← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 79

Sashe 2

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai wurin yayi tsit yarce kasan ba ataɓa hallitar mutum ba, kamar yacce kowane wuri yake kasan cewa aduk lokacin da ta kasan ce ashi, babu sautin da ake ji yana tashi sai na takun ta.
Kallo ɗaya zaka mata ka fahimci ranta amatuƙar ɓace yake, sabo da yarce fuskar ta me ɗauke da zannen tambarin nasarautar su agaban goshin ta take amugun ɗaure, ko kaɗan babu alamun annuri tattare da ita, bare har asa ran samun rahama daga gare ta.

Sun yi tafiya mai ɗan tsayi daga cikin gidan sarautar, tukun suka ɓulla cikin wani ƙaton wuri mai ɗauke da dogayen bishiyu da duwar-warsu zageye dashi.
Kai tsaye ta doshi ƙofar dake kallo su idanuwan ta ƙur akan ta, yayin da suma dakarun nata ke biye da ita har suka ƙarasa bakin jibgegiyar ƙofar dake da matuƙar girma da kauri.

Tsaye tayi cak daga gaban ƙofar ita batayi gaba ba sannan kuma ita batai baya ba, yayin da su kuma ƴammatan nan da suke riƙe da rigar ta sukayi hanzarin sakin rigar, suna masu zube gwiwoyin su tare da durƙusar da kansu ƙasa.

Hannun daman ta tamiƙar tana mai buɗe tafin sa ba tare da tace ƙala ba.

Dasauri ɗaya daga cikin jibga-jibgan mutanen nan da yake daga bayan ta ya juya baya, tukun ya fara tafiya da baya da baya yana mai yin inda take har sai da ya ƙarasa kusa da ita, kana ya zube gwiwoyin sa aƙasa tare da durƙusar da kansa ƙasa, sannan ya zaro wata zureriyar jar takobi ajikin sa yana mai miƙa mata ita, har lokacin kuma bai bari idanuwan sa sun kalli koda fuskar ta ba balle su shiga cikin nata.

Ba tare da ta ɗago ta kalli inda yake ba ta ƙara ware tafin hannun ta, tukun shi kuma wannan ba dakaren ya ɗora mata takobin akan tafin hannun nata, kana tamai da yatsun ta tana mai dunƙule takobin acikin su.

Dasauri badakaran ya ƙara juya mata baya, tukun ya miƙe yana mai cigaba da tafiya da baya da baya har ya koma inda yake, sannan ya ƙara tsayawa cak ya koma tamkar bishiyar da aka dasa.

Rumtse idanuwan ta tayi da ƙarfi, tukun daga bisani ta buɗe su akan ƙofar dake kallon ta, kana ta ɗaga zureriyar jar takobin dake dunƙule atafin hannun ta tana mai nuna ƙofar da ita, tukun ta buɗe bakin ta cikin kakkausar muryar ta mai matuƙar sauti tana mai faɗin. "Gargabiluuuu!"

Take jikin bayin nan mata ya ɗauki rawa yarce kasan mazari, gumi na yanko musu sabo da yarce sautin muryar ta ya daki zuciyar su ba tare da sunyi zato ba, yayin da su kuma jibga jibgan dakarun nan maza suka sake ƙamewa cak a'inda suke yarce kasan icci na.

Ahankali -ahankali murfin ƙofar ya fara buɗewa har ya buɗe duka akan idanuwan ta, tukun daga bisani ta janye ƙwayar idanuwan nata daga kan ƙofar tana mai mai dasu kan tafin hannun ta da yake ɗauke da zureriyar jar takobin nan, sannan ta sake miƙar da hannun gefe ba tare da tace komai ba.

Dasauri wannan badakaran da yakawo mata takobin ya sake tawowa da baya da baya har ya ƙaraso inda take, kana ya zube guiwoyin sa aƙasa, sannan ya miƙa hannu ya ɗauki takobin ba tare da ya kalli fuskar ta ba yanzu ma.
Sake miƙewa yayi ya koma da baya da bayan sa kamar yacce yazo.

