← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 79

Sashe 15

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dum! Dum!! Dum!!! Kakejin sautin ƙarar harbin bindigu na tashi da matuƙar ƙarfi, kasancewa tawowa da Sarki yayi tare da tawagar sa.
Zagaye yake atsakiyar Fadawa da Dogarai, hannuwan su ɗauke da wasu irin zura-zuran bulalai suna ta aikin buɗa hanya, tare da hankaɗe duk wani wanda ya kasance tsaye agaban su. Yayin da fadawa kuma ke aikin sakin kirari da matuƙar karfi yarce kasan zasu tsaga wurin, suna masu fadin.
"Takawarka lafiya garƙami wandon ƙarfe!
Lafiya jinjirin wata shakallo!
Lafiya jijjigen Addini!
Lafiya maida garin wani kango!
Lafiya darzaza amalen Sarakuna!
Lafiya bango madafar Bayi!
Lafiya mai kiran gabas da yamma ta amsa!
Lafiya numfashin duniya!
Lafiya ubangijin Bawa da Baiwa!
Sannu alafiya Alfanda bawanda!
Sannu alafiya Amalen Sarakuna!
Sannu Alafiya toya matsafa!
Lafiya mai ado da kurar yaƙi! Lafiya mai ado da kurar yaƙi!! Lafiya mai ado da kurar yaƙi!!!
Amin zulillah!
Amin kigon gabas maci yammawa!
Lafiya mai shari'ah daf da wuya!
Hifzullahi na Allah!
Kanzullahi bawanda!
Amincinka yafi ga linzami!
Ciki sannu alafiya uban gyayya!"

Haka suke ta aikin yi masa kirari da matuƙar ƙarfi suna masu dosar hanyar futa daga cikin fada. Yayin da maroƙa suma keta aikin sakin kiɗa da busa suna masu faɗin.
"Abdullahi jikan Abdullahi!
Majina gishirin yaro!
Dariyanka kukan yaro!
Tsawa mai ratsa gidan Arna!
Dan Ahmadu Autan Abdullahi!
Balaraben sarakuna jikan Abdullahi!
ÆŠan Massalacin juma'a jikan Massalacin juma'a!"

Haka suma suke ta faɗe suna masu busa algaitu da kakaki. Yayin da shi kuma Sarki Abdallah yake tafe atsakiyar su jikin sa sanye da wata azababbar alkyabba ruwan ƙwai mai matuƙar kyau, sai kansa da yake ɗaure da farin rawanin da yayi matuƙar ƙara futo da kwarjinin sa. Shi kansa hulla idanuwan sa yake acikin jama'a duk da gaba ɗaya fadawa da dogarai sun zagaye sa, dan yaga ta inda zai hango ɗan nasa mafi soyuwa aransa.
Ahaka suka ƙarasa bakin ƙofa gaban wasu danƙara danƙaran dawakuna da suka gaji da jin Ado ajikin su. Tukun fadawan nan suka baza rigunan su suna masu sake rufe sarki tare da faɗin. "Bisa haikawa da alheri, bisa dafkawa, bisa maikawa."

Basu dena faɗe ba har sai da suka tabbatar da ya hau kan dokin, tukun suka saki rigunan su ƴan lufudi kuma suka matso hannuwan su riƙe da bulalai suna masu buɗa hanya.
Yayin da ta fannin Babban yaya shima ya haye saman nasa dokin tini suna masu yin gaba, kasancewar sai bayan sun huce tukun Sarki zai huce, sai dai kuma har lokacin bai fasa faman wurga idanuwan sa cikin mutane ba dan ya hango ƙanin nasa, amma sai dai har suka ƙarasa filin hawa aka fara wasa da dokuna baiga ko Al'amin ba balle har yasa ran zaiga Asad, hakan yasa ya ƙudurta aransa da zarar sun gama hawan nan zai huce wurin Gimbiya Fulani Mamyn su, domin su tattauna da ita akan shawarar da ya yanke akan Yarima Asad, danko ba ƙaramun ciwo sukeji ba acikin ransu na hallayar sa shi da mahaifiyar su.

