← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 79

Sashe 5

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fucewa daga cikin part ɗin nasu ya tsaya cak abakin ƙofa, yana mai kallon yarce jama'a keta hucewa cikin irin banzar shigar da Al'amin ya aje masa da sunan yasa ta shima.

Tsaye yay awurin yana mai ƙan-ƙantar da idanuwan sa tare da kar-katar da kai yana mai bin duk masu hucewa da kallo, yi yake yana taɓe baki tare da yamutsa fuska, ji yay gaba ɗaya bazai iya zama acikin gidan ba idan har baza'a dena waƴan nan kaɗaɗen ƙauyen cin da ake yi ba, domin ko shi ba ƙaramun takura masa sukayi ba, gaba ɗaya bai ɗauki irin waƴan nan bushe bushen ba amatsayin abubuwan nishaɗi, sai zallar gida danci da rashin waye wa kawai yake gani.

"Kai yanzu dan Allah mutanen nan da suke hucewa cikin shigar nan basu burge kaba?" Al'amin ya faɗa alokacin da ya ƙaraso wurin yana kallon sa.

Uhm! Yace kawai yana mai yin parkin space.

Da sauri zagagen da suke tsai-tsaye a area wurin suka taso suna masuyo kan su. Tun daga nesa suka fara faɗin. "Barka da futowa ɗan sarki jikan sarki, takawar ka lafiya bujimin maza, takawar ka lafiya jinin mulki, gaba salamun baya salamun Asadullahi ikon Allah, ɗa ga sarki Abdallah, shalele wurin sarauniya kuma gimbiyar matan hausa, jika ga sarki Ahmadu ƙani ga ciroma uban....
Cak suka tsaya a'inda suke suna masuyin shiru dukan su, sabo da yarce ya É—aga musu hannu sama yana mai dakatar dasu, ba tare da ya waigo ya kalli ko mutum É—aya daga cikin su ba.
Juyawa suka farayi suna masu komawa wuraren da suke, yayin da shi kuma ya cigaba da takawa cikin takusan sa da shi kaɗai ke hautsina ƙwaƙwalen ƴan mata su muto akan sa, yana mai dosar inda wata azababbar farar mota take, wacce take ɗauke da number mai suna YARIMA ASAD 08 sabuwa fidigil da ita.

Tun daga nesa ya sanye remote ya buɗe ta, shi yasa yana ƙarasawa wurin ya sanya hannu ya buɗe murfin yana mai shigewa ciki ya zauna akujerar direba.

Da sauri shima Al'amin ya ƙaraso wurin yana mai buɗe murfin ya shiga.

Lumshe ido Yarima Asad yayi yana mai É—ora tafukan hannayen sa akan stiyarin motar bayan yayi mata key.

"Wai yana ga kayo nan ne Asad, bayan kuma kasan fada zamuje ko?" Al'amin ya faÉ—a yana kallon fuskar sa.
Ƙala bai ce masa ba sai ma buɗe idanuwan sa da yayi yana mai janyo wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya fara shafawa.

"Da kai fa nake Asad kamun banza."

"To kai ɗin ubane ne da bazan ma banza ba, ko kuwa na maka dole ne akan sai ka biyo ni inda zani." Ya faɗa ƙasa ƙasa yana mai cigaba da danna wayar sa ba tare da ya ɗago ya kalle sa ba.

"Me kake nufi da hakan? Idan na fahimta kamar kana so kace ba fada mukai daga nan ba ko?"

"Kai ka juyo kuma."
Yarima Asad ya faÉ—a yana mai danna giyar motar bayan ya rufe motar gam.
Da wani irin mahaukacin ƙarfi ya take ta yana mai lailaya kanta atsakan-kanin wurin da suke ya juya ta.
Tukun ya É—ebe ta atamanin yana mai É—auke hanyar da zata sada sa da main get, ko mutanen da suke faman kai kawo aharabar gidan nasu bai lura dasu ba.

"Wai dallacan Asad me kake shirin yi haka ne?" Al'amin ya faɗa cikin ƙaraji yana mai dukan kujerar motar ransa amatuƙar ɓace.

Inda yake Asad bai É—ago ya kalla ba balle ya tanka masa, saima sake take motar da yayi ahaukace yana cigaba da dosar get É—in da zai sada su da wajen gidan sarautar.

"Kaga malam dallacan samu wuri ka sauke ni anan." Al'amin ya sake faÉ—a cikin fushi yana mai jin kamar ya mammake fuskar Yarima Asad tsabar takaici.

"Ai kana iya buÉ—ewa ka futa yanzu ma tunda ba É—aure ka nayi ba, kuma da kake cewa na tsaya na sauke ka ai ina ce da É—in bani na É—ora ka aciki ba ko?" Yarima Asad ya faÉ—a adai dai lokacin da ya shilla kan motar sa titi aguje.

Gaba ɗaya mutanen dake abakin titi harma da waƴan da suke acikin motocin su bin motar Yarima Asad sukayi da idanu, manya banda zagin sa da shegan tasa babu abun da suke yi, yayin da matasa kuma keta faman kambaba sa suna faɗin guy ɗin na burge su, sabo da yarce yayi matuƙar iya hannun sa.

Acan cikin mota kuwa Al'amin ne ya kalli Yarima Asad yana mai faÉ—in. "Amma Asad kai atinanin ka hakan da kayi ka kyautawa babban yaya kuwa?"

Murmushi Yarima Asad yayi wanda yayi matuƙar ƙara masa kyau, tukun daga bisani ya lumshe idanuwan sa ko damuwa bai ba da cewar kan titi yake duk da uban gudun da yake kwara-rawa, kana ya wara su daga baya yana mai buɗe baki yace. "Shin wai dan Allah ni nace ka biyo ni ne guy, koka na buɗe baki nace Al'amin kar kaje fada kallon naɗi ne?" Ya faɗa yana mai sake sakin murmushi hankali kwance.
Yayin da shi kuma Al'amin yayi matuƙar ƙulewa, sabo da yarce yaga shi ko ajikin sa bai damu bama.

