Sashe 35
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na ɗauki nutsuwa ta, hankali na, tare da kunnuwa na na miƙa su zuwa gareki yake Gimbiyar Masarautar Wasai, uwar Sarkin mu na gobe insha Allah, dan haka ki faɗi kome nene, ni kuma ina mai tabbatar miki da babu abun da zai hana sa yuwuwa awanan karan da izinin Allah." Matar data kira da Jakadiya ta faɗa tana mai gyara zaman ta awurin da take.
Yayin da ita kuma Gimbiya Huwaila ta lumshe idanuwan ta tana mai sake dunƙule ƙullin tsumman ahannun ta, tukun daga bisani ta warasu akan fuskar Jakadiya, sannan ta buɗe baki tana mai yin ƙasa-ƙasa da murya, yadda kasan ba iya suka ɗai bane acikin ɗakin, wurin faɗin. "Wannan ƙullin da kika gani na baki, ba komai bane acikin sa face layoyi tare da garin magani, wanda nake son ayanzu-yanzu da zarar kin futa daga ɓangaren nan kije ki ai'watar dasu, domin kuwa Boka ya bani tabbacin cewa muddin anyi amfani da shi kamar yacce yace, to babu abun da zai hana duk abun da yake acikin cikin ta mutuwa ko mace ko namiji ne kuwa."
Ta faɗa tana mai cigaba da kallon ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Layoyi ne tare da garin magani aciki, yadda zakiyi ai'kin shine, su layoyin zakije ki ajiye su ne aƙar-ƙashin makwancin ta, wato gadon da take kwana akai ita kaɗai, yayin da shi kuma ƙullin garin maganin, zaki zubasa aduk inda kika san zata taka, kuma ana son ya zamto ta takasa ne har kimanin sau ukku arana, wato safe, rana da kuma dare, muddin kikayi hakan dai-dai, ni kuma na miki alƙwarin mallaka miki kuɗi har kimanin Miliyan talatin, tare da sarƙar gwal babba, da kuma gidaje, kamar yacce na faɗa miki abaya."
Ta ƙarasa maganar tana mai buɗe tafin hannun ta ta sakar mata ƙullin maganin acikin sa.
"Ina son daga yanzu kisa aranki cewar gawace acikin Gimbiya Fulani, domin kuwa ina mai baki tabbacin babu abun da zai hana wannan abun faruwa, dan kuwa ayanzu haka da zarar na futa daga ɓangeren nan nata zan huce in ajiye layoyin, sannan kuma in barbaɗa wannan ƙullin maganin abakin ƙofar ta, kana kuma idan dare yayi in sake zubasa abakin ƙofar turakar mai Martaba, tunda kin san yau ɗin kwanan tane." Jakadiya ta faɗa tana mai sakin murmushi.
"Yawwa bayan an gama da wannan aikin kuma, ki sani akwai wani sabo da zaizo, wanda za'ayi sa akan wancan É—an iskan yaron da suke kira da Babban yaya, shima kuma ki sani farashin sa daban ne da wannan bawai duk É—aya ba."
Ta ƙarasa maganar da taune laɓen ta na ƙasa, tare da komawa jikin allon haɗaɗɗen gadon da yake acikin ɗakin nata ta jingi na.
"Daga yau ina son ki fara kallon sa amatsayin gawa shima, domin kuwa muddin aikin yazo, babu wani abu da zaisa na kasa yinsa nima, dan haka yanzu ma bara na tashi domin naje na aiwatar da wannan ɗin." Jakadiya ta faɗa tana mai miƙewa tsaye.
"Da gani sai ke ce maganar nan, bana son bayan mu wani yaji ta ko kuma ya ganta, dan haka sai ki kiyaye." Ta faÉ—a daga zaunen da take tana mai kallon ta.
"Insha Allah Uwar Sarkin gobe." Jakadiya ta faÉ—a tana kallon ta, tukun daga bisani ta É—ora da faÉ—in. "Na barki lafiya." Kana ta juya tana mai fucewa daga cikin É—akin.
Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, zaune take akan tattausan kafet ɗin da yake malale acikin bedroom ɗin nata, ta jingina da kujerar da take abayan ta tana mai ɗan cizon lip ɗin ta tare da ya ƙuna fuska, sabo da yarce take jin ciwon bayan data tashi da shi tun bayan tashin ta daga baccin safe na ƙara ƙaruwa fiye da baya, ga kuma yarce take jin marar ta na karta mata, hakan shine ma yasanya ta saukowa daga kan kujera ta zauna akan kafet, sai dai kuma babu wanda yasan halin da take ciki a masarautar, kasancewar babu wanda ta sanarwa.
Tana cikin wannan yanayin ta jiyo sautin muryar jakadiya tana mai kwaɗo sallama daga bakin ƙofa.
Dasauri ta gyara zamanta tana sakin fuskar ta sosai, tayarce koda jakadiya ta shigo ba zata fuskanci cewar bata da lafiya ba, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wa'alaikumu salam, lale marhabun da Jakadiya." Ta ƙarasa maganar fuskar ta ɗauke da murmushi.
Yayin da itama Jakadiya ta danno kanta zuwa cikin ɗakin bakin ta amatuƙar washe.
Direct ta doshi bakin danƙararen haɗaɗɗen gadon dake cikin ɗakin yake.
Wuri ta samu ta zauna tana mai facing ɗin Gimbiya Fulani, tare da jingina da katakon gadon da yake abayan ta, tukun ta buɗe baki cikin tsantsar far'ah tana mai faɗin. "Barka da hutawa Gimbiya Fulani, ɗiyar Sarki jikar Sarki, kana matar Sarki, sannan kuma uwar Sarkin gobe." Ta ƙarasa maganar tana mai kai hannun ta da yake riƙe da layoyin nan bayan ta ta kifesa aƙasan kafet ɗin nan.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani tayi murmushi tana mai buɗe baki tace. "Jakadiyar Sarki kenan, amintacciya kuwa abokiyar shawarar Sarki, wato ke dai ako da yaushe bakya taɓa gajiya da fasawa mutane kai ko?"
"Haba dai Gimbiyar mu, ai bawani fasa kai, duk wanda kikaji an faÉ—a masa to ya kai afaÉ—a masa ne dama, domin kuwa aduk faÉ—in gidan nan babu wata Æ´ar lele bayan ke a wurin mai Martaba, sabo da ke kaÉ—aice kika ajiye magajin sa acikin gidan nan, kinga kuwa yabo gareki ya zama dole."
Jakadiya ta faÉ—a tana mai sake matsar da hannun ta baya fuskar ta É—auke da murmushi, ba tare da ta bari Gimbiya Fulani ta lura da itaba ko kaÉ—an.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta É—an saki gajeran murmushi, sabo da jin kalamin Jakadiya da tayi, bayan kuma tasan da zata futa daga nan É—in ta tafi wurin wata itama hakan zatai mata, tukun daga bisani ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in. "To Jakadiya abar dai zancen haka kawai, atafi na gaba kuma."
Murmushi Jakadiya tayi tana mai sake kai hannun ta baya tare da gyara zaman ta awurin, tayarce Gimbiya Fulani ba zata gane abun da take yi ba, tukun tace. "Dama mai Martaba ne ya turo ni gareki akan nazo na jiye masa lafiyar jaririn sa, domin kuwa akullum yana faÉ—in cewa mafarkin sa na nuna masa namiji ne É—auke acikin ki wannan karan ma."
Murmushi itama Gimbiya Fulani tayi tana mai lumshe idanuwan ta, domin kuwa harga Allah ta gaji da surutun Jakadiya, gaba ɗaya ma ta ƙagara ta tashi ta futa ko taji da abun da take ji, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata tana mai faɗin. "Hmmmm! Mai martaba kenan, to in kin koma sai kisanar dashi cewa, Baby na cikin ƙoshin lafiya."
