← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 79

Sashe 10

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farace doguwa siririya, tana da dogon hanci tare da ƴan madai daitan idanuwa akan fuskar ta, sai bakin ta da ya kasance shi baza ace masa ƙarami ba haka kuma baza'a kira sa da tafkeke ba, wato ataƙaice dai tana da kyanta dai dai misali.

Sanye take da blue crazy jeans da yayi matuƙar kama jikin ta, sai red t shirt mai gajeran hannu wacce take ɗauke da kwalliyar flawoyi akan ta, yayin da kanta kuma ya kasance abuɗe ko darajar ɗankwali bai samu ba, sai uban jan gashin atach da yake zube agadon bayan ta yana reto.
Riƙe take da ƴar ƙaramar jakar ta wacce ta kanace kala ɗaya da takalmin dake sanye aƙafar ta mai matuƙar tsini da sirantaka, yayin da ɗayan hannun nata kuma ya kasan ce riƙe da wayar ta ƙirar iphon 13 pro max itama. BILKISU ABUBAKAR SARDAUNA kenan, wacce ƙawayen ta suke kiran ta da Billy Baby. Ƴa ga gwamnan Jahar Wasai mai ci ayanzu, sun haɗu da Yarima Asad ne a oxford university dake ingla, alokacin shi yana mastering degree ɗin sa, yayin da ita kuma take degree, tun daga ranar data ɗora idanuwan ta akan sa gaba ɗaya komai nata ya sauya, duka lissafin ta ya rikice take masa wani irin mugun so, ita da kanta takai kanta wurin sa tun suna can, har kuma ya gama karatun sa ya dawo gida basu rabu ba.

Tunda ta tawo har ta ƙaraso wurin bai ɗaga kai daga kan wayar sa ballanta harya kallo ta, duk da yaji zuwan nata sarai.

"Hello baby!" Ta faɗa cikin yauƙi tana mai zama akusa dashi, tukun daga bisani ta faɗa jikin sa tana mai rungumar sa, kana ta kamo wayar da yake aikin shafawa tana mai kai idanuwan ta kanta.
Murmushi ta saki, sabo da ganin da tayi ba tare da wata yake awayar ba, kamar yacce dama batayi tsammanin ganin hakan ba, sabo da yarce tasan sa da mugun jan aji akan ƴammata, domin ko ko ita sai da taci baƙar wuya kafun ta samu ya fara kula ta.

Ƙala baice mata ba, sai ma janye idanuwan sa da yayi daga kanta yana mai ɗaure fuska, sabo da wayar sa data karɓar masa.

"Wai meya faru ne Beb, naga kana ta faman ɗaure fuska ko kallo na ma baka yi ba?" Ta faɗa cikin muryar shagwaɓa tana mai sake kwanciya ajikin sa tare da ɗaukar hannun ta ta ɗora akan ƙirjin sa tana shafawa.

Bige mata hannu yayi yana mai janye ta daga cikin jikin sa, kana yaja dan guntun tsaki.

Kallon kanta ta farayi baki sake, tana mai son sanin laifin da ta masa da har yake ture ta yana mata tsaki.

"Kashh! I'm sorry Baby, wallahi ni bawai na amshi wayar ka bane dan nayi maka bincike." Ta faÉ—a tana mai marai-raicewa, sabo da tino laifin ta da tayi gare sa.

"Ke har kin isa ki hanani kula wata ne idan naso yin hakan?" Ya faÉ—a cikin kaushi yana mai kafe ta da idanuwan sa.

Da sauri ta girgiza masa kai, duk da dai baƙaramun baƙin ciki taji da kalaman nasa ba, sai dai kuma idan da sabo yaci ace zuwa yanzu ta saba da irin waƴan nan magan ganun nasa, domin kuwa tun farkon haɗuwar su yake mata haka, sannan kuma har kawo yau bai taɓa buɗar baki yace yana sonta ba sai dai ita ta furta masa, dama kuma shi ta fannin sa haka yake, tunda yake bai taɓa kallon wata ɗiya mace ba yace yana santa sai dai su suce suna san sa, danko shi acewar sa yace ba'a haifi ƴa macen da zai buɗe baki yace yana sonta ba, kuma baza'a taɓa haiwuwar ta ba aduniya ko ƴar gidan uban wace kuwa.

