← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 79

Sashe 40

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Shigar mai martaba part É—in yayi dai -dai da lokacin da Hadima Larai ta dawo hannun ta É—auke da jinjirin.
Da sauri ta zube guiwoyin ta a ƙasa tana mai faɗin. "Barka da futowa Al..." "Bani, bani shi, taso ki bani Baba na na gansa." Mai martaba ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi, yana mai miƙa mata hannu ba tare da ya tsaya amsa gaisuwar ta ba.
Hakan da taji ne ya sanya ta tashi fuskar ta ɗauke da murmushi, sabo da jin da tai har mai martaba ya basa suna, wato sunan mahaifin sa kenan, tana mai miƙa masa Ɗan a hannu.

"Masha Allah! Alhmdulillahi Alhamdulillah!." Ya faɗa cikin tsantsar farin ciki yana mai kai hannun sa zuwa kan fuskar Ɗan dako wanka ba'a yi masa ba, ya shafi kumatun sa, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Babban Yaya na biyu kenan ko, wato ita Fulani kawai masu kama da ita take haifowa tsabar san kai kenan." Ya faɗi maganar fuskar ɗauke da murmushi yadda kasan ba Sarki ba, domin kuwa shi kansa bazai iya musalta kalar farin ciki da yake ciki ba, haka kuma yana jin bazai taɓa iya ɓoye saba, koda yana cikin fada ne kuwa.
Kallo ɗaya yayiwa jinjirin yaji wata irin soyayyar sa ta lulluɓe duka zuciya da ruhin sa, tayarce har yake jin tamkar bai taɓa haihuwa ba sai akansa, kai ataƙaice dai kallon farko da yayi ga yaron yaji ya shiga ransa fiye duk sauran yaran nasa, har Babban Yaya da yake Ɗan farko namiji gare sa kuwa.

"Yanzu ina ita Fulanin take ne?" Mai martaba ya faɗa yana mai miƙawa Hadima Larai jinjirin, sabo da jin da yay ana tada sallah a cikin masallacin Masarauta.

"Tana cikin ɗaki lafiya ƙalau." Gimbiya Larai ta faɗa tana karɓar Yaron.

"Tom shikenan ki mata sannu yanzu in kin shiga, ni na tafi masallaci bayan an idar da Sallah zan dawo, domin kuwa ban gaji da kallon wannan babbar kyautar da Ubangji yayi mun ita ba."
Ya ƙarasa maganar yana mai juyawa yayi gaba.
Yayin da ita kuma Hadima Larai ta ƙame a wurin ɗaya tana mai bin bayan mai martaba da kallo, sabo da yadda taji ya tsaya a gaban ta yana dogon surutu, abun da bata taɓa ji ance yayi ba ballan tana kuma ta gani, domin kuwa iyakar su da shi gaisuwa ce kawai ke haɗasu, amma sai gashi yau ya tsaya gaban ta yana zuba da nuna farin ciki, yadda kasan a yanzu aka fara masa haihuwa.

"Tabbas ko a kwai badaƙala a cikin gidan nan, muddin mai martaba zai cigaba da rawar ƙafa akan yaron nan ba ƙarama bama kuwa, dan sai dai kawai muyi fatan Allah ya kare." Ta faɗa tana mai yin gaba ta doshi ɗakin Fulani, domin taje ta gyara wurin da a kayi haihuwar da kuma shi kansa jinjirin.

Acan ɓangaren Gimbiya Huwaila kuwa tana shirin fucewa daga cikin falon ta sukaci karo da Jakadiya, ita kuma tana danno kanta domin ta shigo, har lokacin takalman ta riƙe suke a hannun ta, da alamun bata sanya su ba a haka ta tawo tun daga can ɗakin ta har nan.

