← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 79

Sashe 48

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya miƙa hannun sa da yake wata irin rawa yana mai riƙe linzamin dokin da shi, tukun ya fara ɗaga ƙafar sa ɗaya yana mai shirin hawa dokin, amma sai gaba ɗaya yayi baya yana shirin faɗuwa a ƙasa.
Ganin haka da wannan mutumin da yake riƙe da dokin nasa yayi ne, ya sanya matsawa kusa da shi da matuƙar sauri yana mai tarosa a hannun sa, sannan ya ƙara cicciɓa sa yana mai ɗora sa a saman dokin ba tare da ya tsaya kallon fuskarsa ba, domin kuwa shi duk atinanin sa ko rashin sabo da hawan da baiyi bane da kansa ya sanya yanzun ma ya kasa hawa.
Yayinda shi kuma Asad yana hawa saman dokin nan yaji kansa ya sake yin wani irin bala'in sarawa da matuƙar ƙarfi.

Rumtse idanuwansa yayi yana mai ɗanyin zillo akan dokin tare da cije leɓen sa na ƙasa da bala'in ƙarfi, take kuwa leɓen ya futar da wata irin tsartuwar jini, alamun ya fashe kenan!
Tukun daga bisani ya fara buÉ—e idanuwan sa a hankali yana mai jin numfashin sa na wani irin fuzga.

Buɗe idanuwan nasa yayi dai-dai da lokacin da Al'amin ya riƙe linzamin dokin sa yana mai ɗan dukan jikin sa da hannu, take kuwa dokin ya zura a guje yana mai yin gaba, kamar yacce na Babban yaya ya riga yayi gaba tini.
Ganin hakan da Asad yayi ne ya sanya sa shima miƙa hannun sa ɗaya yana mai damƙar linzamin dokin.
Ai'ko kamar jira dokin yake yi ya riƙe sa yayi wata irin zabura yana mai sakin haniniya da matuƙar ƙarfi ya fara sakin gudu.
A kuma dai dai lokacin jikin Yarima Asad ya fara wata irin bala'in karkarawa, numfashin sa na wani irin fuzga da matuƙar ƙarfi.

Wata irin gigitattar ƙara Babban Yaya ya saki a dai-dai lokacin da ya juya dokin sa yana son yayi wani wasa da shi, sabo da yadda idanuwansa suka hango masa Yarima Asad ya saki linzamin dokinsa dokin na kan gudu, yana mai y....................✍

*A GASKIYA NA DENA SAKIN LINK NA GRUOP 'DINA, SABODA YAWAN B'ATA GARI DA WA'YAN DA BA KARATUN SUKE BA DA SUKE SHIGOWA, DAN HAKA GA DUK MAI SON KASANCEWA ACIKIN GROUP 'DIN B'AKAR MASARAUTA, AMMA FA IDAN YASAN YA IYA COMMENT DA SHARHI SAI KU TUNTUB'ENI TA NUMBER WHATSAPP 'DINA KAMAR HAKA. 08038135929. K'OFA ABUD'E TAKE GA MASU SO A TALLATA MUSU HAJARSU A DUNIYA KUMA ZAKU IYA TUNTU B'ATA TA NUMBER.*

*BY*
UMAR FARUQ*D*

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 19*

Yin baya gaba É—ayan sa.
Da matuƙar sauri Babban Yaya ya dire daga kan dokin sa, yana mai hankaɗe mutanen dake wurin yayi wurin da ƙanin nasa yake da bala'in gudu, kamar yadda mutane da dama suka juya wurin, ta sanadin ihun da yayi da yaja hankulan su zuwa wurin, amma sai dai kash, gaba ɗayan su sun makaro, domin kuwa tun kafin su isa wurin Yarima Asad ya faɗo ƙasa ta baya, kana dokin ya take ƙirjin sa da ƙafafuwan sa yana mai yin gaba!

Wata irin zabura yarima Asad Yayi ƙirjinsa na ɗagowa sama adai-dai lokacin da dokin ya taka ƙirjin nasa, tukun daga bisani ya koma yana mai zubewa a ƙasa babu alamun numfashi tattare da shi!

