← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 79

Sashe 37

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gadan-gadan ya ƙarasa zuwa wurin da take yana maj sa hannu da niyyar funcikar Ɗan, amma sai tayi sauri ta ƙara ruƙun-ƙume sa acikin jikin ta, tana mai fashewa da wani irin gigitaccen kuka mai ban tausayi, take kuwa shima jaririn ya tsanyare da kuka da matuƙar ƙarfi, sabo da zafin matsar da yaji, wacce uwar tasa tayi masa gudun kar aƙawace mata shi.

Tas! Tatas!! Tasss!!! Wasu irin ƙarar marika suka tashi a wurin da matuƙar ƙarfi, waƴan da suka sake sanya mutanen cikin jirgin ruɗewa da firgicewa, suna masu toshe bakunan su da hannu.

Badakaran nan ne ya ɗauke matar da wasu gigitattun marika, sabo da yadda yaga yana miƙa hannu zai karɓi Ɗan tana kuma sake ruƙun-ƙume sa, tukun daga bisani ya ɗago tsaye yana mai funciko wata doguwar takobi daga ƙugun sa yayi kan matar da ita.

Wata irin gigitattar ƙara matar ta saki, tana mai rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi.

Funcikar Ɗan ya sakeyi da matuƙar ƙarfi, yana mai mayar da takobin cikin jikin sa ba tare da ya kaita jikin ta ba, sabo da yadda yaga riƙon da tayiwa yaron yayi sakwa-sakwa ta dalilin ihun da ta saki, tukun ya juya jinjirin riƙe a hannun sa, da yake tsala uban kuka yana mai ɗaga kafafuwan sa sama yayi gaba.

Dasauri matar nan ta miƙe tsaye tana mai bin bayan sa cikin tsantsar ɗimaucewa.

Ƙafar sa ɗaya ya ɗaga yana mai harbin ta da ita ta baya, hakan yasa ta tafi taga taga tana mai kifewa a ƙasa kanta ya sake dukan wani icce, tayadda har sai da ya fashe jini ya futo, amna a haka ta sake miƙewa tana mai sakin kuka
Yayin da shi kuma wannan badakaran ya cigaba da tafiyar sa babu ko É—igon imani tattare da shi, yana mai fucewa daga cikin jirgin.

Kai tsaye ya doshi kan shimfiÉ—ar nan mai É—auke da huta a kanta.

Miƙawa Boka mai hutar kasko jinjirin dake tsala uban kuka yayi, yayin da daga can bakin jirgin kuma wani badakaran ya tare wannan matar uwar jinjirin, da take shirin futowa yana mai sanyata ta duƙushe akan guiwoyin ta, tana hangen Ɗan nata daga nesa.

Matsawa Sarki Barbaru yayi zuwa gaban kaskon huta shima, yayin da Boka mai hutar kasko kuma ya tashi daga hurin da yake zaune, hannun sa riƙe da jinjirin, yana mai matsawa gaban kaskon nan, tukun ya durƙusa yana mai kwantar da shi a kusa da kaskon.

Hutsil-hutsil yaron ya farayi yana mai cigaba da tsanyarewa da kuka, sai dai kuma har bayan shuɗewar daƙiƙa goma ko kaɗan ƙafarsa bata taɓa jikin kaskon nan ba, balle harya tuntsirar da shi, hakan da suka ganine yasan ya Sarki Barbaru buɗe baki cikin muryar sa mai matuƙar amo da firgitarwa, yana mai faɗin. "Bashi bane wannan ma, dan haka matso ka caka nasa kibiyar shima." Ya ƙarasa maganar da kallon wani badakare da yake tsaye agefe.

Wata irin ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, sabo da jin abun da Sarki Barbaru ya faɗa da tayi, ga kuma ganin da tayi badakaran yayi wurin jinirin gadan-gadan.

