← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 79

Sashe 21

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin mota kuwa cikin tsantsar takaicin hallayar ƙanin nasa da yake ji aƙasan ransa ya lumshe idanuwan sa, yana mai jingina da jikin kujerar tare da ɗaga kansa sama, kafin daga bisani kuma ya miƙe zumbur yana mai gyara zaman sa akan kujerar, sabo da tino wasu daga cikin shawar-warin Sheikh Ahmad da yayi da yake cewa muddin yana son buƙatar sa ta biya ta ɗora ƙanin nasa akan hanyar dai dai, to dole sai yana binsa ahankali, domin kuwa idan har yace zai masa ta zafi ko kuma yace zai na cewa yayi komai kai tsaye, to bazai taɓa samun yarce yake so ba, face shaƙuwar dake tsakanin su ma ta samu tangarɗa, dan haka muddin yana son yay abun da yake so, to dole sai yana jan sa ajiki tare da lallaɓa sa.
Hakan da ya tina ne kuwa ya sanya sa miƙewa zumbur daga kishingiɗen da yake jikin kujera, tukun daga bisani ya miƙa hannu yana mai janyo wayar sa da take ajiye agefen sa, sannan ya shiga contacts yana mai nemo number ƙanin nasa da ya rubuta My Asad ajiki da ɓaro-ɓaron baki ya doka masa kira, tare da karata akan kunnen sa.

Aɓangaren Asad kuwa yana shirin shiga cikin apartment ɗin nasu yaji sautin wayar sa dake riƙe ahannun sa.
Bai É—ago ta ba balle ya kalle ta har tai ringing É—in ta ta gama tas.

Ko minti É—aya batai da katsewa ba sai ga wani kiran nan ya sake shigowa.

Mtswwww! Yaja wani dogon tsaki yana mai dakatawa awurin da yake tare da lumshe idanuwan sa, tukun daga bisani ya warasa yana mai É—ago hannun sa yakai idanuwan sa kan wayar tasa.

BIG BROS

Shine sunan da ya gani yana yawo akan screen ɗin wayar ɓaro-ɓaro da manyan baki.

"What againe kuma?" Ya faÉ—a yana mai taune lowar lips É—in sa tare da yamutsa fuska, tukun daga bisani yay pickin É—in call É—in lokacin da yake dab da katsewa yana mai kai ta kan kunnen sa.
Shiru yayi ba tare da yace komai ba, sai faman hanci da yake hurawa kawai.
Yayin da acan ɓangaren Babban Yaya kuma yayi gyaran murya yana mai yin shiru ba tare da yace komai ba shima.

Sun ɗauki kimanin mintina biyu ahaka sai sautin futar numfashin junan su da suke ji kawai, tukun daga bisani shi Babban Yaya ya buɗe baki cikin sanyin murya yana mai faɗin. "Ƙanina." Kana yay shiru ba tare da ya ƙara furta komai ba.

"Uhm!" Kawai Asad ya faɗa ba tare da yace ƙala ba.

Murmushi Babban Yaya yayi daga can ɓarin da yake sabo da fahimta da yay ƙanin nasa na fushi da shi ne, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Kana ina ne ƙani na?"

"Cikin ɗaki." Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi tayarce shi kansa Babban Yaya sai da ƙyar ya iya jiyo sautin furucin nasa.

"Ka cire kayan naka ne?" Ya sake faÉ—a agajarce har lokacin muryar sa É—auke da murmushi.

"A'a." Yarima Asad ya faɗa still daga can ƙasan maƙoshi.