"Tom shikenan ni zan huce, na barki lafiya Uwar Magaji." Ta ƙarasa maganar tana mai hulla layoyin nan ƙarƙashin gadon da sauri, sannan ta miƙe tsaye fuskar ta ɗauke da tsantsar murmushi, tana mai sake faɗin sai da anjima."
"Allah ya kaimu na gode." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai miƙar da ƙafafuwan ta akan kafet ɗin nan.
Yayin da Jakadiya kuma ta huce ranta fal farin ciki, sabo da ganin da tayi ta samu nasarar aiwatar da abu É—aya daga cikin abubuwan da zatayi cikin salama.
Tana zuwa ƙofar ɗakin tayi sa'a kuwa babu ko mutum ɗaya dake cikin falon.
Ganin hakan da tayi ne ya sanya ta fara waige-waige, sai da ta tabbatar da babu ko ƙuda dake kallon ta acikin ɗakin, tukun ta sanya hannun ta jikin haɓar zanin ta tana mai ciro ƙullin maganin nan daga cikin sa.
Sake wawwaigawa tayi taga dai still babu kowa, sannan ta kwance sa cikin sauri tana mai zubasa abakin ƙofar ɗakin da matuƙar sauri, tukun ta juya tana mai yin gaba abun ta, bayan ta mayar da maganin cikin haɓar ta da zummar taje ta zuba abakin turakar mai martaba ma.
*ƘASAR MALIN, JAHAR RUMAN.*
Ƙarfe goma dai dai na safe jirgin su ya ɗaga ta cikin ruwa, yana mai ɗaukar hanyar da zata kaisa Ƙasar Hausa, bayan su Aishatu sun gama koke-koke ita da ƴan uwanta, kana suka mata fatan Allah ya sauke ta lafiya, tare da al'ƙawarin suna nan zuwa idan ta sauka.
Sosai zuciyar ta ke cigaba da tsinkewa, gaban ta na wani irin faÉ—uwa, alokacin da jirgin su ya fara nitsawa cikin hanya.
Jin ta take wani iri, gaba ɗaya jikin ta yayi matuƙar yin sanyi, ga kuma zuciyar ta dake cigaba da tsinkewa, yarce kasan ranar da aka sanar mata da mutuwar mahaifin ta.
Addu'oi ta fara karantowa acikin zuciyar ta ba tare da ta sanarwa IshaÆ™ halin da take ciki ba.
Sai dai kuma shima É—in duka yana lura da sauyawar tata, kasancewar akusa da shi take, amma sai bai kawo komai ba aransa, ya dangana hakan kawai da zafin rabuwa da ahalin tane ya sake sanyawa ta koma haka ba komai ba.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Ko da Jakadiya ta bar part ɗin Gimbiya fulani direct ta doshi turakar mai martaba, tayi sa'a kuwa babu wanda ta samu a wurin kamar yacce tai fata, hakan yasa ba tare da ta tsaya ɓata lokaci ba ta sake ciro ƙullin tsuman nan ta kwance sa, tana mai baɗasa abakin ƙofar, tukun tayi sauri ta koma baya cikin tsantsar farinciki.
Aɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, sosai ciwon da take ji ya cigaba da ƙaruwa, barin ma bayan lokacin da aka idar da sallahr magariba amasallacin dake cikin masarautar, amma duk da haka tai shiru da bakin ta ba tare da ta sanarwa kowa ba, haka kuma koda dare yayi bata tafi turakar mai martaba ba, duk da kasancewar itace da shi ɗin yau.
Misalin ƙarfe goma ɗaya na dare ciwon naƙuda ya sake turnuƙe ta mai matuƙar tsanani, banda cizon leɓe tare da yarfa hannu babu abun da take ai'kin yi awannan lokacin.