← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 79

Sashe 53

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuska É—auke da murmushi Mai Martaba ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in.
"To Baba na aje a gaida Mamy ko?"
Ya ƙarasa maganar yana mai shafa kansa, tare da ɗan turasa gaba.
Cikin sanyi Yarima Asad ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai tunkarar inda mamy'n tasu take.

Ba zato ba tsammani sai jin sautin muryar Asad Gimbiya Fulani da gaba ki É—aya sauran mutanen dake a cikin falon sukayi yana mai faÉ—in.
"Ina yini Mamy na!"
Tukun daga bisani ya faÉ—a jikin ta yana mai rungume ta.

Da sauri itama ta durƙushe a ƙasa tana mai rungume sa ƙam-ƙam a cikin jikin ta, tukun daga bisani ta fashe da wani irin kukan farin ciki wanda batan da tawowar sa ba, sai futowar sa da taji kawai, tana mai faɗin.
"Shin da gaske ne ba mafarkin dana saba yi bane nake yi kaine nake jin muryar ka Zaki na?"
Ta ƙarasa maganar tana mai ɗago kansa ta kalle sa.
Jin-jina mata kai yayi ba tare da yace komai ba.

"A'a my Zaki ba da kai nake son ka amsa mun ba, bakin ka zaka buÉ—e ka sake yi mun magana, hakan shine zai sa na tabbatar da ba mafarki nake yi ba."
Ta faÉ—a tana mai É—an girgiza sa da hannuwan ta biyu.

"Ba mafarki kike ba, Mamy na nine a gaban ki nake magana."
Asad ya faÉ—a yana mai sake faÉ—awa jikin ta yayi wani irin lafewa.

"Alhamdulillahi rabil alamin, Alhamdulillahi rabi samawati wal'ard."
Gimbiya Fulani ta faÉ—a cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa.
Yayin da su Baban Yaya da sauran ƴan uwan sa kuma suka saki wani irin ihun murna da matuƙar ƙarfi, suna masu tawowa zuwa wurin da suke aguje.

Suna isowa gaba ɗayan su suka faɗa jikin Asad da Mamy'n tasu suna masu rungume juna ƙam-ƙam.

Haka dai sukai ta farin ciki suna sanya Asad yana maganar da baya son yin ta ko kaÉ—an.
Barin ma da suka iso cikin gidan, gaba ɗaya sai ya jisa a wani irin takure, ga kuma ƙirjin sa dake ta faɗuwa tunda suka doso Masarautar a mota, wannan dalilin shine ya sanya sa kasa sakewa ko da ƴan uwan nasa.

Suna a cikin wannan yana yin na farin ciki sai ga Al'amin nan ya faÉ—o cikin falon aguje bako sallama a bakin sa.

Da matuƙar sauri suka rungume juna shi da Asad suna masu sakarwa junan su murmushi.
Tukun Al'amin ya buÉ—e baki cikin tsantsar murna yana mai cewa.
"Yi mun maganar mana inji idan da gaske ne abun da jummai tazo ta faÉ—a."
Al'amin ya faÉ—a yana mai shafa kan Asad.
Yayin da shi kuma ya É—aure fuska yana mai ture sa daga jikin sa, tare da faÉ—in. "Bazan yi ba É—in, dallacan É—aga ni daga zuwa na har zaka fara danne ni."
Ya ƙarasa maganar da hararar Al'amin.
Wani irin ihu Al'amin ya saki yana mai faÉ—in.
"To jarabbaben banza ai kayi ma maganar baka sani ba, kuma wallahi bazan É—aga kan ba."
Ya ƙarasa maganar yana mai sake hayewa kansa.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya juya yana mai fucewa daga cikin É—akin cikin tsantsar farin ciki, sabo da ganin da yayi gaba É—aya sun manta da shi ma.

Kafun kece me tini labarin dawowar Asad yana magana ya baza ko na- na cikin Masarautar.
Hakan kuwa ba ƙaramun daɗi yayiwa masoyan su ba, yayin da maƙiyan su kuma sukaji tamkar su cinnawa zuciyar su huta dan baƙin ciki.