Ba'a tashi gama hawa ba sai gabannin magariba, tukun jama'a sukai ta watsewa kowa na komawa inda ya futo.

Afannin Babban yaya shima yana sauka daga kan doki ya huce masallacin su na nan cikin Masarautar.

Ko da aka idar da Sallah bai tsaya ko ina ba ya huce sashin mamyn su kai tsaye, domin yaje su tattauna akan yarce zasu ɓullowa Asad kamar yacce suke kanyi kullum.

*JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULDE.*

Cikin tsantsar firgici da ruÉ—u Gimbiya Haddiyal ta É—ago kanta tana mai watsa manya manyan idanuwan ta da suka sake yowa waje akan fuskar Dadden tata.
Tukun daga bisani ta fara ɗaga laɓɓanta tana mai girgiza kai, wasu irin hawaye na ɓallewa daga cikin idanuwan ta, yayin da ita kuma mahaifiyar tata ta janye idanuwan ta daga kan ta tana mai mayar dasu wurin Innahuro da take manne ajikin ta, ta fara shafa gashin kanta.

Zumbur Gimbiya Haddiyal ta miƙe tsaye yarce kasan wacce aka tsikara, jikin ta na tsantsar rawa, banda ai'kin girgiza kai da ɗaga laɓɓa babu abun da take iyayi, sai idanuwa data kefa mahaifiyar tata dasu, tukun daga bisani ta juya da matuƙar sauri yarce kasan zata kifa aƙasa tana mai dosar hanyar ɗakin ta.

Uhm! Mahaifiyar tata ta sauke ɗan gajeran numfashi tana mai bin bayan Gimbiya Haddiyal da idanuwa, tukun daga bisani ta taɓe baki tana mai girgiza kai, kana ta janye idanuwan ta daga kan hanyar tana mai ɗaukar inibin dake cike acikin ƙwarya wanda Innahuro keci ta fara ci itama.

Cilla ƙafafuwan ta kawai take aduk inda ya samu ba tare da tana lura ba, sabo da tsantsar tashin hankalin da take ciki, ahaka har Allah yakai ta cikin ɗakin ta lafiya.
Kai tsaye ta doshi gaban tanƙashe-shen mudubin da yake manne ajikin bango ɗakin, tana ƙarasawa gaban sa taja ta tsaya tana mai ɗora hannuwan ta akan sa ta dafa sa.

Kallon kanta ta farayi acikin madubin tana cigaba da girgiza kai, kana har lokacin kuma hawaye basu bar tseren gudu ba daga cikin idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Shin me Baffah ke nufi ne da zuwan Jauro (Yarima) Masarautar Yamma? Shin ina zan kai shi Gaɗaɗo am kuma? Inyi ya ya da soyayyar sa dake cunkushe aƙasan zuciya da ruhina?
Inaaa hakan bazai taɓa yuwuwa ba wallahi, babu wani ɗa namijin da yakai in kulasa balle har ya zamto miji gareni bayan Giɗaɗo am!
Ni Gimbiya Haddiya an halicceni ne domin Giɗaɗo am kaɗai kamar yacce aka hallice sa domin ni, dan haka babu tayarce za'ai in bari wani mahaluƙi ya zamto shamaki atsakanin mu, Wallahi! Wallahi Jauro'n Yamma kayi kaɗan na zamto taka, domin ko fatar ka bazata taɓa jure zafin bulalar shaɗin aure na ba, darajarkar bata kai ka mallaki ko takalmin ƙafata ba balle har na zamto mallakin ka, zanyi amfani da ƙarfin ikona wurin ganin na lalata gaba ɗaya shirin ku akaina."

