← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 79

Sashe 67

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɗauki tsayin mintina huɗu tana kallon kayan, tukun daga bisani ta miƙa hannun ta zuwa ciki tana mai ɗorasa akan wata haɗɗaɗiyar baƙar riga mai tsananin kyau, da tsayin ta zai iya kai mata har guiwa idan tasa ta.

Ɗauko ta tayi tana mai ajiye ta a gefen gado, tukun ta sake mayar da hannun ta ciki tana mai zaro wani white roba jeans shima sabo fidigil, kana ta ciro wani ɗan ƙaramin mayafi da ya kasance fari shima.
Sannan ta rufe wardrobe É—in tana mai dawowa gaban gadon ta tsaya.

Ɗaukar rigar tayi tana mai miƙar da ita tsaye tare da jingina ta a jikin ta, tukun ta girgiza kai tana mai sakin murmushi, sabo da sanin da tayi na dole ne ma rigar tayi mata kyau, kamar yadda ta kasance mai kyau itama.
Kafin daga bisani kuma ta fara ƙoƙarin zira rigar a jikin ta, bayan ta sanya iner wear's a farko.
Sannan ta zame towel É—in jikin ta tana mai É—auko wandon shima ta sanya sa.

Sosai kayan suka yi matuƙar kama jikin ta-ta ko ina, kasancewar su gaba ɗayan su roba ne.

Dauke rigar take da fararen botura masu matuƙar kyau a gaban ta da bayan ta, yayin da daga saitin ƙugun ta kuma take ɗauke da bell ajikin ta.

Shi kuwa wandon gaba É—aya yabi ya matse mata jiki tamkar dama da shi aka hallito ta.

Tayi bala'in kyau cikin shigar iyakar kyau.

Tafiya tayi zuwa wurin da take ajiye takalmanta da jakun kunan ta, tana mai sa hannu ta ɗauko wani baƙin hill shoe da yake ɗauke da igiyoyi ajikin sa, tare da ƴar ƙaramar baƙar jaka mai tsananin kyau da ta kasance mahaɗin sa.
Tukun ta riƙe su a hannun ta tana mai dawowa wurin da mayafin ta yake a jiye shima ta ɗauke sa ta koma gaban dressing mirrow da su.

Tsaye tayi a gaban madubin tana mai kama uban gashin dokin da yake kitse akan ta, kana ta sanya masa fararen riborm masu tsanin kyau, sannan ta sake sa ya zubo har kan gadon bayan ta, tukun ta durƙusa ƙasa tana mai cire igiyoyin takalmin nata mai tsanain tsini, ta sanya ƙafafuwan ta a cikin sa.
Kana ta sake ɗagowa tana mai ɗaukar mayafin ta ɗora sa akan ta, sannan ta tattare sa daga gaban ƙirjin ta ya zamto a bayyane, tana mai watsa jelolin sa baya.

Iyakar kyau tayi kyau, hakan yasa ta fara bin jikin nata da ruwan turarruka tana mai kallon kanta a cikin madubin, tare da sakin murmushi, domin kuwa ita kanta ta yaba da haÉ—uwar tata ba kaÉ—an na.
Yayin da a zuciyar ta kuma take ta saƙa abubuwan da zata jewa Yarima Asad da su, wanda take tinanin Insha Allah bazai watsar da ita ba.

Cikin takun ta na tsantsar ji da kai ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar falon su.

Ko da ta ƙarasa zuwa cikin falon bata samu Zee aciki ba, hakan ne yasa ta ɗan taɓe baki, tana mai fucewa gaba ɗaya daga cikin sa.

Acan ɓangaren Yarima Asad kuwa, misalin ƙarfe huɗu da rabi ya gama shiryawa tsaf cikin shigar sa ta yau da kullum, wato dai black three quarter tare da wata ƴar yololuwa bluen t shirt da tayi matuƙar kama jikin sa, ta yadda har ake ganin gaba ɗaya surar jikin nasa a fili, sai dai kuma fa kwata-kwata baya yiwa kaya sawa biyu, wato da zarar yasa su yau shikenan kuma ya gama da babin su sai wasu sababbin, wanda hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan da Fulani bata so na dan gane da halayyar sa, sabo da ganin hakan da take amtsayin zallar almubazzaranci.

Wasu tausasan bluen takalma na fata ya sanya fararen ƙafafuwan sa a cikin su, yayin da tsintsiyar hannun sa kuma ta kasance ɗaure da baƙin agogon fata mai tsananin kyau.

Cumb ya É—auka yana mai gyara lallausar sumar da take kwance akan sa mai tsananin yawa, da tasha wani irin shegen aski da yayi bala'in yiasa kyau.

Kana daga bisani ya ajiye cumb ɗin akan mirrow'n da yake tsaye a gaban sa, sannan ya lumshe idanuwan sa yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da yake futa ajikin sa, wanda baya taba gajiya da shi ako da yaushe.
Tukun daga bisani ya buɗe idanuwan nasa yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa ya doshi hanyar waje.

Tamkar ko da yaushe yau ɗin ma yana zama akan kujerar nan da take a gaban swimming pool ɗin, kyakkyawar baturiyar da take aikin a wurin ta tawo wurin da yake hannuwan ta riƙe da wani ɗan ƙaramim plate mai tsanain kyau, tare da cup da yake rife da murfi akan sa.

"Weldon sir."

Baturiyar ta faÉ—a tana mai dire plate É—in akan table É—in da yake a gaban sa.

Inda take bai É—ago ya kalla ba ballan tana har tasa ran zai tanka mata.

A hankali ta É—auko mug É—in da yake É—auke da coppy a cikin sa tana mai sake matowa gaban sa.
Tukun ta ɗan durƙusa tana mai miƙa masa shi.

