← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 79

Sashe 70

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai kuma koda ta sake bud'e idanuwan nata bayan ta janye hannun ta daga kai, da abun da ta gani a farko ta sake yin arba.
Wato Sunan Yarima Asad akan katin, tare kuma da jerin numbobin sa.
Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da Billy take cikin sauri, bakin ta har yana rawa wurin fad'in.
"Ya akai hakan ta faru ne Beb? Ya ki kai? Me kuma kika basa da har ya baki katin sa?
Kai anya ma kuwa da gaske nasan ne Billy?"
Zee ta fad'a cikin tsantsar mamaki, yayin da har lokacin kuma take kallon katin nan tana sake juyawa sa a cikin hannun ta, kana kuma ta sake d'ago kai ta kalli tun daga sama har k'asa.

Ita kuwa Billy wani irin murmushin farin ciki ta saki, kafin daga bisani kuma ta bud'e baki tana mai fad'in.
"Kamar ya anya ma kuwa na san ne?
To na tambaye ki mana, dama akwai wani Prince Asad d'in ne bayan shi wanda kika sani."

Girgaza kai Zee tayi idanuwan ta akan fuskar Billy, tukun daga bisani ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in.
"Shi d'in ne dai kawai."

"To kinga kenan babu wani zancen kokwaton shine ko ba shi bane ba, kuma ma wai mantawa kikayi da abun da na fad'a miki ne tun a ranar dana fara ganin sa."
Billy ta fad'a tana mai gyara zaman ta tare da sake fuskantar Zee sosai.
Tukun ta d'ora da cewar.
"Idan baki manta ba dama na fad'a miki cewar ni d'in ban tab'a neman abu na rasa sa ba tunda nazo duniya, haka kuma dan wasu sunyi sun kasa ba shi ne yake nufin nima zan kasa ba, domin kuwa kowa yana buga kalar nasa salon wasan ne, wanda kuma gashi naje na bugo nawa, sannan nayi wining acikin sa, dan haka ina san ki cire duk wani mamakin dake a cikin ranki ki fara kira na da Billy'n Asad, domin kuwa ya riga da ya zamto nawan."
Ta k'arasa maganar da sakin murmushi, tare da dafa kafad'un Zee.
Yayin da ita kuma Zee ta girgiza kanta tana mai sakin murmushi, tukun daga bisani tace.
"Tabbas na yadda da batun ki, ke d'in ta daban ce Beb, domin kuwa samun kallo daga wurin Yarima Asad ma kad'ai ba abu bane mai sauk'i, amma sai gashi ke yau daga had'uwar farko kin tawo hadda phone number's d'in sa, dan haka Congratulation Friend."
Zee ta k'arasa maganar fuskar ta d'auke da murmushi, kana tana shafa kiston dake d'auke akan Billy, tukun daga bisani ta d'ora da fad'in.
"To wai in tambaye ki mana, dan Allah ke kuwa Billy wani irin salo ne kika jewa Prince Asad da shi da har ya bada kai haka da huri.
Please kiyi sauri ki fad'a mun na k'agu naji yadda labarin yake."
Ta k'arasa maganar tana mai k'ara gyara zaman ta akan kujera.

Yayin da itama Billy ta janye cinyoyin ta daga kan na Zee da ta danne ta, tana mai zama sosai akan kujerar ta fuskan ci Zee sossi.
Tukun ta fara jero mata duk abun da ya faru tun daga A har Z.
Kana tayi shiru tana mai sakin murmushi.

"A gaskiya kam da gaske ke d'in 'yar sa'a ce wallahi Beb."
Zee ta fad'a tana mai mik'awa Billy hannu suka tafa.
Sannan suka d'ora da hirar su cikin tsantsar farin ciki, domin kuwa ko ita Zee tayi natuk'ar taya Billy murna, sabo da yadda taga ta kamu da mahaukacin son sa, sai dai kuma a k'asan zuciyar ta tana mai tausayin irin yadda zata gwaru a wurin Asad, dan kuwa babu labarin da bata sani ba na wahalar da 'yammatan sa suke akan sa, amma kuma dai-dai da kalmar so babu wadda ya tab'a furtawa a cikin su.

A cikin hirar tasu ne Zee take cewa Billy.
"To yanzu kuma yaushe ne zaki koma wurin nasa?"

Shiru Billy tayi tana mai d'aga kanta sama, kafin daga bisani kuma ta sauke sa tana mai watsa idanuwan ta akan fuskar Zee.
Sannan ta bud'e baki tana mai fad'in.
"Ina ganin kamar nan da kwana ukku zuwa hud'u masu zuwa gaba kenan, duk da dai da son samun abun da zuciya take so ne to yanzu ma bata k'i a sake ganin sa ba, sai dai kuma a yadda naji labarin sa tabbas idan na nuna masa maita-ta tun farko zai watsar da ni, domin zaiga kamar nayi mahaukaciyar damuwa da shi, hakan yasa zan bari har sai zuwa nan da 'yan kwana ki sai in koma, in yaso tunda ina da number sa a hannu na yanzu sai nai ta tura masa da message's na fatan Al'khari harma da kira kafin ranar."

"Tabbas hakan ma yayi sosai kuwa, domin kuwa kina komawa gobe ma zai iya fara tinanin ko dama can kin saba mu'amala da maza sosai, da ganan kuma zai fatattake ki, dan kuwa babu abun da ya tsana a rayuwar sa face amasa kishiya, wato kina tare da shi ki kuma ki kula wanin sa, dan haka sai ki kiyaye."
Zee ta fad'a tana mai mik'ewa tsaye.
Itama Billy mik'ewa tayi tsayen tana mai d'aukar jakar ta-ta doshi hanyar bedroom d'in ta, bakin ta na furta kalmar.
"Ai nama kiyaye na gama Beb."

