← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 79

Sashe 42

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai akayi Hawa a kai wasa da dokuna irin wanda ba'a taɓa yin saba tun da ake Haihuwa a cikin gidan, domin kuwa hatta da shi Mai Martaba sai da yayi wasa da doki irin wasan da bai taɓayin kamar sa ba, wato wasa na ban mamaki, wanda yayi matuƙar ƙayatar da al'ummar wurin, yayin da zuciyoyin magauta kuma suka cika dam da baƙin ciki tamkar sayi bindiga, donin kuwa a cewar su wannan wasa da dokin kawai da sarki yayi shi yake nuni da ada duk ba haihuwa ake masa ba sai a yanzu ne akai masa, sannan kuma Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina matan sa suka sa aransu cewar duka bai ɗauki Ƴaƴan wurin su ba amatsayin Ƴaƴa, tunda a lokacin su su duk bai nuna irin wannan farin cikin ba, hakan yasa suka ƙudiri aniyar ganin bayan Baban Yaya da kuma Ɗan jariri Asad mai farin jinin jama'a.

"UNGUWAR ÆŠAN TANKI.*

Tunda su Aishatu suka dawo gida har kawo yau bata dawo hayyacin ta ba, domin kuwa ataƙaice ma har a gadon asibiti sai da aka kwantar da ita, sabo da jinin ta da yayi bala'in hawa.
Sosai hankalin duka jama'ar gidan dama duk dangin su yayi matuƙar tashi, a lokacin da labarin abun da ya faru ya riske su.
Kaka tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai futa da jin wannan baƙin labarin, tayi tsinuwa bila adadin ga mutanen Baƙar Masarauta, sannan kuma tayi nadamar sanya Ishaƙ ya bar Aishatu da tayi yafi a ƙirga, yayin da ta fannin Mahaifin Ishaƙ shima yaji ina ma ace ya hanasu tafiyar tare, sai dai kuma babu wani bawa da ya isa ya canza abun da Allah ya tsaro.

Lokacin da labarin ya riski dangin Aishatu na Jahar Ruman, suma hankulan su ba ƙaramun tashi yayi ba, hakan yasa tun a washegarin ranar suka haɗo kayan su da komai da komai nasu suka sake baro Ƙasar Malin cikin ɗacin rai, suna masu dawowa Ƙasar Hausa, Jahar wasai cikin rugar su da suka bari kafun su koma can.

Sosai Aisahtu ta fige ta rame, ta lalace dukan ta, domin kuwa har yau bata dena kuka ba da surutai kala-kala, musamman ma idan akace dare yayi, sannan kuma kullum idan ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yaron nata a hannun wata mata tana kula da shi.
Ganin da su Ishaƙ sukayi Aishatu taƙi kwantar da hankalin tane ya sa suka fara nemar mata addu'oin dan gana suna bata tana sha, sannan kuma suka sanar a massallatan Unguwar su cewar a taya su da addu'a, kana suma kullum suke kan yin ta, domin kuwa tamkar mahaukaci haka Aishatu take komawa idan tana surutai.
Yayin da su Ahmad da sauran ƙannen sa suke sata a gaba suyita aikin kuka, ataƙaice dai gaba ɗaya gidan sun koma abun tausayi.

*BAYAN SUÆŠEWAR SHEKARA HUÆŠU*

*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Sosai Bir yayi matuƙar girma tare da wayo da kyawu, domin kuwa idan mutum ya gansa muddin ba sanin shekarun sa yayi ba, sai yayi tinanin yakai irin shekara bakwai ɗin nan, sabo da girman jikin sa, har yanzu kuma yana a wurin Iyar Bayi ne, ita take kula da shi take masa komai, domin shi duk a tinanin sa ma itace Uwar sa, hakan yasa yake kiran ta da Iya ta, yayin da itama a koda yaushe take jin sonsa na ƙara ƙaruwa a cikin zuciyar ta fiye dana baya.
Zuwa yanzu shima har ya fara yin wasu abubuwan irin na bayi, waÆ´an da suka haÉ—a da É—ibar ruwa da kuma É—aukar icci na

Yanzu haka zaune suke a ƙasan inuwar wata bishiya suna wasa shi da abokan sa guda biyu.
Sanye suke d.............✍

*A PAGE ƊIN JIYA NAYI MANTUWA A WURIN FAƊIN SUNAN MATAR SARKIN WASAI TA BIYU MAI SUNA AMINA, YAYIN DA NI KUMA NA SANYA SUWAIBA, DAN HAKA AMINA SHINE SUNAN NATA, SUWAIBA KUMA SUNAN ƊAYA DAGA CIKIN ƳAƳAN HUWAILA NE BABBAR MATAR SARKI ABDALLAH.*

