← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 79

Sashe 56

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai akai ta takura masa da naci akan ya kaita amma yaƙi, domin kuwa shi ko karatun addini ma ba damun sa yayi ba balle kuma suce dole sai anyi na bokon, a ƙarshe dai da ƙyar aka samu aka shawo kansa ya bari aka kaita wata makarantar boko da take anan cikin Jahar Kagul, itama ɗin dai ta ƴaƴan masu kuɗin ce, sai dai kuma ya bari ne itama sabo da ance masa bata kwana bace ba, kullum yaro yake zuwa ya koma gida, hakan ne yasa ya tanadi lafiyayyan doki ma tsanin girma da kyawu ya bayar ake kaita akan sa, sannan ajira har a tashi, tukun a ɗakko ta a dawo da ita gida, yayin da masarrafin dokin kuma yake sarrafasa da hannu ɗaya, hannun sa ɗayan kuma yake zamtowa riƙe da lemar da take kare ta daga zafin rana, a haka zasuyi ta tafiya a hankali har sukai makarantar kullum.

Yanzu haka zaune take a gefen wani farin ruwa mai tsanin haske, ta zura ƙafafuwan ta biyu a ciki tana ta faman wawwantsala ruwan da su, yayin da gefe da gefen ruwan kuma ya kasance zagaye da wasu irin korayen ciyayi da furanni masu matuƙar kyau da ƙamshi, da suka yiwa ruwan ƙawan ya.
Sanye take da fararen kaya irin na fulani da sukayi matuƙar yi mata kyau da amsar jikin ta, yadda kasan dan ita kawai aka ƙir-ƙire su, yayin da gashin kanta kuma ya kasance tufke a wuri ɗaya yana ta faman ƙyalli da ɗaukar ido.

Gaba ɗaya gefe da gefen ta tsuntsaye ne a wurin dukan su a diddirƙushe suna kallon ta, yayin da ita kuma take wani irin lumshe idanuwan ta tana mai buɗe su, wani irin farin ciki mara misaltuwa na cigaba da gauraye ilahirin jiki da zuciyar ta, sabo da tino sautin daddaɗar busar sarewar da tayi mafarkin ta adaren jiya mai matuƙar zaki da take mata amsa kuwwa acikin kunnen ta.
Tun da take bata taɓa yin irin mafarkin da tayi jiya ba, hakan ne yasa ya mata arai har kawo yanzu ba tare da ya ɓace ba, kuma ba komai bane ya faru a cikin mafarkin nata sai wani irin saurtin daddaɗar busar sarewa, mai matuƙar zaƙi da ta dinga ji yana dukan dodon kunnen ta, yayin da tai ta faman laluben wurin da sautin yake futowa a cikin mafarkin amma bata gano sa ba har zuwa lokacin data farka daga baccin.
Shine fa yau tun da safe ana gama shiryata ta tawo wurin tsuntsayen ta tana mai basu labarin zaƙin busar da taji ɗin, wacce ta rasa gano ta inda take futowa, sai dai kuma ko yauma tana fatan ta sake mai-mata irin mafarkin nata na jiya.

*JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Tun bayan tafiyar su Asad da Æ´an kwanaki sai hankalin Gimbiya Fulani ya kwanta sosai, sabo da labarin da sukaji na cewar tunda suka bar cikin Masarautar Wasai bai kuma koda firgita ba balle suma.
Hakan ne yasa daga ita har mai martaba sukayi matuƙar jin daɗi, sanan kuma hankulan su ya kwanta, domin kuwa ita Gimbiya Fulani dama damuwar ta tafi ƙarfi ne akan Asad, sabo da shi akafi sanyawa ido fiye da Babban yaya, sannan kuma shine mai wasa da azkar.

Tun da suka tafi basu zo ƙasar ba sai bayan cikar su shekara guda da barin ta.
Sai dai kuma sunzo ne da sabon salo tare da sabuwar al'ada cikin masarautar, domin kuwa ba ƙaramun rikicewa Gimbiya Fulani ta sake yiba alokacin da taga yadda Asad ɗin nata ya koma.
Gaba ɗayan sa ya canza ya koma wani irin miskili, ga wata irin sabuwar al'ada da suka ɗaukko acan garin ta sanya ƙananan kaya, gwanda-gwanda Al'amin ma da yazo yasa manyan kaya akan Asad, domin kuwa shi gaba ɗaya nunawa yayi bama zai iya sa su ba, sannan kuma gaba ɗaya tunda sukazo ɗin bai kalli ko hanyar fada ba, Asalima da Gimbiya Fulani tace suje su gaida mutanne fada nuna mata yayi shi bazai iya zuwa ba, sabo da yana zuwa zasu fara yi masa magana da ƙarfi a cikin kunne, haka tanaji tana gani yaƙi zuwa sai Al'amin ne kawai yaje.

Shi kansa Mai Martaba babu yadda baiyi ba da Asad akan yaje Fada, amma ya ƙeƙyashe idanuwan sa yaƙi, domin kuwa shi kansa sai zamtowa yayi idan yana son ganin sa sai dai yazo nan part ɗin Gimbiya Fulani ɗakin sa ya gansa, ko kuma shi Asad ɗin ya yaje part ɗin mai martaba, amma ba dai cikin fada ba.