"Amma dai ai kasan ban san nan kayo ba da babu abun da zai sa inbar hawan da zamuyi in biyo ka ko?"

Uhm! "To ai yanzu ma bata baci ba idan naje inda zani na tsaya sai ka futo kasamu mota ka juya, domin kuwa kasan ni dai bazan tsaya akan hanya ba, kuma kasan bazan iya zama acikin gidan can ba ana waÆ´an can kaÉ—aÉ—e da bushe -bushen banzan can na gidadanci."

"To karka tsaya ɗin mana ɗan iskan banza kawai." Al'amin ya faɗa cikin zafi yana mai buga ƙwafa, yayin da shi kuma yarima Asad yay shiru yana mai mai da hankali akan tuƙin haukar da yake hankali kwance.

*ASADULLAH PALACE*

Shi ne sunan da aka rubuta daga saman azababben building É—in daya tunkara da motar tasa wanda get É—in wurin kaÉ—ai abun kallo ne bama ginin ba.

Tun daga nesa ya danna horn É—aya daga nan kuma bai sake yin wani ba.
Da sauri wani matashin saurayi ya wangale tamfatse-tsen get É—in yana mai kauce wa.
A hankali ya fara taka motar yarce kasan ba zai tafi ba yana tunkarar cikin wurin, kai idan har ba sani kayi ba ka gansa akan titi yanzu kuma akace maka shine yake irin wannan tafiyar sai ka rantse da Allah kace ƙarya ne, domin kuwa ko mutum dake tafe aƙafa sai ya hucewa sa sosai a'irin yarce yake taka ta yanzu!

*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULÆŠE*

Da gudu ƴar ƙaramar yarinyar mai kimanin shekaru bakwai aduniya ta afka cikin ɗakin tana ta faman numfar-fashi, alamun ba ƙaramun gudu tayi ba kenan.
Durƙushewa tayi akan guiwoyin ta tana ta faman zare ido tare da sakin numfar-fashi.

Ahankali kyakkyawar budurwar da take zaune agefen wani azababben gadon ƙarfe mai matuƙar kyau, wasu matasan ƴammata guda biyu da suke sanye da kayan fulani na tufke mata uban gashin da yake ɗauke akan ta mai tsananin yawa, tsayi da baƙi ta ɗago dara-daran fararen idanuwan ta tana mai watsa su akan ƴar yarin yar data shigo aguje.
Kallon yarin yar tafarayi tun daga sama har ƙasa ba tare da tace komai ba. Yayin da ita kuma ƴar yarinyar har lokacin take durƙushe aƙasa tana sakin nishi.

ÆŠaya daga cikin Æ´ammatan da suke gyarawa budurwar nan gashi ne ta É—ago kai tana kallon yarinyar fuskar ta É—auke da murmushi, tukun daga bisani ta buÉ—e baki cikin harshen fulatanci tana mai faÉ—in. "Shin me ya faru ne uwar gijiya ta beldo?"

Ɗago kai yarinyar tayi tana mai kallon ta, tukun tace. "Ba hulin ki nazo ba." Kana ta mai da idanuwan ta kan fuskar budurwar da ake gyarawa gashi tana mai cewa. "Adda ta gote ki duka sun tashi sun gudu, yanzu naje ansho fulata wani ya kal-kaɗamun jelar sa afuska ta ya tashi sama, kinga kenan gwalo yayi mun ko?" Yarinyar ta faɗa tana mai kallon budurwar bayan tazaro manya manyan idanuwan ta waje, alamun dai abun ba ƙaramun firgita ta yayi ba.
Yayin da waƴan nan ƴammatan bayin guda biyu suka tuntsire da dariya suna kallon ta. Ita ko uwar gayyar wacce aka kawowa labarin taɓe baki tayi tana kallon ƴar yarinyar, kana daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta cikin zazzaƙar muryar ta mai matuƙar daɗi tana mai faɗin. "To uwar shirme ni wuce ki bani wuri." Ta faɗa tana ɗauke kai daga kan yarinyar, yayin da ita kuma yarin yar ta ɗaure fuska tana mai miƙewa tsaye ranta aɓace ta juya ta tafi, sai da taje bakin ƙofar futa daga ɗakin, tukun ta juyo tana mai kallon yayar tata, sannan daga bisani ta buɗe baki tana cewa. "Bama zan ƙala baki labari na ba, kuma Allah yasha kalsu dawo ma." Ta ƙarashe maganar da murguɗa baki, tukun ta juya tana mai fucewa daga cikin ɗakin.

Murmushi dukan su su ukkun sukayi har ita ba tare da sunce komai ba.
Sun É—auki dogon lokaci suna gyaran gashin tukun suka kammala.
Gefe guda suka koma suka tsaya kawunan su durƙushe aƙasa, ko wacce hannun ta riƙe da cumb.

Gyara zaman ta tayi akan gadon da take, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kuna iya tafiya sai na sake neman ku kuma." Ta faɗa tana mai miƙewa daga kan gadon.

"Tom ranki shi daɗe Allah ya ƙara lafiya." Suka haɗa baki wurin faɗin haka, tukun suka juya suna masu fucewa daga cikin ɗakin.

Tafiya tayi zuwa bakin mudubin da yake maƙale ajikin bangon ɗakin, wanda gefe da gefen sa yake ɗauke da ƙarafa masu adon flawoyi kalar ruwan zuma, kamar yacce duka kayan ɗakin suke.
Chapter 5 · 0% Book details