← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 79

Sashe 26

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a kawai ke yanzu abun da za'ayi shine, idan kin sa kayan kije ki ɗauki madarar ki kaita lambun gaban sa, ni kuma yanzu bara naje na ɗauka na kai lambun yamma inda su Hamma Jauro suke, domin kuwa har baƙin sunzo tun ɗazu gashi ba akai musu madara ba." Ya faɗa yana mai juyawa.

"Tom shikenan Hamma Habu." Gimbiya Haddiyal ta faÉ—a tana mai sanya hannun ta acikin wadrobe É—in ta.

"Ki fa yi sauri, sabo da sun riga sunzo harma sun zauna." Ya faɗa yana mai ƙarasa fucewa daga cikin ɗakin.
Yayin da ita kuma ta fara sanya kayan da ta zaro farare na fulani, amma bawai na sarauta ba cikin sauri.
Tukun ta ƙarasa gaban mudubi tana mai kama uban gashin kanta da yake baƙiƙƙirin atsafe ta tufke sa wuri ɗaya, sannan ta ɗauki man leɓe kaɗai ta goga akan pink lips ɗin ta.
Sosai tayi matuƙar kyau yarce kasan sarauniyar kyawu ta duniya, duk dama ba wata kwalliya ce ke ɗauke afuskar ta ba, yayin da gashin kanta da ta tufke sa kuma ya zubo har gadon bayan ta ya kwanta.
Cikin sauri ta juya tana mai kama hanyar da zata sadata da waje, bayan tasanya wani plat shoe aƙafar ta ba tare data ɗaura ɗankwali ba.

*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Ahaka suka cigaba da shigowa cikin filin kafaɗun su ɗauke da iccina masu matuƙar yawa, suna masu dosar wurin da abun bauta Gargabilu yake.
Ahaka har akazo kan Bir da ya shigo shima kafaɗar da ɗauke da nasa iccinan da baya da baya, yana mai faman ɗirkar rawa daga shi sai farin ƙyalle ɗaure aƙugun sa.

Wani irin murmushi Gimbiya Tasmir ta saki alokacin da taga shigowar Bir cikin filin, tana mai cije leɓen ta na ƙasa.
Yayin da su kuma bayin nan daga mazan su har matan su suka cigaba da nufar wurin da abun bauta Gargabilu yake suna masu faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da matuƙar ƙarfi.

Duk wanda yaje gaban daɓen da abun bauta Gargabilu yake akai durƙusawa yake kansa sun kuye aƙasa yana mai faɗin. "Godiya ta tabbata gareka ubangjin mu daka nuna mana wannan rana." Sanna su sake yin juyi agaban sa suyi rawa iyakar rawa, tukun su huce zuwa cikin filin nan suna masu dosar inda Sarki da Iyalan sa suke, domin su kai gaisuwa, har lokacin kuma hannuwan su suna riƙe da kaskwayen hutar nan ne.

Dasari Gimbiya Tasmir ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take alokacin da taga bayin nan sun fara doso hurin da suke, kamar yacce yayin ta biyu maza suma suka miƙe.
Tukun suka doshi wurin da wasu irin zura-zuran bulalai suke masu matuƙar tsayi da kauri cikin wani ruwa, suna masu sa hannu suka ɗauke su, sannan suka juyo suna masu dawowa tsakiyar filin nan ta ɓarin da bayi maza suke tawowa suka tsaya cirki cirko.
Ahaka har bayin nan suka fara isowa zuwa wurin da suke.
Ɗaga bulalun nan suka farayi cikin tsantsar ƙarfi, suna masu antaya musu ita agadon bayan su da ya kasance ko riga babu akansa!
Ana zubawa mutum bulalar yake rumtse idanuwan sa da ƙarfi jikin sa na tsamtsar karkarwa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin ƙaraji yana mai faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!! Godiya muke!"
Sannan ya huce gaba, shima ɗayan da yake agaba ya sake yi masa irin wacce na gaban sa yay masa, kana su huce gaba inda Gimbiya Tasmir take tsaye itama ta yi musu kamar yacce yayin ta sukai musu ba tare da tausayi ba ko kaɗan aranta, ahaka har aka ƙaraso kan Bir da yake ɗauke da iyayen iccina akan sa, jikin sa na rawa da ɗigar gumi.
Haka duk yayyen Gimbiya Tasmir suka masa bulalar nan kamar yacce suka yiwa duk waƴan da suka zo kafin shi, sannan ya huce gaba wurin da Gimbiya Tasmir take idanuwan sa durƙushe aƙasa, aƙoƙarin sa na ganin ya cikawa Iya alƙawarin da ya ɗaukar mata na bazai kalli Gimbiya ba, duk da kuwa yarce yake jin wani irin abu na fusgarsa akan ta, amma ahaka ya daure ba tare da ya ɗago ya kalle taba, ahaka har ya ƙarasa gaban ta.