Da sauri wannan badakaran da yake tsaye a gaban ta ya damƙi tsintsiyar hannun ta, sabo da yadda yaga tana shirin fucewa daga cikin jirgin.
Yayin da shi kuma wancan da Sarki Barbaru yayiwa magana ya ƙarasa gaban Jinjirin nan, tukun ya durƙusa ƙasa yana mai sa hannu ya ɗauki kibiyar da take ajiye kusa da kaskon huta, sannan ya ɗago tsaye yana mai ɗaga ta sama, tukun yayi ƙasa da ita yana mai cakata a dai -dai ƙawon zuciyar jaririn!

Wata irin gigitattar ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, tana mai zubewa a ƙasa sumamma, sabo da yadda taga an yiwa jinjirin nata da bai san hawa ba bare sauka, wanda bashi da haƙƙin kowa a kansa kisan gilla akan idon ta.
Yayinda Aishatu kuma ta saki wani irin salati da matuƙar ƙarfi, wanda ya janyo hankalin duka mutanen wurin, tunda ga kan su Sarki Barbaru har zuwa mutanen cikin jirgin nan da suke tare, tana mai rumtse idanuwan ta tare da yarfa hannun ta, sabo da wani irin mugun murɗawa da taji cikin ta yayi, ga kuma bayan ta daya riƙe gam, banda jujjuya kai tare da sakin nishi babu abun da take iyayi.
Gumi ke yanko mata ta kowace kafar gashi dake jikin ta, sabo da yadda ciwon naƙuda ya taso mata gadan-gadan, a kuma lokaci ɗaya.

Da sauri Ishaƙ ya dafa bayan ta yana mai girgiza kai, hankalin sa a bala'in tashe, kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka ɓalle daga cikin idanuwansa suna tsiyaya akan kuncin sa.
Yayin da Sarki Barbaru kuma ya buÉ—e baki cikin amo yana mai faÉ—in.

"Ga wata nan zata haihu yanzu, dan haka ku shiga ciki ku anso mana sauran yaran kafun muga wanda zaizo natan."
Ya ƙarasa maganar da kallon dakarun nan nasa.
Take kuwa suka tafi zuwa cikin jirgin, domin su anso sauran yaran da suke a ciki, yayin da ita kuma Aishatu take cigaba da sakin nishi, hannun ta dafe da ƙasa tayi durƙushe, yayin da ɗayan hannun nata kuma ya kasance dire akan cikin ta da take jin abun cikin na motsawa, yana neman hanyar futa.

Cikin sauri IshaÆ™ ya fara buÉ—e jakar kayan ta da take ajiye a kusa dasu idanun sa na zubar hawaye, nadamar barin Aishatu tazo gaisuwar mahainfin ta na cika zuciya da ruhin sa.

Zannuwa ya É—auko har kimanin guda huÉ—u.

Ninka guda biyu yayi yana mai shimfiɗa su aƙasa, tukun ya sanya hannu yana mai matso da Aishatu da zuwa yanzu bata fahimtar komai, sabo da tsantsar azabar ciwon da take ji zuwa kan shimfiɗar, sannan ya ware guda biyu yana mai miƙewa tsaye ya fara ƙoƙarin yin dabara wurin ganin yayi mata rumfa da zannuwan, ganin hakan da matan cikin jirgin sukayi ne yasan ya wasu daga cikin su har kimanin mutum huɗu sukayo wurin da suke, gaba ɗayan su hankulan su a tsantsar tashe, yayin da idanuwan su kuma ke tsiyayar da ruwan hawaye yadda kasan an buɗe famfo.

Karɓar zannunwan matan sukayi a hannun Ishaƙ, tukun biyu daga cikin su suka buɗasu suna masu zagaye Aishatu da shi daga tsaye, ya zamto sun mata ɗan ɗaki kenan, yayin da biyu daga ciki su kuma suka shiga cikin dan ɗakin zannuwan, sabo da su taimaka mata.

Acan ɓangaren dakarun nan kuwa, cikin rashin imani suka sake ƙwato wasu yaran har guda biyu a cikin jirgin a hannun iyayen su, suna tsantsar kuka.
ÆŠaya jinjirin duka watan sa biyu aduniya, yayin É—ayan kuma yake da wata ukku aduniya.
Suma ɗin tawowa sukayi da su zuwa kan shimfiɗar nan, tukun aka ajiye na farko a gaban kaskon huta, amma sai dai shima har bayan wucewar daƙiƙa goma da ajiye sa bai bige kaskon nan ba, hakan ne yasa Sarki Barbaru ya sanya aka luma masa kibiyar nan a ƙawon zuciya shima.

