← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 79

Sashe 57

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fannin kaka kuwa yanzu ta koma masifaffiya lamba É—aya, domin kuwa a kullum sai tayi faÉ—a da jikokan nata musamman ma Sheikh Ahmad, kuma ba komai ne yake haÉ—asu ba sai tsohuwar da yaran suke ce mata, yayin da ita kuma ta tsani a kirata da tsohuwa, duk da ita da kanta tasan tsufan yazo mata.

*DUBAI*

Tun bayan komawar Asad da Al'amin ƙasar Dubai gaba ɗaya komai nasu ya sauya, domin kuwa ko ɗaki da aka tashi basu ko wanne guda ɗaya tafkeke aka basa, kamar yadda sauran yaran gidan suka kasance kowa acikin nasa ɗakin.
Yayin da aka zube musu ruwan kuÉ—i kuma suke duk yadda ransu yake so da su, ba tare da kwaba ko hantara ba.
Kwanan su biyu kacal da zuwa Alhaji abubakar ya É—auke su ya kai su wata makarantar miliyoyin kuÉ—i da kansa.
Inda anan ɗin kuma suka haɗu da yaran manya irin su, kama daga kan larabawa har zuwa baƙar fata irin su.

Satin su ɗaya da fara zuwa sukayi wasu abokai a cikin class ɗin nasu ƴaƴan larabawa, irin waƴan da babu kwaɓa tattare da su ko kaɗan, duk da kasancewar su musulmai kuwa, wato Suhaib da Safuwan.

Akullum abun da suke so shi suke samu acikin gidan, haka kuma babu wani mai kwaɓar su da sunyi abun da bai kamata ba, kamar yadda sauran yaran gidan suka kasance, kasancewar su Alhaji Abubakar suna irin rayuwar nan ce wacce turawa da wasu daga cikin larabawa sukeyi agidajen su, wato babu kwaɓa kowa yayi harkar gaban sa.
Wannan saken da su Yarima Asad suka samu shine ya sanya akullum suke abun da ransu yake so, ga yawon bala'i daga yau suje wancan park É—in gobe kuma sai su tafi wancan joint É—in, ta hanyar abokan su guda biyu da suke biye musu amotacin gidan su su tafi.

A yanzu haka daga Yarima Asad har Al'amin ko wanne yana da motar sa ta hawa, mai tsananin kyau da tsada da Alhaji Abubakar ya mallka musu su alokaci guda, tare da É—an sa mai suna Huzaifah, wanda yake sa'an su shima.

Zaune suke akan wasu haÉ—aÉ—É—un kujerun silver, masu azabar kyau da suke a cikin wani haÉ—aÉ—É—en joint su duka biyar É—in.
Wato Yarima Asad, Al'amin, Huzaifah, Suhaib, da kuma Safwan.
Yayin da ga gaban kujerun kuma wani irin tafkeken swimming pool yake.

Sosai wurin yake da bala'in kyau da girma, domin kuwa tsayawa faɗin yadda tsaruwa wurin yake kawai ɓata lokaci ne.
Ƴammata ne da Samari suke ta giftawa ta ko ina, ko wanne da kalar shigar da take sanye a jikin sa.
Yayin da daga cikin swimming pool ɗin nan kuma wasu fararen Ƴammata masu matuƙar kyau suka kasance acikin sa, daga su sai ɗan guntun wando tare da brezia ajikin su, yayin da wasu daga cikin su kuma ya zamto pant ne ajikin nasu ma ba gajeren wando ba.
Kusan dukan su tare suke da samarin su acikin ruwan, suna abun da ransu yake so.

Yayin da gang ɗin su Asad kuma da dukan su ba zasu haure shekara goma shabiyar ba, suka kasance zaune akan waƴannan haɗaɗɗun kejerun da suka yiwa swimming fool ɗin ƙawanya suna musu hira.
Shi kuwa Asad kansa durƙushe yake aƙasa, idanuwan sa akan ƴar wayar sa da aka siya musu ita kwanan-nan, yana aikin latsa ta.

Wasu irin haɗaɗɗun Ƴammata ne da suke sanye da ƙananan kaya, da suka futar da siffar jikin su tas su biyu suka zo wuce ta gaban kujerun da su Asad suke zaune akai cikin tsantsar yauki.
Take kuwa a wurin idanuwan su gaba ɗaya suka koma kan Ƴammatan nan, banda Asad kawai da kansa yake durƙushe aƙasa yana aikin latsar wayar sa.

"Wow!"
Safuwan ya faɗa yana mai janye idanuwan sa daga kan Ƴammatan nan ya juya ɓarin da Asad yake.
Kana ya buɗe baki cikin zaƙuwa yana mai faɗin.
"Hay Prince! Please look at that fine girls."
Ya ƙarasa maganar yana mai taɓo Asad ɗin, tukun ya juya yana mai mayar da idanuwan sa kan Ƴammatan nan da suke cigaba da tafiya, kamar yadda su Al'amin ma duk suke kallon sa.
Yayin da Asad kuma ya janye idanuwan sa daga kan wayar da yake aikin latsawa, tukun ya fara É—ago kansa ahankali yana mai kai idanuwan sa zuwa wurin da Safwan ya nuna masa.

