← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 79

Sashe 77

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gimbiya Tasmir ta fad'a cikin wata irin murya, wacce take nuni da tsantsar kalar b'acin ran da take a cikin sa, ta yadda har iskar bakin ta da ke futowa tana dukan fuskar sa a lokacin da take furucin ta zamto zazzafa matuk'a.

Lumshe idanuwa Bir yayi yana mai d'an juyar da kai gefe ya fesar da iska daga cikin bakin sa, kana ya sake juyowa b'arin da take yana mai d'an dage mata girar sa d'aya, alamun yana jin ta to.
Yayin da ita kuma ta d'ora da fad'in.

"Tunda na taso a rayuwata, ban tab'a sanin wani abu wai shi tsoro ba, sannan kuma ban tab'a sanin b'acin rai ba, kana bansan meye fad'uwar gaba ba, kasan ko me yasa?
Sabo da na taso cikin tsaro da kariya, sannan kuma na taso cikin gata.
Amma tun a karo na da kai na farko komai nawa ya fara sauyawa, b'acin ran da ban san sa ba kasa nasan sa a ranar, fad'uwar gaban da ban santa ba kasa naji ta a ranar, magana da yinta ke wahalar dani kasa ta zamto abaryina ta dole.
Dan haka ayau yau d'in nan, a kuma yanzu-yanzun nan nake son sanin abun da ka taka."

Ta fad'a cikin wani irin yanayi, tukun ta fara d'an d'aga k'afafuwan ta tana mai zagayasa a wurin da yake, kana ta sake dawowa gaban sa ta tsaya, tana mai watsa jajayen idanuwan ta a cikin nasa, ta dora da cewar.

"Shin me ka taka? Wane kalar sihiri kake tattare da shi ne? Ya sunan bokan daya baka shi?
Sannan kuma akan me bugun zuciya ta yake sauyawa a duk lokacin da nayi gamo da kai!!! ?"

Ta k'arasa maganar cikin k'araji tana mai d'aga k'afar ta d'aya ta dire ta a k'asa, kana ta d'ora da sakin numfar-fashi idanuwan ta k'ur akan Bir.

Shi kuwa Bir wami irin farin ciki mara misaltuwa ne yaji ya lullub'e zuciya da ruhin sa, sabo da fahimtar da yayi ba shi kad'ai bane ya afka kenan.
Tabbas sunan da iya ta sanya masa yana gab da zamtowa na gaskiya, wato Jarumi, domin kuwa ya riga da ya sani muddin Gimbiya ta zama tasa to idan da akawai abun da yafi Jarumi ma za'a kira sa da shi.
Hakan ne yasa sa sakar mata murmushi kawai, yana mai sake kafeta da tsumammun idanuwan sa da suke d'auke da wani irin sinadari a cikin su amai-makon ya bata amsar ta.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir yadda kasan saukar tafasash-shen ruwan dalma akan ta haka take jin saukar murmushin sa a cikin jikin ta.

Lokaci d'aya jikin ta ya k'ara d'aukar kyarmar b'acin rai, sabo da ganin da tayi tamkar yana shirin raina mata hankali, tunda gashi nan amai-makon ya bata amsar ta sai kafeta da yayi da idanuwan sa yana aiko mata da murmushi ma.

"Wallahi! Wallahi Azaba mai rad'ad'i zata hau kanka, irin wadda tun da kazo gidan duniya baka tab'a jin labarin ta ba balle har ka ganta muddin kayi wasa da kalami na, dan haka ka gaggauta bani amsar tambaya ta tun kafin raina ya k'arasa dagulewa, hukunci na ya hau kanka."

Gimbiya Tasmir ta sake fad'awa Bir, jijiyoyin kanta na k'ara futowa rad'a-rad'a akan goshin ta.

"To idan kuma ban shirya fad'ar amsar ba fa, ko kuma nima nace ban santa ba fa?"
Bir ya fad'a cikin tsantsar farinciki, yana mai lumshe idanuwan sa.