Hankalin mai martaba bai sake tashi ba sai alokacin da ya kawowa Asad sababbun É—inkunan da yayi musu tare, na wata haÉ—aÉ—É—iyar shadda É—inkin riga da wando tare da malum-malum yace masa ya sanya su ranar wata juma'a.
Take a wurin kuwa Asad ya fara bin kayan da wani irin mugun kallo, tukun aƙarshe ya juyar da kansa gefe yana mai buɗar baki yace.
A gaskiya ni Abba bazan iya sa waƴan nan manyan kayan ba, haba dai, sai kace wani ɗan ƙauye, kuma mai ai idan nasa waƴan nan zafi ma kusa kashe ni zaiyi."
Ya ƙarasa maganar da juyar da kai gefe yana mai ture kayan daga kusa da shi.
Sakin baki Mai Martaba yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba, tukun daga ƙarshe ya durƙusa a gaban sa yana mai dafa kafaɗun sa ya fara lallaɓa sa dan yasa kayan, amma ƙiri-ƙiri Asad ya nuna shifa bazai iya sasu ba, haka Mai Martaba yana ji yana gani dole ya haƙura ya barsa yasa ƙananan kayan sa.

Wata ɗaya cir sukayi a garin, tukun suka juya ƙasar Dubai, kasancewar dama hutun makaranta ne suka yi shiyasa har sukazo ɗin ma.

Haka dai abu yay ta tafiya duk zuwan da Asad zaiyi garin baya tabɓa sanya manyan kaya, sannan kuma baya wani shiga cikin mutane, Asalima ko da sunzo lokacin hawa to in'da ake hawan ma baya zuwa, balle har yace zaiyi sa kamar yadda yake maitar sa abaya, kai ataƙaice ma dai idan Al'amin yace masa yazo suje, haka yake cewa Allah ya kiyaye shi da ba bagidaje ba yaje wurin can, duka uwar me ma ake yi a wurin bayan harkar ƙauyanci da iface-iface.

A cikin duka abubuwan da ake gudanarwa acikin masarautar abu É—aya ne kacal bai barsa ba, wato Doki, domin kuwa har yau idan yazo sai ya hau dokunan sa, kamar yadda yake da su acan ma gidan su na Dubai da Alahaji Abubakar ya siya musu su duka, sabo da masifar son sa da yake yi.

A ɓangaren Babban yaya sosai shima ya girma ya zama saurayi, domin kuwa ayanzu yana da kimanin shekaru Ashirin da biyar ne aduniya.
Yayin da afannin karatun sa kuma yake a matakin masters, kasancewar duka karatun nasa aƙasar turai yayi sa ne shiyasa yay masa matuƙar sauri.

A ɓangaren magautan Gimbiya Fulani su kuma sosai sukai farin ciki da yadda Asad ya dawo, domin kuwa sun riga da sun sani muddin ya ɗore a wannan halayyar da yake ta yanzu, to har Abada babu shi babu zama akan karagar kujerar sarki, hakan ko shine yasanya hankulan su sukayi matuƙar kwanciya ta fannin Asad, kana suka koma suka duƙufa akan Babban Yaya da kullum kuma suke abun baya cin sa.
Sai dai kuma suna ganin ayanzu an kusa azo lokacin da shima zai cisa, tun da yanzu sun riga da sun gama da babin Yarima Asad, to ko mai da zasuyi akan sa ne shi kaÉ—ai yanzu, domin kuwa su dama burin su karsuyi mulki, kuma sun san Asad ayanzu yayi hannun riga da mulki har abada, tun da aikin su yaci akan sa.

*UNGUWAR ÆŠAN TAKI*

Abubuwa da yawa sun fara tun da ga kan marasa daɗi har zuwa kishiyar su, waƴan da cikin su kuwa suka haɗa har da mutuwar mahaifin Ishaƙ da yayi tsawon shekara guda yanzu kenan, da kuma auren Babbar ƴar Aishatu da Ishaƙ da akayi, wato mai bin Ahmad da yanzu kowa ya koma kiran sa da Sheik Ahmad a cikin unguwar su tasu harma da wajen ta, kasancewar sa na Babban matashin malami da ake ji da shi acikin unguwar, domun kuwa yanzu haka yana riƙe da har makarantun islamiyya biyu anan cikin unguwar tasu, yayin da yake koyar da manyan iyaye maza kuma aduk bayan sallar asubahin duniya.

A yanzu haka yana da shekaru Ashirin da biyar ne cif aduniya, amma idan mutum ya gansa muddin ba sanin adadin shekarun nasa yayi ba zai É—auka ya kai irin ashirin da takwas É—in nan ne, sabo da yadda yake da tsan-tsar nutsuwa, haiba tare da kamala tattare da shi, waÆ´an da kuma duk sun samu ne ta dalilin ilimin addinin da yake É—auke da shi acikin kansa, kana kuma yake amfani da shi ako da yaushe.
Yayin da a karatun sa na boko kuma yake amatakin level 4 na jami'ar gwamnantin tarayya da take a nan cikin garin wasai.
Wato Federal University Wasai, inda ya fara karantar Islami study acikin ta, kafin daga bisani kuna ya koma Qur'anic Hadith, alokacin da yaje lavel 3.

Sosai yake da matuƙar ƙwazo fiye da duk sauran ɗaliban da suke a department ɗin nasu, domin kuwa akowane lokaci idan har aka kafe musu exarm makin sa yana fin na duk sauran ɗaliban, wato dai shine over roller na department ɗin nasu gaba ɗaya, wanda hakan kuma yasanya malamai da dama daga cikin malaman su suke bala'in ji da shi.

A ɓangaren Aishatu kuwa har kawo yau bata bar tinane-tinane ba tare da zaman cikin ɗaki, domin kuwa ko da tayi kamar zata dena da zarar ta kwanta bacci idan tayi mafatkin yaron nan da ta saba yi, wanda take ganin sa akullum yana ƙara girma, sai taji komai na dawo mata sabo, kana kuma har yau bata futar da tsammanin sake saduwa da ɗan na ta, da ta rabu da shi tun a wurin da ta haife sa, kamar yadda akullum zuciyar ta take bata cewar yana nan araye ba akashe sa ba shi.
Chapter 56 · 0% Book details