← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 79

Sashe 25

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun ɗauki kimanin mintina talatin zuwa arba'in suna tattaunawa, tukun daga ƙarshe suka yiwa juna sallama su mai girma Gwamna suna masu miƙewa suka doshi hanyar waje.

*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULÆŠE.*

Cikin sauri Gimbiya Haddiyal ta ƙarasa cikin ɗakin ta, direct ta doshi ƙofar ɗakin da kayan tsafin ta na gado suke aciki, tana mai zuwa ta buɗesa, tukun ta mayar da sandar nan tata awurin data ɗauke ta tana mai ɗaukar farin ƙyallan da ake rufe ta da shi ta lulluɓe ta, sannan ta sake juyawa cikin sayri tana mai fucewa daga cikin ɗakin, kana ta doshi hanyar da zata sadata da fallo dan taje ta sanya atatso madara.

"Barka da futowa yake kyakkyawar Gimbiya." Wata matashiyar Baiwa da take share cikin tafkeken falon ta faɗa tana mai ajiye tsintsiyar hannun ta ƙasa tare da zube giuwoyin ta aƙasa alokacin da Gimbiya Haddiya ta futo daga cikin ɗaki.

"Am, kiyi maza yanzu-yanzu ki tashi ki tafi wurin majiaɗin shanu, ki sanar da shi cewar ina buƙatar sabuwar madara cikin ƙwarya ukku kafun nan da giftawar da ƙiƙa talatin gaba." Gimbiya Haddiyal ta faɗa tana mai kallon Baiwar dake durƙushe agaban ta ba tare data amsa gaisuwar da tai mata ba.
Yayin da ita kuma baiwar ta miƙe da sauri tana mai nufar hanyar da zata sadata da waje.
Tukun ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya tana mai komawa cikin É—akin ta.

Tana shiga ta huce gaban wata wadrobe ta ƙarfe mai azabar kyau ruwan zuma da take ajikin bangon ɗakin.
Hannu tasa ta buɗe ta tana mai zaro wani farin towel mai ɗauke da lallausan gashi jikin sa, tukun ta maida murfin ta rufe sa, kana ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da bathroom ɗin da yake acikin bedroom ɗin nata ba tare da ta tsaya cire kayan jikin ta ba, gaba ɗaya tana komai ne cikin sauri duk da yarce ranta yake amatuƙar cunkushe da baƙin ciki.

*****
Misalin ƙarfe shaɗaya da rabi na safe motocin su Babban Yaya suka shigo cikin Masarautar Fulɗe, kasancewar gudu sukayi bana wasa ba, domin kuwa tafiyar kusan awa biyar ce har da rabi, amma su sukayi ta acikin awa biyu da ƴan mintinu.

Tunda suka shigo garin Yarima Asad yake aikin yamutsa fuska tare da wurga kallon ƙasƙanci acikin sa, domin kuwa gaba ɗaya ji yay bazai taɓa iya rayuwa acikin wannan bagidajen garin ba, wanda ya kasance babu wasu wayayyun mutane acikin sa.
Banda aikin yamutsa fuska da taɓe baki babu abun da yake yi, yayin da shi kuma Al'amin yake ta sakin zuba yana mai faɗin. "Agaskiya garin nan yayi, domin kuwa ba ƙaramar ni'ima Allah ya wadata su da ita ba, kaga fa yarce suke da wata irin daddaɗar iska, ga ruwaye da suke ta faman gudu, tabbas mutum na garin nan dole ma fatar jikin sa tai ta ƙare kyau akoda yaushe, domin kuwa daga gani su basu san mece rana bama." Ya faɗa idanuwan sa akan hanyar da suke wucewa yana mai kallon ta ta cikin glass.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwa yana mai jin tamkar ya mammake Al'amin dan takaicin furucin sa, sabo da shi kwata kwata baiga wani abu da ya birge sa acikin garin ba, sai zallar haushi da ya basa ma, domin kuwa ya fuskanci hatta da mutanen cikin sa kusan dukan su duk ƙauyawa ne.
Aƙarshe ma da ya gaji da jin surutun Al'amin earpiece ya zaro acikin aljihun sa yana mai sanya ta cikin kunnuwan sa ya doɗe su da ita.
Ahaka har suka ƙarasa cikin Masarautar Fulɗe wacce take cike da abubuwan burgewa da kyan gani acikin ta, sai dai ta fannin Asad kuma har yanzu bai ga abun da ya burge saba acikin Masarautar.