Da sauri Jakadiya ta miƙa hannu tana mai riƙo hannun Gimbiya Huwaila, sabo da ganin da tayi tana shirin fucewa kamar bata ganta ba.
Janta Jakadiya tayi cikin sauri suna masu nufar É—akin ta, ba tare da tace mata komai ba.

Suna shiga cikin bedroom ɗin Jakadiya ta saki hannun Gimbiya Huwaila tana mai juyawa ta rufe ƙofar bedroom ɗin, tukun ta sake juyowa ga Gimbiya Huwaila data ɗora tafin hannun ta akan goshin ta tana mai sakin numfarfashi, tare da rumtse idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan fuskar Jakadiya, lokaci ɗaya duka sun canza launi sunyi jajahur yacce kasan gauta.

"Shin meye hakan ya faru Jakadiya? Tayaya ma za'a ce Fulani ta haihu, haihuwar ma kuma ÆŠa namiji, ÆŠa namijin ma kuma mai rai, tayaya hakan ya faru ne Jakadiya?" Gimbiya Huwaila ta faÉ—a a wani irin haukace tana mai zagaya cikin É—akin nata.

"Nima abun da ya ɗaure mun kai kenan, ya kuma rikita ni Uwar Sarkin Gob..." "Dakata haka Jakadiya!" Gimbiya Huwaila ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai ɗagawa Jakadiya hannu, tare da rumtse idanuwna ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai faɗin. "Akan me zaki cigaba da kirana da wannan sunan kina samun rai, bayan kuma kin san duk ƙarya ne hakan kuma, bayan kuma keda kunnuwan ki kinji kalar sautin da tamabari ya futar yanzu, bayan kuma wanda ya futar shekaru goma da suka huce baya." Ta ƙarasa maganar da sakin numfarfashi.
Yayin da ita kuma Jakadiya ta buɗe baki tana mai faɗin. "Karki fara faɗin haka yake Shugabata, kar kiyi kuskuren cewa zaki sare tun yanzu, domin kuwa haihuwar Yara biyu maza bashi ke nufin an haifo Sarki cikin su ba, dan kuwa sanin kanki ne hawa karagar Sarki sai wanda ya cancanta ko cikin Ƴaƴan Sarkin, sai kuma ya a jiye abubuwa da yawa, tukun yake da damar hawan ta, kinga kenan tunda har akwai waƴan ka'idojin, to ko ba mutuwa kina iya zamtowa Uwar Sarki muddin kin haifo Ɗa namiji kema." Jakadiya ta faɗa tana kallon Gimbiya Huwaila.
Yayin da ita kuma tayi shiru tana mai lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta buÉ—e su tana mai girgiza kanta, kana ta sake buÉ—e baki tana mai faÉ—in. "To duk naji wannan kuma na amun ta da hakan Jakadiya, amma kafun nan, wai taya ma akai hakan ta faru, taya ya za'ace Yaron yazo da rai, bayan kuma kince mun kinyi duk yadda nace kiyi tun a jiyan?"

"Ta sanadin ikon Allah mana, domin kuwa cikin duka abubuwan da kika sani babu wanda banyi sa ba, sai dai kuma ko idan ita ɗin ce bata kwanta akan gadon ba, sabo da dama lokacin da naje ɗakin nata na same ta ne zaune agefen kujera kamar yacce na faɗa miki tun jiya, kuma ma ba wannan ba, shin wai kin manta ne haka kikece sai an baɗa mata maganin har kimanin sau ukku arana, sannan kuma ta kwanta aƙar-ƙashin layoyin tukun Ɗan zai mace?" Jakadiya ta faɗa tana kallon ta, yayin da ita kuma Gimbiya Huwaila ta dafe goshin ta da tafin hannun ta tana mai faɗin."Kashhhh!"
Tukun ta tafi da baya da baya tana mai zuwa ta zauna yaraf akan gado, tare da cije leɓen ta na ƙasa da ƙarfi.

