Sashe 12
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Insha Allahu zama asame sa nan kusa bada jimawa ba kyakkyawar Gimbiya."
Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye daga durƙushen da yake, tukun ya juya yana mai sake bin hanyar da ya biyo yazo wurin.
Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya tana mai sake ɗaukar wata hanyar ba wacce take kan biba, fuksar nan ta ta aɗaure yarce kasan ba ita bace take aikin sheƙa dariya ɗazu ba.
Ba wata doguwar tafiya tayi ba ta ɓulla wani huri mai kama da daji-daji.
Gaban wani kogo dake jikn wata shirgegiyar bishiyar ɗorawa ta ƙarasa tana mai tsugunnawa, kana ta miƙa hannun ta tana mai janyo wani baƙin kasko aciki ta ajesa agefe, tukun ta sake zura hannu ciki, sai gashi ta ƙara janyo wata ƙatuwar gora wacce take cike da wani yellon ruwa itama ta ajeta kusa da kaskon, sake mai da hannun ta tayi ciki, wasu irin layoyi, tsummokarai da iccina ne masu matuƙar yawa ta sake zarowa aciki, kana suma ta ajesu agaban kaskon.
Buɗe gorar ruwan nan tayi tana mai tsiyaya yellon ruwan dake cikin ta acikin baƙin kaskon nan, sannan ta janyo wani tsumma mai matuƙar ƙura tana mai buɗe sa, wasu irin ciyayi -ciyayi tare da wata kalar ƙasa ne suka bayyana aciki, suma ɗibar su tayi ta zuba su acikin kaskon, kana ta ɗauki layun da suke awurin su kuma ta maƙalasu abakin kaskon.
Take ruwan nan ya fara juyawa da matuƙar gudu kalar sa na sauyawa daga yellow zuwa fari-fari.
Miƙewa tayi tsaye bayan ta ɗauki wata laya tare da wani icce ta rumtse su acikin tafin hannun ta, tukun ta rufe idanuwan ta da ƙarfi tana mai fara zaga wurin tare da buɗe baki cikin sauti tana faɗin. "Zaiba! Zaiba!! Zaiba!!!"
Wani irin hautsinawa ruwan dake cikin tukunyar nan ya farayi da matuƙar gudu, cigaba da furucin ta tayi cikin ƙarfi tana zaga kaskon, har lokacin kuma idanuwan ta arufe suke bata buɗe suba.
Wani irin hayaƙi ne baƙiƙƙirin ya fara futa daga cikin tukunyar yana mai tashi sama.
Dasauri ta buÉ—e idanuwan ta akan tukunyar tana mai zaro su waje tare da ja baya.
"Inaaa!!! Wallahi kai ɗin nawa ne ni kaɗai, babu wata mace da zata kasance mallakin ka aduka duniya bayan ni! Shin har sai zuwa wane lokaci ne zan gano inda kake ne Giɗaɗo am?" Ta faɗa da ƙaraji tana mai girgiza kanta, idanuwan ta akan wannan kaskon da yake futar da hayaƙi, tukun daga bisani ta ɗora da cewar. "Akan me zanga baƙin hayaƙi bayan farin ruwa nake buƙatar gani wanda zai hasko mun hanyar da zanbi zuwa gare ka? Akan me duk lokcin da naso gano inda kake abun baya yiwuwa? Shin me yasa kake bani wahala bayan babu wani abu da na taɓa so ya zamto mai wahala agare ni!" Ta ƙarasa faɗe da ƙarfi tana mai matsawa kusa da kasokon ruwan nan ta tuntsirar da shi aƙasa ya kife.
Sakin layar dake dunƙule acikin tafin hannun ta tayi hawaye na ɓallewa daga cikin idanuwan ta, tukun ta juya tana mai yin taku biyu daga inda take zuwa gaba, kana ta tsaya cak tana mai buɗe baki cikin kakkausar murya tace. "Ko ita ɗin wace ce, ko waye ubanta, koda ko tare kukazo gidan duniya da ita, muddin ya tabbata kuna soyayya dole ne kabarta kasoni ni kaɗai Giɗaɗo am!
