← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 79

Sashe 1

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read


🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎

👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹

_*NA*_

UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*BAƘAR MASAURATA YASHA BAMBAN DA SAURAN LABARAN, LABARI NE IRIN WANDA BAKU TAƁA CIKIN KARO DA KALAR SABA.*

*DUK ABUN DA ZAKU GANI ACIKIN LABARIN NAN ƘIR-ƘIRARRE NE, KAMA DAGA SUNAYEN GARURUWA HAR IZUWA NA MASARAUTU, KAMAR YACCE DUKA LABARIN YA KASAN CE ƘIR-ƘIRARRE.*

*BAN YARDA WANI KO WATA BA SU JUYAMUN LABARI TA KOWACE SIGA BA TARE DA IZININA BA.*

*PAGE 01*

_SHIMFIÆŠA_

*ƘASAR HAUSA*

Ƙasa ce mai tsantsar girma da faɗi, ƙasace wacce Allah ya azurta ta da mayawaitan al'umma, maban-ban ta ƙabilu da mazaunai daban daban, ƙasa ce mai ɗauke da jahohi 30 cif acikin ta, yayin da jahohin suka kasan ce ayanku na daban daban, ƙasa ce wacce ta kasan ce ƙasar hausawa, duk da dai basu kaɗai bane suka kasan ce acikin ta, sai dai kuma mafi yawan jahohin da suke acikin ƙasar yawan cin su duka na hausawa da fulani ne, wato dai sune masu ƙasar.

*MASARAUTAR WASAI*

Ɗaya daga cikin manyan masarautun da suke aƙarƙashin ƙasar hausa kenan.

JAHAR WASAI
Jahace mai matuƙar girma da faɗi, jahace wacce take ɗaya daga cikin manya-manyan jahohin da suke a ƙar-ƙashin ƙasar hausa, jaha ce ta musulunci da musulmai, jaha ce wacce take da manyan ƴan kasuwa tare da manyan kasuwani acikin ta, domin ko itace ta kasan ce cibiyar kasuwan ci ta ƙasar hausa. Yayin da ita kuma masauratar wasai ta kasan ce ɗaya daga cikin manya manyan masarautun da suke acikin ƙasar hausa, sannan kuma ta kasan ce masarauta ɗaya acikin jahar wasai, wato dai itace mamallakiyar jahar gaba ɗaya.

Masarautar wasai masarauta ce mai tsantsar girma da ƙarfin mulki, masarauta ce wacce ta kafa tarihi acikin ƙasar hausa, masaurata ce mai ƙarfin mulki wacce ake ji da ita aduk faɗin ƙasar hausa harma da ƙasashen da suke maƙota ka da ƙasar.

***
*JAHAR KAGUL*

Itama dai jahar kagul ta kasan ce dlɗaya daga cikin manyan jahohi ne da suke aƙasar hausa, sai dai ita kuma jahar kagul tana ayankin yammacin ƙasar hausa ne, saɓanin jarah wasai da take a arewacin ƙasar hausa.
Jahar kagul ta kasan ce jahar fulani ce ita, wato dai kusan duk mazaunan cikin ta sun kasan ce fulani makiyaya ne, sai dai ita kuma ta kasan ce ɗaya daga cikin jahohin da addinin musulunci baiyi zurfi acikin ta ba, domin kuwa mafiya yawan mazaunan cikin ƙasar ko karatun sallah basu iya ba bare aje ga sanin tauhidi da hadisai, kai ataƙaice ma dai sallahr duka bata dame su ba, domin ko hatta da gidan sarautar dake cikin ƙasar shima babu addinin acikin sa, dan kuwa babu abun da suka sanya agaba sai tsafi da harkar kula da dabbobin su, kasan cewar itace babbar jahar kiwo aƙasar hausa, domin kuwa kusan duk wasu shanu da ake kadawa acikin jahohi talatin da suke aƙasar hausa suna futowa ne daga jahar kagul.
Hakan yasa ɗaukacin mutanen dake cikin jahar suka maida hankulan su akan kiwo da asirce asricen da zasu bawa dabbobin su kariya fiye da komai agidan duniya, ciki kuwa har da addinin su, wato dai in taƙaice muku zance jahar kagul itace cibiyar kiwo ta ƙasar hausa.