Abu fa kamar wasa na faÉ—uwar gaban da Asad yake ji, sai gashi yana shirin zamtowa Babba.
Domin kuwa bayan Fulani tayi masa wanka yaci abinci sun shirya, sai ga saƙon Mai Martaba nan ya iso wurin sa, na cewar ya tawo faɗa suyi hira idan bai gaji ba.
Ai kuwa take awurin Al'amin ya miƙe tsaye yana mai jan hannun sa tare da faɗin.
"Taso muje kaji."
Kasancewar a lokacin suna zaune ne babu abun da suke yi.
Miƙewa Asad ɗin yayi yana mai bin bayan Al'amin suka fuce, sai dai kuma sun dosar hanyar fada yaji gaban sa yayi wata irin mahaukaciyar faɗuwa.
Da ƙarfi ya rumtse idanuwan sa yana mai ɗaukar tafin hannun sa ya dafe ƙirjin sa da shi, tukun daga bisani ya cigaba da dɗaga ƙafafuwan sa cikin ƙarfin hali irin nasa suna masu dosar fadar.

Adadin yadda yake ɗaga ƙafafuwan nasa yana cigaba da tunkarar Fada, haka adadin faɗuwar da gaban sa yake yi take ƙaruwa.
Yayin da Al'amin kuma yake ta masa zuba yana basa labaran abubuwan da suka faru a lokacin da baya nan, ba tare da ya lura da halin da yake ciki ba, ahaka har suka ƙarasa bakin fada.

Suna shiga cikin fadar Yarima Asad yaji kansa yayi wata irin mahaukaciyar sarawa, kana daga bisani kuma wata irin hajijiya ta fara ɗibar sa, tukun ya tafi luuu yana mai zubewa a ƙasa sumamme!

Cikin tsantsar tashin hankali da firgici daga Mai Martaba har sauran mutanen da suke zaune a cikin fada suka taso suna masuyowa kansa.
Yayin da Al'amin kuma ya fashe da wani irin gigitaccen kuka yana mai durƙusawa sa a ƙasa ya fara girgiza sa tare da kiran sunan sa.

Da wani irin gudu Mai Martaba ya ƙaraso wurin yana mai h................✍

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 21*

Hankaɗe mutanen da suke tsaye a gaban sa, ya durƙusa ƙasa yana mai ɗaukar Asad ya ruƙunk'ume sa a jikin sa.
Kana daga bisani ya buÉ—e baki cikin tsantsar tashin hankali, ruÉ—u had'i da firgici yana mai faÉ—in.
"Baba na! Baba na!! Baba na!!!
Asad! Asad!! Asad!!!
Zaki! Zaki!! Zaki!!!"
Ya dinga kiran sunayen da duk ake faɗa masa a matuƙar ruɗe yana mai girgiza sa. Kafin daga bisani kuma ya miƙe tsaye zumbur ɗauke da shi a hannun sa.

Zagaye ya farayi da shi a cikin Fada'r yana mai girgza kansa, gaba É—ayan sa ya ruÉ—e ya rasa yadda zaiyi, tukun daga bisani kuma ya juya da sauri yana mai fucewa ya kama hanyar pary É—in sa direct É—auke da shi a hannun nasa.
Yayin da Al'amin kuma ke biye da su a baya cikin tsantsar firgici shima yana kuka.

Shimfiɗe sa Mai Martaba yayi akan haɗaɗɗen gadon sa, yana mai cigaba da girgiza sa tare da kiran sunan, kafin daga bisani kuma ya sake miƙewa zumbur yana mai matsawa gaban freezer dake kafe a cikin ɗakin.

BuÉ—e ta yayi yana mai É—auko ruwa mai sanyi a cikin jarka daga cikin ta, kana ya juyo da sauri yana mai dawowa wurin da Asad yake ya buÉ—e jarkar ruwan, yana mai fara tsiyaya masa shi akan fuskar sa.

