin ƙwarya ke tashi awurare daban daban acikin masarautar, ga kuma yarce jama'a keta kai kawo, wasu asaman doki, wasu akan motocin su, yayin da wasu kuma suke tafe akan ƙafafuwan su. Ko ina ka kalla hadimai ne da sarakai kawai suke giftawa kowanne da kalar shigar dake sanye ajikin sa.

Tsaya yake gaban tamfatsetsen mudubin dake manne jikin bangon ɗakin wankan nasa yana mai kallon fuskar sa ta cikin sa. Ɗaure yake da towel aƙugun sa bako riga jikin sa, yayin da hannun sa kuma ya kasance riƙe da wani ɗan ƙaramin towel ɗin yana tsane lallausar sumar dake kwance akansa tana ɗigar ruwa.
Ya É—auki kimanin minti goma tsaye gaban mirrown yana kallon kansa, tare da cigaba da tsane sassan jikin sa da towel É—in dake É—auke ahannun sa ba tare da ya gama ba.

Ahankali ya juya bayan sa yana mai kai fararen ƙwayoyin idanuwan sa kan ƙofar bathroom ɗin, sabo da yarce sautin noking keta tashi ta yarce har ya fara takura masa, domin kuwa an ɗauki tsayin minti huɗu ana yin sa kenan.

Mtseww! Yaja ɗan ƙaramin tsaki yana mai yamutsa fuska, tukun daga bisani ya janye idanuwan sa daga kan ƙofar ba tare da ya tankawa mai ƙwan-ƙwasowar ba, sai ma juyawa da yayi yana mai zuwa ya ya saƙale ɗan ƙaramin towel ɗin dake riƙe ahannun sa ajikin ƙarfen saƙale kaya, kana ya juya yana mai komawa ɗayan ɓarin inda wata azababbar wadrobe mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali ke manne ajikin bango take, ya tsaya gaban ta yana kallon ta, tukun daga bisani ya lumshe fararen idanuwan sa, kana ya buɗe su yana mai saka zara-zaran yatsun hannun sa masu ɗauke da kwantaccen gashi akan su, ya dire su akan murƙar jikin wadrobe ɗin, kana ya bude ta.

Gida ukku wadrobe ɗin ta kasu. Gida na farko gaba ɗayan sa ɗauke yake da designers bathroob jere aciki kala-kala masu masutuƙar kyau, sai gida na biyu kuma jere yake da designers boxers da singlet gaba ɗayan su sababbi fidigil suma, sai kuma side na ƙarshe da ya kasance ɗauke da haɗaɗɗar loka mai zaman kanta, wacce take ɗauke da haɗaɗɗen murfin roba fari ƙal da aka ƙawata sa da zanen flower's akan sa.

Sake kai yatsun sa yayi kan murfin lokar yana mai buɗe ta. Gaba ɗayan ta cike take da tooth brush sababbi fidigil acikin kwalayen su tare da maclean masu matuƙar tsada.
Hannu yasa ya É—auki brush É—aya tare da maclean, tukun ya maida locar ya rufe, kana ya mai da murfin wadrobe É—in ya rufe ta duka, sannan ya juya yana mai yin wurin wani haÉ—aÉ—É—en sink bathroom da yake manne akan canter yana facing É—in wadrobe É—in nan, yana tafiya yana yage kwalin brush din dake É—auke ahannun sa.

Cilla kwalin brush ɗin yayi cikin dustbin ɗin da yake ajiye awuri ɗaya daga can gefe, tukun ya buɗe sabon maclean ɗin da ya ɗauko ya matsa sa ajikin brush ɗin, kana ya ƙarasa yana mai sa hannu ya kunna tap ɗin da yake manne jikin sink ɗin bayan ya aje maclean ɗin gefe.

Ya dauki kimanin minti shida zuwa bakwai akan brush ɗin kawai yana ta dirzar haƙwara yarce kasan wanda zai canza su, tukun daga ƙarshe yasa ruwa ya ɗauraye bakin sa da shi, sannan ya juya ɓarin da kwandon sharar nan yake yana mai cilla brush ɗin da ya gama amfani da shi aciki, tukun ya juya yana mai dosar ƙofar da zata futar dashi daga cikin toilet ɗin wacce ake ta faman ƙwan-ƙwasawa tun ɗazu, cikin takun sa na tsantsar isa da izza, wanda yake nuni da shi ɗin cikakken jinin sarauta ne.