"Ina da wata shawara, wacce nake ganin ko ita kawai akabi zamu cimma burin mu." Jajadiya ta faÉ—a daga inda take a tsaye, idanuwan ta akan fuskar Gimbiya Huwaila.

"Mene abun tsayawa ɓata lokaci, bayan kuma kin san yana gab da ƙare mana, kawai faɗe ta kai tsaye inji ta mana, idan zatayi mai zai hana abita." Gimbiya Huwaila ta faɗa tana kallon Jakadiya.

Hmmmm! "To ai sirri ne abun shugabata." Jakadiya ta faɗa bayan ta saki wani shegen murmushi, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai matsawa kusa da Gimbiya Huwaila.
Sai da taje har gab da ita, tukun ta ranƙwafa tana mai kai bakin ta dai dai kunnen Gimbiya Huwaila da suke ɗauke da haɗaɗɗen ɗan kunnen gwal, tukun ta fara yi mata raɗa a cikin kunnen nata.
Ta ɗauki kusan mintina biyar zuwa shida tana mata raɗan, tukun daga bisani ta janye bakin ta daga kan kunnen ta tana mai miƙewa tsaye fuskar ta ɗauke da murmushi tace. "To ya kika ji?"

Shiru Gimbiya Huwaila tayi tana mai ɗan taune lowar lios ɗin ta, ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mi faɗin. "Hakan ma tabbas zai yin, amma si dai ina son mu fara yin wanda na faɗa miki, idan baiba sai mubi ita wannan hanyar ɗin." Ta ƙarasa maganar itama da sakin murmushi.

Haka dai duka haihuwar ÆŠa namijin da Fulani tayi ta girgiza gaba É—aya magautan su na cikin gidan, tare da É—imauta su, sannan kuma ko wanne ya fara É—aura É—amarar sake sabon taku, wurin ganin sun kawar da duka yaran biyu, daga Babban Yaya har shi sabon Jinjirin da aka haifa yau.
Yayin da masoyan su kuma murna da farin ciki suka cika su, har suka ransa inda zasu sa kansu, tun kafin agama idar da Sallah Asuba part ɗin Gimbiya Fulani ya fara cika da jama'a, masoya da ma maƙiya, sai dai kuma kowanne da manufar da yake zuwa da ita, su masoya domin taya ta farin ciki, yayin da su kuma maƙiya suke zuwa domin su fara ai'watar da aikin su.

_BAYAN KWANA BAKWAI_

*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA*

Tun daga bakin get ɗin gidan Bayi mutum zai fahimci yau ɗin suna wani gagarumin shagalin ne a ciki, sabo da yadda kiɗa ke tashi da matuƙar sauti tare da daɗi a ɓangaren Bayin, ga kuma manya manyan tukwane da aka ɗora akan duwar-watsu ana aikin basu huta sosai, kasancewar yau ɗin ta kasance sati ɗaya dai-dai da samuwar jinjirin nan, kuma dama a ƙa'idar Baƙar Masarauta koda Bayi ne suka haihu to ana barin su suyi shagalin suna ya junan su, a kuma cikin wurin su, hakan ne yasa tun jiya kuwa suke ai'yika, domin yau ɗin ce takasance ranar sunan sabon yaron da aka kawo musu.
Sosai suke cikin farin ciki daga mazan su har matan su, kasancewar sai a irin wannan ranar ta suna idan tazo musu ne kawai suke samu suyi nishaÉ—i, ayi dariya, a kuma yi kiÉ—a ai rawa cikin farin ciki da junan su, ba tare da an daki kowa ba a cikin su.

Acan É—akin Iyar Bayi zaune take agefen shimfiÉ—ar ta, rungume da É—an jaririn a hannun ta tana mai muts-tsika masa mai a jiki, kasancewar yanzu ta gama yi masa wanka, domin kuwa ko ruwan zafin da tai masa wankan da shi ma ba'a janye sa daga wurin ba.
Chapter 40 · 0% Book details