Sashe 29
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Subahanallah, zo kuga yarce aka nuna baƙin ciki ƙarara tare da hassada, haka jama'ar gidan da basu so hakan ta faru ba suka nuna, domin kuwa cikin su harda waƴan da suka kasa zuwa barka da baƙin ciki, dan ko hatta Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina sai bayan anyi Sallah isha suka iya zuwa ganin Ɗa, bayan kuma haihuwar anyi ta ne tun asubar fari, sosai suke jin baƙin ciki yarce kasan su mutu, dan ko ita kanta bayan ishar ma sunje gudun kar mai Martaba yaji labarin basuje ba ya zargi wani abun aransa.
Yayin da ta fannin mai Martaba kuma tare da masoyan sa na cikin gidan suka kasance cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa da samuwar É—a namijin da sukai
Koda ranar suna tazo sosai akai shagali irin wanda ba ataɓa makamancin sa ba aduk sauran haihuwar da matan mai martaba sukayi, domin kuwa ko kilisar da akayi anyi tane ta bugawa ajarida, dan kuwa hatta da mai martaba sai da yayi wasa da doki irin wasan da bai taɓa yin makamancin saba tunda ya yake duniya, wanda hakan kuwa ba ƙaramun sosa ran mutane da yawa yayi ba acikin masarautar, haka akasha shagali aka watasar da kuɗaɗe kamar ba neman su ake ba, bayan jinjiri yaci suna. USMAN. Yayin da masoyan sa kuma masoyan mai martaba waƴan da sukai marhabun da zuwan sa da gasken-gaske suka yi masa laƙabi da BABBAN YAYA tun aranar da aka haife sa.
Tunda Gimbiya Fulani ta gano akwai masu ƙin dan nata sosai acikin masarautar ta dage dayi masa addu'a ba dare ba rana, sosai ta dage wurin yi masa azikarai irin waƴan da addini ya koyar har da ita kanta, kasancewar ta mace mai matuƙar ililimi da kuma aiki da shi.
Yayin da magauta kuma suka dage wurin ganin sun kassara rayuwar sa.
Bayan haihuwar Babban yaya da shekara biyu da rabi Gimbiya Fulani ta sake haihuwa, sai dai kuma wannan karan Æ´a mace ta haifa, yarinya taci suna Sumayya, bayan ita kuma da shekara wata biyu da rabin ta sake haihuwar wata Æ´ar, still mace dai ita kuma taci suna Nafisat.
Hakan da magautan ta suka gani ne na bata ƙara haihuwar wani ɗa namijin ba yasan ya hankalin su yayi matuƙar kwanciya, domin kuwa ganin su tunda itama bata sakeyo wani namijin ba to abun yazo musu da sauƙi, tunda da zarar sun ɓarar da rayuwar Babban Yaya, ko kuma suka illatasa shikenan ya zamto babu ko ɗaya.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta cigaba da dagewa da yiwa Æ´aÆ´an ta addu'a gaba É—ayan su, sannan ta koyawa Babban Yaya su tun baifi shekara ukku ba, kasancewar yanzu shekarun sa sun kai kimanin biyar aduniya kenan.
Bayan haihuwar Gimbiya Nafisat kuma Gimbiya Fulani bata sake haihuwa ba, sai sauran matan Gimbiya Huwaila da kuma Gimbiya Amina da suka haifi wasu Æ´aÆ´a matan, kowacce É—aya har shekaru suka ja sosai.
BABBAN ZAURE LOCUS.
Azamanin baya Iyayen sheikh Ahmad ba acikin unguwar Babban Zaure locus suke zaune ba, suna cikin wata unguwace wacce ta kasance geto area, da take anan cikin garin Wasai, wato unguwar ÆŠan Tanki.
Mahaifin sa mai suna Ishak haifaffan cikin garin Wasai ne.
Yayin da mahaifiyar sa Aishatu kuma ta kasance bafullatanar daji, makiyaya da suke yada zango awuri kafun su sake yin gaba kuma.