Kallo ɗaya yayiwa Ƴammatan ya janye idanuwan sa daga wurin, yana mai mayar da su kan su Safwan gaba ɗayan su.
Kana daga bisani ya buÉ—e baki cikin muryar sa, wadda yake magana da ita tamkar an masa dole, yana mai faÉ—in.
"Haba dai guys, ku yanzu dan Allah ina abun kallo yake ajikin waÆ´an nan da duk kukabi kuka zuba musu idanuwa haka, salon kawai ku zubar mana da mutunci."
Ya ƙarasa maganar yana mai taɓe baki, kana ya mayar da idanuwan sa kan wayar sa.
Da sauri gaba ɗayan su suka zuba masa idanuwa baki a sake, sabo da jin furucin sa da sukayi akan Ƴammatan da duk kyawun mutum yayi kaɗan ya kira su da munana, tukun daga bisani Huzaifah ya buɗe baki cikin tsantsar mamakin halin Asad yana mai faɗin.
"Haba guy, anya kuwa kagan su sosai, da har zakace basu kai a kalle su ba."

Sake É—ago kai Asad yayi yana mai zuba mayatattun idanuwan su akan su, kamar yadda suma É—in suke kallon sa, kana daga bisani ya janye su ahankali daga kansu yana mai mayar da su kan hanyar da matan nan suke tafiya, tukun ya sake É—auke idanuwan sa daga wurin su, yana mai sake watsa su akan abokan nasa, sannan ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in.
"Uhm! Ku kalle su da kyau guys, both of them are bicths fa."
Ya ƙarasa maganar yana mai juyar da kai gefe ya tofar da yawu, tukun ya sake mayar da idanuwan sa kan wayar sa.
Yayin da Al'amin kuma ya buÉ—e baki cikin sauri yana mai faÉ—in.
"Kai Asad, wallahi koda suke bitch ƙaryar mutum yace dai basuyi ba, kuma-ma mu dai sun birge mu."

Da sauri Asad ya ɗago kansa daga kan wayar da take ahannun sa, sabo da jin furucin da Al'amin yayi yana mai watsa masa wani matsiyacin kallo, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin kausassar murya, yana mai faɗin. "Bu...............✍

*BAK'AR MASARAUTA*

*NA*

UMAR FARUQ*D*

*PAGE 23*

"But you know ko da iskancin zanyi nafi ƙarfin na kula bitch ko, ƙazama sauran wani, tirr Allah ya kiyaye."
Ya ƙarasa maganar yana mai sake jifan su da wani ɗan iskan kallo, tukun daga bisani ya miƙe tsaye yana mai ɗaukar key'n motar sa ya dumfari parking space.
Binsa sukayi da idanuwa gaba É—ayan su ba tare da wani ya iya furta komai ba.
Yayin da shi kuma ya shige cikin motar sa yana mai bata huta yayi gaba, ko inda suke bai ƙara kallowa ba.

"A gaskiya Prince É—an iskan gaye ne, ku duba fah ku gani tsabar rainin hankali muzo wuri tare, amma ya tashi yayi tafiyar sa shi kaÉ—ai."
Cewar Suhaib yana mai kallon su Al'amin.
Yayin da shi kuma Huzaifa ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in.
"KaÉ—an daga cikin rashin mutuncin Asad kenan, kuma fa wai shi fa nan yana nufin yaji ne haushi an haÉ—a sa da bitch, bayan kuma akullum su É—in yake kallo yana jin daÉ—i."

"Kai guys wallahi ba gida Asad ya tafi ba yanzu, ko kuwa kun manta da yaune birthday É—in Taslim."
Al'amin ya faÉ—a yana mai kallon abokan nasu, fuskar sa É—auke da murmushi.
Yayin da Safuwan kuma ya buÉ—e baki cikin tsantsar mamaki yana mai faÉ—in.
"Amma gaskiya kuwa idan haka ne Prince ya raina mana hankali, shegen kullum yay ta nunawa baya son ta, yana faÉ—in Allah ya kiyaye yaso wata yarinya a cikin class, to yanzu uban mene zai kaisa wurin ta."

"Hhhhhh! Lallai ne guy's, wato wai ku haryau baku gane halayyar Prince bane ba ko, to bari kuji in faÉ—a muku, shi fa ya yadda aso-sa, amma shi É—in ne dai bazai ce yana so ba, sabo da yana ganin hakanin tamkar zubar da mutuncin sa ne, sannan kuma ya yadda da yayi abota da yarinya, muddin ta kasance kyakkyawa kuma mai tsafta, kana Æ´ar gayu, dan haka Taslim ma ita take son sa bashi yake sonta ba."
Huzaifah ya faÉ—a yana murmushi.

"To kuma uban mene zai kasa wurin taron ta idan haka ne?" Cewar Suhaib yana kallon huzaifah.

"Haba dai guy, ya keke irin wannan batun ne tamkar wani villager, kai da kanka kasani ko ba soyayya ai zai rage zafi a wurin."
Safuwan ya faÉ—a yana mai É—an kashe masa ido É—aya.

Gaba É—ayan su yara ne É—anyu shakaf, amma sai dai kuma idanuwan su sun riga da sun gama buÉ—ewa da iskanci, ta yadda har suke yiwa kansu kallon cikakkun samari.
Ayanzu haka suna ss 1 ne anan makarantar su wacce sukeyi, yayin da Alhaji Abubakar kuma yayi musu Al'ƙawarin kaisu Oxford University Ingla suyi degree ɗin su acan.

"Any way, ku tashi kawai mubi bayan É—an iska, domin muga abun da zai ai'kata da idanuwan mu, ta yadda koda yazo yana cika mana baki zamu samu abun faÉ—e."
Al'amin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye.
Kana gaba ɗayan su suma suka miƙe tsayen suna masu tunkarar wurin da suka ajiye motocin su.

*BAYAN SHUÆŠEWAR WASU SHEKARU.*

Abubuwa da yawa sun faru acikin shekarun da suka gabata waÆ´an da baki bazai iya furta adadin yawan su ba.
Yayin da su Asad kuma suka zama cikakkun samari masu kimanin shekaru Ashirin da takwas zuwa da tara aduniya.
Chapter 57 · 0% Book details