Sashe 65
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna k'arasawa gaban ruwan wannan badakaran ya kamo k'afafuwan Bir duka biyun da hannun sa, tukun ya d ago su sama yana mai mayar da kansa k'asa, sannan ya d'aga sa daga tsayen da yake yana mai danna kansa a cikin ruwan nan.
Take kuwa Bir ya fara wani irn shure-shure, yana mai hahaura k'afafuwan sa da matuk'ar k'arfi, tare da motsa jikin sa, amma sai dai kuma ko alamun k'wacewa baiyi ba daga hannun dank'are-ren mutumin nan mai sufa da samudawa.
Sai da suka d'auki kimanin minti goma, tukun wannan badakaran ya zaro Bir daga cikin ruwan, yana mai yadda shi a gefe.
Yayin da idanuwan Bir kuma sukayi wani irin kakkafewa, ga cikin sa kuma da yayi matuk'ar girma, alamum ba k'aramun ruwa yasha ba kenan.
Da sauri wani badakare yayi kansa gadan-gadan, a lokacin da wancan d'in yayi cilli da shi a gefe.
Yana mai k'arasawa wurin da yake, kana ya d'aga damb'areriyar k'afar sa d'aya, yana mai taka cikin Bir da ita.
Take kuwa yayi wata irin d'agowa sama, bakin sa na futar da uban ruwa da matuk'ar yawa.
'Daga k'afa badakaran nan ya sake yi da matuk'ar k'arfi, yana mai direta akan cikin Bir.
Wata irin k'ara Bir ya saki k'asa-k'asa, bayan wani ruwan ya sake futa daga cikin bakin sa da matuk'ar yawa, yana mai bud'e idanuwan sa tare da kifewa rufda ciki a k'asa.
Da sauri d'ayan badakaran ya sake matsawa wurin da yake yana mai d'aga k'afar sa d'aya yayi wani irin k'wallo da Bir.
Ai kuwa yadda kasan iska ta d'aga leda haka Bir yayi gefe yana mai zuwa ya gwaru da wata bishiya, tukun ya fad'i a k'asa.
Wani irin jini ne mai matuk'ar gudu ya b'alle daga cikin gashin Bir yana mai tsiyayowa akan fuskar sa.
Yayin da shi kuma yake ta sakin nishi da k'yar, yana mai juya juyi a wurin da yake cikin tsantsar azabar da take ratsa jikin sa, ga kuma idanuwan sa da suka furfuto waje tsabar wahala.
A tare gaba d'aya dakarun nan suka sake d'aga k'afafuwan su suna masu nufar inda yake.
Suna k'arasawa wurin da yake gaba d'ayan su suka zare mahaukatan bulalan su suna masu fara dukan sa da su ta ko ina, yadda kasan sun samu jaki, kai ko jaki ma bai can-canci amasa irin dukan nan ba kasancewar sa abu mai rai, sai dai ace gini ko dutse.
Sai da suka yi masa jina-jina, ta yadda har ya zamto sai da k'yar yake iya motsi a wurin da yake, tukun babban cikin su ya kalli k'aramin su yana mai fad'in.
"Kayi maza kaje ka sanarwa da Gimbiya cewar anyi tamkar yadda tace, umarnin ta na gaba kawai muke jira."
Ya k'arasa maganar yana mai sa k'afa ya shuri Bir da ita.
Yayin da shi kuma wannan badakaran da ya aika ya juya da matuk'ar sauri yana mai nufar hanyar da zata sadasa da wurin da Gimbiya Tasmir take.
A b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa cikin tsantsar zafin rai da k'unar, zuciya ta cigaba da tafiya da matuk'ar sauri tana mai dosar hanyar da zara sadata da b'angaren su.
Sosai takejin zuciyar ta na wani rin k'una da tafar fasa idan ta tuna yadda Bir yayi mata k'uri da ido, har da su busa mata iskar bakin sa akan fuska.