Ɗan gajeran tsaki ya sake ja yana mai ɗan cije lower lips ɗin sa ahankali, tukun daga bisani ya ɗora hannun sa akan jamlock ɗin jikin ƙofar yana mai murɗa sa ta buɗe.

Tunda yaji motsin sa abakin ƙofar yana shirin futowa ya ɗaure fuska, kana ya ture sistem ɗin dake ɗauke akan cinyar sa yana opereting ɗin ta zuwa kan kujera, tukun ya kafe ƙofar da kallo yana mai jiran futowar sa.

Koda ya futo daga bathroom ɗin inda yake bai kalla ba ya doshi bakin dressing mirrow, kai bakace yasan da wanzuwar mutum ba ma acikin ɗakin, sabo da yarce bai ko kalli kujerar da yake zaune akai ba balle har ya tambaye sa yaji dalilin da yasa yake ƙwan-ƙwan sa masa ƙofa.

Yana ƙarasawa gaban mirrow yaja kujera ya zauna akai, tukun ya sanya hannu yana mai janyo haɗaɗɗen man da yake shafawa, wacce robar sa kaɗai ma abar kallo ce, ya fara matsar sa atafin hannun sa yana murza sa, sannan ya shafe akan lallausar fatar jikin sa, wacce take lulluɓe da kwantaccen baƙin gashi akan ta hankali kwance.

Ƙwafa saurayin dake zaune akan kujera ya buga da ƙarfi, cikin jin haushin yarce abokin nasa ya nuna halin ko inkula dashi da yay, bayan yasan tun ɗazu shi yake ta zaman jira acikin ɗakin, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amma dai gaskiya guy baka da mutunci ko kaɗan wallahi, wato tsabar iskanci tun ɗazu ina nan zaune ina zaman jiran ka, amma ka futo shine ko darajar kallo ma bazan samu daga gare kaba balle harka tanka mun ko?" Ya ƙarashe maganar yana mai sake buga ƙwafa tare da buga masa harara ta cikin mirrow, duk da dai shi har yanzu bai nuna yasan da shi bama.

Inda yake bai É—ago ya kalla ba balle harya samu ya tanka masa, cikin kwanciyar hankali ya cigaba da shafa mai asassan jikin sa ba tare da ya juyo ba.
Sai da ya gama mutssike ko ina na jikin sa da mayukan, sannan ya janyo body spray ya shafe ko wanne lungu da saƙo na jikin sa da shi, tukun ya mai dasu ya aje akan mirrown kamar yacce suke tun farko, kama ya miƙe daga kan kujerar da yake azaune yana mai juyawa ya doshi bakin tamfatsetsen royal bed ɗin da yake kwance atsakiyar ɗakin mai tsananin kyau, har kuma lokacin bai juya ya kalli wurin saurayin nan ba balle ya kula sa.

"Please ASAD kayiwa Allah kai maza ka shirya, ko mayi mu ƙarasa cikin fadar nan muma, dan nasan yanzu duk kowa na can mu kaɗai ne bamu ƙarasa ba." Cewar matashin saurayin nan yana mai kallon Yarima Asad, tare da haɗe tafukan hannuwan sa wuri ɗaya alamun roƙo, domin ko yasan har dai ba lallaɓa sa yayi ba to bazai taɓa yin sauri ya shirya ba kamar yacce idan zai kwana yana masifa bazai nuna yasan yana wurin ba balle ya tanka mai.

"Kash!" Yarima Asad ya faɗa yana mai yamutsa fuska tare da dago idanuwan sa ya watsa su akan fuskar abokin nasa, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin muryar sa wacce har dai ba mugun nutsuwa kayi ba ka saurare sa ba zaka taɓa jin abun da yake faɗe ba yana mai cewa. "Uhmm Al'AMIN kake da suna kowa ma?
Shi wai na tsare ka ne anan É—in, ko kuwa nace maka kajira ni ne da zaka tsaya kana mun ihu acikin kunnuwa tun É—azu."
Ya faɗa yana mai janye idanuwan sa daga kan fuskar sa, tukun ya cigaba da dosar bakin bed ɗin nan inda ya hango kaya ajiye awurin, alamun Abokin nasa ne ya zaɓo masa su amatsayin waƴan da zai sanya.

"ÆŠan iska mara mutunci, haka ma zakace kenna ko?" Abokin nasa ya faÉ—a yana mai É—aure fuska takaici fal ransa.
Chapter 3 · 0% Book details