Wata irin gigitattar ƙara uwar jinjirin ta saki, tana mai miƙewa a zabure zata afka cikin ruwa, amma sai wasu maza guda biyu da suke a gafen wurin da take sukayi saurin kamata suna masu kaita ƙasa, yayin da ihun da ta saki kuma ya daki kunnuwan Aishatu da matuƙar ƙaraji, wanda ya ƙara sanya cikin ta ya ƙara wata irin murɗawa fiye da baya sosai.
Cikin tsantsar zafin ciwon da takeji ta sanya hannun ta tana mai dan buɗe zanin da ake zagaye ta da shi, tukun ta zura kanta waje tana mai kai idanuwan ta zuwa wurin da su sarki Barbaru suke, wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da wannan badakaran ya sake ɗaga kibiyar nan yana nai cakawa ɗayan jaririn aƙawon zuciya shima, kasancewar bai bige kaskon nan ba shima ɗin.

Wata irin gigitattar ƙara Uwar jinjirin tare da Aishatu suka saki a lokaci guda, tukun daga bisani kuma sai ga kukan jinjiri nan ya biyo baya da matuƙar ƙarfi...!

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa sosai take jin jiki, yayin da hadimar ta Larai kuma ke tsaye akan ta tana ta faman yi mata sannu, tare da sharce mata gumin dake tsats-tsafowa akan goshin ta.

Kiran sallah'r da aka kwaɗa a cikin masallacin masarautar yayi dai-dai da bayannar kukan jinjiri da matuƙar ƙarfi.

"Alhamdulillahi rabil alami." Gimbiya Fulani ta faÉ—a tana mai mayar da numfashi, tare da lumshe idanuwan ta, kasancewar abun da ke cikin nata na faÉ—owa itama mabiyar ta biyo sa.

"Ayiri-yiri-yiririiiiiiiiiiiiii!"

Hadima Larai ta saki wata mahaukaciyar buɗa mai matuƙar sauti a lokacin data kai idanuwan ta kan gaban jinjirin, sabo da yadda idanuwan ta suka mata arba da santalelen jinjiri Ɗa namiji.
Ƙara sakin buɗa tayi da matuƙar sauti, tukun daga bisani ta durƙusa ƙasa tana mai yankewa yaron cibi, sannan ta ɗauke sa tana mai naɗe sa acikin wani lallausan showel, tukun ta juya cikin sauri tana mai kama hanyar waje hannun ta riƙe da yaron.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta matsa daga hurin da take tana mai mayar da numfashi, tare da lumshe idanuwan ta.

Kai tsaye Hadima Harai ta doshi waje hannun ta É—auke da jinjirin, sannan kuma har lokacin bata bar sakin buÉ—ar da take yi ba, bakin ta na furta kalmar.

"Masha Allahu! Masha Allahu!! Masha Allah da zuwan ka duniya ÆŠan albarka!!! Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai mai kowa mai komai.
Yau ranar tamuce mu mutanen gida, domin kuwa ƙaruwar tamuce tazo, ƙaruwa irin wacce aka daɗe ana mararinta da jiran ta.... Haihuwar Ɗa namiji ba kowa ba a wanga gida, haihuwar namiji sai ɗiyar sa'a a wanga gida, zama Uwar Sarki sai Ƴar Sarki Jikar Sarki, sannan kuma Matar Marki."

Hadima Larai take ta faɗa da tsantsar ƙarfi tana mai cigaba da tafiya tare da sakin buɗa.
Yayin da ɗaukacin jama'ar dake rayuwa a ɓangaren Gimbiya Fulani kuma suka furfuto daga cikin ɗakunan su da tsantsar gudu, domim kuwa koda basu san meke faruwa ba muryar hadima Larai kawai ta sanar da su.
Chapter 37 · 0% Book details