Wata irin mahaukaciyar ƙara Babban yaya ya buga alokacin da ya ƙarasa kusa da ƙanin nasa, sabo da yarce ya gansa a sassanƙare, gashi babu ko alamun numfashi tattare da shi, kana daga bisani ya zube guiwoyin sa aƙasa yana mai janyo Asad cikin jikin sa yana girgizasa, tare da kiran sunan sa.

"Asad! Asad!! Asad!!!"

Babban yaya yake faɗe cikin tsantsar ruɗu yana mai ɗan marin fuskar sa tare da girgiza sa, sabo da yadda yaga gaba ɗaya jikin sa ya sandare ya koma tamkar sanda, domin kuwa babu wata gaɓa da tayi saura wacce ke motsawa a jikin sa.

Kafun kace tak tuni wurin ya cika da Al'umma tako ina ana kallon su.
Yayin da shi kuma Babban yaya ya fashe da wani irin gigitaccen kuka jikin sa na rawa, gumi na tsattsafo masa cikin jikin sa.

"Asad dan Allah ka temake ni ka tashi kar kamutu kabarmu kaji."

Ya sake faÉ—a a gigice yana mai cigaba da girgiza sa.

Acan ɓangaren Gimbiya Fulani cikin gida kuwa, tunda akayi sallahr la'asar ta futo daga cikin ɗakin ta tana me neman Asad, ba dan komai ba kuwa sai dan kawai ta sanya sa yayi azkar ɗin yamma, kamar yacce duk ranar duniya take sasu suke yin su, wato azkarul sabahu wal'masah, da suke a cikin hisnul muslim wanda Annabi yake yi ya kuma koyar.
Amma sai dai har ta gama duba duk inda yake tsammanin zata gansa bata gansa ba, hakan ne yasata fahimtar yana hurin mai martaba ya tafi ya shirya, ba dan ranta yaso ba ta juya zuwa cikin ɗakin ta jikin ta duk ba daɗi, tana mai fatan Allah yasa yayi azkar ɗin da kansa, domin kuwa tasan sa da wasa muddin basa sa tayi ba haka yake cewa ya manta, ba kamar babban yaya ba da baya taɓa ƙinyi ko a ina yake kuwa, hakan yasa ko kaɗan bata da fargaba akan sa, domin kuwa tariga data sani muddin wani abun ya same sa to muƙaddari ne kawai daga Allah, ba wai dan rashin addu'a ba.

Tana nan zaune a cikin ɗakin ta kan tsakiyar gado hannun ta riƙe da Baby, wata kuyanga ta faɗo cikin ɗakin bako sallama a bakin ta, sai faman haki da take ta saki kawai.

Da sauri duka mutanen dake a cikin É—akin suka kai idanuwan su gare ta, yayin da wasu daga cikin su kuma suka buÉ—e baki suna masu faÉ—in. "Ke ko lafiya kika faÉ—owa mutane cikin É—aki a haka?"

Bata iya basu amsa ba, sai gaba da ta cigaba dayi zuwa wurin da Gimbiya Fulani take cikin tsantsar ruÉ—u da tashin hankali.

"Yay...Yarima...ne ya faÉ—o...daga saman doki afil..."

"Me kike son kice mun ne haka, shin wane Yariman ne ma ya faɗo daga saman doki?" Gimbiya fulani ta faɗa a haukace bayan ta diro daga kan gadon da take hannun ta riƙe da ƴar jinjirar ta.
Yayin da sauran mutanen dake a cikin ɗakin ma duk suka miƙe tsaye hankula su a bal'in tashe.

Da sauri Gimbiya Fulani ta ratsa ta cikin mutanen nan da suke a cikin É—akin ta tana mai kama hanyar waje, ba tare data É—au ko da mayafi ba, tsabar ruÉ—un da take a ciki, domin kuwa hankalin ta idan yayi dubu sai da duka ya tashi.

Ganin hakan da sauran matan cikin ɗakin sukayi ne ya sanya su mara mata baya, suma duk hankulan su a matuƙar tashe.

Ƙarasawar ta bakin ƙofar futa daga cikin fallon nata yayi dai-dai da lokacin da Babban Yaya ya danno kansa cikin falon, rungume da Asad a ƙirjin sa yana mai sakin wani irin kuka a matuƙar haukace.

