← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 79

Sashe 61

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yayin da ita kuma Gimbya Tasmir take zaunu akan wannan kujerar ta-ta, ta d'ora k'afa d'aya akan d'aya tana mai girgiza ta.
Gaba d'aya babu alamun rahama ko kad'an tattare da fuskar ta.
Wani irin abu take ji mai kama da icce na tokare mata k'awon zuciya, aduk lokacin da tuna da yadda Bir ya kalli cikin idanuwan ta.

A hankali ta fara sauke idanuwan ta k'asa tana mai kaisu b'arin wurin da Bir yake.
Yayin da shi d'in ma kuma adai-dai lokacin ya d'ago nasa idanuwan yana mai kaisu kan fuskar ta.
Take kuwa idanuwan su suka sark'e cikin na juna.
Yayin da zuciyoyin su kuma sukayi wata irin bugawa a lokaci guda, tukun daga bisani gudun su ya k'aru fiye da yadda suke ada.
Cikin wani irin yanayi wanda Gimbiya Tasmir bata tab'a tsintar kanta acikin sa ba ta ji ta, ta sanadin had'uwar da idanuwan nasu sukayi wuri d'aya, ga kuma zuciyar ta dake wani irin bugu da matuk'ar k'arfi, abun da tun da take arayuwar ta bata tab'a sanin sa ba.
Wata irin tafar-fasa zuciyar ta take jin tana yi mata, sabo da yadda Bir ya kafeta da tsumammun idanuwan sa baya ko k'itawa.
Ita kanta so take ta ja ye nata idanuwan daga cikin nasa, ko ta samu damar yin tinanin kalar hukuncin da ya kamata tayi masa, amma gaba d'aya taji ta kasa, sabo da wasu irin abubuwa da take ganin suna futowa daga cikin idanuwan nasa suna fad'awa cikin nata.

A fannin Bir kuwa ko kad'an bai d'aga kansa ba da niyyar ya kafeta da idanuwan sa tamkar yadda yayin, sai dai kuma d'ago idanuwan nasa keda wuya suka fad'a cikin nata, wanda kuma a take a wurin yaji zuciyar sa tayi wata irin matsananciyar harbawa .
Yaso ya janye idanuwan nasa daga cikin nata, amma gaba d'aya yaji ya kasa yin hakan kwata-kwata, kai asalima ya kasa koda k'ifta su ne daga kan nata, yadda kasan mayen k'arfe da k'arfe ne suka had'u, domin kuwa wani irin haske yake ganin yana futa daga cikin idanuwan nata yana jonewa da nasa idanun, ta yadda har ya manta matsayin wacce yake durk'ushe a gaban nata, domin kuwa tun da ya taso yayi wayo bai tab'a tsintsar kansa a cikin yanayi mai kama da irin wannan d'in ba.

Jini ke tsiyayowa ta cikin gashin kansa sa yana gangarowa ta gefen idanuwan nasa, ta sanadin kansa da ya fashe a lokacin da badakaran nan ke jansa acikin kwazazzaban nan, amma ko kad'an bashi da alamun zai goge sa, gudun karya shigar masa idanun, sai kallon tsakiyar idanuwan Gimbiya Tasmir da ya cigaba dayi zuciyar sa na wani irin bugu da matuk'ar sauri, yayin da tsigar jikin sa kuma ke wani irin tashi, yana mai jin wani irin yanayi a gaba d'aya sassan jikin sa wanda bai saba da shi ba.

Cikin tsantsar k'unar rai Gimbiya Tasmir ta cigaba da kallon tsakiyar idanuwan sa, tana mai jin wani rin mugun bak'in ciki na tokare mata zuciya.
So take kawai ta janye idanuwan nata daga cikin nasa, amma gaba d'aya taji ta kasa.
Babu abun da yafi b'ata mata rai ma sai irin yadda taga shi d'in ma yak'i ya janye nasan, ga kuma zuciyar ta dake wani irin bugu duk ta sanadin kallon-kallon da suke yiwa junan su, abun da bata tab'a jiba kenan dan ta kalli wani mutumin, asalima babu mai iya had'a idanuwa da ita balle har aje ga irin haka.

Lokaci d'aya ta mik'e tsaye zumbur daga kan kujerar da take, tana mai tsayawa akan k'afafuwan ta, tukun daga bisani ta fara d'agasu cikin zafin rai, suna masu futar da sautin k'arar gwala-gwalan da suke manne akan su, ta doshi wurin da Bir yake a durk'ushe, har lokacin kuma idanuwan ta na-nan cikin nasa.

Ko da ta mik'e'n tsaye amai-makon Bir ya hak'ura dakallon ta tunda tai masa nisa, amma sai ya sake d'aga kansa sama yana mai sake danna idanuwan sa cikin nata.

