Sashe 49
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali mai martaba ya ƙaraso wurin da Gimbiya Fulani take riƙe da Asad, yana mai zube guiwoyin sa a ƙasa, yayin da sauran jama'ar dake wurin kuma suka bubbuɗa fili suna masu matsawa gefe.
Janyo Asad yayi daga jikin Gimbiya Fulani yana mai rungume sa a jikin sa, tukun daga bisani ya buÉ—e baki cikin tsantsar tashin hankali yana mai faÉ—in.
"Baba na! Baba na!! Baba na!!! Asad! Asad!! Asad!!!"
Ya faÉ—a cikin ruÉ—u da firgici yana mai girgiza sa, gaba É—ayan sa shima ya ruÉ—e ya firgice yadda kasan ba namiji ba, namijin ma kuma Sarki.
Amma sai dai Asad ko motsi baiyi ba, sai ma wata irin sandarewa da jikin sa yake sakeyi tamkar gawa, domin kuwa su kansu banda sunga zuciyar sa na bugawa da babu abun da zai hana suce ya mutu, sai dai kuma ga zuciyar tasa nan tana bugu da sauri da sauri kowa na gani, kasancewar babu kaya a jikin sa sai boxer kaÉ—ai da yayi ragowa, domin kuwa duka sauran kayan Gimbiya Fulani ce ta cire masa su.
Cicciɓar sa mai martaba yayi yana mai miƙewa tsaye da shi, kana ya mannasa a ƙirjin sa yana mai masa wata irin runguma, tukun ya juya baya cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, yana mai fucewa daga cikin falon gaba ɗaya.
Direct yayi part É—in sa da shi yana mai zuwa ya kwantar da shi a kan tamfatse-tsen gadon sa na al'farma.
Baifi mintina biyar ya É—auka da shigowar sa É—akin ba, sai ga Babban lilkitan su da yake duba su sun shigo cikin bedroom É—in, tare da su Galadima da Waziri da kuma duk sauran Æ´an uwan mai martaba manyan maza.
"Yawwa likita matso-matso ka gaggauta dan Allah kayi sauri ka duba sa, bana son na rasa rayuwar ÆŠana."
Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗa cikin tsantsar ruɗu, yana mai ƙarasawa wurin da Doctor'n yake ya kamo hannun sa.
Bai sakar masa hannun nasa ba har sai da ya kawosa gaban gadon da yarima Asad yake yashe akansa, tukun ya cika masa hannun yana mai komawa ɗayan ɓarin ya riƙo tafin hannun Asad ɗaya yana murza sa.
Yayin da shi kuma doctor nan ya buÉ—e box É—in sa cikin sauri, kana ya fara zaro abubuwan gwaje-gwaje yana mai fara yin abun da ya kamata yayi.
Su kuwa su Galadima da sauran jama'ar gaba ɗayan su jugum-jugum sukai suna kallon Asad da yake kwance sheme akan gado yadda kasan gawa, zuciyoyin su cike da al'hinin wannan abu da ya faru lokaci guda, kana ko wanne daga cikin su da akwai abun da yake saƙawa a cikin zuciyar sa.
Sai da likitan ya É—auki kimanin mintina arba'in yana faman bincikar yaron.
Kana daga bisani ya miƙe tsaye yana mai sharce gumin dake akan goshin sa, idanuwan sa akan fuskar mai martaba da shima yake kallon sa yana gumin, duk da sanyin A'C'n dake ratsa cikin ɗakin, amma hakan bai hana doctor'n haɗa zufa ba kamar yacce bata hana mai martana yin zufar fa shima.
"Ya ake ciki ne doctor? Mene yake damun Asad É—ina?
Shin dokin yay masa illa ne?"
Mai Martaba ya watsowa likitan tambayoyi a jere a kuma tsantsar ruÉ—e duk a lokaci É—aya.
Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa a wurin da yake yana mai yin gyaran murya, tukun daga bisani ya buÉ—e baki cikin sanyi yana mai faÉ—in.
"Ina ganin wannan abun bazai yuwu anan cikin gida ba, dole sai mun dangana da Asibiti, sabo da acan ne muke da kayan aiki tare da kayan gwaje-gwaje waÆ´an da zasu taimaka mana wurin gano abun da ke damun sa, sabo da ni dai a yanzu gaba É—aya ban fahimci komai ba dan gane da ciwon nasa, abu É—aya kawai dana sani shine yana rayuwa har yanzu a doron duniya, but kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, insha Allah hakan ba wata matsala bace Babba."
Ya ƙarasa maganar cikin sanyi.
Gaba ɗayan su suma shiru sukayi babu wanda aka iya samu ya furta komai, domin kuwa ba ƙaramun sanyi jikin su yayi ba duka.
Sun ɗauki tsawon minti na biyar a haka, tukun can mai martaba ya miƙe a wani irin zabure yana mai sake ɗaukar Asad, kana ya juya ya kama hanyar waje cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, ba tare da yace musu komai ba.
Hakan da suka ganine ya sanya suma gaba É—ayan su mara masa baya har likitan, suna masu fucewa daga cikin É—akin.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa cikin tamfatsetsen private hospital ɗin da yayi bala'in gajiya hurin haɗuwa, domin kuwa tsayawa faɗar kyawun asibitin shi kansa ɓata lokaci ne, amma sai dai kallo ɗaya mutum zai masa ya fahimci cewa ba wurin zuwan ko wane irin mutum bane ba, domin kuwa cikin masu kuɗin ma sai waƴan da suka amasa sunan su na masu kuɗi, wayan da futa ƙasar waje ma ba tai musu huya.
Cikin tsantsar hanzari mai martana dake riƙe da Yarima Asad har lokacin a jikin sa ya furo daga cikin motar da wani Bafade ya buɗe masa ita.
