← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 79

Sashe 47

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta waigo ɓarin da suke tawowa, sabo da jin sautin takun tafiyar su da tayi.
Washe baki tayi tun kafun su ƙaraso wurin, tukun daga bisani ta laɓɓan ta tana mai faɗin.
"A'a Æ´an samarin Mai Martaba kuce an futo shiryawar kenan."
Ta ƙarasa maganar tana mai riƙe hannun Al'amin a lokacin da suka ƙarao wurin.

"Ina yini Jakadiya."
Yarima Asad da Al'amin suka haÉ—a baki wurin faÉ—i suna masu sakin murmushi.

"Lafiya ƙalau shalelen Mai Martaba."
Jakadiya ta faɗa tana mai shafa kan Yarima Asad, idanuwan ta ƙur akan sa.
Yayinda su kuma suka juya cikin sauri suna masu shirin shigewa cikin É—akin.

Da sauri Jakadiya ta buÉ—e bakin ta tana mai faÉ—in.
"Am nace ba..."

Waigowa Yarima Asad da Al'amin suka yi a tare suna kallon ta, tare da jiran jin abun da zatace É—in.
Hakan da ta ganine ya sanya ta sake washe baki tana mai faÉ—in.
"Idan kun shirya kun gama sanya kayan sai kuzo nan, ga wula da rawani na amsar muku, yau ni da kaina zan sanya muku su Ƴan gaban goshin Mai Martaba."
Ta ƙarashe maganar da washe baki tana mai yi musu nuni da wular.

Taɓe baki Yarima Asad yayi ba tare da yace komai ba, yana mai juyawa ya shige cikin ɗakin, domin kuwa shi ason samun sa yafi so mai Martaba ya sanya masa hular da rawani da kansa, kamar yacce yake sama sa su ako da yaushe.
Yayinda shi kuma Al'amin ya amsawa Jakadiya da "tom", tukun ya juya yana mai shigewa cikin É—akin shima.

Murmushi Jakadiya tayi tana mai ɗan cije leɓen ta na ƙasa, tukun daga bisani ta koma jikin kujerar da take akai tana mai kishingiɗa.

A ɓangaren su Yarima Asad kuwa suna shiga cikin ɗakin direct ya huce cikin bedroom ɗin Mai Martaba.

Baiyi ko minti biyar da shigar tasa ba sai gashi nan ya futo daga shi sai farar sabuwar singilet tare da sabon farin boxer ajikin sa, yayinda hannuwan sa kuma suke rungume da kayan su waÆ´an da zasu sanya yanzu, kasancewar da ya shiga cikin baiga Mai Martaba ba sai dai motsin ruwa da ya jiyo a bathroom É—in sa, shiyasa ya futo musu da kayan nan domin su shirya.

Kan haɗaɗɗiyar doguwar kujerar da take a cikin fallon ya ƙarasa yana mai ɗora kayan a kan ta, tukun ya juya ɓarin da Al'amin yake zaune a kan ƴar ƙaramar kujera yana mai faɗin.
"Wallahi idan na gama shiryawa ko kallon ka bazan ba, ballan tana na jiraka, tunda naga wuri ka nema kazauna ma."
Ya faɗi maganar ƙasa-ƙasa yana mai juyawa ya fara ware kayan nasa.

"To masifaffe ai sauƙin ta ma nima nasan wurin inka tafin."
Cewar Al'amin yana mai tashi daga kan kujerar da yake ya fara zame kayan jikin sa shima.
Yayinda shi kuma Asad ya cigaba da zura kayan sa ba tare da ya sake cewa komai ba.

Blue ɗin shadda getzner ce da taji uban aiki irin na sarakai a jikin ta mai matuƙar tsada tana walwali, ɗinkin riga da wando tare da malum-malum suka sanya su a jikin su.

Sosai sukayi bala'in kyau acikin kayan, musamman ma Asad shi da ya kasance farar fata.

Wasu sababbin fararen takalma na fata suka sanya ƙafafun su a cikin su, tukun shi Asad ya ƙara ɗaukar farar alkyabbar da take a jiye a gefen sa yana mai ɗora ta akan kayan jikin sa.
Yayin da shi kuma Al'amin yabar iya babbar rigar jikin sa kawai.

"Ɗebo kayan ka muje ka a jiye, daga nan sai mu ƙara sa wani turaren."
Yarima Asad ya faÉ—a yana mai nufar bedroom É—in Mai Martaba, da niyyar yaje ya sake feso turare, duk da wanda ya fesa a jikin kayan kafun ya futo da su kuwa.

Sun ɗauki tsayin mitina biyar zuwa shida a cikin ɗakin, tukun daga bisani sai gasu nan sun futo suna ta faman buga uban ƙamshi mai tsananin daɗi da sanyi.

Shafa kai Yarima Asad yayi da tafin hannun sa yana mai sakin guntun tsaki ba tare da yace komai ba, hakan da Al'amin ya ganine ya sanya sa buÉ—e baki yana mai faÉ—in.

"Mene ne kuma ya faru yanzu?"

"Mtswwww! Da yanzu Abba ne zaisa mun rawani na, amma waccan Jadiyar ta É—auke."
Ya faÉ—a murya acunkushe yana mai fucewa daga cikin É—akin.

Binsa shima Al'amin yayi ba tare da yace komai ba.