Tun daga bakin ƙofa wasu dogarawa suka tarbe su cikin tsantsar girmamawa, sanye suke da kayan fulani, hannuwan su kuma riƙe da sandina, daga nan kuma suka yi musu jagora zuwa fadar Lamiɗon Masarautar Fulɗe.
Kallo ɗaya Yarima Asad yayiwa mutanen nan da suka zo tarbar su, daga nan kuma ya ɗauke idanuwan sa akan su ba tare da ya sake kallon wani daga cikin suba, dan ko gaba ɗaya ƙyanƙyamin su ma yaji shi, sabo da suturar dake sanye ajikin su, wacce yayiwa laƙabi da ta mahaukata ayanzu daga kallo ɗaya da yayi musu acikin zuciyar sa.

Dasauri Babban Yayan su Gimbiya Haddiyal wanda ake kira da Jauron masarautar FulÉ—e yazo ya tarbe su cikin tsantsar mutun tawa, tukun daga nan ya shige gaba suna masu dosar cikin fada da take É—auke da kayan ado na fulani tako ina gadan gadan.

Sosai Masarautar tayi matuƙar birge Al'amin, tayarce har yake jin ina ma ace sai sun kwana biyu tukun zasu barta, yayin da shi kuma Yarima Asad yaji gaba ɗaya wurin ya gundure sa, kana ko kaɗan bai ga wani abun burgewa ba acikin sa sai zallar ƙauyanci da yake gani.

Iso akayi musu har gaban Lamiɗo da yake zaune akan wata irin kujerar Al'farma ta ƙarfe mai azabar kyau, sanye yake da kaya irin na fulani, amma na sarauta tare da Alkyabba wacce ta kasance ta fulani ɗauke ajikin sa, sai farin rawani da yake ɗaure akansa, farine tas da shi yarce kasan ataɓasa jini ya ɓullo, kamar yacce duka ƴaƴan sa suka kasance suma.
Yayin da gefe da gefen sa kuna da gaban sa mutanen fada suka kasance zaune awurin.

Zama su Babban yaya sukayi akan shimfiÉ—ar kafet É—in da take agaban su suna masu kwasar gaisuwa awurin LamiÉ—o.
Cikin mutun taka da far'a ya amsa musu fuskar sa ɗauke da tsantsar annuri, sannan daga ƙarshe suka sake gabatar da abun da yake tafe da su.

Gyaran murya mai martaba LamiÉ—o yayi, tukun ya furta munji komai kamar yacce kuka faÉ—a arubuce, dan haka yanzu kai Jauro ka tashi ka kai su wurin cin abinci, inyaso idan sun gama sun huta sai su dawo ayi ciniki." Ya faÉ—a yana mai kallon Babban É—an sa wanda zai kai kusan shekaru arba'in aduniya.
Amsa masa yayi da tom shima, tukun ya miƙe suma su Babban Yaya da su Yarima Asad da yake ta faman yamutsa har lokacin suka take masa baya.

Suna futa waje Jauron Masarautar Fulɗe ya hangi ƙanin sa mai suna Habu, mai kimanin shekaru talatin aduniya, wato sa'an su Yarima Asad dai.
Ƙwalla masa kira yayi da ƙarfi, cikin sauri Habu ya ƙaraso wurin da suke yana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa baƙi." Fuskar sa ɗauke da murmushi yana mai kallon su Yarima Asad.
Idan ka gansa kai bazaka taɓacewa ɗan nan cikin Masarautar bane, domin kuwa sosai yake awaye shima, kasancewa yayi karatun boko har matakin degree shi.