Sun haɗu da Ishak ne a watarana cikin wata kasuwa da take akusa da rugar su Aisha da suka yada zango awurin, ita sunzo siyen takalma silifas ita da ƙanin ta mai suna Aliyu, yayin da shi kuma ya raka wani abokin sa siyo kaji, kasancewar kasuwar irin kasuwannin nan da suke ci sau ɗaya arana, hakan yasa idan kaje a ranar kasuwar kusan zaka samu komai, hatta da akuyoyi masu su suna zuwa siyarwa, kuma suna yin sauƙi fiye da yarce ake samun su acikin gari.
Shigar su kasuwar kenan sukaci karo dasu har sun siya takalman suna shirin juyawa ita da ƙanin ta.
Aikuwa Ishaƙ na ƙyalle ido ya gansu gaba ɗayan sa ya ruɗe, ataƙaice dai haka ya sanya abokin sa suka bisu abaya, bai bari koda wasa sun ɓace musu ba, kuma basu bari sun fahimci su suke bi ba har suka ƙarasa rugar su.
Tun daga nesa su Ishak suka hange ta ita da ƙanin nata sun durƙusa gaban wasu mutane guda biyu da suke zaune akan tabarma ƙarƙashin inuwar darbejiya, tare da kur'anai buɗe agaban su, da alamun karatu sukeyi dai, tukun daga bisani sukaga sun miƙe suna masu shigewa cikin wani gida da aka masa shinge da karare, wanda yake ɗauke da bukkoki acikin sa.
Hakan yasa su Ishak suka ƙarasa zuwa wurin mutanen nan da suke zaune suna karatu bakunan su ɗauke da Sallama.
Gaba É—ayan su rufe kur'anan su sukayi suna sauraran su, tukun abokin Ishak ya koro musu bayanin abun da ya kawo su.
Take ko awurin yanayin mahaifin Aishatu malam Audu ya sauya, sabo da jin da yay sunce wurin Æ´arsa sukazo, gashi kuma yaga ko kaÉ—an basuyi masa kama da mutanne rigar tasu ba.
Malam Sammani shi ya biye musu suka tattauna sosai, sannana aƙarshe yace suje su dawo bayan kwana biyu, alokacin sun gama yin tunani. Aikuwa ba tare da gardama ba suka tashi suka tafi, tukun shi kuma ya juya ga malam Audu yana mai yi masa nasihohi tare da nuna masa bam-bancin al'adu ko kuma yare bashi ke nufin babu aure tsakanin mutane ba, domin kuwa duk musulmi ɗan uwan musulmi ne. Haka dai yay ta masa nasihohi tare da kawo masa misalai, kasancewar sa malamin sa da yake ɗaukar karatu awurin sa tun da suka sauka agarin, tukun aƙarshe yace masa bincike akeyi shine ke nuni da ko mutum wanene, ba hakanan kawai kai tsaye ake yanke hukunci ba alamarin aure.
Ai kuwa tini ya fahimce sa, da yake dama ya riga ya gama amunta dashi, yasan bazai taɓa cutar dashi ba ko kuma wani nasa amatsayin sa na malami.
Bayan kwana biyu nayi sai ga Ishak da Abokin sa nan sun dawo kuwa, ai kuwa aranar dai basu tafi ba har sai da suka gana da Aishatu, kuma Alhamdulilah sun samu fahimtar juna cikin sauƙi, sannan kuma sunga canji sosai awurin mahaifin ta malam Audu, domin kuwa shi da kansa ya kawo musu fura da tabarma ya shimfiɗa musu, sannan kuma aƙarshe ya jasu sukaje wurin malam Sammani aka musu duk tambayoyin da za'ayi musu.
Ataƙaice dai duka baifi wata biyu sukai da haɗuwa ba aka ɗaura musu aure, aka tafi da Aishatu cikin garin wasai unguwar Ɗan tanki.