Sai da ta ɗauki kimanin daƙiƙa goma atsaye awurin tana kallon ɗakin da yake kallon ta wanda yake baƙiƙƙirin da duhu, ba ahangen komai na cikin sa, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta masu sanye da sarƙoƙin gwal ajiki waƴan da suke futar da sauti aduk lokacin da take tafiya, tana mai dosar ɗakin gadan -gadan.

Cak ta tsaya adai dai bakin ƙofar ɗakin ba tare da ta shiga ciki ba. Dunƙule tafin hannun ta tayi tana mai yin wasu surutai, tukun daga bisani ta buɗe sa tana mai watsa wasu abubuwa da suka bayyana akan sa zuwa cikin ɗakin. Take kuwa haske ya bayyana acikin sa, tukun ta sake ɗaga ƙafafuwan ta tana mai tura kanta cikin sa.

Ɗan ƙaramin ɗaki ne wanda idan da mutane zasu zauna aciki duka baifi yaci shimfiɗun mutum biyu ba zai cike, sai wasu kaskwayen huta (randina) da suke ajiye akowace kusurwa ta ɗakin huta na tashi daga cikin su, wacce tayi matuƙar zafafa ɗakin tako ina.

Tsaye tai daga bakin ƙofa tana mai kallon yarce yake tsaye awurin, gaba ɗayan sa ya jiƙe sharkaf har yana ɗiga da gumi, kai idan baka sani ba zaka rantse kace daga cikin ruwa aka zarosa tsabar yacce ruwan ke sauka akowacce kafa ta jikin sa.

Matashin saurayi ne mai kimanin shekaru talatin aduniya, ɗaure yake jikin wasu ƙarafa masu matuƙar girma, yayin da jikin sa ya kasan ce babu ko riga akai, sai ɗan ƙaramin farin yadi dake ɗaure aƙugun sa kawai. BEER

Ahankali ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar inda yake idanuwan ta ƙur akan sa.

Tun lokacin da ta ƙaraso bakin wurin yaji alamun zuwan nata ajikin sa kamar yacce yake ji aduk lokacin da sukai kusanci da ita, sai dai kuma ayarce kansa ke ɗage asama idanuwan sa na kallon rufin dake saman ɗakin kai bazaka taɓa cewa yasan da wanzuwar mutum awurin ba, domin kuwa motsi baiyi ba daga yarce yake tunda ta shigo balle har ya ɗago kai ya kalle ta.

Cigaba da takowa tayi har ta ƙaraso kusa da inda yake, tukun taja ta tsaya tana mai kafe sa da manya manyan idanuwan ta ba tare da tace komai ba, yayin da har lokacin shima kansa ke ɗage asama ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba.

Sai da suka ɗauki kimanin minti goma ahaka, tukun ta fara ɗaga laɓɓan ta cikin zazzaƙar muryar ta mai matuƙar kaushi tana mai faɗin. "Ina amsar tambaya ta?" Tukun ta ƙara mai da baki ta tsuke tana kallon sa.

Sai da yay kamar bazai yi magana ba, domin ko ita kanta har ta fara fudda tsamannin zai bata amsa, tukun daga bisani ya saukar da kansa daga kallon saman da yake yana mai juyo da manya manyan idanuwan sa zuwa kan fuskar ta.

Lumshe idanuwan sa yayi bayan ya kalle ta ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya sake wara su yana mai watsa ƙwayoyin su acikin tsakiyar nata, kana ya gumtse baki yayi shiru ba tare da yace ƙala ba.

Sosai ranta ya ƙara bala'in ɓaci ta dalilin banzan da ya mata, da kuma yarce ya tsaya ya kafe ta da idanuwa yarce kasan sa'ar sa.