"I'm sorry baby, i promise i would never do that againe." Ta faɗa tana mai durƙusawa ƙasa ta kama kunnuwan ta agaban sa, bayan ta marai raice fuska.

"Its you're own concern." Ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba yana mai taɓe baki.

Murmushi tayi da jin hakan daga gare sa, domin kuwa tasan ya riga da ya huce tunda harta furta haka, hakan yasa ta miƙewa da sauri tana mai faɗawa jikin sa ta rungume sa ƙam-ƙam, tukun ta ɗau fuskar ta tana mai kaita saitin tasa fuskar ta haɗe su huri ɗaya, sannan ta ɗan ɗaga lips ɗin ta kaɗan tana mai hura masa iskar bakin ta akan fuska, kana daga bisani ta buɗe bakin ta tana mai faɗin. "I love you so much My Prince!"

Ƙala baice mata ba sai kallon cikin idanuwan ta kawai da yake yi shima. Ahankali ta cigaba da matsar da fuskar ta saitin tasa har ta samu damar haɗe tsinin hancin ta dana sa, tukun ta matsar da lips ɗin ta tana mai ɗora su akan nasa, kana ta zaro harshen ta tana shirin lasar nasa.
Da sauri ya janye fuskar sa daga jikin tata yana mai juyar da kai gefe.

Galala ta bisa da kallo baki asake, sannan kuma hankali atashe, sabo da baicika yi mata irin haka ba sai har idan yana son suyi faÉ—a da ita.
Cikin rawar murya ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in. "What happened againe Baby?"

"I'm not in the mood!"
Ya faÉ—a yana mai jan wayar sa ya cigaba da shafawa ba tare da ya kalle ta ba.

"Please Baby i said I'm sorry!" Ta sake faɗe tana mai ƙara faɗawa jikin sa.

Uhm!

Ya faÉ—a ba tare da ya kalle tan ba dai.

"To please ka tsaya kaji." Ta faÉ—a tana mai sake kai lips É—in ta kan nasa ta haÉ—e su wuri É—aya.

Bai hana taba yanzu sai dai kuma bai taya ta ba, sai ita kaÉ—ai kawai ya bari tana ta faman aikin ta.
Ganin da tai yaƙi ya ware kamar yacce take sone ya sanya ta ƙara dabai-baye sa sosai acikin jikin ta, tukun ta fara jansa da ƙarfi ba tare da ta sakar masa bakin sa ba daga cikin nata ba.
Binta ya fara yi ba tare da yay mata musu ba har tasamu nasarar matso da su bakin kujerar nan, tukun ta cigaba da kissing É—in bakin sa cikin sauri, kana daga bisani ta shammace sa tana mai funcikar sa suka afka cikin swimming pool É—in nan atare.

*BABBAN ZAURE LOCUS*
Unguwace wacce take agaban gidan slSarkin Wasai, Unguwace ta masu hannu da shuni dai dai gwargwado.
Duk gida jen da suke acikin unguwar sun kasan ce manyan ginin-nika ne na bene, sai dai kuma ahakan wani yafi wani girma.

Wani ɗan madaidl-daicin gida mai matsakaicin girma baƙar motar ƙirar coralla Lx ta danna kanta cikin get ɗin sa da yake abuɗe.

Farfajiyace mai girma dai dai misali acikin gidan, yayin da akabi aka ƙawata ta da wasu haɗaɗɗun kujerun silver daga can gefe.
Zagaye compound ɗin yake da furanni masu natuƙar kyau da ɗaukar hankali.

Direct matuƙin motar ya huce parkin space inda wasu motocin har guda biyu suke fake acikin sa da ita, tukun ya parka ta awurin ta, kana ya buɗe murfin motar ya futo hannun sa riƙe da jakar sa.