Take a wurin kuwa jikin Gimbiya Fulani ya ɗauki wata irin karkarwa, kana ta kasa yin gaba ta kasa yin baya, sai mamewa da tayi a wurin da take idanuwan ta ƙur akan Ƴaƴan nata guda biyu, yayin da zuciyar ta kuma ke wani irin gudu fiye da misali, fargaba da tashin hankalin abun da zata gani ta kuma ji sukayi matuƙar lulluɓe ta.

"Mamy na dan Allah kicewa Asad kar yatafi ya barni, mamy kice masa ya tashi, dama ni sai da nace masa kar yahau doki bazai iyaba, amma yace ya iya kuma yana hawa ai dama, gashi kuma yanzu ya faɗo dokin ya taka ƙirjin sa."
Babban yaya ya faɗa a wani irin haukace yana mai durƙushewa a gaban mamay'n tasu da ya ƙaraso, tare da sakin wani irin gigitacce kuka.
Girgiza kai Gimbiya Fulani ta farayi tana mai zube guiwoyin ta a ƙasa
Da sauri Hadima Larai ta ƙaraso wurin da take tana mai amshe baby'n hannun ta, sabo da yadda taga tana shirin yadda ta ba tare data sani bama.

Cikin sauri ta miƙa hannuwan ta da suke bal'in rawa, tana mai janyo Asad daga jikin Babban Yaya ta dawo da shi kan cinyar ta.
Kana ta É—aga tafin hannun ta É—aya tana mai É—an marin fuskar sa, bakin ta na furta kalmar.
"Zaki! Zaki!! Zaki!!!"
Amma taji shiru ko alamun motsi babu tattare da shi.
Hakan ne yasa ta janye tafin hannun nata daga kan fuskar sa tana mai matsar da shi zuwa wurin rawanin da yake sanye a kansa ta tunɓuke sa ƙasa, tana mai cusa ƴan yatsun hannuwan ta a cikin lallausar sumar kansa.

Da sauri ta rumtse idanuwan ta tana mai janye Æ´an yatsun nata daga cikin sumar sa, sabo da wani irin tururi da taji ya dake su mai tsantsar azabar zafi.

"Ku bani ruwa! Ku bani ruwa!! Sun ƙone mun kan yaro da huta!"" Ta faɗa a wani irn haukace tana mai juyawa ta kalli dandazon jama'ar da suke zagaye da su.

Cikin ƴan sakanni sai ga wasu mata nan har guda biyu sun miƙo mata ruwayen a cikin jarkokin su kamar yacce ta buƙata

Da mtuƙar hanzari ta buɗe murfin jarkar bayan ta warce ta a hannun matar, tukun daga bisani ta ɗaga ta tana mai tsiyaya ruwan a tsakiyar kan Asad, tare da kai yatsun hannuwan ta cikin sumar tasa ta fara cuɗa ta hankali a bala'in tashe.
A kuma dai-dai wannan lokacin Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗo cikin falon a matuƙar hargitse, ba tare da yayi ko sallama ba.

*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULÆŠE.*

Yau take ranar sunan jinjirar da Gimbiya Kaɓel ta haifa, hakan ne yasa ko ina ka kalla a cikin Masarautar kake ganin jama'a iri-iri, tun daga kan Sarakai na wasu masarautun maƙotan su har zuwa hadiman gidan suna ta giftawa, yayin da gaba ɗaya fuskokin su suke ɗauke da tsantsar farin ciki da annashuwa.
Tun bayan Sallah asuba aka yanka shanu har kimanin guda takwas narka-narka lafiyayyu a gidan, kana yarinya taci sunan Kakar ta, wato mahaifiyar LamiÉ—o, amma za'ana kiran ta da HADDIYAL.

Sosai akai shagali irin shagalin da ba ataɓa yin kamar sa ba a cikin gidan, kana aka baiwa jinjirar tsafuka kala-kala, a cewar su hakan shine ƙarshen gatan da zasu yi mata a duniya.

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI MASARAUTAR WASAI.*
Chapter 48 · 0% Book details