Sashe 62
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa tayi b'arin da farin ruwan nan wanda yake zagaye da su yake tana mai kai idanuwan ta kansa, tukun daga bisani kuma ta janye su daga kan ruwan tana mai girgiza kai.
Kana ta sake juyawa tana mai kai idanuwan ta kan dakarun nana nata da suke a tsaye cirko-cirko tamkar bishiyu.
Sannan ta bud'e baki cikin wata iriyar murya wacce take d'auke da tsantsar b'acin rai a cikin ta tana mai cewa.
"Ku d'auke shi ku tafi da shi, a masa azaba mafi muni daga cikin azabobi, a masa azaba irin azabar da baku tab'a yiwa wani makamacin ta ba a duniya, kana idan an tabbatar da jikin sa ya nuna azo asanar mun kafun asake sa."
Ta k'arasa maganar tana mai sakin wani irin huci, tukun daga bisani ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwan ta cikin sauri, ta doshi hanyar da suka biyo alokacin da suke zuwa wurin.
Yayin da su kuma way'an nan dakarun sukayi kan Bir gadan-gadan gaba d'ayan su.
Tamkar zasu kacaccala sa suka kai hannuwan su jikin sa, ko wanne daga cikin su yana mai damk'ar wani sassa daga cikin sassan jikin sa.
Kana daga bisani sauran suka sake sa suna masu barwa mutum d'aya shi.
Shi kuwa wanda aka barwan da hannu d'aya yayi wani irin d'aga Bir sama, tukun ya fara d'aga k'afafuwan sa yana mai nufar bakin ruwan nan da shi, yayin da suma sauran y'an uwan nasa suka rufa masa baya, gaba d'ayan su suma ransu a b'ace da ganin kalar rashin kunyar da yayiwa uwar d'akin nasu.
*K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*
Rayuwa taja, a sannu-sannu kwanaki suka dinga zuwa suna wucewa, kana su koma satika, sannan satika suka koma watanni, yayin da watanni kuma suka dinga ninkuwa ahaka har suka zamto shekaru.
Abubuwa da yawa sun faru acikin shekarun da suka gaba ta, cikin su kuwa har da haihuwar y'a macen da Gimbiya kab'el ta sake yi, yarinya taci sunan mahaifiyar Lamid'o Gimbiya Unau, amma suna kiran ta da Innahuro, ma'ana uwar masu gida a hausance kenan.
Shekaru kusan goma shahud'u ke a tsakanin Gimbiya Haddiya da Inna huro, amma idan mutum yaga yadda Innahuro da take da shekaru biyar zuwa shida yanzu aduniya take yiwa Gimbiya Haddiyal sai ya d'auka baifi tsirayyar shekara d'aya ke tsakanin su ba, domin kuwa ko d'an kunne aka siyawa Haddiya to itama Innahuro sai tace asiya mata shi, wato ta mayar da ita tamkar kishiyar ta dai.
Yayin da ita kuma Haddiyal take matuk'ar son k'anwar tata tamkar yadda sauran y'an gidan suke son ta, duk da dai ita Innahuro a kwaita da shegen surutu, ba kamar haddiyal ba da surutu bai dameta ba kwata-kwata.
A yanzu haka Gimbiya Haddiyal tana da shekaru Ashirin ne a duniya.
Sosai tayi girma ta k'ara yin kyau tamkar ita tayi kanta, domin kuwa babu ta inda Allah ya rage ta aduka hallitar jikin nata.
Tini ta kammalla karatun secondry d'in ta a cikin wannan makarantar data farata tun farko, yayin da akai-akai da Lamid'o ya kaita k'asar waje ta cigaba da karatun ta amma gaba d'aya yace bai san da wannan batun ba, wanda tayi na bayan ma shima ya barta ne kawai dan an masa dole, amma bawai dan ransa yaso ba, hakan ne yasa yanzu take zaune a gida babu wurin da take zuwa, sai wurin tsuntsayen ta da tini suka dade da zamtowa abokan rayuwar ta, domin kuwa tsanin son da take yi musu ne ma da Lamid'o ya gani yasan ya ya nad'ata a matsayin sarauniyar su acikin duka masarautar, kana ya bata jagorancin kula da duk shanun da ake d'ibar madara a jikin su acikin masarautar, ta yadda muddin ana buk'atar madara sai an biyo ta wurin ta kafun asame ta.
