Sashe 55
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Tuba nake ranki ya dade, tuba nake ki mun ai'kin gafara ya shugaba ta."
Baiwar nan ta faɗa jikin ta na tsantsar kar-karwa, a lokacin da wannan badakaren ya durƙusar da ita a gaban Gimbiya Tasmir, Yarinyar da a haife ta haife ta.
Shiru Gimbiya Tasmir tayi ba tare da tace komai ba, sai kawai fitinannun idanuwan ta da ta ɗora su akan fuskar baiwar nan tana mai jifan ta da wani irin kallon ƙasƙan ci, tukun daga bisani ta janye su daga kanta tana mai kai su wurin farin ruwan nan da yake kwance a cikin tafkeken rami.
Kana daga bisani ta ɗaga yatsar hannun ta manuniya, tana mai nuna ruwan nan da ita ba tare da tace komai ba, sannan ta sauke hannun nata ƙasa tana mai sake mayar da idanuwan ta ta lumshe su.
Yayin da shi kuma wannan badakaran ya sake cafkar hannun bawair nan da matuƙar ƙarfi, tukun ya cigaba da janta a cikin ƙasa yana mai nufar bakin ruwan nan da ita.
Suna ƙarasawa wurin ya ya saki hannun baiwar yana mai damƙar gashin kanta ta da matuƙar ƙarfi, kana ya fara danna kanta a cikin ruwan, sai ya nutsa sa tas a ciki tukun yake zaro sa ya sake mayarwa, a haka har sai da yayi kimanin sau ukku, tukun daga bisani ya futar da ita yana mai yin cilli da ita gefe.
Da sauri ta kife a ƙasa tana mai fara tafiya da rarrafe, ta doshi hanyar da zata ɓatar da ita daga wurin tana sakin wani irin tari, yayin da idanuwan ta kuma suka kaɗa sukai jajajir tamkar gauta, alamun ba ƙaramar wuya taci ba kenan, a tsomen da aka mata a cikin ruwan.
A ɓangaren Bayi kuwa sosai Bir yayi matuƙar girma, kana ya fara zama saurayi, domin kuwa a yanzu yana da kimanin shekaru goma shabiyar ne a duniya.
Kyakkyawa ne lamba ɗaya, dan ko ataƙaice ma shine ya zamto mafi kyawun mutum a cikin duka Bayin dake a cikin Baƙar Masarauta.
Har kawo yau yana nan da maitar kwari da gwafar sa, domin kuwa akan ta baiƙi ya yini cir da yunwa ba, dan kuwa mafi akasarin lokuta ma idan ya futa da ita baya dawowa cin abinci, har sai Iyar Bayi ta bisa ta tattago sa.
A yanzu haka bashi da wani buri wanda ya huce na haɗuwa da Gimbiya Tasmir domin ya ganta, sabo da tun da yake a cikin Masarautar har yau Allah baisa sun taɓa cin karo da itaba a hanya, kai asalima ganin sa da ita duka sai ya irgu, shima kuma yana faruwa ne aduk lokacin da ake wani taron biki a cikin Baƙar Masarauta, amma bayan wannan bai taɓa cin karo da ita ba, sai dai yaji labarin cewar yau ta huce ta wuri kaza a wurin su Mauzum, haka kuma zai ga sunzo jikin su na tsantsar kar-karwa, kana a kullum sai yaji bayi na labarin kwarjinin ta da rashin tausayin ta, wannan shine kawai dalilin daya sa yaji yana matuƙar son ya haɗu da ita wataran shima, domin ya gwada tsayuwa a gaban ta yaga mai zata masa, ko kuma shima zata masa kwarjini kamar yacce mutane suke faɗin tana musu, kasancewar sa mutun mara tsoro da shakkar kowa, domin kuwa babu wanda bai sansa da wannan halin ba a cikin bayi, kai harma da wasu daga cikin dakarun dake zaune a Baƙar Masarauta, sai dai kuma babu yadda zasuyi da shi, sabo da koda an dake sa ba ya fasa yin abun da yake yi, wato yiwa dakarun rashin kunya, gashi kuma gaba ɗayan su Sarki Barbaru ya shimfiɗa musu sharuɗa akan sa tare da gargaɗi, kana suma dukan su sun san tarihin samuwar sa a cikin masarautar.
A kusan kullum sai ya ritsa Iyar Bayi yana mai tambayar ta su waye mahaifan sa, amma sai dai kuma aduk lokacin da ya taso mata da maganar sai yaga gaba ɗayan ta-ta rude ta fuce daga hayyacin ta, a ƙarshe ma sai dai ta-tashi ta basa wurin, ko kuma tai ta roƙon sa akan kar ya ƙara yi mata wanna batun, muddin ba gajiya yayi da ganin ta a duniya ba.
To da zarar fa tace masa hakan sai ya haƙura ya tashi yay gaba, amma bawai dan ransa yaso ba, kuma hakan baya hanawa washe gari ya sake taran ta da maganar ma.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*
Tun bayan haihuwar Gimbiya Haddiyal Gimbiya Kaɓel mahaifiyar ta bata sake wata haihuwar ba, yayin da ita kuma Gimbiya Mairamu ta sake yin wata haihuwar amma ɗa namiji, wato har yanzu dai Gimbiya Haddiyal ce kawai ƴa mace a gidan.
Yayin da take da Shekaru bakwai dai-dai a duniya yanzu kenan.