*MASARAUTAR FULÆŠE*

Masarauta ɗaya ƙwal dake acikin jahar kagul, wato dai itace mammallakiyar jahar gaba ɗaya.
Masauratar fulɗe tana ɗaya daga cikin masarautu masu tarin dukiya da kafaffen tarihi acikin ƙasar hausa, masarauta ce ta fulani wacce ta kafa tarihi ta fannin harkar kiwo, domin kuwa duk wasu makiyaya da suke acikin ƙasar hausa kusan suna aƙar-ƙashin mulkin masarautar fulɗe ne.

Masaurata ce wacce ta haɗa wasu irin mutane acikin ta, waƴan da ko kaɗan babu Allah azuciyar su, duk da dai suna iƙirarin su musulmai ne ako da yaushe, sai dai gaba ɗaya jama'ar cikin masarautar babu wanda zaka tambaye sa wani abu akan addini ya iya baka amsa, ciki kuwa har da sarki mai ci, bar su dai su ta fannin tsaface tsaface anan suka fi ƙarfi, domin kuwa hatta da ɗan ƙaramin yaro dake cikin masarautar zaka same sa ɗauke da tsafin sa ne, wato ya iya tsafuka kala kala ankoya masa an kuma basa tun yana ƙarami, ga su kuma da wata irin baƙar zuciya wacce bata tanƙwaru wa, wato dai idan suka ce hakan za suyi babu wanda ya isa ya canza su daga hakan, haka kuma idan suka ce baza suyi ba to fa babu wanda ya isa ya sasu suyi, sannan kuma basa yafiya ga mutumin da ya zalince su ko kuma yake shirin cutar da su, ko yake farautar wani abu nasu muddin suka gano sa.
Hakan yasan ya babu wasu da suke iya shigo musu cikin ƙasa suyi musu satar dabbobi, duk da dai ansha kawo hara-hare daga jahohi daban daban, sai dai ako da yaushe idan ɓarayin sun shiryo sunzo babu wata riba da suke samu sai dai ma akarɓi ransu anan tsabar ƙarfin asirin su.

Gaba ɗaya mutanen cikin jahar kusan sun kasan ce fararen fata ne, masu matukar kyawun hallitar jiki da fuska, tare da yalwataccen gashi, kama daga mazan su har matan su, hakan yasa masu kuɗin ƙasar hausa suke yawan zuwa jahar ta kagul neman aure cikin ta, sai dai kuma koda sun je ɗin duk da yawan dukiyar da suke da ita ba afiya basu ba, kasan cewar su mutane waƴan da basu fiye yadda da wani bare ba musamman ma bahaushen mutum, balle kuma har su sake da shi.

****
*ƘASAR MALIN*
YAN KIN JAHAR KARFUZ.

Jahar karfuz ta kasance jaha mai matuƙar girma da faɗi, jahace wacce take aƙar-ƙashin ƙasar malin, jahace wacce Allah yayi ta da yawan manya-manyan ruwaye, tare da dogayen bishiyu da duwarwatsu, domin kuwa duk inda zaka bulla acikin jahar kusan zaka yanka ne ta tsakan-kanin dogayen korayen itatuwa tare da manya manyan ruwaye masu kwaranya.
Ba afiya yi musu rana ba duka ajahar tasu, koma nace kusan aƙasar tasu ta malin baki daya, sai dai kuma aduk lokacin da aka tashi yi musu to bata zuwar musu da sauƙi, dan ko hatta futa ba kowa ke iyayi ba idan ba dare ne yayi ba a'irin yana yin.
Ita dai jahar karfuz ta kasan ce jahar da babu musulunci acikin ta ko kaÉ—an, asalima gaba É—aya basu san mene ne musuluncin ba, mutane ne su waÆ´an da suke bautar gumaka, huta, ruwa da rana, wato dai gaba É—ayan su basu san Allah ba.

