← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 79

Sashe 11

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tana sama tana ai'kin tinanin ta na sabo daka tafi kabar ta cikin sa mana." Mahaifin nasa ya faÉ—a yanayin sa na sauyawa lokaci guda.
Shima Sheikh Ahmad gaba ɗaya sauyawa yay, jikin sa duk yay mugun yin sanyi, yayin da ita kuma kakar tasu ta buɗe baki tana mai faɗin. "Aini na rasa gane wace irin mace ce Ai'shatu, ace shekaru ɗai-ɗai ɗai-ɗai har kimanin shekaru talatin da faruwar abu amma kullum jiya iyau abu yaƙi hucewa."

"To duk wace sila, da kinbi ta maganar Abba da yace baza taba ai'da duk hakan bata faru ba." Sheikh Ahmad ya faɗa yana mai miƙewa ya doshi hanyar stairs.

"To mara kunya fitsararre, daka tsaya baka tashi ba mana kaga yarce zansa yanzu yanzu ubanka ya mammake mun kai, sha-sha-shan yaro kawai, Sheikh ɗin ƙarya Malamin kwali kawai." Tsohuwar ta faɗa da ƙarfi tana mai bugawa bayan sa harara.

"Ke kika jiyo dai." Sheikh Ahmad ya faɗi haka ƙasa ƙasa yana mai ƙarasa hayewa sama.

"Gunguni kake min ko, ai'ko wallahi zaka futo ne kasame ni ina nan babu inda zan matsa daga ni har baban naka, ai dai nasan ba kwana zakai aciki ba dole ka futo ka tafi wurin bursun-sunar matar nan taka da ko É—aurin zani bata iya ba."
Sheikh Ahmad ya jiyo sautin kakar tasa tana faÉ—in haka adai dai lokacin da yake shirin shiga É—akin mahaifiyar tasa.
Taɓe baki yay yana mai danna kansa cikin ɗakin.
Zaune ya hange ta acan ƙarshen gado sanye da maroon ɗin hijab ta haɗa kai da guiwa.

Tsaye yay daga bakin ƙofar yana mai kallon ta ba tare da yace komai ba. Sosai yake jin ciwo acikin rai da zuciyar sa aduk lokacin da zai tadda mahaifiyar tasa cikin damuwa, ji yake ina ace yana da yarce zaiyi ya yaye mata damuwar ta, tabbas da ko kwana ɗaya baza'a sake ba sai ya samar mata da abun da take so, kafun ta koma ga mahallicin ta.

"Assalamu alaikum ya Ummi na." Ya faÉ—a da sauti cikin tattausar muryar sa daga inda yake.

Ahankali ta janye kanta daga tsakan-kanin cinyoyin ta, tukun ta ɗago fuskar ta ɗauke da murmushi wanda kallo ɗaya zaka mata kasan na yaƙe ne tana mai faɗin. "Wa'alaikumu salam yaro na!"

Ajiye jakar dake ɗauke ahannun sa yayi akan kujerar da take agefen sa, tukun ya fara ɗaga ƙafafuwan sa ahankali yana mai dosar gadon.

Hawa yayi kan gadon yana mai matsawa kusa da inda mahahifiyar tasa take ya zamto suna facing ɗin juna, tukun ya tanƙwashe ƙafafuwan sa agaban ta, kana ya miƙa hannuwan sa yana mai kamo tafukan hannayen ta ya haɗa dana sa ya rumtse su wuri ɗaya, tukun ya ɗaga idanuwan sa yana mai kallon ta, kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa ƙwalla na tattaruwa acikin nata idanun, kana ya buɗe baki cikin sanyin murya da taushi yana mai faɗin. "Sh...............✍

#COMMENTS ND SHARE PLS

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹

_*NA*_

UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*PAGE 04*

"Shin har sai zuwa wane lokacin ne zakicire damuwa aranki ummi na?" Ya faÉ—a yana mai kallon ta tare da murza tafin hannhn ta dake cikin nasa ahankali -ahankali.