"Tabbas ko hakan tamkar dai-dai yake da ka kira mutuwar ka kai da kanka zuwa gare ka domin ta d'au ranka, domin kuwa azaba ta ta huce gaban kwatance, dan haka dak'ik'a d'aya kawai na baka, ka gaggauta bani amsa ta ko kuma komai ma ya faru da kai k'ask'antacce mara galihu."

"To banda amsar nace miki 'yar gata."
Bir ya fad'a yana jifan ta da murmushin sa tamkar ba zagin sa ita tayi ba.

Wani irin juyi Gimbiya Tasmir tayi daga wurin da take, tukun ta mik'a hannun ta-tana mai kamo linzamin dokin ta, kana ta d'ane kansa tana mai rumtse idamuwan ta, tare da mik'ar da takobin ta-ta saita Bir da ita.
Wasu irin surutai tayi da matuk'ar k'arfi, tana mai nuna Bir da takobin nan tata.
Kana ta daki cikin dokin nata da k'afar ta tana mai nuna masa hanyar da zasu bi.

Wata irin iska mai matuk'ar k'arfi Bir yaji ta dake sa, kana ta k'udun-dune sa acikin ta, tukun ta fara wani irin fuzgar sa a cikin k'asa, ta yadda kawai yaji sa yana bin bayan dokin Gimbiya Tasmir daga kwancen da yake a guje.

Sosai take gudu akan dokin nata tana mai nutsawa wata hanya.
Yayin da Bir kuma ke biye da ita abaya iska na jansa da matuk'ar k:arfi, sosai kansa da wasu wurare na jikin sa duk suka farfashe, sabo da duwatsun da yake cin karo da su akan hanyar.
A haka har suka b'ulla gaban wani gini wanda yake d'auke da wata irin k'ofa a jikin sa, wato d'akin Azaba.

Cak dokin Gimbiya Tasmir ya tsaya a gaban k'ofar d'akin nan.
Shima kuwa Bir adai-dai wurin yaji iskar nan ta dena funcikar sa, amma kuma bawai sakin sa tayi gaba d'aya ba, har yanzu dai yana k'udun-dune a cikin ta ne.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir cikin wani irin yanayi ta duro daga kan dokin nata, tukun ta juya b'arin da Bir yake tana kallon sa, kana ta bud'e baki cikin kaushi tana mai fad'in.
"Shin ka shirya bani amsar tambaya ta yanzu ko k..."
Maganar ta-tace ta katse, sabo da yadda taga Bir ya girgiza mata kai yana sakar mata murmushi a yadda yake tun kafin takai k'arshen zancen nata ma, alamun bai shirya ba d'in kenan.

Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da k'ofar nan take da wani irin sauri, kana ta d'aga takobin ta sama tama mai nuna k'afor da ita, sannan ta bud'e baki cikin k'araji, tana mai fad'in.
"Gargabiluuu!!!"
Take kuwa a wurin k'ofar ta fara bud'ewa har ta bud'e duka.
Kana ta sake juyawa b'arin da Bir yake tana mai sake yin wasu surutan.

Ai kuwa tini iskar nan ta sake d'ibar sa a guje zuwa cikin d'akin da ya kasance d'an k'arami da shi, mai zagaye da kaskwayen huta a cikin sa suna ta faman ci.

D'aga k'afafuwan ta ita tayi tana mai bin bayan sa.

Shi kuwa Bir iskar nan bata sake sa ba har sai da ta dangana da shi gaban wasu irin k'arafa, tukun ya jisa sakayau gaba d'ayan sa, ta yadda har ya samu damar mik'ewa tsaye yana mai kallon ciwu, kan jikin sa, amma sai dai kuma ko gama mik'ewar baiyi ba yaji wasu irin k'arafa sun tawo daga sama sun d'ad'd'aure sa gagam a jikin su.