Ta ƙarasa maganar da ƙaraji tana mai kaiwa bango duka, tukun ta juya tana mai yin taku biyu daga inda take, kana ta sake ja ta tsaya cak awuri ɗaya, tukun ta sake ɗaga laɓɓa cikin kaushi tana mai faɗin.
"Kai da kanka zaka koma kace musu banyi ba Jauron Yamma, domin ko bazan taɓa yimaka ba kamar yacce ba ayini dan nayiwa wani ba bayan Giɗaɗo am."
Ta ƙarasa maganar tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi bakin gadon ta.

Zama tayi akai tana mai buga uban tagumi da hannu bibbiyu, tare da kafe bangon dake kallon ta da idanuwa.

*JAHAR WASAI*
Anan cikin Masarautar wasai kuwa baki É—auke da sallama Babban yaya ya tura kansa cikin bedroom É—in Mamy'n tasu, kasancewar bai sameta afallo ba shiyasa yayo nan ciki.

Zaune ya hangeta akan darduma tafukan hannayen ta É—age asama tana addu'a, da alamun yanzu ta idar da sallah itama.
Wucewa yayi can ciki yana mai ƙarasawa bakin gado ya zauna tare da ɗaga tafukana hannayen sa shima suka ƙarasa addu'ar tare.

ÆŠago kai tayi tana mai kai idanuwan ta inda yake.
Dasauri ya sakko ƙasa yana mai ƙarasowa kusa da ita ya zauna, tare da tanƙwashe ƙafafuwan sa akan haɗɗaɗen kafet ɗin da yake shimfiɗe aƙasan ɗakin, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar ladabi da biyayya yana mai faɗin. "Barka da hutawa, tare da fatan kina yini lafiya Mamy na."

Murmushin ta wanda ya zamto kalar nasa dana Asad kamar yacce kamannin su suka zamto É—aya sak ta sakar masa tana mai kallon sa, tukun daga bisani ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in. "Alhamdulillah, fatan kuma duka kuna lafiya."

"Kowa lafiya ƙalau wallahi mamy na." Ya faɗa yana mai sakar mata murmushi, yayin da ita kuma ta sake gyara zama tana mai ƙara fuskantar sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Ya kuma taro ya tashi."
"Alhmdulillah Mamy." Ya faÉ—a shima yana mai sake fuskantar ta.

Gyaran murya tayi, tukun daga bisani ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in. "To ni dai nasihar da zan maka amatsayina na mahaifiyar ka kan wannan jagorancin da aka baka itace.
Atakaice shidai shugabanci ba wani abu bane face wani babban nauyi da Allah yake ɗorawa mutum, dan haka nake shawartar ka da ka zamto adalin shugaba wanda al'umnar sa zasuyi alfahari da shi, kayi koyi da shugabanci irin wanda fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wassallam yay. Domin ko ita shugaba garkuwace da ake yaƙi abayan ta, ake kariya da ita, dan haka idan shugaba yayi umarni da tsoron Allah yayi adailci to yana da lada, in kuwa ya ai'kata saɓanin haka to wannan laifi yana kansa. Bukharine ya rawaito.
Hakanan kuma wajibi ne shugaba ya zama mai adalci tsakanin sa da talakawan sa, sabo da adalci shine tushen rayuwa, kuma sai da adalci ne al'amura ke dai-daita duniya da lahira.
Sannan kuma Sheikhul Islam Ibni taimiyya yana cewa. Al'amuran mutane na duniya suna dai-daita ne da adalci da yake haɗe da nau'ika na zalunci, fiye da yadda al'amura zasu miƙe da zalunci acikin haƙƙoƙi, ko da kuwa basuyi tarayya azunubi ba, dan haka akace Allah yana tsayar da daular mai adalci koda kuwa musulma ce, hakanan akace duniya tana dawwama da adalci da kafirci, amma bata dawwama da zalunci da musulunci."
Ta faɗa idanuwan ta akan sa, yayin da shi kuma babban yaya ya durƙusar da kansa ƙasa yana mai sauraran ta jikin sa na tsantsar ƙara yin sanyi, kana kuma yana godiya ga Allah da ya azurtasa da uwa tagari acikin zuciyar sa.
Chapter 15 · 0% Book details