Suna futowa daga cikin ɗakin Jakadiya tayi saurin miƙewa daga kishingiɗen da take a kan kujera tana mai faɗin.
"Kai Masha Allah ƴan samarin mai martaba, a gaskiya kunyi matuƙar yin kyau, dan haka ku maza ku matso nasa muku rawani kafun a fara hawa baku."
Ta ƙarasa maganar baki a washe tana mai ɗauko hular ɗaya ta ɗora ta a kan al'amin daya ƙaraso gaban ta.
Sanya masa hular da aka riga aka gama naÉ—a rawanin a jikin ta tayi ta zauna das akan sa, tukun ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in.
"Masha Allah É—an saurayi ya futo, dan haka matsa a sawa É—an Uwanka shima."
Ta ƙarasa maganar tana mai ɗauko ta Asad ɗin idanuwan ta ƙur akan sa.

Kallon ta shima Asad ya tsaya yi ido cikin ido daga wurin da yake ba tare da ya motsa ba.
Hakan da ta ganine ya sanya ta buÉ—e baki cikin rawar murya tana mai faÉ—in.

"Ya dai shalelen Mai Martaba, ko kuwa ka fasa yin hawan ne naga kaƙi ka matso, bayan kasan ƙila yanzu an farama."
Ta ƙarasa maganar tana mai sakin wani irin murmushi, wanda za'a iya kiran sa da na yaƙe.
Yayinda shi kuma Asad ya sauke wani ɗan gajeren numfashi yana mai janye idanuwan sa daga kanta, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai matsawa kusa da ita, sabo da jin furucin nata, kuma yana gudun kar a fara hawan babu shi.

"Yawwa ko kaifa Autan Mai Martaba."

Jakadiya ta faɗa tana mai fara ɗora masa hular a kan sa idanuwan ta ƙur a kan fuskar sa.

Da ƙarfi Yarima Asad ya rumtse idanuwan sa, jijiyoyin kansa na futowa raɗa-raɗa a kan goshin sa, sabo da wani irin mahaukacin nauyi da yaji kan nasa yayi lokacin da Jakadiya ta ɗora masa hular, tukun daga bisani kuma ƙafafuwan sa suka fara wata irin kar-karwa suna rawa.

Da sauri Jakadiya ta miƙe tsaye tana mai ƙara cusa hular da take haɗe da rawani cikin kansa idanuwan ta ƙur a kan fuskar sa, tukun ta buɗe baki tana mai faɗin.
"Kuyi maza-maza ku tafi ga sautin bindiga can na jiyo, da alamun Mai Martaba ya futa ta ƙofar baya ne muna nan bamu sani ba."
Jakadiya ta faɗa da matuƙar sauri tana mai girgiza Asad.
Yayinda shi kuma ya taune leɓen sa na ƙasa da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani ya fara bud'e idanuwansa da yake jin sun masa wani irin mahaukacin nauyi a hankali ahankali, harya buɗe su duka a kan fuskar Jakadiya.

Da matuƙar sauri Jakadiya ta sake sa tana mai juyawa baya ta fara tafiya, bakin ta na furta kalmar.
"Kuyi maza maza ku tafi kar ayi babu ku mana."

Ba dan komai ta tafin ba kuwa sai dan yadda taga idanuwan Yarima Asad sun koma Jajahur yarce kasan garwashin huta, a lokacin da ya buÉ—e sun.

Cigaba da tsayuwa Asad yayi a wurin yana mai jin jikin sa na wani rin É—aukar zafi, yarce kasan ana zuba masa garwashi.

Ganin da Al'amin yayi Asad bai motsa daga wurin da yake ba ne ya sanya sa buÉ—e baki yana mai faÉ—in.
"Muyi sauri mutafi mana aboki, sabo da kaji fa Jakadiya tace amma fara."
Ya ƙarasa maganar yana mai jan hannun Yarima Asad yayi gaba ba tare da ya tsaya kallon sa ba, ballantana ya lura da sauyawar da yanayin sa yayi.

Jin hakan da Yarima Asad yayi ne da kuma yadda yaji Al'amin na ƙoƙarin jansa ne, yasan ya sa fara ɗaga ƙafafuwan sa da yake jin suna karkarwa yabi bayan sa cikin tsantsar azaba, domin kuwa shi kansa bazai so ace hawan nan da yayi mahaukacin tamasa ba ya huce sa.

Tafe suke gumi na yanko masa ta tsakar kansa yana tsiyayowa ta cikin hular dake sanye a kansa zuwa kan fuskar sa sosai, amma a haka ya cigaba da bin bayan Al'amin da yake jan hannun sa ba tare da ya tsaya ba, duk da yadda kuwa yake jin jikin sa na sake É—aukar zafi tamkar ana hura ta a cikin sa.

Basu tsaya ba har sai da sukaje gaban Dokunan su da suke riƙe a hannun wasu mutum biyu daga cikin ƴan sulke, tukun Al'amin ya saki hannun Yarima Asad yana mai faɗin.
"Ga naka nan ka hau, nima bari na hau nawa."
Ya ƙarasa maganar yana mai matsawa kusa da danƙareren baƙin dokin da yake riƙe a hannun wani mutumi, ba tare da ya kalli fuskar Asad ba har lokacin.
Yayinda shi kuma Asad ya sake rumtse idanuwan sa jikin sa na fara karkarwa, tukun daga bisani ya buɗe su a hankali, kana ya fara ɗaga ƙafafuwan sa da yake jin suna ƙara yin nauyi, yana mai matsawa zuwa gaban wani farin danƙareren doki da yaji uban ado ta ko ina a jikin sa, da alama dai shine Dokin nasa.
Sosai dokin yake da matuƙar girma, ga kuma fatar jikin sa da takasance fara ƙal, babu ko ɗigon baƙi a jikin ta sai faman shigning da take tana ɗaukar ido, alamun ba ƙaramun hutu dokin yake ciki ba kenan.
Chapter 47 · 0% Book details