Sashe 68
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Acan wurin baturiyar na kuwa sosai taciyo uwar kwalliya cikin shigar wasu irin ƴan iskan kaya da suke kusan ɗaya da babu a jikin ta, danniyar ta na zuwa wurin dan ta bawa Asad haƙuri akan abun da tayi masa ko Allah zai sa ya haƙuran, duk da dai tasan hakan abu ne mai tsananin wuya, amma sai kuma tana doso wurin ta hango wata zaune a gaban sa.
Lokaci ɗaya kuwa taji wani irin baƙin ciki tare da mugun kishi sun zo sun tokare mata aƙawon zuciya.
Bata sake jin ranta ya ƙara matuƙar ɓaci ba sai da ta ƙara kusanto wurin da ta fahimci wacce take zaune agun, wato wannan yarinyar ta jiya da tazo kanta tayi mata tsaki tai gaba, hakan yasa ta fahimtar cewar sonsa take itama, shi yasa jiya har tayi mata tsaki ta huce.
Hakan kuwa shi yayi matuƙar harzuƙata, har bata san lokacin da ta durƙusa ƙasa ba tana mai zame takalmin da yake sanye aƙafar ta wanda ya kasance mai matuƙar tsini da tsayi, tana mai riƙo sa a hannunta ta nufo wurin Billy gadan-gadan.
Ita kuwa Billy ko kaÉ—an bata san da tawowar ta ba, domin kuwa hankalin ta gaba É—aya yana kan Asad ne da take jiran taji yace wani abu.
Da wani irin ƙarfi baturiyar nan ta ɗaga tsinin takalmin ta dai-dai lokacin da ta ƙaraso gaban Billy tana mai saita goshin ta da shi, tare da faɗin.
"Who the h..."
Maganar tace ta tsaya, sabo da yadda taga Yarima Asad yayi wani rin miƙewa tsaye a matuƙar zabure, yayinda Billy kuma ta juya da matuƙar sauri tana mai kai idanuwanta ɓangaren da tajiyo muryar nan, wanda hakan kuma yayi dai-dai da isowar tsinin takalmin gab da goshin ta.
Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwanta jikin ta na matuƙar rawa, sabo da tabbatarwar da ta riga tayi na an riga da anji mata ciwo.
Amma ba zato ba tsammani kawai sai ji tayi anyi wani irin funcikar ta, tana mai kifawa kan lallausan wani abun da bata fahimci ko menene shi É—in ba.
Hakan yasa ta fara buÉ—e idanuwanta a hankali, tana mai sauke ajiyar zuciya, har ta buÉ—e idanuwan nata duka akan faffaÉ—an Æ™irjin sa mai matuÆ™ar taushi, da yayi mata rumfa da hannuwansa duka biyu................âœ
_MUN KUSA KAMMALA BOOK 1, KAFIN MU SHIGA BOOK 2 KUMA IDAN MUN DAWO DAGA HUTUN SATI ƊAYA._😅
*BY*
UMAR FARUQ*D*
*BAK'AR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 27*
Wato dai ya rungume ta ƙam-ƙam a cikin ƙirjin sa.
Wani irin farin ciki mara misaltuwa Billy ta tsinci kanta acikin sa, hakan ne yasa ta sake maƙal-ƙale sa gam-gam, tana mai sake kwantar da kanta akan ƙirjin sa, yayin da daddaɗan ƙamshin turaren sa ke dukan hancinta yana ratsa har tsakar ƙwaƙwalwar ta.
Shi kuwa Yarima Asad tsaye yake a wuri ɗaya rungume da ita a ƙirjin sa, yana mai aikawa wannan baturiyar wani matsiyacin kallo mai kaɗa hanjin ciki.
Ita kuwa wannan baturiyar cikin tsantsar baƙin ciki da takaicin yadda taga Asad ya rungume Billy a gaban ta fashe da wani irin kuka, kafin daga bisani kuma ta kaiwa mug ɗin tea ɗin da yake ajiye akan table damƙa, tana mai sake saita goshi Billy ta jefa mata shi.
Amma sai Asad ya sake janye Billy daga wurin da matuƙar sauri, kana ya fara tinanin abun da zaiyi wanda zai ƙara ƙona mata rai fiye da yadda take yanzu, domin ta gane cewar shi ɗin muddin ya riga ya bar abu to fa ya barsa kenan har abadan abada, domin kuwa yana faɗa babu wata mace da ta isa ta ɓata masa rai a duniya, ballan tana kuma har ya rarrashe ta.
A wani irin haukace baturiyar nan tayi kansu gadan-gadan, bayan ta saki wata irin ƙara.
Hakan da Yarima Asad ya gani ne ya sanya sa yin sauri ya suri Billy gaba ɗayan ta a cikin hannunsa, yana mai yi mata ɗaukar jarirai, ba dan komai ba kuma yayi hakan, sai dan kawai ya ƙara harzuƙa zuciyar ta.
Yayinda ita kuma Billy tayi wani irin maƙal-ƙale sa, tana mai sa hannuwan ta duka biyu ta saƙalo wuyan sa da su.
Kana tana wani irin sakin kukan ƙaryar da take ƙwaƙulo sa, tana nuna cewar a tsorace take sosai.
Yayin da azahirin gaskiya kuma wani irin farin ciki mara misaltuwa ya lulluɓe zuciya da ruhinta, domin kuwa tana ganin tamkar ta riga da ta gama mallakar Asad har abada, hakan ne yasa taji ina ma ace tare da Zee suka zo wurin nan, domin ta ganewa idanuwanta, dan tasan yanzu ko taje ta bata labarin abun da ya faru ba lallaine ta yadda ba.
