← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 79

Sashe 39

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wani irin haukace Ishaƙ yayi kanta yana mai sakin wani irin gunjin kuka mai tsantsar sosa rai da ban tausayi, gumi na yanko masa ta ko ina na jikin sa, tayadda har ya jiƙa sa duka sharkaf yadda kasan wanda ya shiga ruwa.

Acan ɓangaren badakaran nan kuwa yana ƙarasawa kan shimfiɗar ya miƙawa Boka mai hutar kasko jinjirin.

Kallon sa boka mai wutar kasko ya tsaya yi daga tsayen da yake, yana mai yaba kyawun halittar yaron da ya gani aransa, tukun daga bisani ya matsa kusa da kaskon nan dake ci da wuta acikinsa, yana mai ajiye jinjirin da yake tsirara jikin sa ɓace da jini a gaban kaskon, kana yaja baya yana mai komawa ya zuba ido akan sa kamar yadda duka sauran mutanen dake wurin suka zuba nasu idanun.
Yana diresa a wurin kuwa jinjirin ya ƙara tsanyarewa da kuka, yana mai kai hannun sa baki ya fara wawurar sa, tukun daga bisani ya fara hahaura ƙafafuwan sa yana mai cillasu sama cikin kukan da yake, hakan da suka gani ne ya sanya su sake zuba idanuwan su akan sa.
Yayinda shi kuma jinjirin ya cigaba da harba ƙafafuwan sa har suka dako kaskon wutar nan.
Take kuwa a wurin kaskon ya tungule ƙasa yana mai rabewa gida biyu dai-dai.............!!!✍

_KUNA MUGUN SON KARARU TA YADDA HAR IDAN KUKAJI SHIRU BAKWA IYA HAKURI SAI KUN TAMBAYA, AMMA KUMA COMMENT NA KANKANIN LOKACI NA MUGUN YI MUKU WUYA. TO BANA TINANIN ZAKU SAKE GANIN WANI PAGE DIN DAGA WANNAN MUDDIN BANGA COMMENTS DA SHARHI SOSAI BA GASIYA._

*BY*
UMAR FARUQ*D*

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 16*

Wani irin ihu su Sarki Barbaru suka saki cikin tsantsar farinciki suna masu É—aga hannuwansu sama, tare da faÉ—in.
"Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!"
Sabo da yadda suka ga gaba É—aya kaskon nan ya dare gida biyu, kana wutar cikinsa ta mace tas, kamar yadda boka ya faÉ—a, yayin da su kuma mutanen dake cikin jirgin nan suka sake fashewa da kuka mai sosa rai, shi ko IshaÆ™ banda faman girgiza Aishatu yana kiran sunan ta, bayan ya watsa mata ruwa a fuska babu abun da yake iya yi.
Wani irin kuka yake jikinsa na tsantsar rawa tamkar ƙaramin yaro.

Sarki Barbaru da kansa ya durƙusa a ƙasa, yana mai ɗaukar jaririn dake ta aikin tsala kuka har yanzu a hannun sa, tukun ya buɗe baki cikin muryar sa mai futar da amon sauti, yana mai kallon dakarun sa tare da faɗin. "Ai'ki kuma ya ƙare daga yau, domin ko Ubangiji Gargabilu ya yaye mana wahala, ya aiko mana da mafutar mu, yanzu rayuwar mu zata dawo kyakkyawa ba tare da fargabar komai ba, tamkar yadda muka kasance ada, dan haka ku koremun waƴan nan mutanen, tare da jirgin su gaba ɗaya daga cikin ƙasa ta."
Sarki Barbaru ya faÉ—a yana mai nuna Jirgin su Aishatu.
Tukun ya juya É—auke da ÆŠan a hannun sa.

Da wata irin gigitattar ƙara Aishatu ta farka da ita tana mai faɗin. "Ɗana! Ɗana!! Ɗana!!! Kuyi haƙuri! Kuyi haƙuri karku kashemun shi, kuyi haƙuri kubani shi ko ɗaukar sa ne nayi, kumun afuwa kubarni inji ɗumin sa yaji ɗumin jiki na shima, kumun gafara ku barni nayi rayuwa da jinjiri na!" Ta faɗa a wani irin haukace tana mai funcike jikin ta daga riƙon da Ishaƙ yayi mata ta sake yin bakin Jirgin aguje tana shirin fucewa, sabo da yadda ta hango Sarki Barbaru ya juya yana tafiya riƙe da jinjirin nata, ga kuma yadda kukan jaririn ke dukan dodon kunnuwan ta.