"Har sai ranar da rabbi samawati wal'ard ya karɓi rai da ruhina." Ta faɗa tana mai kallon cikin idanuwan ɗan nata ƙwalla na tsinkewa daga cikin idanuwan ta.

"Subahanallah! Ummi na me yasa zakice haka? Ina al'ƙawarin da kika mun na cewar ba zaki ƙara kuka ba?" Ya faɗi haka muryar sa na rawa shima. Yayin da ita kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kayi haƙuri yaro na, domin ko na kasa cika sa, sannan kuma bana tinanin zan'iya cika sa!
Ba daga ni ɗin bace ba, ƙaddara tace tazo da hakan yaro na."

"Tabbas na sani ƙaddarar kice tazo da haka Ummi na, amma ya kamata ace kinyi abun da zaki cinye ta, ko dan kisamu tagomashi awurin ubangijin mu, domin ko duk musulmi na ƙwarai mumini ansan sa da yarda da ƙaddar mummuna da kyakkyawa ne Ummi na, shin me yasa kema ba zaki rungumi taki da hannu bibbiyu ba, zuwa yanzu kibarwa Allah komai." Sheikh Ahmad ya faɗa yana mai cigaba da murza tafin hannun ta, tukun daga bisani ya ɗora da cewar. "Dan Allah Ummi na ki taimaka ki rage sanya kanki acikin damuwa ko domin lafiyar ki, kinga gaba ɗaya yau satin ki biyu da baro asibiti duk ta sanadin damuwar da kike yawan yi, dan haka dan Allah ina son kimun al'ƙawarin bazaki ƙara yin kuka ba, ko kuma zama wuri ɗaya kina tinane-tinane Ummi na." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi yana mai kallon ta.

Murmushin yaƙe ta saki tana mai kallon sa itama, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Na gaji da ɗaukar al'ƙawain dana san bazan iya cika sa ba, idan har nace na maka al'ƙawarin bazan ƙara tinani ba daga yau ba to kasani tabbas ƙaryace kawai na faɗa, domin ko koda nayi ƙoƙarin yin hakan ako da yaushe bana iyawa, ko kaɗan nima ba'ason raina nake haka ba, kuma bawai dan hakan na rage mun raɗaɗin abun da nake ji azuciya ta ba, sai dai babu yarce zanyi tinani agareni ya zama dole Yaro na.
Akullum ako da yaushe idan na tuna yarce aka rabani da jariri na ta ƙarfi, awurin dana haife sa ba tare dako ɗaukar sa nayi ba, ina mai jin zuciya ta na wata irin suya ne, ina mai jin raina na tsan-tsar tafasa da ƙuna, ina mai jin ƙwaƙwalwa ta na zafi, hankalina na sake tashi, komai na dawo mun sabo in dinga ganin kamar alokacin abun ke faruwa! Abu na biyu kuma da yake ƙara sanya ni cikin damuwa shine, canzawar mafarkin dana sabayi akan matashin da nake faɗa maka daga mai daɗi zuwa akasin sa, rabon da nace maka nayi bacci mai daɗi ni kaina har na manta Yaro na, domin ko da zarar na kwanta nake ganin sa acikin mugun yanayi yana mai miƙo mun hannun sa dan na taimake sa, amma sai dai da zarar na matsa wurin sai nima awurgar dani gefe, sannan aja sa ai gaba. To ko taya ya kake ganin zan iya dena tunani da shiga damuwa Ahmad?"
Mahaifiyar tasa ta faɗa ƙwalla na jiƙa mata fuska, har kuma lokacin bata fasa kallon saba kamar yacce shima bai fasa kallon ta ba.

