Sashe 33
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jim tayi itama ba tare da tace komai ba tana kallon Aishatu, tukun daga baya ta buɗe baki cikin sanyi tana mai faɗin. "Aishatu ina so..." "Dan Allah, dan rajara fiyayyen hallita, na roƙeƙi Umma kar kema kice bazan je ba, sabo da ayarce nake ji ayanzu muddin banje ba to bazan taɓa samun sauƙi ba acikin raina. Ina son nima naje akarɓi gaisuwar mahaifina tare dani, sanna kuma naga yarce ahalina suke ciki." Ta faɗa cikin kuka bayan ta sauko daga kan kujerar da take, ta durƙushe akan giuwoyin ta gaban Kaka.
Yayin da Kaka kuma tayi shiru ba tare da tace komai ba, sai tinani da ta tafi ma tana kallon Aishatu, tukun daga bisani ta girgiza kanta tana mai juyawa ta kalli IshaÆ™, sannan ta buÉ—e baki cikin sanyi tana mai faÉ—in. "Ka barta ku tafi tare IshaÆ™, nina sanya ka." Ta faÉ—a tana mai rumtse idanuwan ta.
"Amma Umma bakya ganin ha..." "Dan Allah karkace komai ishaƙ, domin kuwa komai da kake ganin ya faru agidan duniya muƙaddari ne daga Allah, sannan kuma babu wani abu da yake faruwa face dama can Allah ya rubuto zai faru, dan haka kuje wurin Baban ku kuyi masa bayani, muddin yace ku tafi tare to kuje Allah shine zai kare ku, kuma Insha Allah zaku isa lafiya kamar yacce zaku bar nan lafiya." Kaka ta faɗa cikin sanyi tana mai kallon sa.
Taune leɓen sa yayi na ƙasa tare da rumtse idanuwan sa, domin kuwa ko kaɗan shi dai bai so Aishatu zata bisa ba, sai dai kuma babu yarce zaiyi, tunda har mahaifiyar sa tace ya tafi da ita bai isa yaja da umarnin ta ba, sai dai kuma azuciyar sa yana fatan Allah yasa idan sunje wurin mahaifin nasa, shi yace bai aminta ba.
Miƙewa tsaye kaka tayi tana mai faɗin. "Ni na tafi, sai ku same ni aɗakin Baban ku, kuma kutabbatar kun gama duk shirin da zakuyi yanzu kun futo, sabo da bana son ku huce yau ba tare da kun shiga cikin Ƙasar Malin ba." Ta ƙarasa maganar tana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Zaman ta keda wuya sai gasu nan suma sun shigo É—akin bakunan su É—auke da Sallama, kasancewar dama gaba É—aya sun riga da sun gama shiryawa tas.
Ko da IshaÆ™ ya faÉ—awa Baba yadda ake ciki, shima É—in sai ya zamto ya faÉ—i magana irin wacce Kaka ta faÉ—a.
Hakan yasa ba dan ran Ishaƙ yaso ba ya haƙura ya ɗauki jakun-kunan nasu, bayan sunyi sallama da iyayen nasu suna masu yi musu fatan Alkhairi suka tafi.
Ƙarfe shida saura dai dai suka isa bakin ruwa.
Lokacin da sukaje sun tarar da har an fara shiryawa, domin kuwa duka -duka baifi minti goma ya rage jirgin ya tashi ba, hakan yasa IshaÆ™ ya huce cikin sauri yana mai zuwa wurin da ake biyan kuÉ—i, tare da sauran abubuwa yayi musu komai su ukkun.
Tukun suka shige cikin tafkeken jirgin ruwan da yake ɗauke da komai na buƙata acikin sa.
Tafkeke ne jirgin ba kaÉ—an ba, gaba É—ayan sa rufe yake da tamfol saman sa, wato ba'a iya ganin mutanen da suke cikin sa daga waje.
Ƙarfe shida dai dai jirgin nasu ya tashi, yana mai ɗaukar hanyar da zaibi ta kaisa Ƙasar Malin a cikin ruwan nan.
ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.