Gida ɗaya suke da mahaifan sa, sai dai kuma su nasu part ɗin daban yake, wato dai akwai katanga tsakanin su. Sosai suke zaman lafiya da junan su, sannan kuma mahaifan Ishak suke matuƙar ƙaunar Aishatu yarce kasan ƴar cikin su, barin ma mahaifiyar sa Baba Zulai, wanda hakan ko ba ƙaramun daɗi yayiwa mahaifan Aishatu ba alokacin da sukaji labari daga gare ta, tukun bayan bikin Aisha da shekara ɗaya da rabi kuma iyayen ta suka bar rugar su, suna masu sake yin gaba zuwa sosai, domin kuwa gaba ɗaya Ƙasar Hausa ma suka bari da su da shanayen su zuwa Ƙasar Malin, can wani yanki mai suna Jahar RUMAN, alokacin kuma Aisha ta haifi ɗan ta na farko ita da Ishak da suka sanya masa suna AHMAD, suna masa inkiya da mu'allim.
Sosai Aishatu tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai futa alokacin da suka yiwa iyayen ta rakiya zuwa bakin ruwa, kasancewar azamanin ana tafiya mai nisa ne ta cikin ruwa ga mutumin da yake neman sauƙi.
Bayan haihuwar Ahmad Allah ya sake azurata su da samun wasu ƴaƴan har guda ukku, amma su kuma duk mata ne. Bilkisu, Maimuna sai kuma ƙaramar su Ruƙayya. Dukan su suna da tazarar shekara bibbiyu har da rabi-rabi ne tsakanin junan su.
Afannin iyayen Aishatu kuwa tunda suka koma Kasar Malin yankin Jahar Ruman basu kara canza wuri ba, kasancewar nan É—in sun same sa da tsantsar ni'ima ga kuma wadatar abincin dabbobi acikin sa, sannan kuma mutanen garin mafi akasarin su Musulamai ne masu san Æ´an uwan su musulmai, ba kamar yankin Jahar Karfuz ba.
Sau ukku Aishatu da Ishak suna zuwa garin abayan komawar su, domin kuwa zuwa na ƙarshe ma har da ɗan su mu'allim da yake da shekara bakwai da rabi yanzu suka je.
JAHAR KAGUL, MASARAUTAR FULÆŠE.
Lamiɗo Sulaiman mahaifin Gimbiya Haddiyal shine sarki na goma acikin Masarautar Fulɗe, yana da mata biyu tare da Ƴaƴa biyar.
Matar sa ta farko itace Gimbiya Kaɓel, tana da ƴaƴa ukku, na farko shine Ummaru wanda sukewa laƙabi da Jauron Fulɗe, daga nan kuma bayan shi da shekara huɗu ta sake haifo wani ɗan namiji yaci suna Halilu, amma suna kiran sa da Bammi, bayan shi kuma sai Abubakar wanda suke kira da Buba.
Yayin da ita kuma matar sa ta biyu take da suna Gimbiya Maraimu, ita kuma tana da Æ´aÆ´a biyu ne duk maza suma, Habibu shine É—an ta na fari wanda suke sa'nni da Jauro Ummaru, bayan shi kuma ta sake haihuwar wani yaron mai suna Harisu wanda suke sa'anni da Buba, domin kuwa duka tsiran su baifi tazarar wata ukku ba.
Sosai Lamiɗo yake matuƙar son samun ƴa mace, hakama kuma afannin matan nasa da ƴaƴan sa suma duk suna son sugan su da yarin ƴa mace, amma sai dai Allah bai basu ba duka yaran maza ne.
Ita dai Masarautar Fulɗe ta kasance masarauta ce wacce ko kaɗan mutanne cikin ta basu da ilimin addini, duk da suna ikirarin su ɗin musulmai ne ako da yaushe, sai dai kuma ko kaɗan basa amfani da faɗar Allah, ataƙaice ma ko tauhidi basu sani ba, dan kuwa sun mayar da tsafi ba komai ba awurin su, domin kuwa babu wani Ɗa dake tasowa acikin gidan sarautar harya girma ba tare da ya iya tsafi kala-kala ba, a cewar su wannan itace kaɗai hanya wacce zasu iya kare kansu daga kowanne irin mugun mutum cikin sauƙi.