Tabbas yau ɗin ta ƙara tabbatar da cewa ita ɗin mai sa'a ce a duniya, kana kuma ta ƙara yadda da cewar babu wani abu da zai taɓa yi mata wuyar samu muddin taso samunsa a duniya.
A ɓangaren Asad kuwa ganin da yayi wannan baturiyar ta sake yowa kansu ne, yasa sa wurga mata wani irin matsiyacin kallo daga wurin da yake.
Ƙam ta cake a wuri ɗaya kuwa jikin ta na matuƙar karkarwa, domin kuwa ba ƙaramun firgita tayi ba da irin kallon da yake watso mata.
Yayin da shi kuma ya juya yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa yayi gaba, hannuwan sa rumgume da billy tamkar jaririya.
Wani irin kuka baturiyar nan ta ƙara fashewa da shi, tana mai ɗora hannuwan ta duka biyu aka tare da durƙushewa a ƙasa.
Ita kuwa Billy cikin tsantsar farin cikin da ya lulluɓe ta lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan fuskar baturiyar nan, bayan ta zuro kanta ta saman kafaɗar Asad.
Kana ta zaro harshen ta tana mai yiwa baturiyar nan da itama take kallon ta gwalo, sannan ta sake mayar da kanta cikin ƙirjin Asad, tana mai lumshe idanuwan ta-ta cigaba da shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren sa, da yake saukar mata da wata irin nustuwa da kasala a cikin jiki.
Wani irin gigitaccen kuka baturiyar nan ta saki tana mai jin tsanar Billy na sake mamaye zuciya da ruhin ta, ta yadda har take jin zata iya kashe ta muddin zata same ta a hannu.
Shi kuwa Yarima Asad direct ya doshi room ɗin sa rungume da Billy a ƙirjin sa.
Haka nan shima yaji yarinyar ta É—an kwanta masa arai, ta yadda har yake ganin zai iya dinga kulata, sai dai kuma ba wai yaji yana son ta bane a zuciya, asalima har yau shi baici karo da wadda takai yaso ta ba a cikin Æ´ammata.
Hannun sa ɗaya ya sanya a cikin aljihun wandon sa yana mai zaro key'n ɗakin, sannan ya zura sa yana mai buɗe sa, kana ya murɗa handle ɗin ƙofar yana mai ƙara tura ta da ƙafar sa, sannan ya danna kansa zuwa cikin ɗakin.
Da sauri Billy ta lushe idanuwan ta, sabo da daddaɗan ƙamshin turaren da ya daki hancin ta.
Tabbas komai nashi na daban ne, tamkar yadda shi kansa ya kasance na daban, haka kuma komai nashi yayi, kamar yadda shima yayi É—ari bisa É—ari.
Ta faÉ—a a cikin ranta tana mai bin kyakkyawan falon nasa da idanuwan ta daga saman hannun san da take.
Shi kuwa Yarima Asad yana ƙarasawa cikin ɗakin ya dire Billy a ƙasa ba tare da yace mata komai ba, asalima ko kallon fuskar ta baiyi ba, sai hucewa da yayi zuwa gaban ɗan mini fridge ɗin da yake acikin ɗakin nasa yana mai buɗe sa, kana ya zaro robar ruwa ɗaya aciki mai matuƙar sanyi, yana mai dawowa ya zauna akan kujerar da take kusanci da shi.
Sannan ya buɗe murfin jarkar yana mai kafa bakin ta akan ɗan ƙaramin bakin sa ya fara shan sa.
Bashi ya É—auke kai daga kan jarkar ba har sai da yasha kimanin rabin ta, tukun ya ajiye ta akan É—an mini center table É—in da yake agafen sa yana mai lumshe idanuwan sa a hankali, tare da sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya akai-akai.
Ita kuwa Billy jin da tayi ya sauke ta anan É—in ne, ba tare da kuma ya tanka mata bane ya sanya ta samun wuri akan kujerar da take akusa da ita, wacce ta kasance tana facing É—in wacce Asad yake akai ta zauna.
Kana ta durƙusar da kanta ƙasa tana mai yin wasa da ƴan yatsun hannun ta.
Kafin daga bisani kuma ta buÉ—e baki a hankali tana mai faÉ—in.
"I'm very sorry please."
Sannan tayi shiru tana mai cigaba da wasa da Æ´an yatsun hannun ta.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya buɗe idanuwan sa a hankali yana mai ɗan ɗaga kai ya kalle ta, kana ya ɗan taɓe baki yana mai mayar da idanuwan sa kan wayar sa.
Kafin daga bisani kuma a lokacin da Billy ta fara futar da tsammanin zaice wani abu taji sautin daddaÉ—ar muryar sa yana mai faÉ—in.
"Sorry for what?"
Duk da har lokacin bai kalle ta ba.
Jin hakan da Billy tayi ne ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali, tukun daga bisani ta buÉ—e su tana mai É—ago kanta ta kalle sa, sannan ta furta cewar.
"Da abun da naja wata tayi maka yanzu mana, tun da nasan da banzo wurin ba da ba zata yi hakan ba."
Tayi maganar cikin wata irin murya, wacce take tattare da shagwaɓa a cikin ta.
A hankali ya ɗan ɗago idanuwansa yana mai kaisu kan fuskar ta tare da ɗan taɓe bakin sa, tukun daga bisani kuma ya basar yana mai yin tamkar bai kalle tan ba, domin kuwa azahirin gaskiya ko ita bata san ya kalle tan ba.
Kafin daga bisani kuma ya furta.
"Uhm!"
"Please! Please!!"
Billy ta sake faÉ—a tana mai sake marairaicewa, tare da haÉ—e tafukan hannayen ta wuri É—aya.
"Is ok."
Ya faɗa a gajarce, kana kuma a saman lips ɗin sa, yana mai miƙewa tsaye da niyyar shigewa cikin bedroom ɗin sa.