Wasu irin ƙarfa-fan ajiyar zuciya Asad ya fara saki da sauri da sauri, tukun daga bisani kuma ya buɗe idanuwan nasa duka akan fuskar Mai Martaba da yake tsaye a gaban sa.

Da sauri Mai Martaba yayi cilli da jarkar ruwan da take riƙe a hannun sa a ƙasa, kana ya durƙuso zuwa kan gadon yana mai janyo Asad cikin jikin sa.

Da wani irin ƙarfi Asad ya rungume sa jikin sa na rawa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar tsoro yana mai faɗin.
"Ina Mamy na Abba na, ni zan tafi wurin Mamy na, ni bana son wurin nan."
Ya ƙarasa maganar yana mai shirin zame jikin sa daga cikin na Mai Martaba ya tafi.

"Meke damun kane Baba na, me yasa ba zaka zauna anan wuri na ba?"
Mai Martaba ya faÉ—a cikin rawar murya, yana mai sake rungume É—an nasa da yake jin tamkar shi kaÉ—ai ya haifa a duniya.
Wani irin kuka Asad ya fashe da shi jikin sa na matuƙar karkarwa, tukun daga bisani ya fara ƙoƙarin ɓan-ɓare jikin sa daga cikin na Mai Martaba yana mai faɗin.
"Abba na mutafi daga gidan nan, mu koma gidan Sheik yafi nan daÉ—i."
Ya ƙarasa maganar yana mai funcike jikin sa daga na Mai Martaba.
Yayin da Al'amin kuma keta aikin kuka yana mai riƙe da tafin hannun sa.
Ganin hakan da Mai Martaba yayi ne ya sanya sa miƙewa tsaye shima yana mai sake riƙo ɗan nasa, tukun ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"To muje in kaika wurin Mamy'n taka Baba na."
Kana suka juya suna masu kama hanyar da zata sadar dasu ɓarin Gimbiya Fulani, ta cikin wata ƙofa da suka bi da take anan cikin part ɗin su duka ukkun, har zuwa lokacin kuma jikin sa bai bar rawar da yake yi ba.

Suna shirin shiga cikin falon sukaci karo da Gimbiya Fulani bako mayafi a jikin ta tana shirin futa cikin tsantsar firgici.
Da sauri taja da baya ta tsaya, sabo da jin da tai kanta ya daki ƙirjin mutum, tukun daga bisani ta ɗago kan nata tana mai sauke idanuwan ta akan fuskar Mai Martaba, kafin daga bisani kuma ta sake yin ƙasa da kanta nata, idanuwan ta na dira akar fuskar ɗan nata.

Da matuƙar sauri tayi wurin da yake tana mai durƙusawa a ƙasa ta janyo sa cikin jikin ta.
Wani irin ƙan-ƙameta shima yayi da matuƙar ƙarfi, jikin sa na karkarwa.

"Zaki na aka cemun baka da lafiya, ka sake sumewa a cikin Fada"

"Mamy na mutafi-mutafi, ki mayar dani gidan ya Sheikh ni bana son gidan nan."

Asad ya faÉ—a cikin tsantsar ruÉ—u yana mai fashewa da kuka, ba tare da ya bata amsar tambayar da tayi masa ba.
Take kuwa a wurin hankalin su daga ita har Mai Martaba da Babban yaya da ya ƙaraso wurin yanzu yayi bala'in tashi.

Da sauri Gimbiya Fulani ta cicciɓe sa a jikin ta tana mai miƙewa tsaye ɗauke da shi, tukun ta juya tana mai kama hanyar bedroom ɗin ta cikin tashin hankali.
Rufa mafa baya su Mai Martaba sukayi suma, gaba É—aya shi yanzu ma ya rikice ya rasa mai ya kamata yayi, domin kuwa gaba É—aya kansa ya riga da ya gama kullewa da yanayin yadda yaga Asad É—in ya koma yanzu.
Chapter 53 · 0% Book details