A b'angaren mafarkin ta da tayi na busar sarewa kuwa, haka kullum ta cigaba da yin sa a wancan lokacin, sai dai kuma har ta d'auki tsayin watanni shida tana mafarkin bata tab'a ganin mai busar ba, sai dai sautin ta kawai da take ji, kafin daga baya kuma mutumin dake busar ya bayyana acikin mafarkin nata, sai dai kuma ako da yaushe bata ganin fuskar sa, kawai dai tana ganin sa ne ya juya mata bayan jikin wani k'aton dutse da yake tsayuwa, sanye da shiga irin ta Sarakai a jikin sa, haka zataje ta samu wuri daga bayan sa ta zauna tana mai kallon sa, busar na ratsa ko wane lungu da sak'o na ilahirin jikin ta.
A haka har aka shafe sama da shekaru biyu tana wannan mafarkin aduk daran duniya.
Kwatsam rana d'aya sai taga mutumin dake busar ya sauya kalar shigar dake sanye a jikin sa ko da yaushe, amai-makon ta gansa da shigar sarauta, sai ta gansa sanye da d'an guntun bakin wando'n da tsayin sa bai huce iyakar guiwar sa ba ajikin sa, sai wani d'an kyalle kuma da yake yafe ajikin sa amai-makon riga, kana kuma babu abun busar rik'e a hannun sa tamkar yadda ta saba ganin sa ako da yaushe yana yin busar.
Hakan ne yasa ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin sanyi tana mai nufar wurin da yake.
Tsaye tayi cak a bayan sa a lokacin da ta matsa dab da shi, tukun daga bisani ta bud'e baki cikin zazzak'ar muryar ta tana mai fad'in.
"Yau kimanin tsawon shekaru kenan kullum kana zuwar mun da shigar Sarakai jikin ka, kana sautin daddad'ar busar ka na ratsa gangar jiki da jijiyoyin jiki na, ta yadda har take kwanciya acikin b'argo na.
Amma kuma yau sai na ganka da sabon tufa ba waccan ba, kana kuma babu abun busar dake sanyaya mun zuciya ta.
Shin ko zan iya sanin abun da ya hanaka zuwar mun da sarewa ta a yau, bayan kuma ka riga da kasabar mun da jin daddad'an sautin ta a cikin kunnuwa na?"
Ta k'arasa maganar cikin sanyi, tana mai gyara tsayuwar ta a wurin da take.
Amaimakon taji sautin muryar sa yana bata amsar tambayar da tayi masa, sai kawai taga ya fara juyowa gare ta ahankali-ahankali, har ya juyo duka b'arin da take yana mai fuskantar ta tare da jifan ta da wani irin sassanyan murmushin sa, abun da tunda take da shi bai tab'a yi ba kenan, wato juyowa gare ta balle har taga kamannin sa sai yau.
Hakan ne kuwa ya sanya ta tayi suma tsaye a wurin da take tana mai binsa sa da dara-daran idanuwanta, kamar yadda taga shima yana kallon ta da nasa idanuwan, tare da sakar mata murmushi.
Kyakkywa ne ajin farko, danko atak'aice tana iya cewa tunda take aduniya bata tab'a ganin mai kyan sa ba.
Sun d'auki tsayin mintina goma ahaka suna kallon-kallon ba tare da wani daga cikin su yayi magana ba, sai kawai murmushin da suke ai'kawa junan su da shi.
Kana daga bisani kuma Gimbiya Haddiyal ta fara d'aga k'afafuwan ta daga wurin da take tana mai sake nufar sa cikin tsantsar farin ciki.
Tana dab da zuwa gare sa ne kawai ta farka daga baccin da take.