Sosai take da wani irin kyawu mai matuƙar ɗaukar hankali tare kwarjini da Izza.
Ko kaÉ—an magana bata dame ta, kamar yacce hayani kuma ke takura mata, domin kuwa hatta da yayyin ta maza idan suka haÉ—u wuri É—aya suna hira takura take yi sosai, wannan dalilin ne yasan ya akoda yaushe take ware kanta ta tafi can lambun da jinsin tsun-tsayen masarautar FulÉ—e suke rayuwa a cikin sa.
Yayin da wurin kuma yafi mata daɗi sama da kowane wuri dake a cikin gidan nasu, hatta da ɗakin ta kuwa, domin kuwa ba ƙaramun birge ta tsun-tsayen suke ba, haka ako da yaushe zata tafi cikin su tun tana da shekara huɗu aduniya ta zaune tana watsa musu gero, kana kuma tai ta kawo labarai tana basu ba tare da tana da tabbacin suna jin abun da take faɗen ba, domin kuwa muddin kana son jin sautin muryar ta to da zarar kazo wurin tsun-tsayen har dai ta kasance itama a wurin, to zakaji hirarar ta har ka gaji, yayin da acikin gida kuma take tamkar kurma a koda yaushe.
Ada idan taje wurin tsun-tsayen tun daga nesa suna jin motsin ta gaba ɗayan su suke tashi su gudu, amma a haka zata ƙarasa zuwa mazaunin ta wanda ta saba zama akai, ta zauna ɗauke da ƙwaryar hatsi a hannun ta.
Kana ta fara ciko tafin hannun ta tana wats musu shi.
Ai kuwa haka gaba É—aya zakaga sun sauko ahankali-ahankali suna tsintar geron, yayin da ita kuma zata tai kallon su tana sakin mirmushi, tare da lumshe idanuwa.
Haka kullum take yi musu ba safiya ba rana, tun tsuntsayen suna guduwa idan tazo wurin, har ya zamto anzo lokacin da suka dena gudun ta gaba É—aya, wato sun gane ba mai cutarwa bace gare su ita É—in, domin kuwa gaba É—aya dawowa sukai suna hangen ta zasu yo wurin da take a guje, kamar yadda dama can kaji da agwagi suka yi saurin sabawa da ita, kuma suke tawowa wurin ta a duk lokacin da taje wurin su, domin kuwa tsun-tsayen da suke a cikin masarautar FulÉ—e sun kasance kaloli daban-daban ne, haka kuma babu wata kalar tsuntsuwa da kusan za'ace basu da ita.
A duk lokacin da tsuntsayen nan zasuga ta shigo wurin, to haka zasu tawo aguje suna masu yowa kanta ko wanne na sakin nasa kalar kukan, yayin da ita kuma zatai ta ɓaɓɓaka dariya tana mai shafa su tare da shawagi a cikin wurin, cikin tsantsar farin ciki da annashuwa, tukun a ƙarshe kuma ta koma kan shimfiɗar ta-ta zauna, kana suma duka su biyo ta suna masu sauka a gefen shimfiɗar, sannan ta fara ciko tafukan hannyen ta da gero tana watsa musu, tana yi tana basu labarai tare da dariya cikin tsantsar farin ciki.
Yayin da shi kuma malam buɗa mana littafi ya zamto abu na farko data fiso sama da komai arayuwar ta idan aka cire ahalin ta, domin kuwa shi yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka zamto mahaɗi na tsafin da yake ɗauke a jikin ta, wato muddin tana buƙatar yin wani abun, to da zarar ta buga sandar tsafin ta, ko kuma taje wurin da ciyayi suke ta buge su, zakaga sun taso da yawan su masu tsanin kyau suna hawa kan tafukan hannyen ta, kana kuma idan har tana son su nuna mata wani abun, to da zarar ta faɗa musu buƙar ta zasu tashi su kaita har wurin da abun yake, sannan kuma zata iya cutar da mutum da su muddin taso yin hakan, sai dai kuma ita ɗin ta kasance babu ruwan ta ko kaɗan, domin kuwa ko bayin gidan su ba ƙaramun jin daɗin ta suke yi ba, kana kuma bata damu da sai an mata rakiya ba dan zataje wani wurin, asalima ita tafison tayi tafiyar ta ita kaɗai, sabo da a ganin ta duk ƙarin hayaniya ne dogarawan zasu sanya mata ba wai tsaro zasu bata ba.
Wannan dalilin ne ya sanya ko lambu idan zata tafi take tafiyar ta ita kaÉ—ai ba tare da ta bari sun biyo ta ba.
Babu yadda ba ayi ba da Lamiɗo akan ya bari akai ta Makarantar Boko dake ac ikin Jahar Wasai ta kwana, wacce aka yita domin ƴaƴan sarakai da kuma ƴaƴan attajirai kawai, amma gaba ɗaya ya yaƙi amicewa, a cewar sa ba zai taɓa barin ta tayi nisa da shi ba amatsayin ta na ɗiyar sa ƴa mace ƙwalli ɗaya ƙwal da yake da ita a duniya, domin kuwa shi afannin sa har yau baiga wani amfani da karatun bokon yake da shi ba, suma kuma su Buba ya yadda an kaisu ne sabo da babu yadda zaiyi, gwamnati ce tace dole sai ya bayar, amma banda haka da ba zai bada su ba.