Sashe 43
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai sukayi wata irin mahaukaciyar shaƙuwa tsakanin sa da ƙanin nasa, kamannin su ɗaya sak, sai dan hasken fata da Asad yafi Babban Yaya da shi.
Ko kaɗan Fulani bata son yawan yawon da Asad yake yi, asonta tafi son ace kullum yana gaban ta tana masa addu'oi kamar yacce suke tare da Babban yaya, sabo da tsaro badan tsoro ba, domin kuwa babu wata hallaya ɗaya ta mutan gidan nasu da bata santa ba, yayin da shi kuma yaran kwata-kwata baya son zama a cikin gida, asalima kullum a Fada yake yini kusa da Mai Martaba suna hira, sabo da ko kaya yanzu haka kullum iri ɗaya suke sawa da shi da Mai Martaba, hatta da alkyabba kuwa, wanda hakan kuwa ba ƙaramar shaƙuwa ce ta ƙara shiga tsakanin sa da Mai Martaba ba, tayarce har yake jin sa fiye da duka sauran yaran sa a zuciyar sa, sannan kuma yake gaza ɓoye soyayyar sa a gaban kowa, wannan dalilin ne yasan ya Fulani bata fiye samun damar yi masa addu'oi ba, kamar yadda take yiwa sauran yaran, sannan kuma shi kansa Asad ba damuwa yayi da addu'ar ba kamar yacce Babban yaya yake yin ta a lokacin da yana ƙarami kamar sa, asalima ko yi masa Fulani zatayi wataran sai ta riƙe sa, tukun take samu ta masa azkar ɗin, idan kuma ba haka ba tana cikin yi zai ruga ya barta a wurin ba tare da ta gama ba, hakan ko ba ƙaramun tsoratata yake ba, sai dai kuma ako da yaushe cikin kaiwa Allah kukan ta take yi.
A yanzu haka Abokin Asad guda ɗaya ne, wato Al'amin ɗan gidan Galadima ƙanin Mai Martaba, da aka haife sa bayan haihuwar Asad da wata ukku.
Sosai sukayi matuƙar shaƙuwa yaran, yadda kasan waƴan da aka haifa a tare, domin kuwa hatta da abinci tare suke ci ako da yaushe, haka kuma shima Al'amin a cikin Fada yake yini wurin su Mai Martaba, kamar yacce Asad yake yini anan ɗin.
Ko hawa aka tashi yi, shiga iri ɗaya ake yi musu su biyun, sannan kuma kusan ajere ake riƙo dawakunan su suna asaman su.
Haka mutane zasuyi ta ɗaga musu hannu ana kiran sunan su, barin ma Asad da yake da wani irin farin jinin al'umma tun yana ɗan ƙarami, domin kuwa aduk lokacin da aka futa da shi akan doki sai jama'a sun tsaya suna kallon sa, yayin da shi kuma zakaga yana ta ɗaga musu hannu sama yadda kasan Babban mutum.
A ɓangaren magautan su kuwa har yau basu dakata da asirce- asicen da sukeyi ba akan yaran biyu domin ganin bayan su ta kowace hanya, wato Asad da Babban Ƴaƴa, barin ma Asad a yanzu, dan kuwa sunfi tsanar sa sama da Babban Yaya nesa ba kusa ba, sabo da yadda suka ga kaga Mai Martaba naji da shi fiye da Babban Yaya, hakan yasa mutane suka fara zargin tsaf yaron zai iya hawa kan karagar mulki muddin ya ɗore da san zaman Fada har girman sa, wannan dalilin ne yasan ya su suke jin tsanar sa fiye da yadda suke jin ta Babban yaya a zuciyar su, sannan kuma suka mayar da hankali wurin ganin sunga bayan sa ta kowace irin hanya ce, domin kuwa hakan ne kawai zai sama musu salama a rayuwar su.
*UNGUWAR ÆŠAN TANKI.*
Sosai su Ishaƙ su kaci wuya akan Aishatu, kafin daga baya kuma Allah ya sanya mata dangana ta sanadin addu'oin da aka dage ana tayi ba dare ba rana, masallatai da cikin gida akan ta, sai dai kuma gaba ɗaya ta canza, halayyar ta dawo sabuwa, domin tun lokacin da abun ya faru ta koma shiru shiru, gaba ɗaya magana ma sai dole ke sata take yi, ako da yaushe sai dai ta shige ƙuryar ɗaki ta zauna kan gado tai ta faman aikin tinani, wani lokacin ma harda kuka.
Hakan da ta dawo ɗin kuwa ba ƙaramun sosa zuciyar Ishaƙ da mahaifan sa yake ba, sosai take matuƙar basu tausayi da yarce ta koma ɗin yanzu.
Tun bayan haihuwar ÆŠan da tayi a cikin jirgi ruwa bata sake yin wata haihuwar ba, yayin da Ahmad kuma yake da shekaru goma shahuÉ—u dai -dai a duniya yanzu.
Sosai yaron yake da matuƙar hankali da nutsuwa, uwa uba kuma ga san addini da ƙoƙari, domin kuwa har ya sauke izu sittin na alƙur'ani akan sa, ga kuma litattafai da yayi matuƙar sani na addini.
Afannin boko ma yanzu haka yana matakin ajiki ukku ne na ƙaramar makarantar secondry, wato Jss 3.
Sosai halin da mahaifiyar tasa take ciki yake matuƙar damun sa, tayarce har wani lokacin yake zama yay kuka shi kaɗai.