Da sauri wani Badakare da yake abakin hanyar yasan ya hannun sa yana mai hankaɗata baya ta faɗi ƙasa.
Tukun suka ƙara zare mahaukatan makaman su suna masu saitawa direbobin jirgin hanya, tare da basu umarnin suyi gaggawar yin gaba tun kafin su canza shawara duka suka kashe su suma.
Jin hakan da matuƙan Jirgin nan sukayi kuwa ba ƙaramun sake hatsina musu ƙwaƙwalwa yayi ba, domin kuwa sun tabbatar da babu abun da mutanen nan zasu ce zasuyi sa suka sa yin sa, hakan yasa cikin gaggawa ko wanne ya koma wurin sa, tukun suka sake yin gaba suna masu ɗaukar hanyar su, yayin da suma mutanen Baƙar Masaruta suka ƙara shigewa cikin jirgin su suna masu binsu abaya domin suyi musu rakiya.

Tunda wannan Badakaran ya sake hankaɗa Aishatu ta faɗi a ƙasa, sai Ishaƙ ya sake zuwa ya riƙe ta gam, irin riƙon da bazata taɓa iya ƙwatar kanta ba, domin kuwa ya sani muddin zata cigaba da haka to Ba ƙaramun aikin su bane su kashe ta duka itama.
Sosai take kuka na tashin hankali mai tsanin ban tausayi daga kwancen da take acikin jirgi, banda raɗaɗi da suya babu abun da take jin zuciyar na nayi mata, tayi nadamar zuwan ta Jahar Ruman gaisuwar mahaifin ta tafi sau dubu, taji inama ace tabi maganar mijin nata tayi haƙuri tabar zuwan, tabbas da tasan babu wani abu wanda zai rabata da Ɗan ta a lokacin da ta haife sa.

Sosai take hango kamannin yaron a cikin idanuwan ta, sabo da yarce suka zauna mata a cikin idanuwan nata das, wato kamannin ta kenan sak kamar yacce ta gani akan fuskar jinjirin.

Sai da har suka rakasu ƙofar futa daga cikin Ɓakar Masarauta duka, tukun suka juyo da kan nasu Jirgin hankulan su akwance babu damuwar komai tattare da su, yayin da su kuma mutanen cikin Jirgin su Aishatu suka sake fashewa da wani irin azababben kuka, musamman ma waƴan da aka ƙwacewa Ƴaƴa, suna masu kallon hanyar garin, hanyar da suka raɗa mata suna Bakar Hanya, kamar yacce suka raɗawa wannan rana ta Alhamis suna Baƙar Rana, mai tsantsar muni da ƙuna a cikin rayuwar su.

Acan ɓangaren su Sarki Barbaru kuwa kai tsaye suka doshi ɓangaren bayi.
Tafe suke suna masu furta sunan Gargabilu da matuƙar ƙarfi, yayin da jinjirin nan kuma yake ta cigaba da sakin kuka, har lokacin kuma Sarki Barbaru bai ajiye sa ba.

Suna zuwa ɓangaren bayi suka tsaya dukan su a wuri ɗaya, tukun daga bisani wani Bafade ya buɗe baki cikin sauti yana mai faɗin. "Kuna inane ne Ƴaƴan matsiya ta ƙasƙantattu? To kufur-futo ga Uba ga kowa nan ya ƙaraso, ku fur-futo ga bujimin mazaje nan ya ƙaraso, ku fur-futo ga zakin duniya nan na jiran ku."
Tun kafin ya kaiga rufe bakin sa sai ga su nan suna futowa da baya da baya daga cikin ɗakunan su na iccina, da matuƙar yawan su mazan su da matan su a guje kuma.
Sanye mazan su suke da ƴan gajerun fararen wandina na yadi, babu ko riga ajikin su, yayin da matan su kuma suke ɗaure da wani ɗan guntun baƙin ƙyalke a ƙugun su, tare da wata wargajejiyar rigar yadi ajikin su, gaba ɗayan su babu mai takalmi a ƙafar sa.