"To kawai kabar abun ka basai kacanza ba, nima sai bayan ka tafi naga ne ba ƙaramun kyau kayi ahakan ba, dan haka yanzu kayi sauri katawo mutafi kai kaɗai muke jira." Baban Yaya ya faɗa ahankali muryar sa ɗauke da murmushi har lokacin.
Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi wani irin haɗ..................✍

*SAI DA NA GAMA TYPPING ƊIN 6K WORDS (READ MORE GOMA) INA EDITING DUKA YA GOGE, SO KUYI HAƘURI DA WANNAN KUYI MANAGE, INSHA ALLAH IDAN NA SAMU LOKACI ZA KUGA PAGE 9 ZUWA DARE.* 😭

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹

_*NA*_

UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*FREE PAGE 09*

Haɗe rai yana mai ɗaukar tafin hannun sa ya kaisa kan goshin sa ya dafe sa tare da rumtse idanuwan sa da ƙarfi, yana mai jin takaicin kiran sa da yayan nasa yayi, tukun daga bisani ya buɗe idanuwan nasa yana mai juyawa ya koma hanyar da ya biyo.
Yana ƙarasawa wurin da suke, suka buɗe murafan wata haɗaɗɗiyar mota ba wacce Babban Yaya yake aciki ba shi da al'amin suna masu zama daga gidan baya.
Tukun matuƙan motocin sukayi musu key suna masu ɗaukar hanyar da zata futar dasu daga cikin masarautar.

Ƙarasawar su bakin get yayi dai dai da isowar motocin Gwamnan Wasai tare da tawagar sa, ba tare da sun tsaya sauraran junan su ba bare su gaisa ko wanne yayi gaba, su suka shilla zuwa kan titi, yayin da motocin da gwaman da ƴan rakiyar sa suke aciki su kuma suka hulla kan motocin su zuwa cikin masarautar.

*JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULÆŠE*

Tun daga lokacin da tayi arba da fuskar Yariman Yamma take cikin baƙin ciki tare da ƙunci, tayarce har takasa sanya komai acikin ta, domin kuwa ko alamun yunwa bataji ba balle har tayi ƙoƙarin cin abincin, duk da yarce aka jere mata su kala kala agaban ta kuwa, sabo da tsantsar baƙin cikin da take ciki.
Babu abun da yafi ƙona mata rai da sanyawa ta sake jin ta tsanar sa fiye da kowa, sai irin kalaman da ya dinga faɗa mata na cewar ita ɗin tasace.

Koda ta kwanta bacci cikin dare mafarki tayi wai gata kan saman wani tafkeken dutse. Yayin da ƙasan dutsen kuma ya zamto zagaye da wani farin ruwa mai matuƙar girma da haske, sai daga can gaban ruwan kuma ta dinga jiyo wani irin sautin busa mai tsantsar daɗi da kwanciya arai yana tashi.
Hakan yasa tai ta shawagi akan dutsen fuskar ta ɗauke da murumushi, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance kafe akan ruwan nan tana mai tinanin ta hanyar da zatabi ta tsallake sa, domin ta ƙarasa wurin da daddaɗan sautin da ke dukan kunnen ta yake.

Sanye take da kayan fulani bana sarauta ba yau, wato irin waƴan da kowa ke sanyawa farare ajikin ta, yayin da kanta kuma ya kasance ɗauke da wasu manya manyan kitso guda biyu ƙwal akai, sai sandar gadon ta ta tsafi da take riƙe ahannun ta tana mai cigaba da juyi asaman dutsen nan.
Babu abunda yafi mata daɗi awurin sai yarce wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi take tashi tana dukan jikin ta awurin, ga kuma ƙamshin korayen ciyayin da suke dashe agefen dutsen, waƴan da suka ƙara sanya ta cikin shauƙi.

Ta ɗauki kimanin daƙiƙa kusan talatin asaman dutsen tana mai neman hanyar da zata sauka daga kansa, domin tabi ta cikin ruwan nan ta ƙarasa wurin da take jiyo sautin busar, amma bata samu ba.
Lokaci ɗaya yanayin ta ya fara sauyawa, gaba ɗaya jikin ta ya farayin sanyi, sabo da rasa hanyar da zatabi ta sauka daga kan dutsen da tayi, sai can taga wasu kyawawan tsuntsaye guda biyo sun tawo aguje suna masu zuwa suka gogi gefen fuskar ta da fuka-fukan su, tukun daga bisani suka ƙara yin gaba suna masu tsayawa asaitin fuskar ta tare da karɗada jelinan su.

Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata take awurin, sabo da ganin tsuntsayen nan da tayi, tukun daga bisani ta gayara tsayuwar ta awurin tana mai ɗaukar sandar dake riƙe ahannun ta ta maƙale ta akan ƙafadar ta, sannan ta buɗe baki cikin tsantsar shauƙi tana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa gareni masoya na." Ta faɗa tana mai sakin murmushi tare da lumshe kyawawan idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai ɗorawa da cewa. "Dama ni nasan bazaku taɓa barina cikin wani hali ba, duk inda mafuta take zaku samo mun ita Shale am, dan haka idan kun shirya nima na shirya, muje ku nuna mun hanyar da zata kaini wurin wancan daddaɗan sautin."
Ta faɗa tana mai sake gyara tsayuwar ta tana kallon su tare da sakin murmushi, yayin da suma ɗin suka juyo ɓarin da take suna masu shawagi akan ta tare da sakin kuka, alamun suna amsa batun ta kenan, tukun daga bisani suka juya atare suna masu dosar wata hanya dake akan dutsen.
Bin su itama tayi abaya cikin takun ta wanda shi kaÉ—ai ke É—aukar hankulan jama'u akan ta.

Wata hanya suka ɓulla da ita akan dutsen wacce ta kasan ce gangare ce, tukun suka sauka daga sama suna masu sauka akan dutsen, suka fara ɗan tsallawa da ƙafafuwan su suna masu sauka daga kan dutsen.
Binsu itama tayi abaya idanuwan ta ƙur akan hanyar da take jiyo sautin busar nan cikin tsantsar farin ciki, ahaka har suka sauka daga kan tafkeken dutsen nan dukan su suna masu tsayuwa agaban makeken ruwan nan, tukun daga bisani tsuntsayen suka ƙara tashi sama suna masu dawowa dai dai saitin fuskar ta, sanann suka karkaɗa mata jelolin su tare da shafar gefen fuskar ta da fuka fukan su.

"Shin ina kuma zaku tafi kubarni ba tare da kun nuna mun hanyar da zanbi in tsallaka wannan ruwan ba." Ta faÉ—a tana mai marai-raice fuska idanuwan ta akan su.
Cigaba da zagaya ta sukayi suna masu sakin É—an kuka, tukun daga bisani suka tashi sama gaba É—ayan su atare suna masu yin gaba suka barta awurin.

Lumshe idanuwan ta tayi tana mai shaƙar sassanyar iskar dake wurin, tare da ƙamshin turare.
Ta É—auki kimanin mintina biyu ahaka, tukun daga bisani ta buÉ—e idanuwan ta fuskar ta É—auke da tsantsar murmushi, sabo da tinawa da tayi da Birbillon ta (malam buda mana littafi)
Hakan yasa ta juyawa da sauri tana mai dosar wurin da wasu korayen ciyayi suke dashe agafen ruwna nan, fuskar ta ɗauke da murmushi, yayin da har lokacin hannun ta yake riƙe da sandar nan ta.

Durƙusawa tayi aƙasa gaban furannin bayan ta aje sandar ta agefen ta, tukun ta lumshe idanuwanta tana mai kai tafin hannun ta ta bugi korayen ciyayin nan da shi, tukun ta buɗe tafin hannun tana mai ɗora sa akan ciyayin.
Take wasu irin kyawawan malam buÉ—a mana littafi kala-kala suka taso suna masu yin shawagi adai dai saitin fuskar ta, tukun sai su koma su haye kan tafin hannun ta.
Ahakan har sai da suka cika duka tafukan hannayen ta biyu da ta buɗe, tukun daga bisani ta wara fararen idanuwan ta masu ɗauke da blue black ɗin ƙwayar ido akan su.
Chapter 21 · 0% Book details