Yayin da ita kuma tayi wani irin rumtse ido da matuƙar ƙarfi tana mai yin wasu irin surutai ahankali, bayan ta dunƙule tafin hannun ta, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata tare da tafin hannun nata tana mai kaisa kan bulalar dake riƙe ahannun ta ta shafeta da shi.
Take awurin bulalar ta ƙara wata irin miƙewa tare da banƙarawa tana motsi yarce kasan abu mai rai, tukun Gimbiya Tasmir ta ɗaga ta da matuƙar ƙarfi bayan ta cije leɓen ta na ƙasa idanuwan ta akan Bir, tana mai zambaɗa masa ita agadon baya!

Da ƙarfi ya rumtse idanuwan sa jikin sa na tsantsar rawa da karkarawa, sabo da tsantsar azabar da yaji ta ratsa jikin sa wacce bai taɓa jin makamanciyar ta ba, yayin da jini kuma yayi wani irin tsartuwa daga cikin jikin sa yana mai tsalle aƙasa.

"Gargabilu! Gargab..." Maganar ta ɗauke daga cikin bakin yana mai sakin ihu lasa-ƙasa, tayarce ya zamto ita kaɗai taji sabo da yarce ta ƙara zambaɗa masa bulalar agadon bayan sa!
Wani irin feshin jini jikin sa ya sake futarwa yarce kasan wanda aka tsaga da reza!
Tukun daga bisani ya ɗago kansa amatuƙar firgice yana mai watsa manya-manyan idanuwan sa cikin na Gimbiya Tasmir.

Ƙara ɗaga bulalar tayi da iyakacin ƙarfin ta tana mai sakar masa ita asaitin wuyan sa, tare da sakar masa wani irin murmushin mugun ta.
Amma amai-makon taji yayi ihu kamar yacce yayi ɗauzu sai kawai taga ya dake yana mai sake watsa ƙwayoyin idanuwan sa da suka canza launi daga fari zuwa ja cikin nata, tare da sakar mata wani irin shegen murmushi shima, tukun daga bisani ya lumshe idanuwan sa yana zaro harshen sa ahankali ya lashi gefen bakin sa da shi, sannan ya sake buɗe idanuwan sa akan ta yana mai sake jifan ta da kyakkyawan murmushin sa!

Wani irin baƙin ciki ne taji yazo ya caki zuciyar ta da matuƙar ƙarfi, take awurin kuwa ranta yayi matuƙar ɓaci, tayarce har idanuwan ta suka fara canza launi daga fari zuwa ja, tukun daga bisani ta rumtse tafin hannun ta tare da rufe idanuwan ta tana mai buɗe baki tace. "Rai Rai Rai Buuu Hooo Reee!" Kana ta buɗe sa tana mai watsa masa wasu abubuwa da suka bayyana acikin tafin hannun nata akan jikin sa tare da yin gefe da shi.