Cikin wani irin yanayi na tsantsar firgici da tashin hankali ya d'ago idanuwan sa yana mai watsa su akan fuskar Gimbiya Tasmir da take tsaye a gaban sa, sabo da yadda yaji k'asusuwan jikin sa tamkar zasu warwatse.

"Rai Rai Rai Buuuu Hooo Reeee."
Gimbiya Tasmir ta fad'a tana mai nunasa da takobinta.
Take kuwa yaji wani irin bala'in zafi, irin wanda bai tab'a riskar saba tun da yazo gidan duniya ya lullub'esa, ta yadda har bai san lokacin da ya saki wani irin gigitaccen ihu ba.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir tana jin ya saki ihun nan ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwanta ta doshi hanyar waje.
Wasu surutan ta sakeyi a lokacin da ta futa bakin k'ofar d'akin.

Ai kuwa take wani irin bak'in duhu ya mamaye gaba d'aya ilahirin cikin d'akin.
Tukun ta juya tana mai hayewa saman dokin ta.
Sannan ta sake nuna k'ofar da takobin ta tana mai kiran sunan Gargabilu.
Take kuwa k'ofar ta koma ta rufe gam.
Sannan ta damk'i linzamin dokin ta tana mai juyawa suka doshin hanyar da zata mayar da ita gida da tsananin gudu.

_CIGABAN LABARI_

*K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*

Kallon kallo Yarima Asad da Gimbiya Haddiyal suka cigaba da jifan junan su da shi.
Yayin da Al'amin kuma ya saki baki yana kallon su, zuciyar sa cike da fargabar abun da Yarima Asad zeyiwa Gimbiya Haddiayl, sabo da yadda yaga gaba d'aya cinyoyin sa sun b'aci da madarar shanun nan.

Shi kuwa Yarima Asad a hankali ya k'ara janye idanuwan sa daga kan fuskar ta yana mai sake kallon jikin sa, kana ya k'ara d'agowa yana mai k'ara kafeta da su.
Yayin da yake jin zuciyar sa na wani irin bugu da matuk'ar sauri, abun da tun da yake a rayuwar sa bai tab'a ji ba kenan dan ya tsaya da wata yarinya.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal haka nan taji wani irin haushin sa ya lullub'e gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyar ta.
Amai-makon ta basa hak'uri a matsayin ta na wacce tai masa laifi sai tak'i yin hakan gaba d'aya, a karshe ma sai idanuwanta da ta janye daga cikin nasa a hankali.
Kana ta mik'e ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwan ta da niyyar komawa.

Amma sai ji tayi an cafki yastun hannuwan ta da matuk'ar sauri.

Cak ta tsaya a wurin da take tana mai rumtse idanuwan ta, sabo da yadda taji wani irin abu ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har izuwa 'yantsun k'afafuwan ta a lokacin da ya rik'o yatsun hannun nata.
Kafin daga bisani kuma ta fara juyowa gare sa fuskar nan ta ta a matuk'ar d'aure.

Ido hud'u suka suka sakeyi da shi yana mai cigaba da kallon ta da tsumammun idanuwansa.

'Dauke nata idanuwan tayi daga kan fuskar sa, tana mai mayar da su kan 'yantsun hannuwan sa da suka kasance had'e da nata wuri d'aya.

'Dan taune leb'enta tayi na k'asa da d'an k'arfi, tana mai jin wani irin mugun bak'in ciki da takaici na cakar ta, kafin daga bisani kuma ta janye idanuwanta daga kan 'yantsun nasu, tana mai mayar da su kan fuskar Yarima Asad.

Hakan da Yarima Asad ya gani ne ya sanya sa sakin hannun nata da sauri.

Yayin da ita kuma ta hurga masa wani irin kallo, kafin ta juya tana mai kama hanyar da ta biyo tazo wurin, ba tare da ta d'auki ko k'waryar ta ba.
Chapter 77 · 0% Book details