Sashe 54
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ShimfiÉ—e sa tayi akan gadon ta tana mai fara tofa masa addu'oi.
Ƙarasowa su Mai Martaba sukayi ciki suma suna masu hayowa kan gadon, tukun dukan su suka haɗu suna masu karanto addu'oi suna tofa masa.
Ba suyi minti biyar da fara addu'oin ba ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya ajere-ajere, kana daga bisani kuma wani irin bacci ya fizge sa.
A tare daga Gimbiya Fulani har mai martaba suka sauke nannauyar ajiyar zuciya, tukun suka juya suna masu kallon junan su cikin tsantsar aljabi da firgicin abun da ke faruwa.
Zaune sukai a wurin gaba É—ayan su jugum-jugum ba mai tankawa wani, sai faman kallon Asad da suke ta ai'kin yi da idanuwa kawai.
Acan cikin Masarautar kuwa tini labarin sake suman Asad ya baza ko ina da ina na cikin ta.
Sosai kuwa abun yayi matuƙar ɗaurewa jama'a da dama kai, yayin da wasu kuma hakan yayi musu tsantsar daɗi, wasu kuwa gaba ɗaya suma sun firgita da lamarin ba kaɗan ba.
Ko da dare yayi ma haka Asad ya farka yana surutai tare da zabure-zabure akan cewa dole sai ya koma wurin Sheikh Yaƙub, shi baizai ƙara zuwa fada ba baya sonta.
Sosai hankalin su Mai Martaba ya sake matuƙar tashi, haka su kai ta aikin tofa masa addu'oi da shi da Gimbiya Fulani har su samu yayi bacci kafin ya sake farkwa, kai ataƙaice dai ranar kwanan zaune sukayi dukan su, har Babban Yaya da sauran ƴan uwansa masu girma, domin kuwa shi kansa Al'amin sai bacci ɓarawo ne ya sace sa anan cikin ɗakin Gimbiya Fulani, amma bai koma part ɗin su ba.
Washe gari kuwa misalin ƙarfe ɗaya na rana, Abokin Mai Martaba kuma ɗan uwan sa mai suna Alhaji Abubakar ya duro cikin Masarautar Wasai, domin taya murnar samun lafiyar Asad da yaji labari jiya.
Alhaji Abubakar nabban ɗan kasuwa ne wanda sunan sa yay shuhura aduniya, domin kuwa ataƙaice dai yanzu haka ma yana Dubai dukan sa da zama da shi da iyalan sa.
Sun taso tare da Mai Martaba a matsayin aminai tun suna yara, kasancewar shima É—in Asalin mahaifin sa É—an nan cikin Masarautar Wasai ne.
Yana shigowa gidan shima ya riski wannan rikicin da ake ta fama da shi na Asad, domin kuwa har kawo yanzu kuka yake yana cewa bazai zauna a cikin Masarautar ba.
Shima ɗin shigowa falon Gimbiya Fulani yayi yana mai zama a kusa da kujerar da Mai Martaba yake zaune akai riƙe da Asad.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani take zaune a gefen Mai Martaba, gaba ɗaya idanuwan ta a kumbure, alamun ba ƙaramun kuka taci ba kenan.
Ko da Alhaji Abubakar yaga abun Asad É—in da gaske ne ba wasa ba, sai ya gyara zaman sa akan kujerar da yake yana mai yin gyaran murya.
Sautin gyaran muryar sa da su Mai Martaba sukaji ne ya sanya su juyowa ɓarin da yake dukan su suna kallon sa.
Fuskantar su shima É—in yayi sosai, tukun ya buÉ—e baki cikin nutsuwa yana mai faÉ—in.
"To ni a gani na Alhaji, tunda abun nan yazo da haka shi yaron yana ta faÉ—in bazai zauna ba, mai zai hana abani shi in tafi da shi can wuri na, in yaso sai ya cigaba da karatun sa acan kafin zuwa wani lokaci muga yarce hali zaiyi."
