Sashe 60
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sake mirginar da kai Bir yayi gefe, yana mai yin narai-narai da idanuwan sa, tukun daga bisani ya É—aga tafukan hannayen sa duka biyu yana mai haÉ—e su wuri É—aya, idanuwan sa akan fuskar Iyar Bayi.
Kana ya buɗe baki cikin muryar roƙo yana mai faɗin.
"Ki temake ni Iya ta, ina mai tabbatar miki da babu wani abun da zai faru dake.
To waima wane ne zai sani bayan daga ni sai ke a cikin wurin nan, ballantana har akai rahoton da kike gudun akai."
Girgiza kai Iyar Bayi tayi tana mai rumtse idanuwan ta, tukun daga bisani ta buÉ—e su akan sa tana mai kallon sa, kana ta buÉ—e baki cikin muryar raÉ—a tana mai faÉ—in.
"Amma me yasa kake son dole sai ka sani ne Jarumi?
Shin me ma sanin zai amfana maka, bayan kasan ba zaka taɓa ganin su ba, asalima ni ɗin kaina ban san komai ba dan gane da su Jarumi."
Girgiza kai shima Bir yayi yana mai ɗan taune leɓen sa na kasa, tukun daga bisani shima ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, kamar yadda suke yi ako da yaushe idan suna irin wannan batun yana mai cewa.
"Kawai ina son jin tushe nane nima, badan komai ba kuwa sai dai in tabbatar da ni ɗin ƙas-ƙantaccen Bawa ne kamar yadda mutane suka sha faɗamun hakan.
Ina son ki faÉ—a mun da gaske ne tsinto ni akayi Iya ta."
Bir ya ƙarasa maganar yana mai sauke tafukan hannayen sa daga haɗen da suka ya miƙa su yana mai riƙo na Iyar Bayi a cikin nasa, ya damƙe su wuri ɗaya, yana mai kallon ta da jajayen idanuwan sa.
Yayin da Iyar Bayi kuma ta furzar da wata zazzafar iska daga cikin bakin ta, tana mai jin gaban ta na duka tara-tara, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin matuƙar sanyi, tana mai faɗin.
"Kayi haƙuri Jarumi, haƙiƙa a yanzu bakina bazai taɓa iya furta abun da kunnuwan ka suke son jiba, sai dai kuma ina son kasani akwai lokacin dana tanada domin na faɗa maka, duk da dai zanyi hakan ne ba ason raina ba, dan haka na maka al'ƙwarin muddin lokacin nan yayi to babu abun da zai hana ni baka tsakuren tarihin ka, sai dai kuma ina son kasani, sannan kuma kasa aranka, wannan ranar da bakina zai furta maka labarin da kake son ji, itace kuma zata zamto rana ta-ta ƙarshe a gidan duniya."
Ta ƙarasa maganar tana mai zame hannayen ta daga cikin na Bir, kana daga bisani ta miƙe tsaye a hankali tana mai fucewa daga cikin ɗakin, ba tare da ta tsaya jin ta bakin sa ba.
Shi kuwa Bir gaba ɗayan sa mutuwar zaune yayi a wurin da yake, sosai yake matuƙar gigicewa aduk lokacin da yaji Iya tayi irin wannan furucin, kana kuma yake jin yana matuƙar ƙara son jin labarin nasa, domin yaji dalilin da ya sanya iyar bayi take tsoron faɗa masan, duk da dai shima ɗin yana matuƙar firgita idan ya tuna da magan-ganun ta, sa yake cewa zata mutu akan tarihin nasa.
Ya ɗauki tsawon mitina goma shabiyar zaune a wurin yana mai faman tinane-tinane, tukun daga bisani da yaga abun bazai yi masa ba ya miƙe tsaye cikin sanyi yana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Dogo ne sosai lamba ɗaya, yana da ƙiba dai-dai misali tare da murɗaɗɗen jiki irin wanda kowa ke so ya kasance da shi.