Wata irin tafar-fasa take jin zuciyar ta nayi mata tsabar b'acin rai, lokaci d'aya taji bata da wanda ta tsana sama da shi.
Babu abun da ke k'ara k'ona mata rai sai yadda zuciyar ta ta dinga wani irin bugu a gaban sa, babban abun takaicin kuma shine tana barin wurin da yake d'i taji ta dawo gudu dai-dai, hakan ne yasa taji aranta tana mai son sanin dalilin da yasanya taji haka dan ta tsaya a gaban sa, tana son sanin me ya taka, wana kalar sihiri gare sa da har kallon sa ya sanya ta fad'uwar gaba.
Har ta kusa k'arasawa b'angare nasu taja ta tsaya a wuri d'aya, ba tare da ta cigaba da tafiyar ba, tana mai rumtse idanuwan ta da matuk'ar k'arfi, sabo da tinanin da ya fad'o mata aranta, na sanin muddin ta shiga cikin gidan nasu a wannan yanayin na b'acin ran da take dole ne tasan sai wani daga cikin a halin ta ya tambaye ta dalili, wanda idan hakan ta faru take ganin bata da amsar da zata bayar, domin kuwa ba zata tab'a iya bud'e baki tace wani k'ask'antaccen Bawa ne ya b'ata mata rai, sabo da hakan zai zamto babban abun kunya mai muni ne gare ta, wato a matsayin ta na d'iyar Sarki Barbaru yar lelen sa, kuma ace Bawa ya b'ata mata rai, harya sanya bak'in ciki a ckin ranta ta yadda har ya bayyana akan fuskar ta kowa ya gani.
Da matukar sauri ta juya baya zuciyar ta na cigaba da tafar-fasa, sabo da wannan tinanin da ya fad'o ranta, domin kuwa data fad'awa wani abun da ya faru da ita cikin 'yan gidan su, tana jin gwanda ta kwana ba a cikin sa ba.
Hakan ne yasa ta d'auki hanyar wani lambu da yake acan bayan b'angaren su, wanda nan d'in ma dama yana d'aya daga cikin wuraren da take zama domin hutawa a lokuta da dama, kasancewar ba k'aramun dad'in wurin take ji ba.
Kan wata had'ad'd'iyar kujerar gini ta zauna akai, tana mai d'ora k'afa daya akan d'aya, tare da lumshe kyawawan idanuwan ta.
Zaman ta baifi da minti Ashirin ba a wurin wannan badakaran da aka aiko sa wurin ta ya k'araso wurin, kasancewar nan d'in ne wurin da ya fara yowa d'in dama, sabo da sanin da yayi na zai iya cin karo da ita a wurin, tunda wurin zaman ta ne dama.
Tun daga nesa da ya hange ta zaune akan kujera ya juya baya da sauri, tukun ya fara tawowa da baya da baya yana mai yowa wurin da take, yana mai k'arasowa kusa da ita ya juya kansa sunkuye a k'asa yana mai fad'uwa k'asa wanwar yayi ribda ciki, kana daga bisani kuma ya tashi yana mai cake guiwoyin sa a k'asa, sannan ya bud'e baki cikin k'ank'antar da murya yana mai fad'in.
"Anyi duk abun da kikace ayi ranki ya dad'e, yanzu kawai umarnin ki na gaba muke jira."
Ya fad'a yana mai yin shiru tare da k'ara sunkuyar da kansa a k'asa.
Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir take ta aikin karkad'a k'afarta ba tare da ta bud'e idanuwan ta ba har lokacin.
Kana daga bisani bayan shafewar mintina bakwai da gama maganar tasa, ta d'aga masa tafin hannu ba tare da tace komai ba.
Hakan da ya ganine ya sanya sa mik'ewa tsaye da sauri, tukun ya bud'e baki yana mai fad'in.