Da baya da baya suke ƙarasowa har wurin da su Sarki Barbaru suke a tsaye jikin su na karkarwa, tukun sai su juyo ta gaba suna masu zubewa rufda ciki a ƙasa wanwar gaban su Sarki Barbaru.

"Ina Iyar Bayi take?" Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa da take matuƙar firgitar da su yana kallon su.
Wata mata ce mai kimanin shekaru arba'in ta miƙe daga kwancen da take tana mai futowa jikin ta na tsantsar rawa da karkarwa, yayin da kanta kuma yake durƙushe a ƙasa, ta ƙaraso gaban Sarki Barbaru tana mai zube guiwoyin ta a ƙasa.

"Tsaye zaki miƙe nan." Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa mai firgitarwa yana mai kallon Iyar Bayi da take durƙushe a gaban sa.
Yayin da ita kuma ta miƙe tsaye cikin sauri ƙafafunwan ta na wani irin rawa tana mai jin kamar ba zasu ɗauke ta ba, sabo da fargabar laifin da za'ace ta ai'kata da tayi matuƙar lulluɓe ta, domin kuwa ko kaɗan bata lura da ɗan da yake riƙe a hannun Sarki Barbaru ba, duk da kukan da yaron yake tsalawa kuwa tsabar tsoro.

Miƙa mata jinjirin dake tsala kuka Sarki Barbaru yayi.
Hannuwan ta da suke tsantsar rawa ta miƙa masa su idanuwan ta akan jaririn, tukun shi kuma ya Sarki Barbaru ya ɗora mata Ɗan akan hannun sa.
Take kuwa yaron yayi tsit yana zuwa hannun ta, yayin da ita kuma ta zuba masa idanuwan ta tana mai kallon sa tare da yaba kyawun hallitar sa a cikin zuciyar ta.
Lokaci guda taji yaron yayi matuƙar shiga ranta, ga kuma wata irin soyayyar sa da taji ta lulluɓe zuciya da ruhinta, tayarce har take jin sa tamkar ita ta haife sa.

Sosai ta shagala da kallon sa tana mai É—an sakin murmushi, domin kuwa ganin kyakkyawan yaron ya sanya ta manta ko a gaban suwa take duka ma.
Yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in. "Ga sabon ÆŠa nan na kawo miki shi da kaina, shi kuma wannan jinjirin da kika gani ba kowa bane face rayuwar mu mu dukan mu kamar yadda kukaji labari, hakan yasa nazo da kaina har inda kike na baki shi, dan haka saiki kula mana da Rayuwar mu."
Muryar Sarki Barbaru ta daki dodon kunnen Iyar Bayi, wacce tai sanadin dawowa hayyacin ta daga duniyar kallon jinjirin data tafi tana mai faɗin. "Tabbaci tare da alƙawari gare ni zuwa ga kai ya shugabana, babu wani abu da zai faru da wannan yaron, zan kula da shi tamkar yacce na saba kula da sauran Yaran da yardar Ubanguji Gargabilu." Ta ƙarasa maganar muryar ta a ƙasa.
Yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya juya yana mai tafiya ba tare da yace komai ba.
Binsa a baya suma mutanen sa da suka zo tare sukayi.
Yayin da su kuma bayin nan duka suka miƙe daga kwancen da suke suna masu yowa wurin da Iyar Bayi take a tsaye, hannun ta ɗauke da jinjirin kowa na kallon sa.

Murmushi Iyar Bayi ta sake yi a lokacin da Ɗan ya ƙara tsanyara kuka yana wawurar yatsun sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wayyo yunwa ma yake ji, dan haka bara naje na haɗa ruwan zafi nai masa wanka, in yaso sai asamo mun madara na basa yasha." Ta ƙarasa maganar tana mai yin gaba zuwa wurin da ɗakin ta yake.
Chapter 39 · 0% Book details