Sanye yake da ɗan gajeran baƙin wandon sa babu riga a jikin sa kamar yadda suka kasance ako da yaushe, duk tsanin sanyi da damina kuwa.
Gaba ɗaya ƙirjin sa cike yake da uwar gargasa mai matuƙar laushi da duhu, amma ahaka yake tafiyar sa baya jin kunyar kowa ya gansa, kasancewar hakan al'adar masarautar tasu ta koyar da su, kuma haka ko wane Bawa yake kasancewa a cikin ta.
Kai tsaye ya doshi hanyar da aka faÉ—a masa Gimbiya Tasmir nabi ta ita idan zataje wurin hutun ta.
Tafe yake cikin sanyin da kalaman Iyar Bayi suka haifar masa, kansa durƙushe a ƙasa.
Yayin da a cikin zuciyar sa kuma yake fatan haÉ—uwa da Gimbiya Tasmir a futowar tasa ta yanzu.
Ai'kuwa ba zato ba tsammani ya jiyo sautin gudun mutane rada-da-da-da ta ko ina, hakan ne yasa sa É—ago kansa cikin sauri domin yaga abun da ke faruwa.
Bayi ne suke gudu iyakar ƙarfin su, kama daga mazan su har mata suna masu neman hurin ɓuya.
Cikin tsantsar mamaki ya fara waige-waige yana bin su da kallo, domin kuwa shi bai taɓa ganin ana irin wannan gudun ba tun da yake acikin masarautar sai yau.
Tsaye yayi a wuri ɗaya yana waige-waige, sabo da yadda yaga cikin ƴan sakanni duka bayin dake a wurin sun ɓace-ɓat.
Yana shirin janye idanuwan sa daga kan hanyar da yake kallo ya hangi tawowar mace sanye da wata irin blue'n doguwa riga mai azabar kyau a jikin ta, wacce take manne da adon duwatsu a jikin ta tana jan ƙasa, yayin da wasu irin danƙara-danƙaran mutane waƴan da ba yau ya fara ganin su ba acikin masarautar, amma sai da ya saba ganin su ne aduk lokacin da ake yin hukunci akan wani, dan shima yasha shiga hannun su, suna biye da ita hannuwan su riƙe da mugayen bulalai tare da makaman su.
Da sauri ya janye kansa daga wurin da yaga suna tawowa, yana mai yin tamkar bai san da zuwan su ba, ya cigaba da ɗaga ƙafafuwan sa yana tafiyar sa, yayin da a ƙasan zuciyar kuma yake jin wani irin tsoro sama-sama, ga kuma ƙirjin sa dake ɗan bugawa, sabo da sanin muguntar dakarun nan da yayi, sai dai kuma neman fitina irin tasa gaba ɗaya ta sanya ya kasa guduwar shima.
Acan kuwa ɓangaren su Gimbiya Tasmir cikin takun ta na tsantsar Izza, wanda shi kaɗai ke nuni da ko ita ɗin wace-ce, ta cigaba da takowa wurin dakarun ta na biya da ita.
Sosai tayi matuƙar kyau cikin shigar dake sanye a jikin ta, abunka da mai kyau ɗin dama, shiya sanya duk irin sitirar da tasa a jikin sa sai tayi mata kyau.
Kanta É—aga asama tana kallon hanya fuskar nan tata babu alamun annuri tattare da ita ta cigaba da dumfarar wurin nan.
Lokaci ɗaya ta tsaya cak a wurin da take adai-dai lokacin da suka ƙaraso saitin wurin da Bir yake, sabo da motsin sautin tafiyar mutum da taji acikin kunnuwan ta.
A ɓangaren Bir kuwa shima ya lura da isowar su wurin da yake ɗin, hakan ne yasa sa durƙusawa ƙasa jikin wata bishiya da take a gefen sa, yana mai ɗaukar wani icce ya fara kakkarya sa ba tare da ya ɗago ya kalli wurin da suke ba.