Ya ƙarasa maganar yana mai binsu da idanuwa daga shi har Fulani.
Yayin da su kuma gaba ɗayan su sukayi shiru ba tare da wani yace komai ba, tukun daga bisani Fulani tayi ƙarfin halin buɗe baki cikin sanyin murya, tana mai faɗin.
"Tabbas hakan ma yayi, domin kuwa ni kaina tun É—azu tunanin yadda zamuyi da shi nake, sabo da gashi nan daga jiyan da ya dawo zuwa yau har ya rame, dan haka ni na amince ku tafi tare muddin zai samu nutsuwa acan É—in, in yaso daga baya sai muga yadda za'ayi."
Ta ƙarasa maganar cikin sanyi tana mai jin ranta na ɗaci da ƙuna.
Jin hakan data faÉ—a ne ya sanya Mai Martaba shima amicewa, amma bawai dan ransa yaso da hakan ba ko kaÉ—an, sai dai shima É—in zai so yaga É—an nasa ya samu nutsuwa bawai ya cigaba da rayuwa ahaka ba.
Hakan ne yasa ya buÉ—e baki cikin sanyi yana mai faÉ—in.
"Tom shikenan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, amma ni ina ganin idan kun tashi tafiyar sai ahaɗa har da Al'amin ku tafi tare duka, domin kuwa in bahakan akai ba shima bazai taɓa sakewa anan ɗin ba, duba da yadda ya koma alokacin da muke acan London sabo da rashin abokin nasa, kuma shima Asad ɗin zaifu samun sakewa acan ɗin idan suna tare."
"To masha Allah hakan ma yayi sosai, Allah kuma ya ƙara masa lafiya."
Cewar Alhaji Abubakar cikin sanyi shima.
Haka dai ranar ma suka yini cir jugum-jugum sai sallah ce kawai ke tayar da su, domin kuwa ko Fada ma Mai Martaba bai leƙaba kwata-kwata, ahaka har dare ya riske su suna a hakan.
Washe gari kuwa tun da sanyin safiya aka shirya Al'amin da Asad tas, misalin ƙarfe goma na safiya aka musu rakiya Airpot, kana ƙarfe shaɗaya na safe dai-dai jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasar Dubai, ba tare da sun ɗauki ko da ƙyalle ba na sutura, sai waƴan da suke sanye a jikin su kawai.
_Musababbin canzawar rayuwar Asad da Al'amin kenan._
_BAYAN SHUÆŠEWAR SHEKARU BAKWAI._
*KASAR MALIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*âœ
*KUYI MANAGE BANDA CAJI NE YAU.*
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 22*
Tafe Ƴar yarinyar take a cikin tsakiyar wasu garadan maza da suke riƙe da bulalai a hannun su, suna masu tunkarar wata kujera da take kafe a ƙarƙashin wata inuwar bishiya.
Yayin da gefe da gefen bishiyar kuma wani irin farin ruwa kar yay mata ƙawanya.
Sanye take da wata doguwar riga ruwan hanta mai matuƙar tsayi a jikin ta tana sharar ƙasa, yayin da kanta kuma yake ɗage a sama tana mai yin wani irin taku, babu alamun far'a a fuskar ta ko kaɗan, ƙafafuwan ta kuwa sanye suke da wani irin azababben takalmin fata, yayin da ƙaurikan ƙafafuwan ƙafar ta kuma suke sanye da wasu irin saraƙunan gwal, masu matuƙar ƙyalli da ɗaukar ido suna futar da sauti.