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 17*

Sanye suke da ƴan guntayen baƙaƙen wandina na yadi iyakar guiwoyin su babu ko riguna a jikin su dukan su.
Riƙe Bir yake da kwari da gwafa a hannun sa yana mai gyara danƙon jikin ta, kasancewar tana ɗaya daga cikin abubuwan da yake matuƙar so a rayuwar sa.
Tun da ya taso yaga mayaƙan Baƙar Masarauta na amfani da ita, sai shima abar take matuƙar birge sa, hakan yasa ko da yasuhe da ya futo daga ɗakin su muddin suna nan yake hucewa wurin su yaje ya tsaya yay ta kallon su, wani lokacin ma har ya ɗauki abar ya fara shirin gwada harbawa shima, hakan da ɗaya daga cikin maharban nasu ya gani ne yasan ya sa haɗawa Bir wata ƴar ƙarama dai-dai da shi ya basa, a ranar kuwa ba ƙaramar murna da farin ciki yayi ba, sannan kuma wuni yay adaji yana harbin tsuntsaye, har sai da Iyar Bayi taje ta kamosa da kanta da taji shiru, domin ko ita ko kaɗan bata son harkar kwari da gwafar da Bir ɗin yake yi, sabo da tana tsoron kar wataran aga ya ƙware da harkar amayar da shi cikin Maharban Masarautar, sabo da idan hakan ta faru to rabin rayuwar sa zata ƙare ne a yawon dajika, sannan kuma koda wani faɗan ya taso to yana ɗaya daga cikin mutanen da za'a na turawa, hakan yasa take ƙin abar sosai, sai dai shi kuma Bir akullum ƙara ƙaunar kwari da gwafar sa yake.

Tun yana ɗan ƙaramin sa yake da wata irin halayya ta taurin kai da kafiya, domin kuwa muddin baiyi niyyar yin abuba to ko ance yayi bazai taɓa yin sa ba, ko da za'a dake sa ne kuwa, haka kuma dan an dake san a banza, sabo da baya kuka kwakwata, sai dai mutum yayi ya gama, wannan dalilin ne yasa Iyar Bayi take kiran sa da suna JARUMI, saboda yadda yake da tsantsar jarumtar a ɗan ƙaramin sa.

"Jarumi! Jarumi!!"

Muryar Iyar Bayi dake tawowa wurin da suke ta daki dodon kunnen Bir da yake shirin harba tsinken gwafar sa jikin bishiya.

Da sauri ya juya ɓarin da take yana mai kai dara-daran kyawawan idanuwan sa kan fuskar ta, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Me ayi ne Iya yanju ma?"

"Wanka da cin abinci mana Jarumi, kaga su Mauzum tun ɗazu nayi musu wanka, gasu nan har sunzo kuna wasa tare, amma kai tun da kafuce tun safe kaƙi ka dawo kana nan kana shirme."
Iya Bayi ta faɗa tana mai ƙarasawa kusa da Bir ta riƙo hannun sa.
Yayin da shi kuma ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in.
"To a ƙoshi Iya ta, idan a gama halbo cuncuna zanjo kimun wanka, she ki shoya mana shi mucinye ko."
Ya ƙarasa maganar yana mai sakar mata dariya, tayarce har sai da kyawawan jerarrun fararen haƙwaran da suke a bakin sa suka bayyana.

"A'a Bir bani gwafar nan haka, in yaso bayan na maka wankan kaci abinci sai kadawo ka cigaba da harbo sun, domin kuwa idan ba haka ba nasanka sai ka kai har dare a wurin nan ba tare da ka gama ba."
Iyar Bayi ta faɗa tana mai ƙwace kwari da gwafar da suke riƙe a hannun sa, sabo da sanin da tayi muddin ba amsar sun tayi ba to bazai taɓa binta ba.

Diddira ƙafafuwan sa ya farayi a wurin yana shirin sakin kuka, sabo da ƙwace masa da tayi.
Hakan da Iya ta gani ne yasan ya ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in.
"Haba dai Jarumi da kuka, ka taimaka kar kabani kunya mana, kasa yau mutane suyi mana dariya."
Ta ƙarasa maganar tana mai jan hannun sa sukayi gaba.

Ba dan Bir yaso tafiya ba yabi Iyar Bayi suka tafi, yayin da suma abokansa su Mauzum suka biyo su a baya.

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

A yanzu haka shekarun Babban Yaya goma shahuɗu a duniya, sosai ya ƙara girma tare da nutsuwa da kuma hankali, wanda hakan kuma ba ƙaramun ƙona zuciyar magautan su yake ba, domin kuwa babu kalar asirin da basuyi masa ba amma duk a banza har yau yaƙi cin sa, sai dai kuma suma ɗin har kawo yau basu haƙura sun dena ba, kamar yacce har yau Fulani bata sare ba wurin yiwa Ƴaƴan nata addu'a, sannan kuma suma ta koya musu sukeyi da kansu.

Tunda Fulani ta haifi Asad har yau bata sake haihuwa ba, sosai yaron yayi girma bana wasa ba, domin kuwa babu wanda zai gansa yace bai kai shekara bakwai ba a duniya muddin ba sanin sa mutum yayi ba, yayin da kyawunsa kuma a kullum yake ƙara futowa.
Gaba ɗaya halayyar sa ba iri ɗaya bace da ta Babban Yaya, dan kuwa shi akwai shi da san yawo, tare da maitar Doki, wanda har hakan da mai Martaba ya gani yasa ya siya masa dawakai har guda ukku ƙanana ƙosassu ana kula masa da su, sannan kuma ake ɗora sa akan su aduk lokacin da za'ayi hawa, ko kuma ranar juma'a, kai wani lokacin ma haka nan kawai ake ɗora sa saman dawakan ayi ta zageye da shi acikin gari, shi kuma yay ta aikin dariya yana jin daɗi, kasancewar sa yaro mai yawan fa'arh da dariya.
Yayin da shi kuma Babban Yaya bai damu da shiga mutane ba, asalima ya fison ya gansa a kusa da mahaifiyar su Fulani ako da yaushe, sannan kuma ko kaɗan basa da maitar dokin da Asad yake da ita, dan shi a yanzu haka ma duka dokunan sa guda biyu ne, saɓanin Asad da yake da guda ukku.
Chapter 42 · 0% Book details