Take ya fara yin wani irin layi awurin yana mai shirin zubar da iccinan da suke ɗauke akafaɗun sa, tukun daga bisani ya fara tafiya adurƙushe cikin tsantsar azabar dake ratsa jikin sa yana mai fucewa daga cikin filin ya doshi wata hanya can daban, har lokacin ƙafadar sa ɗauke da iccinan yana layi, ganin hakan da Gimbiya Tasmir tayi ne ya sanya ta juyawa itama cikin tsantsar ɓacin rai tana mai nufar hanyar da yabi gadan-gadan!

*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*

Tana futa daga cikin babban falon nasu taci karo da wata baiwa, hannun ta ɗauke da wata haɗaɗɗiyar ƙwarya wacce take rufe da fai-fan kaba tare da ludayin duma har guda biyu akan ta.
Dasauri Baiwar taja baya tana mai faÉ—in. "Tuba nake ranki ya daÉ—e, ban san da zuwan ki ba shiya sa na sanyo kaina ciki."

Hannu kawai ta miƙa mata tana mai karɓar ƙwaryar ba tare da ta tanka mata ba, tukun ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da lambun gabas.
Tafiya take iska na kaɗa jikin ta, tayarce har gashin ta yake reto agadon bayan ta, sai dai kuma yau ɗin gaba ɗaya bata jin daɗin yana yin garin ko kaɗan, sabo da yarce take cikin tsantsar baƙin ciki, wanda ba komai ne yasan ya ta cikin sa ba sai zuwan Yariman Yamma jiya wurin ta, da kuma mafarkin ta na yau, tare da abun da ta gani alokacin da tayi bincike.
Gaba dayan ta jinta take asaɓule yarce kasan babu laka ajikin ta, ahaka har ta ɓulla cikin lambun gabas ba tare da tasan ta shigo sa bama, sabo da yare tayi nisa aduniyar tinanin hanyar zatabi wacce zata sadata da Giɗaɗon ta.

Afannin su Yarima Asad suma dukan su babu wanda ya lura da shigowar ta wurin, domin kuwa shi Al'amin farfesun naman cikin nan kawai yake ci yana lumshe idanuwan sa, yayin da shi kuma Yarima Asad har lokacin kansa yake durƙushe idanuwan sa akan wayar sa da yake aikin shafawa.

Tafiyar ta ta cigaba dayi cikin sanyi ba tare da tasan taƙamai mai cikin wurin da take bama, ahaka har ta ƙaraso gab da shimfiɗar da suke bata lura da suba, kamar yacce suma ɗin babu wanda ya lura da ita.

"Ashhh!" Ta faɗa da ɗan sauti cikin zazzaƙar muryar ta, sabo da yarce taji tayi tuntuɓe da wani abu wanda batasan ko menene shi ba, ga kuma yarce ƙwaryar madarar da take ɗauke ahannun ta mai ɗumi ta suɓuce daga kan hannun nata duka.

Atare dukan su suka ɗago kawunan su, shi Yarima Asad cikin tsantsar zafi da ƙuna rai, sabo da yarce ta kifo masa ƙwaryar madara akan duka cinyar sa, yayin da ita kuma ta ɗago domin taga abun da ya tokare ta ta faɗi, suna masu sanya ƙwayoyin idanuwan su cikin na juna!

Ƙurr sukayiwa juna da ido ba tare da wani ya iya ƙiftawa acikin su ba, barin ma Yarima Asad da gaba ɗaya yanayin sa ya sauya, tayarce har idanuwan sa suka farayin ja, yayin da ita kuma take kallon sa tana mai jin wata irin tsanar sa da haushin sa na lulluɓe ilahirin jiki da ruhinta, wacce bata san dalilin taba.

Ahankali ya janye idanuwan sa daga kan nata yana mai mayar dasu zuwa kan jikin sa da yayi faca-faca da madarar shanu, tukun daga bisani ya sake É—ago su yana mai sake kafeta da su, kamar yacce har lokacin itama take kallon sa cikin wani irin yana yi, yayin da shi kuma Al'amin ya saki baki tare da ajiye naman dake hannun sa yana mai aikin kallon wannan, sannan ya koma ya kalli wannan ba tare da ya iya furta komai ba!
Chapter 26 · 0% Book details