*BAYAN SATI 'DAYA.*

*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Tun bayan had'uwar da Bir yayi da Gimbiya Tasmir har yau Allah bai sa sun sake cin karo ba, duk da yadda yake aikin ziryar bin kan hanyoyin ta ako da yaushe, domin kuwa ba k'aramun matsuwa yayi da ya sake ganin fuskar ta ba, ta yadda har sai da ya d'an fara, sabo da yadda kullum yake yini da tinanin ta, ga kuma mafarkin ta da yake yi a cikin yana yi daban-daban a duk lokacin da ya kwanta bacci.

Gaba d'aya ya dena zuwa ko ina hatta da daji wurin harbo abubuwan da ya saba, sabo da yadda yake yini ko da yaushe akan hanyar Gimbjya Tasmir.

Babu yadda iya batayi ba da shi akan ya fad'a mata abun da yake damun sa a 'yan kwanakin nan, sabo da ganin da tayi yana ta ramewa, ga kuma yadda ya sake komawa shiru-shiru fiye da da, duk da dai dama shi can ba mutum bane mai hayaniya, amma sai dai kuma a yanzu ya ninka bayan nesa ba kusa ba.

Amma Bir yak'i fad'a mata, sai dai yace mata ba komai kawai, sabo da sanin da yayi na muddin taji silar komawar sa hakan to ba k'aramun tashin hankali zata shiga ciki ba, wanda shi kuma bazai tab'a son haka ya faru da ita ba.
Wannan dalilin ne ya sanya sa b'oye mata gaskiyar damuwar sa, duk da yadda ya saba fad'a mata komai nasa kuwa.

Tsaye yake jingine jikin wata bishi da take akan hanyar da Gimbiya Tasmir take bi lumshe da idanuwan sa.
Yayin da yake hangen ta a cikin idanuwan sa tana mai jifan sa da wani irin kyakkyawan murmushi wai.
Yana a cikin wannan yanayin ya fara jiyo sautin gudun jama'a acikin kunnuwan sa tamkar a mafarki.
Hakan ne yasa sa bud'e idanuwan sa cikin sauri, yana mai bin Bayin da yaga suna aikin gudu da kallo.
Kafin daga bisani kuma wani irin murmushin farin ciki ya sub'uce masa daga cikin baki, sabo da fahimtar da yayi na Gimbiya ce zata huce.

Take kuwa yaji gaba d'aya zuciyar sa na yin sanyi, ga wani irin nishad'i da yake lullub'e sa ta ko ina.
Amai-makon shima ya gudun sai ya koma bayan bishiyar nan da yake jingine da ita, yana mai lab'ewa a jikin ta, ta yadda baza su tab'a hango sa ba a lokacin da suke tawowar har sai dai idan sun k'araso wurin da yake.
Yayin.da shi kuma ya tsara abun da zai aiwatar a cikin zuciyar sa kafun su iso gare san.
Wannan dalilin shine ya sanya sa b'oyewar.

A b'angaren su Gimbiya Tasmir kuwa tun bayan waccan had'uwar tasu ba ta sake futowa tayo nan ba, sabo da ganin da take a kullum tamkar zata gansa ne idan ta futon, hakan yasa gaba d'aya ma ta dena bin hanyar, sai yau data tawo domin zuwa kan kujerar nan tata.

Sanye take da irin shigar ta-ta koda yaushe, wato doguwar riga mai jan k'asa, amma ta yau d'in ta kasance blue ce mai azabar kyau.
Yayin da gashin kanta kuma ya kasance a bud'e an tufke sa wuri d'aya, sai wasu irin takalman fata da suke sanye a k'afafun ta blue suma, duk da dai ba ganin su ake iya yi sosai bama, sabo da yadda rigar nan ke bin k'asa, a hakan ma wai dan wa'yan nan 'yammatan bayin na rik'e da wani sashi na daga jikin ta ne.

Zane fuskar ta take da tambarin masarautar tasu yau da akayi sa da k'walli, sai dai kuma ba k'aramun kyau yayi mata ba.

Ko kad'an babu alamun rahama tattare a fuskar ta-ta tamkar ko da yaushe.

Cikin takun ta na tsantsar nuna isa da izza tare da tak'ama ta cigaba da tafiya kanta d'age a sama.
Yayin da dakarun nan nata na ko da yaushe kuma suke biye da ita a bayan ta.

Acan b'angaren Bir kuma ta gefen Bishiyar nan yake ganin su, hakan ne yasa yana ganin sun kusa k'arasowa wurin kawai ya futo kai tsaye yana mai dumfaro inda suke.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir ba zato ba tsammani taga bayyanar mutum a gaban ta kawai yana tafiya, domin kuwa kwata-kwata bata lura da lokacin da ya tawo ba sai dai kawai ganin sa da tayi.

Cak ta tsaya a wurin da take zuciyar ta na wani irin bugu da matuk'ar k'arfi, tamkar yadda ta Bir take yi shima, sabo da idanuwan su da ya sark'e cikin na juna a lokacin da ta kai duban ta gare sa.

Wani irin kallon-kallo suka fara aikawa junan su da shi, zuciyoyin su na wani irin gudu a d'ari-d'ari, ta yadda har suke jin tamkar sa fasa k'irji nansu su futo waje.
Chapter 70 · 0% Book details