← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 79

Sashe 20

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai aka ƙawata wurin da ado kala-kala, yayin da tambarin masarautar tasu kuma ya kasance manne akowane wuri, acan ƙarshen filin kuwa daga jikin bango wata irin haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujerar ƙarfe ce aka jere awurin, yayin da gefe da gefen ta kuma aka aje wasu ƙananan kujerun masu azababben kyau suma na ƙarfe masu dauke da tambarin baƙar masarauta ajikin su, yayin da tsakiyar filin kuwa aka ƙawata sa fiye da yarce aka ƙawata ko wane wuri.

Wani tafkeken daɓe (floor) ne akayi awuri mai matuƙar tudu da tsairs ajikin sa, gaba ɗayan sa zage yake da randinan da suke ɗauke da Huta acikin su suna matuƙar ci sosai, yayin da saman daɓen kuma aka ajiye wani danƙareran gunkin da akayi sa da taɓo da basa da kyan gani ko kaɗan, yayin da gefe da gefen sa kuma ya kasance ɗauke da fulawoyi zube aƙasa zageye da shi masu matuƙar yawa da wal-wali, sai kuma tambarin baƙar masarauta da aka bi aka manna sa aduka ƙasan daɓen.

Acan ɓangaren bayi kuwa ko wanne shiryawa yake cikin kalar shigar sa.
Yayin da ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ta kasance zaune akan wata ar'niyar kujerar ƙarfe mai azabar kyau da sheƙi acikin ɗakin ta, yayin da wasu ƴammata da suke ɗaure da ɗan guntun baƙin ƙyalle iya guiwar su tare da ƙatuwar farar rigar yadi ajikin su mai ɗauke zanen tambarin masarautar tasu suke aikin tsan-tsara mata wata irin azababbiyar kwalliya mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kallo ɗaya zaka musu katabbatar da amatuƙar tsorace suke, sannan kuma ko kaɗan basa cikin nutsuwar su, sabo da yarce suke aikin wasu sassa na jikin su na kar-karwa.
Yayin da ita kuma ta kasance lumshe da idanuwan ta tana mai ɗan taune leɓen ta na ƙasa ahankali, tare da ɗan sakin murmushi lokaci bayan lokaci, wanda yayi matuƙar bawa ƴammatan da suke yi mata kwalliya mamaki, domin kuwa zasu iya cewa tunda suke da ita basu taɓa ganin ta tana murmushi irin haka ba sai yau, duk da dai dama bawai suna iya kallon fuskar ta bane ba ada, yanzun ma dan suna mata kwalliya ne shiyasa har suka samu wannan damar kallon ta, amma sai dai tun da suke basu taɓa jin ko alabari ba ance tayi murmushi sai yau da suka gani azahiri .

Afannin ta kuwa ba komai ne ke sata murmushi ba sai tunawa da take yi yauce ranar da zata koyawa ƙasƙantaccen ƙazamin bawan can Bir da yake ganinta tamkar tsaran sa hankali, domin kuwa ta tanadi azabobi kala kala waƴan da zata yi masa su ayau fiye da duk sauran da ta masa abaya muddin bai bata amsar tambayar ta ba.

Sanye take da wata doguwar riga mara kafaɗa wacce ta kasance ruwan ƙasa mai duhu sosai, yayin da kanta kuma ya kasance ɗaure da abun ɗaurin ɗan kwali kalar ruwan zuma da aka mata ɗauri irin mai hawa hawa da shi, sai sarƙar goshi mai azababben kyau ta goal da take zagaye akan ta. Yayin da ƙafafuwan ta da hannuwan ta harma da wuyan ta suka kasance ɗauke da sarƙoƙin goal masu matuƙar kyau da tsada suna ƙyalli.

Sosai tayi matuƙar kyau tana ta faman sheƙi ta ko ina.

