← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 79

Sashe 45

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Kaka ta gama mayar da komai banda sandar nan, tukun ta mai da ƙofar bukkar ta rufe ta, sannan ta juya tana mai ɗaukar sandar ta doshi hanyar ɓangaren Gimbiya Kaɓel, domin taje ta damƙa mata sandar jinjirar tata.

*JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Yau aka tashi da tsantsar farin ciki a ɓangaren Gimbiya Fulani, sabo da haihuwar Ƴa macen da tayi da asuba itama, bayan shafe shekara takwas da tayi rabon ta da haihuwa, wato tun bayan haihuwar Yarima Asad da yayi matuƙar girma da wayo yanzu kenan.
A lokacin da sautin kiɗin tambarin Ƴa mace ya daki kunnen magautan ta ba ƙaramun farin ciki sukayi ba, domin kuwa dukan su dama suna cikin tsantsar fargaba ne ako da yaushe, sabo da tsoron abun da kunnuwan su zasu juyo musu.
Yayin da ita kuma a ɓangaren ta sukayi matuƙar farin ciki da samuwar ƴar, wacce ta ɗebo kamannin mai martaba sak, yarce kasan kaki yayi ya tofar.

A ɓangaren Asad kuwa yafi kowa farin ciki da murnar haihuwar da Mamayn tasu tayi musu, badan komai ba kuwa sai dan sanin da yay na za'ayi hawan suna a ranar suna, gashi shi kuma dama ya kasance mayen doki, sabo da yaga yacce akayiyyi a lokacin da Gimbiya Huwaila ta sake haihuwar ƴa macen da bata so ba, sannan kuma da lokacin da Gimbiya Amina itama ta ƙara haifo ƴa mace, wannan dalilin yasa yake ta fatan asake yin wata haihuwar a gidan su, sabo da mai martaba yace masa ya bari sai an sake wata haihuwar, tukun sai ya fara yin kilisa, shima a lokacin ya ƙara girma, sabo da yarce yaso abar sa shi kaɗai akan dokin sa shekaru biyu baya da suka huce lokacin da Gimbiya Amina ta haihu, amma mai martba yaƙi, hakan ne yasa yayi matuƙar farin ciki da haihuwar da mamyn tasa tayi fiye da duk sauran yaran, domin kuwa yanzu shi da kansa yake hawa dokunan sa ba tare da wani ya riƙe sa ba.

A ɓangaren Babban Yaya sosai yayi ya zama saurayi, domin kuwa a yanzu yana da shekaru goma shatakwas ne a duniya dai -dai, a karatu kuma yana matakin ajin ƙarshe na secondry ne, kuma da zarar ya kammala za atura sa ƙasar turai jami'a, kamar yacce sauran yayyan sa mata da kuma ƴan gidan duka suke karatun su acan.

*UNGUWAR ÆŠAN TANKI.*

Sai da Aishatu ta shekara bakwai da haihuwar da tayi a Baƙar Masarauta, tukun ta sake haihuwar wani Ɗa namijin, wanda yake da shekara ɗaya a duniya yanzu kenan, mai suna Salman.

Har kawo yau dai tana nan da halayyar ta ta rashin son yin magana da kuma zaman cikin ɗaki, sannan kuma bata bar tinane-tinanen nan da takeyi ba, kamar yacce a kullum daren duniya take mafarkin wannan yaron da koda yaushe yake ƙara girma.
Yayin da Ahmda kuma yake da shekara goma shatakwas yanzu a duniya.
A fannin karatun boka yana matakin ajin ƙarshe na secondy ne yanzu, yayin da fannin na addini kuma ya sake yin matuƙar zurfi, domin kuwa a yanzu haka har aji yake da shi a Islammiyar su, sannan kuma yake jan sallah a wani sabon masallacin kamsu salawat da aka buɗe anan cikin unguwar tasu aka basa limancin sa, kasancewar duk yafi sauran yaran harma da manyan ilimi a unguwar, hakan kuwa ba ƙaramun farin ciki ya sanya iyayen su ba.

*ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFU CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Cikin tsantsar farin ciki ta durƙusa ƙasa, tana mai sa hannu ta ɗauki kyakkyawa jinjirar dake ai'kin tsala kuka da matuƙar ƙarfi, ta ɗora ta akan showel ɗin da yake ninke a gaban ta, bayan ta yanke mata cibi, tukun ta ɗago tsaye tana mai rangaɗa w..............✍

_HAR YANZU LABARIN BAI FARA BA FA. DOGUWAR TAFIYA CE, MAI 'DAUKE DA ABUBUWA KALA-KALA ACIKINTA. AZABABBIYAR SOYAYYA, SADAUKARWA, TSANANIN BAN TAUSAYI, TARE DA MATUK'AR ZALINCI DUK SUKE ACIKIN LABARIN BAK'AR MASARAUTA. AYI COMMENT DA SHARHI HAKAN SHI ZAI SA MUJE HAR ZUWA WURIN DA NAKE FA'DA MUKU._

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 18*

Wata irin buɗa mai matuƙar sauti, yayin da ita kuma ɗaya ta juya a guje tana mai fucewa daga cikin ɗakin domin taje takai rahoto.

Cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya labarin haihuwar Ƴa macen da Gimbiya Salwa tayi ta zagaye duka cikin Baƙar Masarauta.

Lokacin da labarin ya isa kunnen Sarki Barbaru ba ƙaramun farin ciki yayi ba, domin kuwa tsabar murnar da yayi da jin labarin a take a wurin yayiwa Hadimar da ta kawo masa Albishir ɗin kyautar Raƙumi ɗaya.
Tukun ya miƙe daga kan kujerar sa cikin sauri yana mai kama hanyar waje.

Ko da ya ƙarasa cikin ɗakin zaune ya samu mahaifiyar sa riƙe da jinjirar a hannunta, tana shafeta da mai.
Da sauri ya ƙarasa zuwa inda suke yana mai zube guiwoyin sa a ƙasa, tukun ya buɗe baki cikin tsantsar farin ciki, idanuwan sa a kan fuskar kyakkyawan jinjirar da ya gani, yana mai faɗin. "Shin da gaske ne ba mafarki nake ba, wannan kyakkyawar jinjirar ta wace?" Ya faɗi maganar ta sigar tambaya, yana mai kai yatsun hannuwan sa zuwa kan ƙafar jaririyar ya riƙe.

"Tabbas kuwa ɗiyar kace a gaske kake ganin ta ba mafarki ba, haƙiƙa Ubangiji Gargabilu yay mun kyautar jika mace." Tsohuwar matar da take zaune tukuf riƙe da Ƴar ta faɗa tana mai kallon fuskar Sarki Barbaru ɗauke da murmushi a bakin ta.

"Godiya ta tabbata ga Ubangiji Gargabilu, haƙiƙa kagamamun komai da kabani kyautar ƴa mace." Sarki Barbaru ya faɗa yana mai miƙa hannu ya ɗauki Ƴar.

Zaman sa ya gyara a wurin da yake, yana mai tanƙwashe ƙafafuwan sa, sabo da yaji daɗin riƙon ƴar da kyau, tukun daga bisani ya miƙa hannun sa zuwa inda yaga wata ƴar roba mai matuƙar kyau da take a gaban Mahaifiyar tasa, yana mai janyo ta gaban sa, tukun ya buɗe murfin ta.

Baƙin fenti ne tare da soso mai yankan Tambarin Masarautar tasu a cikin sa.

Hannu ya sanya yana mai zaro soson daga ciki, bayan ya dangwalo fentin, sannan ya É—ago sa yana mai kai sa kan fuskar yarinyar ya manna mata shi a kan goshi, kana ya sake manna mata akan kumatunan ta duka, har lokacin fuskar sa É—auke da tsantsar murmushi.