Ni Gimbiya Haddiyal Ɗiyar Lamiɗon Masarautar Fulɗe nayi rantsuwa da mahallicin Shanu da Mutane sai ka zamto nawa, bazan taɓa gazawa ba wurin neman ka kamar yacce soyayyar ka baza ta taɓa yin gibi acikin zuciya ta ba, tabbas idan har tsafi gaskiya ne to ka sani zanyi amfani da wanda ya kasance acikin jiki na tun zuwa na gidan duniya domin na gano ka, haɗuwar bazata taɓa tsayawa cikin mafarki ba, tunda har na tabbatar da kai ɗin ba Aljan bane mutum ne kamar kowa." Ta ƙarasahe maganar muryar ta na rawa kamar ba itace ta fara ta ba akausashe, tukun daga bisani ta sake juyowa tana mai yowa wurin kaskon nan.
"Ina sonka Giɗaɗo am, kai ɗin ka zamto wani tsagi na daga tsagin zuciyar Haddiyal." Ta faɗa cikin sanyi hawaye na sauka daga cikin idanuwan ta, tukun ta durƙusa gaban kayan tsafin ta tafara haɗasu wuri ɗaya.
Sai da ta haɗe kansu tsaf, sannan ta mayar da su cikin kogon nan, kana ta tashi jiki atsan-tsar saɓule tana mai dosar hanyar da zata sadata da gidan sarautar nasu.
Duk inda ta gifta sai bayi sun zube suna kwasar gaisuwa, amma ko kallo basu isheta ba balle ta amsa, ahaka har ta ƙarasa cikin tamfatsetsen falon su kanta durƙushe aƙasa, ba tare da ta kalli kowa dake cikin falon ba ta doshi hanyar ɗakin ta kai tsaye.
"Haddiyal!"
Cak ta tsaya adai dai bakin ƙofar ɗakin nata da take shirin shiga sabo da muryar mahaifiyar ta data daki dodon kunnuwan ta, lokaci ɗaya taji wata irin faɗuwar gaba ta ziyar ceta, sabo da mahaifiyar tata bata fiye kiran ta da Haddiyal ba, sai idan zata faɗa mata wani abu mai muhimmanci ko kuma zata mata faɗa.
Cikin sanyi ta juyo tana mai kai duban ta inda tajiyo sautin muryar mahaifiyar tata.
Zaune take akan kujera yanzu hannun ta riƙe sa tufa tana ci, yayin da innahuro kuma take zaune agafen ta ta ɗora kanta akan kafaɗar mahaifiyar tasu tana cin inibi ita kuma.
"Gani Dadde na." Gimibiya Haddiyal ta faɗa adai dai lokacin da ta ƙaraso inda suke bayan ta samu wuri ta zauna itama.
"Me ya sameki ne naga idanuwan ki sunyi ja?" Mahaifiyar tata ta watso mata tambaya tana mai kafeta da idanu.
Uhm! "Dama.. Damm.. Fuffiken shale ne ya taɓan ido." Ta faɗa cikin in-ina tana mai sake sunnar da kai ƙasa.
Shiru mahaifiyar tata tayi ba tare da tace mata komai ba, sai idanu kawai da tacigaba da bin ta dasu.
Ta fannin haddiyal kuwa ta futar da tsamannin Dadden nata zata ƙara magana, sai daga bisani kuma ta tsunkayo sautin ta asama da yayi matauƙar hautsina zuciya da ƙwaƙwalwar ta tana mai faɗin. "Aɗazu bayan tafiyar ki Mahaifinki Lamiɗo ya shigo, yace in sanar miki atanadi madara da kayan itatuwa, gobe zakiyi baƙo ɗan Lamiɗon Masarautar Yamma zaizo batun auren ku, dan haka sai kitashi kije ki fara gyarawa!"
***
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA*
Sai da suka tabbatar da tabar duka yankin, tukun suka dumfaro inda suka hangi Bir kwance cikin ƙasa da gudun su.