Tsayuwa Gimbiya Tasmir ta cigaba dayi a wurin tana mai jiran taji ƙarar sautin gudu a kunnuwan ta, amma sai dai har ta ɗauki tsawon daƙiƙa ukku a wurin bataji ba, kai asalima sai daina jiyo sautin tafiyar tayi, sai kawai ƙarar karya iccina, wanda hakan kuma ya tabbatar mata da cewar akwai mutum a wurin.
Take kuwa ranta yayi matuƙar ɓaci lokaci guda, domin kuwa tunda take futowa ba'a taɓa yi mata haka ba sai yau.
Hakan yasa cikin tsantsar ɓacin ran da ya lulluɓe ta lokaci guda ta fara juyar da kanta ɓarin da take jiyo motsin ahankali.
Karaf kuwa idanuwan su suka haÉ—u da na juna, adai-dai lokacin da ya É—ago shima domin yaga ko sun kauce.
A hankali ya janye idanuwan nasa daga cikin nata yana mai yin tamkar bai ganta ba, ya cigaba da karya sandar dake riƙe a hannun sa.
Yayin da ita kuma ta kafesa da nata idanuwan da suka fara sauya launi tsabar ɓacin rai, tana mai mamaki tare da tinanin abun da ya taka da har ya hanasa guduwa a lokacin da ta tawo, bayan kuma ta tabbatar da yaga lokacin da sauran ƴan uwan sa bayi ke gudu, kana kuma duk wannan laifin da yayi bai ishesa ba sai da ya ƙara sanya idanuwan sa a cikin nata, abun da ba ataɓa samun wani yayi ba bayan ahalin ta a duniya.
Cikin tsantsar ɓacin rai ta ɗago hannun ta da yake wata irin kar-karwa tsabar ɓacin rai, tana mai nuna sa daga wurin da take, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta a hankali cikin muryar ta da kafun ajita ake yarawa, tana mai faɗin.
"Waye shi É—in, mai kuma ya taka da har zai ganni ya zauna?"
Ta ƙarasa maganar da sakin huci ba tare da ta janye yatsar tata daga nuna san da take yi ba, yayin da shi ɗin ma yake lura da duk abun da take yi ta ƙasan ido da yake kallon ta, kana ta sake buɗe baki cikin fushi tana mai faɗin.
"Ina buÆ™atar ganin sa durÆ™ushe a gabana kafun nan da giftawar daÆ™iÆ™a daya kacal".................âœ
*BAK'AR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 24*
Ta k'arasa maganar cikin zafi tana mai sakin huci, tukun ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai dosar wurin da kujerar nan take cikin tsantsar zafin rai.
Yayin da su kuma dakarun nan sukayi kan Bir aguje ransu atsantsar b'ace da abun da sukaga yayiwa uwar d'akin nasu, domin kuwa zasu iya cewa tun da suke da ita basu tab'a ganin ranar da ranta ya b'aci ba irin na yau.
Ko kad'an Bir bai lura da isowar su ba, sai dai kawai hannun sa da yaji an funcika da wani irin k'arfi tamkar za'a cizge sa, ta yadda har sai da ya kife ak'asa wanwar kansa na gwaruwa da wani dutse dake a kusa da shi.
Yayin da shi kuma wannan badakaran da ya funcike sa yana mai fara jansa a k'asan wurin da yake d'auke da duwar-watsu da matuk'ar k'arfi.
Rumtse idanuwa Bir yayi da k'arfi yana mai jin yadda kansa ke had'uwa da duwar-watsun kan hanyar.
Suna k'arasawa gaban kurar da Gimbya Tasmir take a k'ark'ashin bishiyar nan, ya durk'usa yana mai sannu hannu ya damk'o huyan Bir da matuk'ar k'arfi, tukun daga bisani ya d'agosa yana mai durk'usar da shi a kan guiwoyin sa.