Kyakkyawa ce a jin farko jinjirar, gata da wani irin yalwataccen gashi da yake sunƙum tun da ga kan ta har zuwa kan fatar jikin ta.
Sosai take da girma yacce kasan wacce tayi irin sati ukkun nan a duniya. Banda wawurar yatsu tana kaiwa baki tare da wuwwurga manya-manyan fararen idanuwan ta masu ɗauke da baƙar ƙwaya huluk a cikin su babu abun da take yi.

Ɗago ta Sarki Barbaru yayi, bayan ya gama manna mata tambarin masarautar a jikin ta yana mai riƙe ta a hannun sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin farin ciki, idanuwan sa ƙur a kan jinjirar, yana mai faɗin.
"Shekarau da dama ina zaman jiran zuwan ki, idanuwan sun daɗe suna tsumayen ganin ki, kunnuwa sun jima suna son jin sautin muryar ki, yayin da hannuwa kuma suka ɗau tsawon shekaru suna nararin jinki akan su, amma Ubangiji Gargabilu bai yaddar ba sai yanzu, dan haka na miki alƙawarin zamtowa Uban da babu kamar sa a duk faɗin duniya a gareki, Uban da ko a lokacin baya ba ayi kamar sa ba.
Zan baki gata irin gatan da babu ɗiyar data taɓa samun kalar sa a duniya, zan hanaki kuka, sannan kuma na sanyaki dariya ɗiya ta, zan baki kariya irin kariyar da ba'a taɓa baiwa wata ƴa kamar taba a gidan duniya, sannan kuma zaki zamto Jaruma irin Jarumar da babu kamar ta a faɗin duniya, zaki zamto jaruma wacce tarihin ta zaiyi shuwura ya zagaye duk duniya, Jarumar da tarihin ta bazai taɓa gushewa ba, wannan alƙawari ne na ɗaukar miki yake Ƴata."

Ya ƙarasa maganar yana mai rungume ta a ƙirjin sa, tukun daga bisani ya janye ta yana mai miƙa ta zuwa hannun mahaifiyar sa, sannan ya miƙe yana mai juyawa ya fuce daga cikin ɗakin.

*BAYAN SATI ÆŠAYA.*

Yau ta kasance ranar sunan jinjirar da aka haifa, hakan ne yasa tun daren jiya ake ta shirye-shirye a cikin Baƙar Masarauta, tare da girkuna kala-kala.
Duk inda ka gifta banda Bayi Mazan su da Matan su babu abun da ake gani.
Yayin da filin da za'ayi bikin suna kuma ake ta aikin shirya sa, wani irin kiɗa mai matuƙar sauti da daɗi na tashi daga cikin sa.

Zagaye yake da randina manya manya da suke ci da huta ta ko ina, yayinda daga can jikin bango kuma aka a jiye wasu irin kujeru masu tsananin kyau da suka ji uban ado a jikin su, daga can tsakiyar filin kuwa nan ma ɗin wani ƙatoton kaskon hutar ne a ajiye.
Yayinda acan kan wani dakali kuma da yake a gaban filin aka saƙale wasu irin danƙara-danƙara Shanu har kimanin guda goma shabiyu, sai daga gefen sa kuma manya-manyan tukwane ne ɗore akan duwar-watsu suna ci da huta, har kimanin guda takwas, da alamun dai girki akeyi ne a wurin, duba da yarce matan hurin suke ta faman ƙara iza wutar, ga kuma kayan ayukka irin su robobi da fanteku da suke a jiye a gaban su da matuƙar yawa.

Misalin ƙarfe goma na safe dai dai salon kiɗan da ake bugawa a wurin ya canza, tukun daga bisani sai ga tawagar Bayi nan Mazan su da Matan su sun fara shigowa cikin filin da rawa, sai dai kuma a wannan karan babu wani abu da yake ɗauke a hannuwan su, kasancewar ba bikin godiya bane ake yi, sai ma tsantsar murmushi da annashuwa ne da suke a kwance a kan fuskokin su.

Shigowar su duka baifi da muntina biyar ba, sai ga tawagar su Sarki Barbaru nan sun tawo Dakaru na take musu baya.
Chapter 45 · 0% Book details