Dan-dazon mutanen cikin masarautar ne suke ta ɓullowa ta ko ina, hankulan su abala'in tashe, banda ihu tare da sunan Gargabilu babu abun da bakunan su ke iya furtawa, sabo da yarce gaba ɗaya garin ya ƙara rikiɗewa yayi wani irin jajahur daga ɓangaren kudu, yayin da ɓangaren arewa kuma ya kasance baƙiƙƙirin, ga kuma ƙasa da take wani irin tashi sama, ƙura na buɗe ko ina da ina.
Cikin tsantsar ɗimuwa Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin. "Kayi wani abun mana Boka mai hutar kasko, kayi wani abun mana tun kafin komai ya ƙarasa lalace." Ya faɗa cikin hargowa yana mai kallon Boka mai hutar kasko.
Yayin da shima Boka ya sake ruÉ—ewa fiye da da, sabo da yadda yaga garin nasu na sake juyewa.
Da matuƙar ssuri ya juya yana mai komawa cikin ɗakin sa.
Ko daƙiƙa biyu baiyi aciki ba sai gashi nan ya dawo hannuwan sa ɗauke da wasu irin layoyi, tukun ya buɗe baki tun daga inda yake yana mai faɗin. "Na tuna da hanya ɗaya da tarage wacce zanbi, domin na samu ganawa da abun bauta Gargabilu, dan haka yanzu maza maza ka biyo ni zuwa bakin daji gaban ruwan ruwa, domin kuwa anan ne kaɗai zanyi iya ai watar da wannan aikin." Ya faɗa yana mai juyawa ya doshi hanyar ba tare da ya jira Sarki Barbaru ba, yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya juya cikin sauri yana mai komawa wurin da dokin sa yake.
Tun daga nesa ya buga tsalle yana mai hayewa saman dokin, tukun ya damƙi linzamin sa yana mai saita masa hanya.
Wata irin zabura dokin yayi yana mai bin hanyar da mahaukacin gudu, yarce kasan zai tashi sama.
Yayin da jama'ar nan kuma suke ta cigaba da ihun kiran Gargabilu, hankulan su na tsantsar sake tashi.
Acikin daƙiƙun da basu zarta biyar ba Boka da Sarki Barbaru suka isa bakin daji, wanda yake zagaye da wani irin tafkeken ruwa, da ko ƙarshen sa ba a iya hange ta kowane ɓangare nasa.
Gaban wani kogo da yake manne jikin wata danƙareriyar bishiya da take manne a gefen ruwa suka ƙarasa.
Hannu Boka mai Hutar kasko ya zira acikin kogon yana mai zaro wani baƙin kasko, yayin da cikin kaskon kuma ya kasance ɗauke da wasu irin karikitai kala-kaka acikin sa.
Cikin sauri yasa hannun sa yana mai furfuto da duka abubuwan dake cikin kaskon, sannan ya ɗebi wasu daga cikin su yana mai zubawa aciki, kana ya damƙi wata laya guda ɗaya da take riƙe ahannun sa da matuƙar ƙarfi yana mai rumtse idanuwan sa tare da faɗin. "Gargabiluuuu!"
Take awurin kaskon nan ya kama da wuta Bal, bal, bal, yana ci yarce kasan wanda aka zubawa fetir acikin sa, yayin da boka mai hutar kasko kuma ya cigaba da kiran sunan Gargabilu da ƙaraji, ta yarce har wurin ke amsawa yana mai haɗawa da wasu irin surutai, har kuma lokacin bai fasa matse layar dake cikin tafin hannun sa.
Ƙara tashi hutar nan tayi tana ci sosai, tukun daga bisani harshen ta ya rabu gida biyu daga tsakiyar su wani irin baƙin hayaƙi na tashi, kana kuma daga saman hayaƙin ya zamto kalar shuɗi.
Sosai Hutar ta kasu kala kaka har kimanin kusan kala biyar, yayin da Boka mai hutar kasko kuma yayi shiru daga furucin da yake yana mai durƙushewa awuri ɗaya ya nutsu sosai, sai dai kuma har lokacin bai buɗe idanuwan sa ba, kamar yadda bai buɗe layar dake cikin tafin hannun sa ba.