*BAƘAR MASARAUTA*

Masarauta ɗaya ƙwal dake cikin jahar karfuz, masarautar da basu san Allah ba bare suyi aiki da faɗar sa, masarautar da basu mai da kisan rai abakin komai ba, masarautar da rashin imani da yahudanci ya tattaru ya ƙare acikin ta, masarautar da suka mai da zubar da jinin mutum tamkar zubar da jinin rago.
Masarautar da take da matuƙar girma tare da ƙarfin mulki da iko, tsantsar zalunci da tarin yahudanci, dan ko ataƙaice su ko sallah ma basu san ta ba balle su san falalar ta har suyi ta.

Wannan kenan.

Tafe take cikin takun ta na tsantsar izza, isa tare da ji da kai.
Kyakkyawa ce ajin farko, duk da dai bata kasance farar fata ba, sai dai kuma baƙin ta shima bai zamto na muni ba, irin baƙin nan ne wanda hausawa kewa laƙabi da wankan tarwatsa. Tana da tsayi tare da faɗi da tudun jiki dai dai misali irin wanda kowa ke so. Tana da manya manyan idanuwa farare masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, yayin da bakin ta kuma ya kasance ɗan tsukut da shi mai ɗauke da jajayen laɓɓa akan sa, sai dogon hancin ta siriri da yake tsaye cak akan fuskar ta yarce kasan ɗora sa tayi. Kai ataƙaice dai gaba ɗayan ta bata da makusa tako ina, dan ko hatta da gashin dake kan idanuwan ta idan ba ƙura mata ido kayi ba sai ka rantse kace ɗora sa tayi, sabo da yarce suke da matuƙar tsayi.

GIMBIYA TASMIR kennan, ƴa mace ƙwalli ɗaya ƙwal ga sarki barbaru shugaban baƙar masarauta, gimbiya mai matuƙar kwarjini, wacce sautin takun ta kawai ke girgiza zuciyoyin bayi, gimbiyar da da zarar ta biyo hanya to babu wanda ya isa ya bayyana awurin idan aka cire ƴan rakiyar ta muddin bata kai ga wucewa ba tsabar ƙarfin ikon ta, gimbiyar da sautn muryar ta ke hautsina ƙwaƙwalen bayi, duk da dai ba fiye yin maganar tayi bama, dan azahirin gaskiya magana ma matuƙar wahalar da ita take yi, domin kuwa sai akawana atashi ba tare da ta furta koda kalma ɗaya ba ga kowa.

Sanye take da wata doguwar riga baƙa mai matuƙar tsayi da faɗi, tayar ce har take sharar ƙasar duk wurin da ta taka, yayin wasu matasan ƴammata guda biyu suke riƙe da wasu yankuna na daga jikin rigar sabo da ta rage sharar ƙasa. Ɗaure suke da baƙin ƙyalle aƙugun su, wanda duka tsayin sa ya tsaya a'iyakar gwiwoyin su, sai wasu ƴan ɓingilallun fararen riguna na yadi masu matuƙar faɗi babu tsayi sanye ajikin su, yayin da jikin rigunan kuma daga gaban su suka kasan ce ɗauke da zanen tambarin masarautar tasu, wanda aka ɗinka sa da baƙin zare adai dai ƙirjin su, sai fuskokin su suma zane suke da tambarin masarautar da sukayi ado da kwalli ta ko ina.

Yayin da gefe da gefen su harma da bayan su kuma wasu irin danƙara- danƙaran maza ke biye da su, hannuwan su ɗauke da zura zuran bulalai tare da takubbai soke aƙugunan su, wanda hakan ke nuni da sune dakarun ta, babu wanda ke sanye da riga ajikin sa, sai baƙin ƙyalle mai haɗe da gajeran wando iyakar gwiwa dake ɗaure aƙugun su, gaba ɗaya jikin su zane yake da tambarin masarautar tasu ta ko ina da akayi sa da baƙin fenti tun daga fuska har ƙafa. Kallo ɗaya zaka musu kayi matuƙar razana idan baka saba ganin su ba, sabo da yarce ƙwayoyin idanuwan su suka kasan ce jajaye, gasu su kuma baƙaƙe huluk dasu, duk wanda ya gansu ba sai anfaɗa masa ba zai san babu imani tattare da su, kai ataƙaice ma basu san saba ko kaɗan.
Chapter 1 · 0% Book details