Acan ɓangaren su Bir kuwa tun cikin dare Iyar Bayi ta sake zaunar da shi tana mai sake roƙon sa akan karya ko kalli fuskar Gimbiya Tasmir, balle har tai masa wani abun.
Da tom ya amsa mata shima yana mai ƙudurtawa ransa cewar zaiyi yarce Iyar tasa ta roƙe sa yayi ko domin farin cikin ta, amma bawai dan yana tsoron wani abu da Gimbiya Tasmir zata masa ba, asalima yasan sai yayi tsantsar kai zuciyar sa nesa, tukun zai iya haƙura ya kasa ɗaga kai ya kalle ta muddin sukai kusanci da juna, gashi kuma yasan wajibine suyi kusancin, tunda akwai gaisuwa ta daban da Bayi suke kaiwa ahalin Sarki aduk irin wannan ranar.

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Tun misalin ƙarfe takwas da minti arba'in Yarima Asad ya gama shirin sa tsaf kamar yacce Babban yaya ya umarce sa akan ya shirya da wuri.
Sai dai kuma irin shigar da yay ta yau tafi ta kusan koda yaushe muni, domin ko sanye yake da wani farin wando three quarter wanda yake akekkece daga saitin cinyoyin sa, tayarce har ake hangen farin net boxer ɗin dake sanye jikin sa, wato crazy, sai wata baƙar t shirt mai ɗan guntun hannu da take sanye ajikin sa da tayi matuƙar kama jikin sa, tayarce har ta bayyana gaba ɗaya murɗaɗɗiyar surar sa.
Yayin da sumar dake ɗauke akansa sa mai tsananin yawa kuma ta kasance atsage gida biyu, banda wal-wali da sheƙi babu abun da take yi, sabo da ruwan mayukan da ya mulketa dasu har zuwa ƙasumbar sa, sai wuyan sa kuma da yake ɗauke da wani silin sarƙar goal mai matuƙar ƙyalli, yayin da hannun sa ɗaya kuma ya kasance ɗaure da wani azababben baƙin agogo yayi matuƙar ƙara haskaka fatar hannun, sai kuma ɗayan hannun da ya bisa da wasu abun hannuwa na roba suma baƙaƙe. Banda faman ciccin magani yana kumbura babu abun da yake aikin yi, donin ko koda Al'amin yazo yana masa magana ma ko kai bai ɗaga ya kalle sa ba balle ya tanka masa, hakan da Al'amin ya gani ne, sannan kuma ya fahimci dalilin fushin nasa ya sanya yake ta faman tsokanar sa yana sheƙar uwar dariya, domin ko shi sanye yake da manyan kaya ɗinkin riga da wando na shadda.

Ƙarasawa yayi zuwa inda takalman sa suke yana mai sa hannu ya ɗauko wani sabon baƙin boot yana mai sanya ƙafafuwan sa acikin su, tukun ya janyo wayar sa ya riƙe ahannun sa yana mai komawa gefen bed ɗin sa ya zauna tare da mai da idanuwan sa kanta.
Ko minti biyu baiyi ba da zama sautin ringing ya fara tashi daga cikin wayar tasa.
Yamutsa fuska yayi yana mai sake É—aure fuska, sabo da sunan da yaga yana yawo akan screen É—in wayar tasa, wato Yaya na. Tukun daga bisani yayi picking yana mai kai wayar kan kunnen sa.

Lumshe idanuwan sa yayi yana mai ɗan taune lower lips ɗin sa da haƙora ba tare da yace komai ba, da alamun dai yana sauraran abun da ake faɗe ne daga can, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tom shikenan gamunan." Daga can ƙasan makoshin sa, kana ya janye wayar daga kan kunnen sa yana mai miƙewa tsaye.

"Ka taso Malam ana jiran mu." Ya faÉ—i haka yana mai yin gaba.

Murmushi Al'amin yayi ba tare da yace komai ba shima, tukun shima ya miƙe yana mai bin bayan sa.