Tun daga wannan ranar kuma take mafarkin sa acikin yanayi daban-daban.
Yayin da zuciyar ta kuma ta kamu da wata irin mahaukaciyar k'aunar sa, ta yadda har sai da ko wane mutum na cikin gidan nasu yasan da labarin sa, kana kuma ta fara k'ok'arin ganin ta gano wurin da yake zaune ta hanyar tsafin ta, amma gaba d'aya abun ya cutura.
Hakan ne yasa tasan ya d'aya daga cikin bayin gidan nasu data aminta da shi sosai ya fara yi mata bincike akan mutumin mafarkin nata, domin kuwa tun da suke had'uwa da shi tun lokacin data fara zama budurwa har kawo yau bai tab'a furta mata wata kalma ba sai dai kawai murmushi, yayin da ita kuma take zama tayi masa zuba acikin mafarkin nata.
A lokacin da labarin mutumin mafarkin Gimbiya Haddiyal ya isa kunnen Lamid'o sosai hankalin sa yayi matuk'ar tashi, domin kuwa duk atinanin sa Aljanu ne suka shafi d'iyar tasa, hakan ne yasa ya fara nemar mata magun-guna gadan-gadan, kana kuma ta ko wacce hanya, amma kuma abanza, domin ko amaimakon abu yayi sauk'i sai haukacewa da kullum Gimbiya Haddiyal take k'arayi akan mutumin cikin mafarkin nata, wanda tai masa lak'abi da Gid'ad'on ta, wato Masoyin ta a harshen hausa kenan.
Yanzu haka tsaye take a gaban had'ad'd'iyar wardrobe d'in k'arfen da take manne ajikin bangon d'akin ta, tana mai zaro kayan baccin ta, kasancewar tini dare ya fara nisa, domin kuwa har k'arfe goma ta gota.
Cikin sauri ta fara ware had'ad'd'iyar jar doguwa rigar baccin da take rik'e a hannun ta, kafin daga bisani kuma ta zurata a jikin ta.
Sosai rigar tayi mata mahaukacin kyau, abun ka da kyakkywar dama, kana ta d'auki hular ta tana mai sanya ta akan ta, bayan ta cusa mayawaicin gashin ta cikin ta.
Tukun ta rufe murfin wadrobe d'in tana mai juyawa ta haye kan luntsumemen gadon k'arfen ta na alfarma, mai kalar ruwan zuma, tamkar yadda gaba d'aya sauran kayan d'akin suka kasace kalar.
Da sauri ta lumshe idanuwan ta bayan ta janyo lallausan eskimon dake shimfid'e a gadon jikin ta.
Tukun ta lumshe idanuwan ta tana mai fatan bacci ya d'auke ta a yanzu-yanzu, domin tayi arba da Gid'ad'on ta farin cikin ranta.
Ai kuwa batai ko minti goma da kwanciyar tata ba wani nanauyan bacci mai matuk'ar dad'i ya sure ta.
Cikin kyakkywan lambum da suka saba had'uwa da shi ta samu kanta.
Sanye take da shigar su ta fulani da tayi matuk'ar amsar jikin, kana ta tai mata bala'in kyau tamkar koda yaushe.
Tsaye ta hange sa jikin w...................âœ
08038135929
UMAR Faruq D
*BAK'AR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 25*
Wata k'atuwar bishiyar gwanda ya juya baya tamkar koda yaushe.
Sanye yake da d'an guntun farin wando na yadi kamar yadda ta saba ganin sa ako da yaushe.
Cikin tsantsar shauk'in da ta tsinci kanta a ciki ta cigaba da dosar wurin da yake tsaye, fuskar ta d'auke da tsantsar far'a.
Jin ta take tamkar wacce aka yiwa bishara da gidan Aljanna aduk lokacin da zata ganta-gata gasa.
Tana masa wani irin so irin wanda ita kanta ba zata iya misaltasa ba, tana mai jin sa tamkar yadda take jin rayuwar ta.