Ba tare da ya tsaya É—ora sa akan gadon marasa lafiyan da wasu nurses suka kawo wurin ba ya huce gaba rungume da abun sa, ganin hakan da doctor'n yayi ne ya sanya sa bin bayan sa cikin sauri shima.
Ko da aka zo shiga da Asad da ya zamto tamkar gawa ɗakin da za'ayi masa gwa-gwajen, dagewa mai martaba yayi yace sai ya shiga shima, amma likitan yay ta basa haƙuri yana mai basa tabbacin zai tashi insha Allah, har ya samu ya shawo kansa ya haƙura da shigar, ta sanadin bakin da ƴan uwan sa suka sanya akan yayi haƙurin.
Tukun ya juya yana mai zuwa ya zauna akan kujerar da take a bakin ƙofar ɗakin, tare da ɗaga kansa sama ya lumshe idanuwan sa, yana mai jin zuciyar sa na tsantsar tafasa da ƙuna.
Yayin da su kuma likitocin suka shige cikin É—akin dukan su, domin su fara ai'watar da abun da ya kamata suyi.
Acan cikin masarauta kuwa, ɓangaren Gimbiya Fulani, gaba ɗaya mutanen da suke a cikin falon jugum-jugum sukayi a lokacin da Mai Martaba ya fuce da Yarima Asad, yayin da Gimbiya Fulani kuma take wani irin kuka tana mai yiwa ɗan nata addu'oi, domin kuwa ba ƙaramun firgita tayi ba da halin da tagan sa a ciki, barin ma kuma da taji wannan azababben zafin da yake futa daga cikin jikin sa.
Shima Babban yaya gefe ya koma ya zauna yana mai aikin rusar kuka, domin kuwa shi duk a tinanin sa ƙanin nasa ya riga da ya mutu.
Suna cikin wannan halin sai ga Jakadiya nan ta afko cikin falon a matuƙar ruɗe, tana mai yowa wurin da suke.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yau nayi mummunan ji, naji labarin da ya hargitsa ƙwa-ƙwalwa ta, shin ina ma shi shelelen yake ne yanzu?" Jakadiya ta faɗi haka a hargitse, hannun ta dafe da kanta.
Shiru gaba ɗaya mutanen dake wurin sukayi ba tare da wani ya tanka mata ba, jin hakan da tayi ne ya sanya ta sake buɗe baki cikin muryar ta da take tsantsar rawa, alamun kuka na shirin ƙwace mata tace.
"Dan Allah kuyi mun magana mana, ku faÉ—umun inda Shalelen Mai Martaba yake tun kafin zuciyata tai bundiga."
"Kiyi haƙuri Jakadiya, Mai Martaba ya ɗauke sa sun tafi asibiti ance."
Ɗaya daga cikin matan da suke zaune a wurin jugum-jugum ta faɗa, tana mai dafa kafaɗar Jakadiya da tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskar ta.
Acan Asibiti kuwa sai da har likitocin suka ɗauki tsawon awa ɗaya suna binciken abun da ke damun Asad, amma basu gano komai ba da zasu iya cewa shi yayi sanadin sa-sa sumar, domin kuwa ko ƙirjin nasa da akace doki yabi takai su ba suga wani abun da ya same saba kwata-kwata, wato dai normal ƙirjin nasa yake kamar na kowa, sai dai kuma zuwa yanzu sun samu numfashin sa na futa dai-dai, ta sanadin oxygen da suka sanya masa, kana kuma bugun zuciyar tasa shima ya koma ya saitu kamar yacce yake a baya, sai dai kuma zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu a kan na baya, sai ma sake ƙaruwa da yake yi fiye da da.
Jiki a tsantsar saɓule Doctor Muhammad ya juya yana mai kama hanyar futa daga cikin room ɗin.
Yayin da sauran Nurses É—in kuma suka samu wuri suna masu zama akan kujeru, kamar yacce tsarin Asibitin yake, wato su da kansu suke jinyar patiant É—in su ba wai ahalin mutum bane zasu zauna masa, sai dai kuma idan mutum ya takura akan shi zai zauna suna barin sa, tun da dai su baza a fasa basu kuÉ—in su ba cas, kamar yacce kowa ke bayarwa.
Doctor Muhammad na tura kai waje Mai Martaba da yake zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera da take abakin ƙofa anyi-anyi ya shiga office amma yaƙi, ya miƙe tsaye zumbur yana mai faɗin.
"Ya jikin nasa doctor, ina fatan dai yaro na yaki sauƙi yanzu ko?"
Ya watso masa tambayoyin a jera, sannan kuma a matuƙar ruɗe.
"Kayi haƙuri mu ƙarasa zuwa cikin office ranka ya daɗe."
Cewar Doctor Muhammad yana mai ɗan durƙusawa ya rage tsayin sa a gaban Mai Martaba, kamar yacce ya saba a koda yaushe.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya rumtse idanuwan sa yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa, tukun daga bisani ya buÉ—e su akan fuskar doctor ba tare a yace komai ba.
Ganin hakan da Doctor Muhammad yayi ne ya sanya sa yin gaba yana mai faÉ—in.
"Bismillah'n ku to."
Gaba ɗayan su miƙewa sukayi suna masu bin bayan sa, ko wanne a cikin su zuciyar sa cike da son jin abun da ke faruwa, yayin da wasu daga cikin su kuma suke murna da jin daɗi, tare da fatan Allah yasa mutuwa yaron yayi, idan kuma bai ba zaiyi, wato magautan su kenan, munafukai masu fuska biyu, su kuwa masoyan su cike suke da fargabar jin abun da Doctor zai ce.