A kullum rana ta Allah idan ya same ta zaune a ɗaki tayi tagumi, sai ya zauna gaban ta yay mata nasihohi, sannan kuma ya zauna yay ta kawo mata labarai dan ya ɗauke mata kewa, haka itama kaka take zuwa su haɗu su duka biyu, wani lokacin ma har da sauran Ƴaƴan ta mata ƙannen Ahmad, su sata a gaba suna bada labarai ana shan dariya, to anan ne itama zakaji ta tsoma bakin ta ana hirar da ita, wani lokacin ma har tayi dariyar itama.
A kullum rana ta Allah idan ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yaron nan da take yi, sai dai kuma yanzu ba'a jariri take ganin sa ba, tana ganin sa ne a ɗan matashin yaro, haka zai ta miƙo mata hannu yana son ta kama sa, amma sai kuma gaba ɗaya taji ta kasa ɗaga ƙafafuwan ta zuwa wurin da yake, gaba ɗaya sai ƙasa ta riƙe su, yayin da shi kuma idan ya tawo domin yazo gare ta, sai wasu irin mutane masu wata kalar siffa mara kyan gani suzo su janye sa suyi gaba da shi, haka zatai ta ɗaga masa hannu shima yana ɗaga mata suna kuka, amma mutanen nan su janye sa suyi gaba da shi, tukun sai ta farka daga baccin ta cikin tsantsar tsoro da firgici.
_BAYAN SHUÆŠEWAR SHEKARA HUÆŠU._
*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*
Tun bayan haihuwar Buba Gimbiya Kaɓel bata sake haihuwa ba tsawon shekaru takwas kenan, sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, domin kuwa har ya shiga watan haihuwar sa cikin.
Yayin da ita kuma Gimbiya Mairamu matar Lamaiɗo ta biyu ta sake haihuwar ƴaƴa maza har guda biyu a bayan haihuwar hairisu, tayarce Ƴaƴan Lamiɗo suka zamto har su bakwai, amma sai dai cikin su duka babu Ƴa mace gaba ɗayan su maza ne, hakan ne yasa dukan su suke fatan Allah yasa wannan karan Gimbita Kaɓel ta haifo musu ɗiya mace.
Sosai suka shiryawa haihuwar, kuma suke zumuɗin ta yadda kasan ba'a taɓa haihuwa ba gidan.
*ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Tun bayan haihuwar Yarima Sairan da Gimbiya Haiwa Babar matar Sarki Barbaru tayi har kawo yau tsawon shekaru goma shabiyar bata sake wata haihuwar ba.
Yayin da ita kuma Gimbiya Salwa Amarya ta haifi Ɗa namiji mai suna Saufan shekaru tara baya da suka huce kenan, tun daga lokacin kuma bata sake haihuwa ba sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, sosai suke fatan Allah yasa wannan karan ta haifo musu ƴa mace dukan su, domin kuwa ba ƙaramun san Ƴaƴa mata suke ba, hatta da shi Sarki Barbaru.
Acan ɓangaren Bayi kuwa yanzu Bir yana da shekaru takwas dai dai aduniya, yayin da wayon sa da girman sa da kuma taurin kansa duk suka zarce shekarun nasa, domin kuwa tun a yanzu bako wane aiki bane ake sa sa yayi sa kai tsaye, sannan kuma muddin akace yaran Bayi sunyi laifi to zaka same sa yana ɗaya daga cikin ƴan laifin, domin kuwa ko kaɗan basa da tsoro, sannan kuma ko wane irin duka za'a masa baya taɓa yin kuka.
A yanzu ya fahimci ba Iyar Bayi bace ta haife sa, sabo da yadda wasu daga cikin ƴan uwansa bayi suke goranta masa cewar shi da ma tsunto sa akayi bashi da Iyaye, idan sukayi faɗa, hakan kuwa ba ƙaramun sosa masa rai yake ba, sannan kuma aduk ranar da aka faɗa masa haka to yaran da ya faɗa ɗin ya shiga ukku a wurin sa, domin kuwa baƙaramun duka yake masa ba, sannan kuma haka zaizo ya tasa Iyar Bayi a gaba yana ce mata ta faɗa masa ina babar sa take, su waye suka haifosa, sannan kuma a'ina ta tsinto sa, sai dai kuma koda wasa Iyar Bayi bata taɓa gigin basa amsa ɗaya ba daga cikin amsoshin tambayoyin nasa, asalima idan ya fara yimata tambayar tashi take tana barin wurin, domin kuwa kotace zata lallashe sa ba lallasuwa yake ba, gashi ita kuma tana matuƙar tsoron faɗa masa, sabo da gudun abun da zai faru da ita daga baya, domin kuwa ba ƙaramun gargaɗi Sarki Barbaru yayi mata ba da kansa, akan cewar kar a taɓa barin yaron yasan tarihinsa ko da wasa, saboda kar ko wataran yay gigin cewa zai bar su, muddin kuwa ta bari hakan ya faru, to tasani abakin rayuwar ta.
Wannan dalilin shike sanya Iyar Bayi tana tashi tabar wurin Bir aduk lokacin da yazo mata da batun, sannan kuma magan-ganun nasa suke matuƙar firgita ta.
Afannin harba kwari da gwafar sa ma kullum abu gaba yake ƙarawa, domin kuwa ba ƙaramun jin daɗin harkar yake ba, sannan kuma baiƙi ba ya yini adaji yana harbe-harbe ba tare da damuwar komai ba aransa.
_BAYAN KWAN BIYU_
Yau Gimbiya Salwa ta tashi da masifaffen ciwon naƙuda mai matuƙar tsanani, tun cikin daren jiya take abu ɗaya, amma har kawo yanzu misalin ƙarfe shaɗaya na rana shiru kakeji bata haihu ba.
Durƙushe take a cikin ɗakin ta daga gefen gado tana mai faman cize leɓen ta, yayin da gumi kuma ke yanko mata ta ko ina a jikin ta.