Yayin da ta fannin Sarki Barbaru kuma yaji wani rin daÉ—i, sabo da fahimtar da yay Boka mai hutar kasko ya samu damar ganawa da abun bautar su.
Sai da ya ɗauki kimanin daƙiƙa talatin rumtse da idanuwan nasa, tukun daga bisani ya sake miƙewa tsaye yana mai buɗe idanuwan sa, yayin da kalar Hutar nan kuma ta koma ja kamar yacce take tun farko.
"Shin meke faruwa ne Boka?" Sarki Barbaru ya jefowa Boka mai hutar kasko tambaya cikin sauri, yana mai matsawa kusa da shi.
"Haƙiƙa Al'amarin babba ne kamar yacce na faɗa maka tun farko, domin kuwa ayarce ubangiji Gargabilu ya sanar mun, sannan kuma nima na gani da idanuwa na, muddin bamuyi da gaske ba to komai na shirin rushewa, idan nace kuma komai ina nufin komai da komai." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai kallon Sarki Barbaru.
Yayin da shi kuma kwata kwata ya kasa fahimtar abun da yake nufi ko kaÉ—an, hakan ne yasa sa ya buÉ—e baki cikin sauri yana mai faÉ—in. "Kamar ya komai kenan Boka, domin kuwa har yanzu ban fahimci komai ba daga cikin abun da kalaman ka suke nufi."
"Tabbas bazaka fahimta ba ayanzu dama na sani, sai dai kuma ayanzu yanzu zan sanar maka tayarce zaka gane.
Da nace maka komai ina nufin komai namu zai lalace, duniyar mu zatazo ƙarshe, tarihin mu zai shafe tun daga na can baya har kawo na yanzu shafewa ta har abada, sunan Baƙar Masarauta zai ɓace acikin littafin tarihin duniya!"
"Shin me kake faÉ—e ne haka mai tsantsar raÉ—aÉ—i acikin kunnuwa Boka? Shin taya ya kake ganin hakan zata faru kuwa?"
"Ta hanyar barin Jinjirin adoron duniya, ko kuma kashe sa!"
"Har yanzu dai ban fahimce ka ba yakai shugaba Boka, na roƙeka da abun Bauta Gargabilu kayi mun yarce zan gane tun kafin ƙoƙon kaina yay bunduga awurin na." Sarki Barbaru ya sake faɗa amatuƙar rikice, da kuma tsantsar ƙaraji.
"Kanka bazai taɓa bunduga ayanzu ba, sai dai ko idan daga baya-bayan ka gama jin bayanin abun da ke faruwa, muddin ba asamu mafuta ba, domin kuwa ni ayanzu zan warware maka komai." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai juyawa yay taku ɗaya, biyu, zuwa ukku daga wurin da yake, tukun daga bisani ya sake juyowa ɓarin da Sarki Barbaru yake yana mai cewa. "Za'a samu shigowar wani baƙon Jaririn yaro namiji ne cikin ƙasar nan tamu, sannan kuma zai huce ta cikin jahar mu, shi kuma wannan jaririn bakowa bane face musiba da bala'i gare mu, domin kuwa ayarce ubangiji Gargabilu ya sanar mun kuma na gani da idanuwa na, shi yaron zai zamto mana musiba da bala'i acikin masarautar mu, domin kuwa zai wargaza ta, sannan kuma zai rusa gaba ɗaya tarihin mu, zai dawo ya yaƙe mu alokacin da bamuyi tsammani ba bayan ya girma, muddin muka barshi ya wuce ta cikin garin nan, domin kuwa gaba ɗaya wannan yanayin sauyawar garin da aka sama ansa mesa ne ta zuwan da zaiyi ya huce ta cikin kwanakin nan, sai dai kuma ni kaina ban san ko awace ranar zai huce ba, amma ayarce ubangiji Gargabilu ya faɗamun shine daga rana irin ta gobe har zuwa nan da makwanni huɗu masu zuwa zai iya hucewa." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana kallon sarki Barbaru.