Shi kanshi sheikh Ahmad wani irin raÉ—aÉ—i da suya yake jin zuciyar sa nayi masa.
Cikin sanyi ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Zaki iya denawa Ummi na, addu'a kawai zaki dingayi kamar yacce kika kasance kina yi abaya, sannan kuma aduk lokacin da zakiji abun na faɗo miki arai, to ki yawaita ambatar. *Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, lahaula walaƙuwwata illah billah! Allahumma ajirni fi musibati, wa'aklifni kairan minha! Hazbunallahu wani'imal wakil.* Da izinin Allah zaki samu sauƙin raɗaɗin da kike ji azuciyar ki tsawon shekara da shekaru, dan haka yanzu ki tashi mu tafi fallo wurin Abba da Kaka, sabo da idan kina zama cikin murtane shine bazaki dinga tinawa da abun ba akai-akai ba.
Ya ƙarshe maganar yana mai ɗaukar yatsun hannun sa ya fara ɗauke mata hawayen da suke kwance akan fuskar ta.

"Allah yayi maka albarka Yaro na, rabbi yasa kaima ƴaƴan ka suji ƙanka kamar yacce kake jin ƙanmu muma." Ta faɗa tana mai sakarwa Sheikh Ahmad murmushi, yayin da shi kuma ya miƙe tsaye yana mai sauka daga kan gadon fuskar sa ɗauke da murmushin shima, tukun ya sake miƙa mata tafin hannun sa ta riƙe sa, sannan itama ta sauko suka kama hanyar da zata sadasu da waje tare.

*JAHAR KAGUL, MASARAUTAR FULÆŠE.*

Sai da ta gama shawagin ta tare da abubuwan nishaÉ—in ta, tukun ta juya cikin takun ta wanda shi kaÉ—ai abun kallo ne, tana mai kama hanyar da ta biyo.
Tayi nisa sosai tana shirin fucewa daga cikin wurin, sai ga wani mutumi nan mai kimanin shekaru arba'in ya dunfaro inda take da matuƙar sauri har yana ɗan haɗawa da gudu gudu.

"Ranki ya daɗe!" Mutumin dake sanye da kayan fulani rataye da sanda akafaɗar sa ya faɗa da ƙarfi, sabo da ganin da yayi tana shirin yin nisa, kasancewar shi ta ɓangaren kudu ya ɓullo wurin, saɓanin ita kuma da take yin gabas.

Juyawa tai baya dan taga ko wanene. Murmushi ta saki daga inda take sabo da fuskar da tai arba da ita, tukun ta koma jikin wata bishiya da take kusanci da ita tana mai jingina da ita tare da É—aga kanta sama.

"Barka da warhaka kyakkyawar Gimbiyar Masarautar Fulɗe, Sarauniya kuma ga tsuntsayen Masarautar Fulɗe." Ya faɗa adai-dai lokacin da ya ƙaraso gaban ta yana mai durƙusar da kai ƙasa.

"Barkan ka dai amintacce na." Ta fada tana mai kallon sa itama, tukun ta ɗora da cewar. "Ya aka kwana ne, me ake ciki dan gane da binciken ka tun daga na jiya har kawo na yau?" Ta faɗa idanuwan ta ƙur akan sa.

Sake durƙusar da kansa ƙasa yay, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amsar dai duk itace take mai-maita kanta ya shugaba ta, ma'ana jiya da yau ɗin ma duk Duhu ne yake bayanna amai makon ganin wurin da yakasnce ashi, amma sai dai abu ɗaya dana sake ganowa shine, tabbas mutum ne shi ɗin ba Aljan ba." Ya ƙarashe maganar yana mai sake durƙusar da kai ƙasa. Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai juya baya ta fara taku daga inda take zuwa gaba, sai dai tayi yayi taku biyar, tukun ta tsaya cak awurin da take tana mai juyowa ta sake fuskantar mutumin nan da ta kira da Amintaccen ta. Sannan ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Na riga na daɗe da sanin Giɗaɗo am mutum ne ba Aljan ba, dan haka daga yau bana buƙatar sake jin wannan daga gare ka, yanzu kai zaka iya tafiya, amma katabbatar ka ƙara azama wurin tayani binciken inda yake agaba, domin ko gaba ɗaya shine duniya ta ayanzu, sannan kuma ina jin muddin ban same saba to komai na iya faruwa dani." Ta faɗa tana mai rumtse idanuwan ta da ƙarfi.
Chapter 11 · 0% Book details