Acan ɓangaren Babban yaya kuwa sanye yake da manyan kaya harda alkyabba ajikin sa.
Tsaye suke agaban wasu arnayen motoci da suke ta faman ɗaukar ido, tare da dogaran sa da suke sanye da uniform da zura zuran bulalai riƙe ahannun su, suna masu kallon hanyar da su Yarima Asad zasu ɓullo, alamun su ɗin kawai suke jira kenan.

Al'amin ne ya fara ɓullowa tukun Yarima Asad ya biyo bayan sa, tun daga nesa Babban yaya ya saki baki tare da zuba idanuwa akan ƙanin nasa saboda shigar da ya hango sanye ajikin sa, yayin da suma dakarun nan gaba ɗaya suka bisa da kallo, duk da dai hakan ba sabon abu bane awurin su, sai dai amma gaba ɗaya cikin su babu wanda yay zaton ganin sa ahaka yau, duba da wurin da suka san zasuje.

Tafe suke babu mai cewa wani ƙala daga shi har Al'amin, dan shi Yarima Asad ma kansa sunkuye yake aƙasa, ahaka har suka ƙaraso bakin motocin nan.

"Ina kwana Yaya." Al'amin da Yarima Asad suka faɗa adai dai lokacin da suka ƙaraso gaban Ciroma.

"Da alamu ka manta sunan wurin dana faɗa maka zamuje ne, ko kuma ka kurmance alokacin da nake faɗa maka jiya, shiyasa har ka sanyo waƴan nan ƴan iskan kayan ajikin ka ko?" Babban yaya ya faɗi haka ransa aɓace ba tare da ya amsa gaisuwar da suka masa ba, sai idanuwa kawai da ya kafe yarima Asad dasu yana kallon sa.
Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa awurin da yake yana mai ɗaure fuska tare da ɗaukar yastun hannuwan sa ya kai kan ƙeyar sa yana sosawa ba tare da yace komai ba.

"Wai ba magana nake maka bane da kamun shiru kana bina da idanuwa?" Babban Yaya ya faɗa da ƙarfi ransa na ƙara tafar fasa.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwan sa da ƙarfi yana mai danna lower lips ɗin sa cikin baki ya cije su, sabo da tsawar da yayan nasa yamasa ransa na ɓaci shima, tukun daga bisani ya buɗe baki still yana sosa ƙeya tare da faɗin. "Am dama Yay.... "Kamun shiru, bana son jin duk wani shirmen banzan da zai futo daga bakin ka, dan haka yanzu yanzu ka huce kaje ka canzo kayan nan kasanya kayan mutunci, minti biyar kawai na baka ina jiran ka anan." Ya katse sa da faɗin haka cikin tsawa ba tare da ya bari yaji ƙarshen abun da zai ce ba.

"Girgiza kai Yarima Asad yayi tare da sake rumtse ido ransa na ƙara ɓaci, domin kuwa aduk duniya idan da akwai wani abu da yafi tsana to ya biyo bayan tsawa da takura, hakan yasa lokaci ɗaya yaji gaba ɗaya tafiyar ta gama fuce masa arai, tayarce har ya ƙudiri aniyar cewa muddin ya koma to wallahi babu abun da zai sanya sa ya dawo, domin kuwa bazai taɓa sanya barguna ajikin sa ba, sai dai komai zai faru ya faru.
Yayin da shi kuma Babban Yaya ya buɗe murfin motar dake gaban sa yana mai shigewa ya zauna ransa na tsantsar ɓaci.

Sai da ya É—auki kimanin minti biyu daga tsayen da yake rumtse da idanuwan sa, tukun daga bisani ya buÉ—e su gaba É—aya har launin su ya fara sauyawa daga fari zuwa ja, kana ya juya yana mai dosar hanyar da suka biyo suka zo daniyyar ko yaje bazai dawo ba wallahi.
Chapter 20 · 0% Book details