Gimbiya Tasmir kanen, Yarinya mai kimanin shekatu bakwai a duniya cif-cif yanzu kenan, Yarinyar da ta-taso da tsantsar Izza, girman kai tare da miskilanci, domin kuwa ba taƙi ta kwana kana kuma ta yini ba ba tare da ta furta komai ba, haka kuma muddin ta biyo hanya to babu wani mahaluki da ya isa ya gifta wannan hanyar, idan aka cire mutanen da suke tare da ita tun a yanzu da take ƴar ƙaramar ta, idan kuma har akayi rashin sa'a mutum bai lura da tawowar ta ba har ta ƙaraso wurin da yake, to fah ranar ya shiga ukku ya lalace, domin kuwa Dakarun ta da suke take mata baya a kowane lokaci take sanyawa su zane masa jikin sa tas sa bulalai.
Ko kaÉ—an bata da tausayi, kuma bata san-sa ba ma, kamar yadda ta taso taga ahalin gidan nasu suke.
Ƴar gatace lamaba ɗaya a wurin mahaifin ta Sarki Barbaru, tare da kuma Yayen ta Maza.
Duk abunda ta nuna tana so to komun wahalar sa sai an samo mata shi, haka kuma muddin tace bata son abu to fa bata son sa, kuma babu wanda ya isa ya sanya ta taso shi.
Ci gaba da tafiya tayi kanta É—age a sama, yayin da mayawaicin gashin dake É—auke akan ta kuma yake ta reto a gadon bayan ta.
Cak ta tsaya lokaci ɗaya a wurin da take ba tare da ta sake ɗaga ƙafar ta ba, ba wai kuma dan ta cimma wurin da take son zuwan bane, sai dan kawai motsin sautin tafiyar mutum da ta jiyo a cikin kunnuwan ta.
A hankali ta fara sauke kanta daga saman da yake, tukun ta juyar da shi ɓarin hannun ta na hagu, tana mai kai idanuwan ta zuwa wurin da take jiyo sautin nan.
Take kuwa idanuwan ta sukayi mata arba da matashiyar budurwar da take gudu amatuƙar firgice, tana neman wurin ɓuya, sanye take da kayan Bayi ajikin ta, da alama dai bata lura da tawowar tasu bane da wuri sai da har suka ƙaraso wurin da take, shi yasa ba tayi saurin ɓuya ba.
Da sauri dakarun nan suka juya ɓarin da su kaga Gimbiya Tasmir ta kai idanuwan ta, domin kuwa sun sani bata waige idan har tana tafiya, sai idan taji sautin motsin wani abun ne.
Take kuwa suma suka hango wannan baiwar da take ƙoƙarin ɓuya hankalin ta atsan-tsar tashe.
Ɗaga hannu Gimbiya Tasmir tayi, tana mai yi musu nuni da ita ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta sauke hannun nata ƙasa, tana mai cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta tayi gaba, yayin da su kuma waƴan nan dakarun nata su kayi wurin da suka hangi baiwar nan gadan-gadan.
Cikin sakwannin da basu gaza talatin ba duka suka cimmar wa wannan baiwar.
Ɗaya daga cikin sune ya miƙa hannun sa zuwa wurin da take yana mai riƙo hannun ta da matuƙar ƙarfi, tukun ya funciko ta yana mai janyo ta ta faɗi a ƙasa, kana ya fara janta a cikin ƙasar yana mai juyawa ya doshi wurin da Gimbiya Tasmir take, suma sauran duka suka take masa baya.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir cigaba da tafiya tayi har ta ƙarasa ƙar-ƙashin inuwar bishiyar nan, inda wannan haɗaɗɗiyar kujerar take ajiye a kafe.
Tsaye tayi a gaban kujerar tana kallon ruwan nan da yake zagaye da bishiyar, wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi na dukan jikin ta.
Kana ahankali ta juyawa kujerar baya, tukun daga bisani ta zauna akan ta tana mai ɗaukar ƙafar ta ɗaya ta ɗora ta akan ɗayar.
Kana ta fara girgiza ta a hankali, tana mai lumshe dara-daran fararen idanuwan ta masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali .
Tukun daga bisani ta wara su akan wannan fuskar baiwar da aka janyo ta cikin ƙasa, jikin ta na wata irin kar-karwa.