🎠*BAƘAR MASARAUTA* ðŸŽ
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
ðŸðŸŽ ðŸ„ðŸ¹
_*NA*_
UMAR FARUQ*D*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*PAGE 05*
Durƙusawa sukayi ƙasa suna masu kamo sa, yayin da shi kuma yake ta faman juya kai har lokacin yana mai taune leɓen sa na ƙasa.
Ɗagosa sama sukayi ya zamto yana jingine ajikin su, tukun suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar kudu tare da jera masa sannu.
Sanye suke suma da fararen gajerun wandina na yadi kamar yacce shi É—in ma ya kasance babu riga ajikin su, sai uban zanen tambarin masarautar tasu da ya kasance manne akan fatar su tako ina.
"Sannu ɗan uwa Bir, dama sabo da gudun shiga irin wannan matsalar ya sanya kullum nake ce maka kadena shigewa Gimbiya, amma sai dai kai ɗin ko kaɗan bakaji, to yanzu wa gari ya waya kenan, dubeka kaga yarce ka koma, gashi kuma kariga da kasan jibi -jibin nan ne ranar zagayowar bikin godiya ga Abun Bauta Gargabilu, kuma kasan muddin kana cikin BAƘAR MASARAUTA babu ruwan wani da larurar ka ko wace kalace ,sai ka ɗauki iccina har dai bikin godiya ya zagayo."
Ɗaya daga cikin matsan da suke dafe da Bir waƴan da zasu iya yin sa'anni a shekaru ya faɗa suna masu cigaba da dosar inda wasu ɗakuna da aka haɗasu da iccina suke jera da matuƙar yawa.
"Ai dama ka dena wahalar da bakin ka É—an uwa Mauzum, domin kuwa duk abun da zakace akan Bir ya dena shish-shigewa Gimbiya kayi abanza ne, dan ko ba saurara yake ba balle harya dauka ma, shiyasa ni yanzu tsakani na dashi kawai idone babu ruwa na, sabo da karma ya gogamun laifin da ban janyo ba." Cewar É—ayan yana mai kallon É—an uwan nasa.
Yayin da shi kuma Bir ya lumshe dara daran idanuwan sa yana mai yin shiru ba tare da ya tanka musu ba, duk da dai yana jinsu sai aikin kawai taunar leɓan ƙasan bakin sa da yake yi da haƙoran sa ahankali, ahaka har suka ƙarasa wurin da ɗakunan itacen nan suke ajere re-ras ta kowanne ɓangare.
Sai da suka shigar dashi har cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki dako daɓe babu akasan sa, sai ƙasa da kuma shimfiɗun tsummokara waƴan da suke kwanciya akan su, tukun suka ajesa. Miƙewa tsaye sukai suna kallon sa, yayin da shi kuma yake akwance rigin-gine idanuwan sa na kallon iccinan da aka jera asama wurin rufin ɗakin.
"To Bir bara mu muje musanarwa Iya cewar kadawo, domin kuwa tun lokacin da Gimbiya ta rufeka hankalin ta yake atashe ko abinci bata ƙara ciba." Suka faɗa suna masu juyawa suka fuce daga cikin ɗakin.
Ahankali Bir ya miƙe daga kwancen da yake yana mai taune laɓen sa tare da yamutsa fuska, alamun har yanzu jikin nasa nayi masa ciwo kenan.
Waige waige ya farayi acikin ɗakin nasu har idanuwan sa suka sauka akan wasu curin kaya da suke ƙulle wuri ɗaya.
Jan jiki ya farayi har ya ƙarasa inda kayan suke, tukun ya sanya hannu yana mai bubbuɗasu, kana ya janyo wata ƙatuwar kwari da gwafa daga cikin kayan yana mai riƙe ta ya jujjuya ahannun sa yana kallon ta, tukun ya miƙe tsaye ahankali yana mai dafa katakwayen da suka kasance bangon ɗakin, kana ya fara ɗingisa ƙafafuwan sa yana mai dosar hanyar waje.