Cikin zafin rai da tafasar zuciya ta ƙara buɗe baki tana mai faɗin. "Nace maka ina amsa ta ƙasƙantacce!" Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kallon cikin idanuwan sa.

Murmushi gafen baki ya saki yana mai ƙare kafeta da dara -daran idanuwan sa, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin kakkausar muryar sa shima yana mai furta cewar. "Ke ɗin yarin ce har yanzu, shiyasa har kika gaza samun amsar tambayar ki ke da kan ki, amma ba damuwa, shima girman lokaci ne da shi, kuma ina mai tabbatar miki idam naki lokacin girman yayi keda kan ki zaki samo amsar ki."
Ya faɗa cikin kaushi yana mai ƙareshe maganar tasa da sakin murmushi, har kuma lokacin ƙwayar idanuwan sa suna cikin nata yana aika mata da wani irin kallo.

Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta jikin ta na tsantsar rawa, tsabar yarce maganar sa tayi matauƙar ƙona mata rai, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sake watsa su acikin nasa.
Lokaci ɗaya duka idanuwan nata suka rikiɗe daga launin fari zuwa na ja, jan ma irin jajahur ɗin nan tsabar ɓacin rai, wani irin huci take futarwa daga cikin bakin ta yarce kasan wacce tayi tseren gudu, yayin da jijiyoyin kanta kuma suka futo sukai ruɗu-ruɗu agaban goshin ta duk ta sanadin furucin sa.

Ta fannin sa kuwa har lokacin bai ɗauke idanuwan sa daga kan fuskar ta ba, kamar yacce bai dena jifan ta da kyakkyawan murmushin sa ba da yake yi, da alama dai shi ko kaɗan yana yin da ya ganta aciki bai razana saba, duk da dai kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da ba ƙaramun jigatuwa yayi ba, koma ace yana kan jigatuwa sabo da yarce gumi ke tsattsafowa daga cikin gashin kansa yana dira akan kafaɗun sa da fuskar sa.

"Tabbas azaba mai raɗaɗi zata hau kanka fiye da wacce kake ciki muddin ka bari daƙiƙa huɗu suka shige agaba ba tare da na jiyo abun da nake san ji daga gare ka b...."
"Azaba? Shin dama har akwai wata azaba da zata zamto sabuwa gare ni ne acikin *BAƘAR MASARAUTA*?
Shin koko kin manta ita kanta azabar acikin ta na taso na samu kaina ne?" Ya katse mata maganar da take kanyi da faɗin haka yana mai sakin numfarfashin wahala ba tare da ya bari yaji ƙarshen abun da zata faɗa ba, har lokacin kuma idanuwan sa suna acikin nata kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa tana sakin huci da nata jajayen idanun.
Harshe yasa ya kamo leɓen sa na ƙasa da shi, tukun ya sanya haƙwaran sa na sama dana ƙasa yana mai cige leɓen tare da sakin murmushi, har kuma lokacin bai bar kallon ta ba.

Wani irin ɓacin rai gimbiya tasmir taji ya ƙara cakar zuciyar ta, lokaci ɗaya jikin ta ya fara rawa idanun ta na sake rikiɗewa suna yin ja.

Cikin zafin nama ta ɗago tafin hannun ta na dama tana mai dunƙule ƴan yatsun ta cikin sa, sannan ta ɗaga ƙafar ta ta hagu tayi ball da kaskon hutar dake ci agaban ta ya tuntsire ƙasa ya fashe, kana ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai buɗe baki cikin tsantsar sauti tace. "Rai Rai buuuu Hooo Reee!" Tukun ta wara tafin hannun nata bayan ta buɗe jajayen idanuwan ta tana mai watsa wasu abubuwa da suka bayyana acikin sa akan fuskar Beer.

Wani irin baƙin hayaƙi ne ya tashi awurin yana mai lulluɓe masa duka jiki.
Wata irin gigitattar ƙara ya buga wacce tasanya gaba ɗaya komai dake wurin amsawa.
Chapter 2 · 0% Book details