"Yawwa."
Babban yaya da Al'amin suka faɗa cikin far'ah, yayin da shi kuma Yarima Asad ya faɗa ƙasa ƙasa ba tare da ya kalle sa ba.

"Yawwa Habu ga abokai nan kaja su ku tafi cikin lambu, sannan ka tabbatar an samar musu abinci da madara yanzu yanzu"

"Tom shikenan Hamma." Habu ya faɗa yana mai sake miƙa musu hannu suka sake yin musabaha, tukun yace ku tawo muje ko.

Jerawa sukai suka tafi suna tafiya suna hira da shi da Al'amin cikin raha, yarce kasan sun san juna dama. Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi shiru yana sauraran su kawai ba tare da yace komai ba, ahaka har suka ƙarasa cikin wani ni'imtaccen lamubu mai ɗauke da korayen ciyayi tare da sanyi acikin sa.
Direct sukayi kan wata shimfiÉ—ar Al'farma ta fata da take É—auke da tum-tum akan ta daga can nesa.
Tunda suka shigo masarautar Fulɗe Yarima Asad baiga wurin da ya burge saba sai wannan kaɗai, hakan yasa ya jujjuya yana mai kai idanuwan sa ko wane sashe dake cikin wurin, tukun ya maida idanuwan sa kan shimfiɗar da suka ƙarasa gaban ta yana mai cire takalman dake sanye aƙafar sa ya hau ya zauna, kamar yacce Al'amin da suke uwar hira da Habu suka zauna.
KishingiÉ—a yayi jikin tum-tum É—in dake gaban sa yana mai lumshe idanuwan sa ba tare da yace komai ba.
Kallon sa Habu yayi fuskar sa ɗauke da murmushi, tukun daga bisani ya buɗe bakin sa yana mai faɗin. "Shin wai kai ɗin Bebe ne amma ko?" Ya ƙarasa maganar cikin raha.

Wara idanuwa Yarima Asad yayi akansa yana mai sakar masa murmushin yaƙe, still ba tare da yace komai ba, yayin da shi kuma Al'amin ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bebe ko kuma miskili ba."
Ya faÉ—a yana mai hullawa Yarima Asad da ya zaro wayar sa yana shafawa harara.
Yayin da shi kuma Habu ya saki dariya yana mai faÉ—in. "Any way, ga dai abinci nan yanzu kuci tukun sai acigaba da hirar."
Ya faÉ—a yana mai fara buÉ—e haÉ—aÉ—É—un kwanukan da suke jere akan tray.
Farfesun naman ciki ne dana kaji da suka gaji da haɗuwa suna ta faman tashin turiri da ƙamshi acikin kwanika biyu da suke daga farko, sai kuma wani haɗaɗɗen kwandon kaba da yake ɗauke da Tufa, Inibi, Ayaba, Lemo, acikin sa da matuƙar yawa.

BubbuÉ—e kwanukan duka yayi yaga babu madara kwata- kwata awurin.
Hakan ne yasa sa miƙewa yana mai kallon su tare da faɗin. "So sorry dan Allah fa, ashe wai basu kawo madaraba, but please ku ɗan jirani yanzu bara naje naji dalilin da yasa ba akawo ba." Ya faɗa yana mai miƙewa ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya jin ta bakin su ba.

Bai tsaya ako ina ba sai acikin É—akin Haddiyal da take zaune agaban madubi tana mutsikka mai afatar ta.
Da sauri ta juyo bayan ta tana mai kai idanuwan ta bakin ƙofa sabo da motsin da taji.

"Mai ya hana kisa akaiwa baƙi madara amatsayin ki na shugabar shanu, bayan kuma nasan an sanar miki da zuwan su tun kafin yau?" Ya faɗa yana mai kafeta da idanuwan sa.

"Kayi hakuri dan Allah Hamma, wallahi na sha'afa ne, amma nasa atatso ta tun ɗazu, kuma yanzu haka nasan an gama ma ƙila ma sun shigo da ita, dan haka bara na sanya kaya sai naje nasa akai madarar." Ta faɗa tana mai miƙewa ta doshi gaban wadrobe ɗin ta.
Chapter 25 · 0% Book details