Sai da tazo dab da shi tukun taja ta tsaya tana mai sakin numfarfashi, yayin da zuwa lokacin kuma idanuwan ta suka kad'a sukai jajajir tsabar b'acin rai, duk a tinanin ta idan yaga ta mik'e tsaye zai janye idanuwan nasa daga cikin nata, amma sai taga ya sake d'aga kansa sama yana mai mayar da su ciki, hakan da yayin kuwa ba k'aramun sake dagula mata lissafi yayi ba, kana kuma ranta ya k'ara kaiwa k'ololuwa wurin b'aci, sannan ta fara tinanin to wai shi d'in uban waye ne ma da har zai tsaya a gaban ta yana kallon ta ido cikin ido, sannan kuma mai ya taka da har dan ta kalle sa bugun zuciyar ta ke sauyawa, bayan a yadda ta gansa tariga da tasan Bawa ne k'ask'antaccen mutum gare ta.
Hakan ko shi yayi matuk'ar k'ara harzuk'ata, ta yadda har k'wak'walwar ta ta gaza sanar da ita abun da ya kamata tayi masa.

Cigaba da kallon sa tayi daga tsayen da take, kafin daga bisani kuma ta durk'ushe a k'asa tana mai cake guiwar k'afar ta d'aya a cikin k'asa, yayin da d'ayar kuma ta dire tafin ta akan k'asa, kana ta dafa k'asa da hannun ta d'aya, yayin da d'ayan kuma ta dunk'ule sa da k'arfi, tana mai cigaba da kallon cikin idanuwan Bir, kamar yadda shim yake kallon nata, zuciyoyin su na wani irin bugu atare, ta yadda har kowanen su ke iya jiyo sautin bugawar zuciyar d'an uwan sa.

Bud'e bakin ta tayi tana mai furzar da wata irin zazzafar iska daga cikin sa akan fuskar Bir.

Da sauri ya lumshe idanuwna sa ba tare da ya shirya yin hakan ba, sabo da iskar bakin ta mai matuk'ar turiri da ta daki k'wayoyin idanuwan nasa, yayin da ita kuma ta fara d'aga lab'b'an ta cikin kausassar muryar ta da take futa k'asa-k'asa, tana mai fad'in.
"Shin waye kai?
Waye ubanka?
Me kuma ka taka acikin Bak'ar Masarauta?"
Ta k'arasa maganar da k'yar, tana mai sakin numfarfashi, gaba d'aya alamun gajiy sun bayyana k'ara-ra akan fuskar ta, kasancewar bata saba yin doguwar magana irin wannan ba aduk lokaci d'aya, sai dai kuma a yadda take jin zuciyar ta na zafi akan wannan mara kunyar Bawan na gaban ta, zata iyayin fiye da haka ma.

A hankali Bir ya sake bud'e idanuwan sa akan fuskar ta, tukun daga bisani ya mayar da su ya lumshe yana mai sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, tamkar yaron da yaci kuka ya more, kana daga bisani ya sake bud'e su akan fuskar ta yana mai sake watsa su cikin nata da yaga gaba d'aya sun canza launi, daga farin kar d'in da ya gansu d'azu zuwa jajawur yanzu.

A hankali ya fara d'aga lab'b'an sa idanuwan sa acikin nata tamkar zaiyi magana, tukun daga bisani kuma ya b'ige da aika mata da wani irin sassanyan murmushi, kana a k'arshe ya k'arasa rufe bakin nasa da hura mata sassanyar iskar dake cikin sa shima, yana mai jin wani irin abu tamkar mayen k'arfe na fuzgar sa zuwa gare ta.

Da sauri Gimbiya Tasmir ta lumshe idanuwan ta tana mai sakin wata irin ajiyar zuciya da ko kad'an bata shirya ma yin ta ba, sabo da yadda taji saukar sassanyar iskar bakin sa mai matuk'ar k'amshi akan fuskar ta, ta yadda har sai da ta daki k'wayoyin idanuwan ta.
Wanda hakan kuma ba k'aramun sake b'ata mata rai yayi ba.
Yayin da su kuma dakarun nan nata gaba d'ayan su sukayi suman tsaye a wurin da suke suna masu bin su da idanuwa, yayin da mamakin k'arfin halin Bir kuma gaba d'aya ya cika zuciya da ruhin su, domin kuwa kosu tun da suke da ita tun tana y'ar k'aramar ta ba a tab'a samun wani ya kalli cikin idanuwan ta ba ko da na second d'aya kuwa, tsabar kwarjinin da take yi musu, amma sai gashi yau sun gani akan idanuwan su wani Bawa wanda ko su suka fisa galihu ya kafe ta da nasa idanuwan.

Wata irin kar-karwa jikin Gimbiya Tasmir ya farayi sabo da tsantsar b'acin rai, tukun daga bisani kuma ta wara idanuwan nata tana mai mik'ewa tsaye zumbur tamkar wacce aka tsikara.
Kana kuma ta d'aga k'afar ta-ta dama tana mai harbin Bir da ita da matuk'ar k'arfi, ta yadda har sai da yayi baya taga-taga yana shirin fad'uwa akan wani dutse, amma sai yayi sauri ya dafe wani k'aton icce da ya gani agaban sa yana mai sake cake guiwoyin sa acikin k'asa, tukun daga bisani ya d'ago kansa yana mai sanya idanuwan sa a cikin nata, tare fa sakar mata wani irin murmushi mai tafe da ma'anoni da yawa a cikin sa.

Da k'arfi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwan ta da tafukan hannayen ta duk alokaci guda, tukun daga bisani ta bud'e su tana mai juyawa bayanta ta fara waige-waige, tana mai tinanin kalar hukuncin da ya dace da shi.
Chapter 61 · 0% Book details