Farin ne dogo mai kimanin shekaru arba'in aduniya. Sanye yake da dack bluen shadda tare da baƙar wula akan sa, yayin da takalman kafar sa ma suka kasance baƙaƙe, sai tsintsiyar hannun sa kuma da take ɗaure da baƙin agogon fata mai tsananin kyau itama.

Ɗaga kai sama yayi yana mai kallon yarce giza-gizai keta haɗuwa, alamun ruwa na kusa kenan kasancewar yana yin damuna da ake ciki, tukun daga bisani ya sauke kan nasa ƙasa, yana mai kai tafin hannun sa kan fuskar sa ya shafi sajen da yake kwance lup-lup akan ta har zuwa dogon gemun dake manne ajikin haɓar sa da yasha gyara yana ta faman shignin, kana daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai dosar ƙofar da zata sada sa da cikin gidan nasu.

Da sallama ɗauke abakin sa ya danna kansa cikin ɗan madai -daicin falon da yake ɗauke da kujerun ƙasar turki acikin sa.

"Wa'alaikumu salam!" Datijjon mutumin da shekarun sa zasu kai sittin da biyar aduniya ya amsa masa, tare da wata tsohuwa da take zaune akan kujera dattijon mutumin na ɓare ayaba yana bata.

"Barka da hutawa Abba, ina yini." Matashin mutumin ya faÉ—a yana mai zama akan kujerar da take facing É—in wacce suke akai.

"Lafiya ƙalau Malam Ahmad, fatan ka dawo lafiya kaima." Dattijon ya faɗa yana mai sakarwa ɗan nasa murmushi.

"Lafiya ƙalau wallahi Abba, sai dai kawai gajiya dana kwaso sosai." Shima mutumin da aka kira da Ahmad ɗin ya faɗa yana mai ɗan yamutsa fuska.

"To ai dama gajiya ta zama dole, tunda anyi aikin da za'a gajin ai." Mahaifin nasa ya faÉ—a yana kallon sa.

"Kai dallacan rufen baki kaima, gajiya ko ko zallar ragwanta irin tasa." Tsowuwar matar dake zaune akan kujera tana cin ayaba ta faÉ—a tana harar wanda aka kira da Ahmad. Tukun ta É—ora da cewar. "Yanzu Abdulkarimu kana gani É—anka ya shigo har inda nake, amma bai gaishe niba sai kai kaÉ—ai ya gaisar, shine ko kayi masa faÉ—a tsabar duniya ta lalace ko." Ta faÉ—a tana mai marai-raicewa kamar zata saki kuka.

"A'a Umma ta kiyi haƙuri, ai yanzu shima zai gaishe ki, kinga magana muke yine shiyasa baiyi ba tun farko." Ya faɗa yana kallon ta. Tukun ya juya ɓarin da ɗan nasa yake yana mai sakin murmushi yace. "Kai gaishe mun da uwata tun kafin ranka ya ɓaci yanzu yanzu."

"Ina ai abun bama zaije da haka ba Abbana." Ya faÉ—a yana sakin murmushi, tukun ya sake buÉ—e baki yana mai faÉ—in. "Kaka ta ina yini, barka da gida ya akaji da tsufa kuma?"

ÆŠaure fuska tayi tamau ba tare data amsa masa ba, sai wata muguwar uwar harara data bugo masa, tukun daga bisani ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in. "Amma ai da uwarka kake gaisarwa ba zakace mata ya tsufa ba."

Taɓe baki yay shima ba tare da ya tanka mata ba, yayin da shi kuma mahaifin nasa yake ta faman gumtse dariya, domin ko shida kansa yasan Umman tasa bata so jikokan ta suna ce mata ya tsufa.

"Ina Ummi take ne Abba?" Shekh Ahmad ya faÉ—a yana mai kallon mahaifin nasa.
Chapter 10 · 0% Book details