"An gama ranki ya dad'e, na barki lafiya."
Kana ya juya cikin sauri, yana mai dosar hanyar da ya biyo yazo wurin, domin kuwa tana nufin asake sane da da'ga hannun da tayi, sabo da tinanin da tayi na karta koma wurin kallon fuskar sa ya sanya ranta ya sake b'aci, duk da yadda tayi niyyar zuwa ta gansa bayan an gama masa hukunci a d'azu, shiyasa kawai ta bada izinin asake sa, domin kuwa tariga da ta sani tunda har suka ce an gama, to tasan anyi fiye da yadda take zato ma, wannan dalilin ne ya sanya ta bada izinin a sake san, sabo da tariga da tasan ko yanzu ya gane bam-bancin dake a tsakanin su.
Cikin 'yan k'alilan lokaci wannan badakaran ya k'arasa wurin da 'yan uwan sa tare da Bir suke.
Tukun ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Tace asake sa kawai."
Hakan da Babban cikin nasu yaji ne ya sanya sa sake d'aga gundumemiyar k'afar sa d'aya, yana mai k'ara yin k'wallo da Bir, tukun suka juya suna masu yin tafiyar su.
Yayin da shi kuma Bir ya sake yin sama tukun ya fad'o k'asa, sannan ya fara shirin tashi daga kwancen da yake, cikin tsantsar azabar da yake jin tana ratsa ko ina na ilahirin jikin sa, dan kuwa hatta da idanuwan sa sai da k'yar yake iya bud'e su, ga kuma jini da yake ta zuba a jikin sa.
Jin da yayi ya kasa tashi zaune ne ya sanya sa fara jan ciki a wurin da yake, yana mai nufar hanyar da zata sada sa da b'angaren su na bayi, cikin tsantsar azabar da ke cigaba da ratsa jikin sa, amma a hakan fuskar Gimbiya Tasmir kawai yake hange acikin idanuwan sa, tare da d'an k'aramin bakin ta, da kuma dogon hancin ta, yana mai jin ina ma zai sake arba da ita yanzu a gaban sa, domin kuwa ko kad'an baiji ya gaji da ganin kyakkyawar fuskar ta ba, wacce ada bai tab'a tinanin haka take da kyau ba, sai yau da suka yi kusanci da ita dab da dab.
Cikin tsantsar tashin hankali su Mauzum sukayo wurin da yake suna masu sakin Ihu tare da kiran sunan Iya, sabo da hango sa da sukayi daga can nesa yana tawowa da jan ciki, ga kuma jini dake bin jikin sa, dama kuma tini tun d'azu an kawo musu labarin ya had'u da Gimbiya bai gudu ba, har hankalin iyar bayi ya tashi.
Cikin tsantsar rud'u Iyar Bayi ta futa daga cikin d'an-d'akin ta tana mai gyara d'aurin d'an guntun k'yallen da yake a k'ugun ta.
Tukun tayi wurin da ta hangi Bir su Mauzu na shirin d'aukar sa, hankalin ta a tsantsar tashe.
Yayin da su kuma su mauzum sukayo wurin da take hannun su d'auke da Bir, gaba d'ayan su suma a rud'e.
A k'ark'ashin inuwar Bishiyar darbejiyar da take a gaban d'akin Iyar Bayi suka a jiye Bir.
Yayin da Iyar Bayi kuma tayi saurin matsawa kusa da shi jikin ta na tsantsar karkarawa, tukun ta d'ago kansa da tafukan hannayen ta tana mai d'ora sa akan cinyar ta.
Kana ta shafa lallausar sumar da take kwance a kansa, tana mai fad'in. "J...............âœ
*BAK'AR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 26*
"Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!!"
Iya ta faÉ—a cikin tsantsar ruÉ—u, tana mai shafa lallausar sumar dake kansa tare da bin burÉ—ikan bulalan da suke kwance a jikin sa da idanuwa.