Still dai bai ɗago ya kalle ta ba ya miƙa hannun sa yana mai karɓar mug ɗin, sannan ita kuma ta juya tana mai komawa wurin da ta futo.

Acan ɓangaren Billy kuwa tun misalin ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta ƙaraso wurin, sai dai kuma yau ɗin ma kamar ko da yaushe, wurin da take zuwa ta laɓe taje ta zauna.
Hakan yasa tun tawowar sa wurin take kallon sa har zuwa yanzu da wannan baturiyar ta bar wurin sa.

Cikin tsantsar fargabar rashin sanin yadda zai tarbe ta tasa hannu tana mai gyara kiston da ya ɗan sakko kan fuskar ta zuwa baya, sannan ta miƙe tsaye daga wurin da take tana mai ɗaukar jakar ta ta fara takawa.
Yayin da take jin zuciyar ta na wani irin bugu aɗari-ɗari, sai dai kuma ta ƙudirtawa ranta cewar ko wane kalar tsoro zataji ayau ɗin sai ta ƙarasa wurin sa, domin gudun kar ta tsaya sanya wata tazo ta bangaje ta, wannan dalili ne ya sanya tayi shahada yanzu tana mai nufar wurin da yake gadan-gadan.

Canza taku tayi a lokacin da taga ta kusa zuwa inda yake, tana mai komwa yin wata tafiya mai tsantsar jan hankali.
Yayin da fuskar ta kuma take ɗauke da annuri, duk da ba ƙaramun tsoro ne ke danƙare a ƙasan zuciyar ta ba.

Cikin wani irin taku na tsantsar jan hankali ta ƙarasa wurin da yake.
A hankali kana kuma cikin wata iriyar murya mai matuƙar sanyi ta buɗe baki tana mai faɗin.
"Excuse me."
Yayin da idanuwan ta kuma suke kasance ƙur akan sa, ƙirjin ta kuwa wani irin bugu yake wanda ba zai misaltu ba.

A fannin Yarima Asad kuwa tun lokacin da ta kusa ƙarasowa wurin da yake ya lura da ita, sai dai ko kaɗan batasan ya ganta ba, sabo da yadda taga ko motsi bai canza ba daga yadda yake ballan tana ya ɗago ya kalle ta, yayin da shi kuma yake kallon ta ta ƙasan ido yana mai jiran yaji abun da tazo da shi ita kuma, kafin ya yanke hukunci.

Cikin wani irin salo Billy ta É—an janyo Æ´ar kujerar robar da take kafe a gaban table É—in da Yarima Asad yake, wato wacce take fuskantar mazaunin sa tana mai zama akan ta itama.
Tukun ta ɗauki ƙafa ɗaya tana mai ɗora ta akan ɗaya, kana ta lumshe idanuwanta bayan ta ɗan ɗaga kanta sama.
Tukun daga bisani ta sauke kanta ƙasa tana mai wara idanuwanta a hankali akan fuskar Yarima Asad, kafin daga bisani kuma ta ɗan juyar da kai gefe tana mai fesar da wata sassanyar iska daga cikin bakin ta, sannan ta sake dawo da kallon ta gare sa, tana mai ƙara buɗe baki cikin wata irin murya tace.

"I'm Bilkisu Abubakar Sardauna by Name."

Ta ƙarasa maganar tana mai lumshe idanuwanta, yayinda shi kuma Asad ya cigaba da sipping ɗin copy ɗin sa ba tare da ya nuna yasan da zamanta a wurin ba har lokacin.
Yayinda azahiri kuma yake aikin kallonta ta ƙasan ido, yana mai mamakin ƙarfin halin yarinyar.

ÆŠan muskutawa Billy ta sakeyi akan kujerar da take bayan ta sake wara idanuwanta akan fuksar Asad.
Kana ta sake buÉ—e baki cikin tattausan lafazi tana mai É—orawa da cewar.

"I was born in Ƙasar Hausa Wasai state.
And then the daughter of Wasai Governor."

Ta sake yin shiru tana mai ɗan sauke numfashi ƙasa-ƙasa, tare da jifan sa da wani irin shu'umin kallo ta ƙasan idanuwa.
Yayinda shi kuma Asad ya janye mug ɗin dake riƙe a hannun sa daga kan bakin sa, kana ya dire sa akan table ɗin nan, sannan ya ɗago kai a hakanli yana mai kai idanuwansa kanta cikin wani irin kallo, azahirin gaskiya tini ya gaji da surutun ta, sa'ar ta ɗaya ma shine ƙasa-ƙasa take maganar itama, sannan kuma aɗan kallon da yayi mata na ƴan daƙiƙu ya fahimci ba bitch bace ita ɗin, domin kuwa yanayin nutsuwar ta wacce ta ara ta yafa kawai yasa ya kawo hakan aransa, amma banda haka da tini ya dakatar da ita ma.
Kana daga bisani kuma ya ɗaga laɓɓan sa idanuwansa akan ta cikin yin ƙasa-ƙasa da murya yana mai faɗin.

"Then what nex...."

Maganar tasa ta yanke yana mai lumshe idanuwan sa, sabo da hango tawowar baturiyar budurwarsa ta jiya da yayi ta nufo wurin da suke cikin tsantsar fushi.
Hakan ne ya sanya sa lumshe idanuwansa yana mai tafiya tinanin abun da zaiyi, wanda zai ƙona mata rai tayi nadamar zuwa wurin yanzu-yanzu.

Yayinda ita kuma Billy ta ƙara gyara zaman ta akan sit ɗin da take tana mai fuskantar sa, tare da zumuɗin jin abun da zai futo daga bakin sa, domin kuwa tana tinanin tarkon ta ya kama sa.
Chapter 67 · 0% Book details